Ya dauka alfarma a tsakanin shi da Datti ta kare daga ranar da ya fara ja masa Allah ya isa, har kasan zuciyar shi ya dauka babu wata rana da zata sake zuwa da zaizo gaban Datti ya tsugunna da nufin neman alfarma. Sai dai wacce zuciyar? Zuciyar da take kirjinshi da ya dauka mallakin shi ce, mallakin shi da yake da iko da ita, ya santa, suka zauna na tsayin shekaru harma ya tabbatar tsayawarta dai-dai yake da tsayawar shi. Sai da zuciyar nan ta nuna masa iyakarsa lokaci daya, ta mayar da duk wata yardarshi ta koma. . .