Idan yaji ana cewa lokaci na gudu ada sai yayi ta mamaki, saboda shi sam baya ganin gudun lokaci. Musamman idan yana gida, yini daya sai ya zame mishi kamar yini biyu. Amman wannan karin zai saka baki idan ana maganar gudu na lokaci, saboda da gaske kamar idanuwan shi ya rufe a aji hudu ya bude su ya ganshi yana zana jarabawar gama sakandire ta aji shidda da ake kira da WAEC. Randa suka zana ta karshe sai yake jin abin kamar a mafarki, har Julde yaje ya dauko su bai dana jin shi kamar a mafarki yake yawo. . .