Gidan yayi mata fili, filin da ba'a iya waje take jin shi ba harma da zuciyarta. Idan ta rufe idanuwanta ta tuno lokuttan da take dariya kamar a duniya bata da wata matsala, sai taga kamar a wata rayuwar ce daban, wadda ta sha bamban da wadda take ciki yanzun. Tazarar da take tsakanin wancen lokacin da kuma yanzun tayi nisan da take ganin kamar dorata akan wasu yan shekaru yayi kadan. Saboda babu yanda za'ace farin ciki ya bace daga rayuwar dan adam lokaci daya haka. A yanayin da zuciyarta take ciki ko wani taji yayi dariya. . .
Allah y saka da alkhair Allah y jikan iyayae