Datti take kallo da yake kwance, motsin kirki ma baya son yi, yanzun saiya wuni cikin gida baj fita ba. Kamar babu wani abu daya rage masa a waje, duka duniyar shi na cikin gidan, na tare da ita yanzun da babu yaransu. Sauran gonakin su na cikin Marake akwai masu kula dasu da suke karkashin Julde, kome suke da bukata yana kawo musu. Datti ma bai nuna hakan na damun shi ba, tunda ya daina fita in ba da wani dalili mai karfi ba. Akwai hasken fitilar da suka kunna,amman tunda Julde ya dauke Nawfal kamar duk wani haske da zata kunna iya idanuwan Datti suke tsayawa. Kamar Nawfal din wani haskene da suka kwana biyu basu gani ba.
Kuma Nawfal din wata alama ce da ta tabbatar mata da kadaicin da Datti yake ciki, idan har zai ture tsanar da yake yiwa Bukar ya rungumi Datti haka, tabbas kewar ganin yaran shi a gabanshi da yake ta wuce yanda zata iya hasashe. A karo na farko yanayin shi na sakata tunanin duk yaran da suka binne, da sun rayu watakila da basuyi kadaici haka ba. Da ba zasu rasa a cikinsu ko da kwara dayane da zai zauna tare dasu ba, da basu ji kamar a filin duniya basu da kowa sai junansu ba.
Akwai wani mataki na shekaru ko rayuwa da yara suke kaiwa sai su dinga dauka babu wani abu da iyayensu suka fi bukata sama da kyautatawa, rage musu ko ma dauke musu duk wani nauyi da yake kawunansu, ci, suttura da ma duk wani abu na jin dadin rayuwa. Albarkar nan da ita sukan bi hadi da addu’o’i da suke nuna jin dadin su na wannan kyautatawar. Amman yawanci a kasan zukatansu akwai muradi na daban, akwai kewar da gudun yanda yaran nasu zasu dauki maganar in sun fito da ita yasa suke kara danneta. A karo babu adadi, zasu dauki kasancewa da yaransu na wuni daya akan wannan tarin sutturar da suka kawo suka juya a cikin wasu yan mintina, ko suka aiko da ita.
Amman yara sun kasa fahimtar wannan, rana daya bayan makwanni biyu, uku, harma hudu yayi mata kadan, taya zata tattara abinda ya faru a kwanakin nan, ta takaita shi harta sanar da Julde?
“Babu wata matsala.”
Shine amsar da takan bashi duk idan ya tambaya, saboda babu, matsalar ba irin wadda yake tunani bace ba. Kuma da yanda yake nuna akwai uzururruka a gabanshi sai ta zabi barin shi ya tafi don korar wannan uzurin da yake gabansa. Ba sai da matsala ba, wasu rabakun labari ne iyaye zasu so su baka, abinda ya faru dasu na farin ciki, abinda ya faru dasu mai muhimmanci da akasin hakan, wani abu daban wanda daga kai harsu dinma baku da alaka dashi. Babu kalar labaran da baka basu ba, suka saurara, badon basu da abinda yafi labaran naka muhimmanci ba a lokacin kuruciya, sai don soyayyarka data danne komai.
A yayin girmansu, reshen ne yake juyewa, sune suke bukatar wannan kulawar ko da bata kai rabin wadda suka bayar ba. Duk halin ko in kula da Datti yake nunawa akan Julde abin yana damun shi, yana ci masa rai fiye da yanda zai iya misaltawa. Dije tace kuskuren nasu ne, nashi kason yafi na kowa, daga ranar har zuwa yanzun akwai wani bangare na zuciyar shi da kalamanta suka zauna suke nukurkusa. Ta saka shi maimaitawa kanshi tambayoyi da dama. Akan Yelwa, a batunta da Kabiru, a zancen aurenta da Modibbo. Baya son amsa ko daya da yake samu, saboda duka suna kamanceceniya da juna, idan aka dunkule ma’anarsu zata zagaya ta dawo kan yanda komai yake laifin shi.
Amman akan Julde fa? A ina ya kuskure? A gadarar da yakeyi ta yafi karfin ya haifi mazinaci? Yafi karfin dauda irin ta zina ta rabi ahalin shi? Ko aibata iyaye tare da yaran da suka tsinci kansu cikin irin halin da yake yanzun? Shi kam yayi kuskure, Dije ta fada masa yayi kuskure, sauran iyayen yaran fa? Kuskuren sukayi suma? Ko kuwa kaddarar da yake ganin kamar katin gayyata ake bawa marar kyauce ta yi musu ziyarar gayyar sodi? Me yake faruwa? Duk da ba ilimi gare shi ba, a kasan zuciyar shi yasan wasu tambayoyin ko karen hauka ya cije shi huhun shi ba zai busama sautin shi iskar da zasu rabo kirjin shi zuwa makoshin shi har harshen shi ya furta su a matsayin sauti ba.
Saboda hakan zaiyi dai-dai da fitar dashi daga musulunci. Sai dai shin duk wannan laifin nashi bai cancanci Julde ya sake bashi hakuri ba? Ya nemi yafiyar shi tare da kokarin gyara alakarsu ba? Idan ya gaishe dashi ya dauke kai shikenan? Bai isa ya sake bashi hakuri ba, bacin rai da karyewar zuciyar daya ja masa. Ko kuma bai ga shi kadai ya rage masa bane? Duk da kullum sai zuciyar shi ta tabbatar masa da cewa duk inda Yelwa take tana da rai, babu yanda za’ayi ace baiji a jikin shi ba idan har ya rasa ta.
“Idan Yelwa ta rasu a wani wajen fa? Idan hakuri ya kamata mu ba zukatan mu a maimakon duban hanya fa? Ya zamuyi?”
Dije ta tambaye shi wani dare suna kwance, hannunta ya laluba ya damtse a cikin nashi.
“Su biyu ne dani, su kadai suka rage mun a fadin duniya kaf da zan kalla in kira nawa Dije… Babu yanda za’ayi in rasa Yelwa jikina bai bani ba, zata dawo.”
Gyara kwanciya tayi, hannun shi da ta kara dumtsewa cikin natane kawai shaidar daya samu cewar taji abinda ya fada, sai kuma yanayin numfashinta da alamar kuka takeyi. Amman batace komai ba. Har bacci ya dauketa tana barin shi da juyayin tambayarta. Shisa wata asabar din daya tashi ya kwana da zazzabi, ya sake jera hakan har talata Dije tace masa.
“Ba zan aikama Julde sako ba kuwa yazo ya daukeka zuwa asibiti?”
Kai ya girgiza mata, baya so ya furta, baya so ya fada mata yanda yake jin kamar yana gab da cike iya kwanakin da aka dibar masa zaiyi a duniya. Ya sha jin karshen duniyar yazo masa, akwai dararen daya kwanta yayi mamakin bude idanuwan shi da safe, saboda bai kwanta da sa ran zai tashi ba. Yayi rashin lafiya da tafi wannan zafi, amman yanajin wani sanyi cikin kasusuwan shi duk da zafin zazzabin da yake jikin shi. Sannan koya ya mike sai yaga garin yana jujjuya masa. Ga shi larabar daya kwanta, alhamis saiya tashi harda ciwon kai. Abinda duk yaci a yinin ranar saiya dawo. Yanayin daya daga hankalin Dije ba kadan ba.
Da yammaci likis, yayi kokarin tashi zaune, bayan ya gama jin yanda take jaddada masa Julde na zuwa juma’ar asibiti za’a kai shi ko ya amince ko bai amince ba, tunda har kayan sirace an samo tayi masa zazzabin bai sauka ba. Baiyi kokarin musa mata ba, saboda yanaji a jikin shi bama zai kai juma’ar da take kira ba, duk kuwa da tsakanin su da juma’ar awanni ne ya rage da za’a iya kirgawa da yatsun hannu, musu da ita bashi da wani amfani. Kallonta dai yakeyi, kallo cikin sigar daya dauki wasu shekaru baiyi mata irin shi ba, kallonta yakeyi yanajin kwanakin da ya rage a tsakanin su, sai yakejin son rike ko da hannunta ne, ya kara bar mata abubuwan da zata tuna shi dasu.
“Idan ba Dije ba, babu wanda zai iya zama da kai Datti.”
Ya tuna zancen Hammadi a yau, yana ganin gaskiyar da ya kasa gani a wancen lokacin. Dije, matar shi, amanar shi, uwar yaran shi. Yaran da halin shi ya raba shi dasu amman Dije tana nan tare dashi, kamar yaran ba daga jikinta suka fito ba. Dije da take shanye duk wani mugun halin shi.
“Dije…”
Ya tsinci kanshi da kiran sunata, saita dago kai ta saka idanuwanta cikin nashi
“Hamma ya sha fadamun idan bake ba babu macen da zata iya hakurin zama dani, da gaske ne, da ban gani ba, amman yanzun na sani. Ban taba miki godiya ba ko?”
Wani abu ya canza a cikin idanuwanta, ya hangi fargaba da tsoro a cikin su, amman saiya dake
“Nagode, nagode da yanda kika dinga hakuri dani duk shekarun nan, duk da halayena sun kawo mu inda muke yanzun… Idan nace ki yafe mun duk abinda nayi miki naso kaina da yawa ko?”
Hawayene cike da idanuwanta wannan Karin,
“Bana jin kinmun wani abu da na rike ki dashi a iya zaman mu, amman idan kinyi mun din, ko menene na yafe miki.”
Hawayenta ne ya zubo.
“Kaga kukana kashi-kashi Datti, bai isa ba saika kara sakani wani yau? Waye yace kamun wani abu dana rike ka? Ka daina maganganun nan kamar kana mun bankwana, kayi ciwo da yafi wannan kuma ka tashi, da wa zaka barni ma to in ka tafi? Ko dai dabara ce aure zaka kara kake son karya mun zuciya da batun mutuwa?”
Dariya yayi, dariyar daya kwana biyu baiyi ba, dariyar da sautinta bai gama karade zuciyarta har tayi dogon nazari kan ranar karshe da taji dariyar shi haka ba, muryar da ko da Datti bai yanke kauna da sake jinta ba, ita kam Dije ta dauki wannan hanyar tayi musu kutse cikin tunanin su tana girgiza duk wani bango na ruhinsu.
“Baba…”
Yelwa ta kira muryarta na rawa, idanuwanta tsaye akan shi, shima ita yake kallo. Yelwa ce, yar shi, tilon yar shi da duhu da kuma ramar da tayi bata boye kyawun fuskarta ba. Yar shi ce da yake da yakinin ko fuska aka canza mata zai ganeta. Sosai yake kallonta, atamfa ce a jikinta da wata hijabi da asalin kalarta ya kode kamar hijabin jikinta. Daga duk inda ta fito rayuwa ta tara mata gajiyar wasan cikar shekara. Karasawa tayi, yanajin sautin takunta a cikin zuciyar shi kamar tambari. Hannunta ta mika da Datti baiko yi tunani ba ya kama, ta lumshe idanuwanta, wasu siraran hawaye na zubo mata, ta bude idanuwanta akan Dije da batama san hawaye takeyi ba.
“Daada… Daada Am.”
Yelwa tayi maganar cikin karyewar murya kuma a wahalce, har lokacin hannunta na cikin na Datti. Sai da tayi kokarin zama, yanayin yanda take yin hakan da dabara, tukunna daga Dije har Datti suka sake kallonta, kallo fiye da na mamakin ganinta, kallo daya wuce canjin da fuskarta tayi, sutturar jikinta da kuma tarin tambayoyin da suke yawo a kawunan su, kallo na son gane dalilin da yasa take dabara wajen zama. Kusan a lokaci daya sakon abinda idanuwan su ya gani ya karasa har cikin kansu yana saukowa zuwa zuciyoyin su. Ciki ne a jikin Yelwa, ciki tsoho, idan Dije bata kuskure ba, yanayin yanda cikin ya dunkule waje daya ya kuma yo kasa, ko yanzun ciwon nakuda ya kama Yelwa babu wanda zaiyi mamaki, saboda ko meye a cikinta gab yake da fitowa duniya.
Babu jaka ko daya a hannunta, sai yar karamar leda mai layi layi da take sakale a tsintsiyar hannunta, har bayan zamanta kuma batayi kokarin ciro ledar ba balle ta ajiye. Numfashi dai take ta kokarin saukewa kamar zaman ma aikine. Ta kuma kara matsawa yanda zata iya dora kanta a kafadar Daada tana wani irin sauke ajiyar zuciya.
“Nayi kuskure Daada… Nayi kuskure mafi girma a rayuwata.”
Ta tsinci kanta da furtawa wasu sababbin hawayen na saukar mata. Sai dai an rasa wanda zai fara korar shirun daya biyo bayan maganarta a tsakanin su. Sai kiran sallar Magriba daya karade gidan. Har aka dire babu wanda ya yunkura, sai da Daada taji alamar an kira sallar tukunna ta iya samun karfin mikewa. Ita tayi alwala, roba da buta ta kawo ma Datti da bashi da karfin tashi har inda yake. Yelwa ce ta karba, ita ta dinga zuba masa ruwan yana alwalar. Shi yaba Dije damar shiga daki ta dauko wata tabarmar ta shimfida harta tayar da sallah, yelwar ma inda Datti yayi alwala tayi tata.
Daga zaune ya gabatar da tashi sallar saboda yana kara jin sanyin nan ya kara lullube kasusuwan shi, sai yaga kamar daya idar zai iya farkawa daga mafarkin da yakeyi na dawowar Yelwa. Kamar zai ga komai ba gaskiya bane ba, da idanuwa Datti yake rokon Dije ta rike tambayoyinta, shima yana da tarin su, ta dan basu lokaci zuciyar su ta gama gamsuwa da cewa Yelwa ce a cikin gidan, Yelwa ce a tare dasu, kafin wani abu ya sake biyo baya. Suna zaune shiru kowa da magana a bakin shi amman yana tsoron ya zamana wanda ya fara korar shirun. A haka isha’i ta same su suka kuma gabatar da ita.
“Ki zuba mana abinci muci.”
Datti yayi maganar, Dije batayi musu ba, a waje daya ta hado musu abinci, su duka sunayin kamar basu kula da duk lomar da Yelwa zata kai bakinta sai ta kai dayan hannunta ta share hawayen da suka zubo mata ba. Hawayen da Datti yakejin zafin su har a zuciyar shi, ko dandanon abincin baya ganewa, hakama Dije, sun kasa cire hannaye ne saboda Yelwa, sai da ta fara cirewa tukunna. Suka wanke hannuwa suka sha ruwa. Jin da Yelwa tayi bayanta ya amsa yasa ta kiran sunan Allah.
“Lafiya? Me ya faru? Baki da lafiya ne?”
Datti ya riga Dije tambaya. Maimakon amsa wani irin kuka ne ya sake kwacewa Yelwa, kamar ta kwana biyu bata ji wani ya damu da al’amarinta ba balle ya tambayeta me yake faruwa da ita.
“Ba ku tambayeni daga inda nake ba har yanzun Baba… Daada baku tambayeni ba.”
Kauda kai gefe Dije tayi kamar hakan zai hana hawayen dake idanuwanta zubowa
“Ki huta Yelwa… Gobe duk sai muyi wannan maganar… Ki huta yau, kije ki kwanta.”
Kai Yelwa ta girgiza tana sake matsawa kusa da Datti, kamar duk abinda zai sake rabata da shi ba karamin shiri zaizo dashi ba kafin hakan ya faru, gefen hijabinta ta saka tana goge fuskarta, amman hawayenta sunki daina zuba. Shirun da yake cikin gidan zai zaka iya tattara shi ka rufe jikinka.
“Da alamar hadari a garin nan, mu koma daki kar ruwa ya sauko.”
Dije ta fadi tana mikewa, hannun Datti ta kama ta taimaka masa ya tashi tana kaishi har daki, ta dawo ta mikama Yelwa da take kokarin tashi itama hannu, bata ki ba, ta bari Dije ta taimaka mata ta mike, bata jira Dijen ba ta shiga dakin da Datti ya shiga, a kasa ta zauna gefen gadon da yake kai tana jingina kanta a jiki, wasu sababbin hawayen na zubo mata. Dije sai da ta gama kaye-kayen da takeyi a tsakar gida saboda hadarin kara haduwa yakeyi, taurari duk sun bace a cikin shi. Ga iska na kadawa alamar kowanne lokaci ruwa zai iya saukowa sannan ta shiga dakin.
Shimfidar da tayiwa Datti ita ta samu waje ta sakeyi a kasa ta kwanta, wata irin gajiya takeji tana saukar mata, yawon da tunani da ruhinta sukeyi ne tun batan Yelwa suka samu tsayawa yanzun da suka sake kasancewa karkashin rufi daya. Wata irin gajiya ce da bata da kalaman da zatayi bayaninta balle ta iya fahimtar da wani. A tsakanin yawon da tambayoyi suke mata cikin kai wani irin bacci mai nauyin gaske ya dauketa.
Baccin da bata san tashi daga shi zaiyi dai-dai da tarar da duniyarta a birkice ba
Da tayi yaki dashi bata bari yayi galaba akanta ba.
Daada Kinga tashin hankali kala kala