Da idanuwa Khalid yake bin Salim da yana shigowa falon wajen TV ya nufa ya rage sautin gabaki daya tukunna ya wuce kitchen ya zubo abinci ya fito.
“Tashi ka koma waccen kujerar.”
Ya fadi yana sake hade girarshi da take a sama tun da ya shigo. In dai sunyi kallo a bangaren su to baya nan ne, ko a laptop dinsu ne sai dai su saka earpiece. Nawfal baya zama bangaren Nanna, sai da wani kwakkwaran dalili zaka ganshi a ciki. Shisa Khalid dinma ya hakura, tafiyar Nawfal karatu, a ranaku irin yau idan yazo cin abinci sai yai zaman shi ya danyi kallo, idan film dinma yaja hankalin shi sai yaje yayi sallah ya dawo ya cigaba da kallon abin shi. Ya nemi dalilin da zai sa Salim yawan zama bangaren Nanna a satikan nan ya rasa.
“Ba magana nake maka ba?”
Salim din ya karasa yana kai masa duka a kafada.
“Ouchhh… Hamma.”
Cewar Khalid yana murza wajen hadi da mikewa dan yaji zafi sosai. Salim baya ganin girman shi dana sauran mutane ba daya bane ba, baya ganin laifin Lukman da yake kauce ma duk wani abu da zai hada shi da Salim din tun rannan daya mare shi. Ranar ne shi kanshi Khalid din ya ajiye shan kamshin da yake yiwa Salim din a gefe, bai san sanda ya tsinto muryar shi yana gaishe dashi a ladabce ba, gaisuwar da Salim din bai amsa ba, kallon shi kawai yayi yana wucewa. Kafin ma ya fito yabar falon, Salim ba zai taba duba shekarun shi ba balle kuma dan gemun daya fara tarawa.
“Ka dauko mun ruwa.”
Salim ya fadi, kanshi ciwo yakeyi, ga zuciyar shi bata masa dadi ya kuma rasa dalilin hakan. Tun a hanyar dawowa daga wajen aiki yakejin son ganin Madina, ta zama abu na farko da zaici karo dashi daya shiga gidan. Amman tun dawowarta gidan sai yaga kamar yafi sakata a idanuwan shi lokacin da take gidan Daada. Yanzun tsakanin Magriba da Isha’i da yayi mata magana me yasa bata fitowa falon sai tace masa
“Azkar nakeyi Hamma…zuciyata bata da natsuwa saboda Daada, idan nayi addu’a ina samun sauki.”
Ba kalaman bane ba, yanayin yanda tayi maganar ne ya taba tashi zuciyar, saiya kasa ce mata komai, ya kasa fada mata abinda yake tashi zuciyar, a maimakon.
“Ni fa? Ni da bana ganin ki? Me yasa bana ganin ki kaman da yanzun kuma muna cikin gida daya? Lokacina da yake hade da naki fa? Bakya kewar mu?”
Da tarin maganganu masu ma’ana da akasin haka da yake son yi mata, saiya gyada mata kai alamar ya fahimta. Saboda ita yake yawan zama bangaren Nanna yanzun, lokuttan daya kamata ace yana bacci sai yayi su a zaune yana jiran yaji fitowarta. Baya son yaje ya kwankwasa mata kofa ko tana bacci, ga waya tana kashewa.
“Wayarki a kashe Mug.”
Kai ta dan daga masa.
“Sai inta kallo ina jiran kiran Hamma Nawfal.”
Zuciyar shi ta sosu, sai da yayi dana sanin mata magana akan kashe wayar, zuciyar shi batayi masa dadine idan yaso jin muryarta bai samu hakan ba. Kalamanta sunsa zuciyar shi tayi wani irin zafi, kiran Nawfal take jira? Me yasa zata jira kiran Nawfal? Idan saboda Daada ne me yasa ba zatace masa tana jiran kiran Nawfal dan ya hadata da Daada bane ba? Me yasa ba zata hada da Daada a cikin maganar ba? Nawfal fa? Tunda Daada ta fara rashin lafiyar nan Madina take gwada shi akan Nawfal.
“Ga ruwan.”
Muryar Khalid ta kutsa cikin tunanin shi, kallon da yayi masa yasa shi ajiye robar yana komawa dan ya dauko kofi. Karar shigowar sakon waya yaji, haka kawai ya mika hannun shi bayan shi ya zaro wayar duk da yasan ba tashi bace ba, ya kuma saka hannu yana kasa da sakon ganin daga banki ne, idon shi ya kai zuwa kudin daya rage a gabaki daya asusun bankin. Wayar ya ajiye yana tsintar kanshi da kirga kwanakin wata a ranar, ko rabi watan baiyi ba. Abincin shi yake ci a nutse kamar taunawar na masa wahala.
“Account nawa kake amfani dashi?”
Ya tambayi Khalid da ya kalle shi cikin rashin fahimta, bai maimaita tambayar ba, barin shi yayi ya sake juyata cikin kanshi har saida ya gane yana amsawa da
“Guda daya…”
Kamar Salim din ba zai sake magana ba, don saida ya karasa cinye abincin shi ya ajiye plate din, ya dauki robar ruwan ya kwance, ya kafa bakin shi yasa yana saka Khalid dan kankance idanuwa tunda baiga amfanin kofin da yasa shi komawa ya dauko ba tunda yasan ba amfani zaiyi dashi ba
“Me ya samu motar ka?”
Yana kula dashi baya daukar motar kwana biyu
“Na kunna taki tashine fa.”
Khalid ya amsa a takaice, kai Salim ya jinjina, da kudin da yake asusun Khalid din ko shine ba zai kira bakanike ba tunda baisan nawa motar zata ballo masa ba. Yasan tunda suka fara tsayawa da kafafuwan su, Julde kuma ya zabi ya kyalesu don su koyi rayuwa dai-dai da samun su, yanayin kashe kudinsu da Khalid ya bambanta, tunda samun su ba daya bane ba. Har ranshi, lokutta da dama yakan so ya dauki kudi ya ba Khalid saboda bayason ganin yanda sai yayi tunani fiye da sau daya kafin ya siyi wasu abubuwan. Amman bayason ya sa Khalid din yaji kamar ya raina masa abinda yake samu ne.
Idan wani ya kalle su sai yayi tunanin basu da matsalar kudi, tunda basu da nauyin iyali, amman motocin dake hannuwansu ma kadai iyali ce, sau nawa yaji abokan aikin shi na cewa idan mota ta ballo maka wani gyaran ko matarka ba zataci kudin a wata daya ba. Kamar kowa suna da kananun bukatu, suna da hidindimu, kuma duk da Julde na da wadata, su suna neman albarka, zakayi siyayya ka kawo gida, lokaci zuwa lokaci zaka shigo da cefane, shi ko takalman yaga sun masa kyau yakan siyowa Saratu. Iya farin cikin da take nunawa a fuskarta yakan rage masa duhun da yake ji a kirjin shi.
Yana da kashe kudi ya sani, yakan alakanta hakan da wadatarsu da yake da ita. Amman yanda Khalid bashi da kashe kudi.
“Ba’a biyanku da kyau a wajen aikinku ne Khalid?”
Ya karasa tambayar yana daga kai ya kalli fuskar Khalid din da yayi wani murmushi da Salim yaji baya so, saboda hade yake da wani yanayi na kamar duk bayanin da Khalid din zai masa ba zai fahimta ba
“Ana biya”
Ya amsa, bayason wannan takaitattun amsoshin da Khalid yake bashi
“Nawa?”
Ya sake tambaya yana tsare shi da idanuwa.
“Dari da goma.”
Sosai yake kallon Khalid din kamar yana son ya gano amsoshin da suke masa yawo batare da ya fito da tambayoyin su a fili ba. Albashine me kyau, a hidimar shi kawai bai kamata ace sun kare haka ba. Me yakeyi da kudi?
“Sako ya shigo wayarka, na duba. Magana mai yawa ba dabi’ata bace Khalid, shisa zan tambayeka kai tsaye…me kake da kudi?”
Gyara zaman shi Khalid ya sakeyi, kallon Salim din yakeyi sosai shima
“Na sake ganinka.”
Ya furta muryar shi na fitowa a dishe, da zuciyar Salim da abincin daya gama ci suna yo masa wani irin tsalle, ko da yana da abin da za fada shiru zai zaba, dan yanajin maganar shi dai-dai take da dawowar abincin da yake cikin shi.
“Na sani, nace ba sai kamun bayani ba, amman ina son sanin dalili, me yasa?”
Ya karasa maganar yana kallon idanuwan Salim din daya sauke daga cikin nashi. Ba’a taba masa tambaya mai nauyin wannan da Khalid yayi masa ba. Ba kuma amsa bace bata da ita, ta inda zai fara furta amsar ne bai sani ba. Mutuncin Daddy zai zubar a idanuwan Khalid? In ba haka ba ta ina zai fara fada masa saboda Daddy ya fara neman mata? Abinda yake tattare da matan da yasa bai duba lahirar shi ba, bai duba Nanna ba, balle kuma ya duba su ya so yaji shima, yaji din, ya kuma rasa ta inda zai fara dainawa yanzun. Saboda tun kafin a ajiye masa wasu dalilai yake jin Khalid kadai ya isa ya zama dalilin da zai daina in har yasan ta inda zai fara.
“Daddy?”
Khalid ya fadi cikin wata irin murya, yana dorawa da
“Saboda Daddy ko?”
Yana ruguza wani abu a kirjin Salim da baisan yana wajen ba. Numfashi Khalid yaja yana fitarwa cike da kunar rai. Ya sani, ya dade da sanin abinda Julde yakeyi, saboda shi mutum ne mai kula da al’amuran mutanen da yake so. Har Lukman kuwa da ake tunanin rayuwar shi ta bambanta data kowa a gidan, Khalid zai iya fadar karfe nawa yake zuwa makaranta ya dawo, ranakun da yake zuwa islamiyya da wanda baya zuwa yanzun, wanne abinci ya fiso da wanda baya so, saboda yana kula. Fiye da yanda suke tunani, idanuwan shi nakan duk wani motsi nasu.
Shisa ya dinga jin kamar ya dauke ido da yawa daga kan Salim shisa bai gane halin da yake ciki da wuri ba, amman Salim ne, yaushe ma ya bude bakin shi yayi magana da matan balle har ya bisu? A cikin halaye marassa kyau wannan ne karshen abinda za’a jingina Salim dashi saboda ya sha bamban da dabi’un shi. Sai dai kaddara bata zabe, babu kuma wanda yazo duniya da rubutun yanda halayen shi zasu kasance a goshin shi. Idan duniya ta tashi miko maka farantin dabi’u sai ta cakude maka mai kyau da marar kyau a waje daya, waresu hankalin ka da karfin yaki da zuciyarka ne kawai zaiyi maka hakan.
Shirun Salim din ya tabbatar masa da komai, numfashi ya sake ja yana fitarwa
“Akwai Angry Ustaz a manhajar twitter, yanayin wani aiki build a well, suna bin garuruwa su duka kauyukan dake karkashin garin inda suke wahalar ruwa sai mutane su tara kudi a gina rijiya a garin…da dan tsada idan mutum daya zai biya duka kudin, inayin biya uku ko hudu, saboda Daddy, saboda bansan ya zanyi ba, duk idan naga ya fita ya dawo ina kallon shi da nauyin da yake kafadun shi, yanzun gaka…”
Har lokacin Salim bai dago kanshi ba, cikin wata irin murya yace,
“Rijiya kayi a madadina Khalid?”
Dan daga kafadu Khalid yayi, kirjin shi yayi nauyi. Wanne zabi suka bar masa? Yana kaunar su, wannan rayuwar ta duniya yana da yakinin mutuwa ce kawai zata raba tsakanin su, yana musu kaunar da yake fatan kasancewa tare dasu a aljanna,hakan ba zai faru ba idan suna wasa da lahirarsu haka.
“Ya zanyi Hamma?”
Mikewa Salim yayi, baice komai ba ya fice daga dakin zuwa bangaren su. Ya rasa dalilin da yasa baya ganin hanya sosai har saida ya shiga dakin shi ya mayar da kofar ya kulle tukunna ya gane hawaye ne cike da idanuwan shi, kirjin shi yayi wani irin nauyi cikin yanayin da bai taba sanin akwai shi ba tunda yake a duniya. Iska yake ja yana fitarwa hadi da kokarin mayar da hawayen dake ta yi masa barazana
“Pull yourself together Salim”
Ya furta cikin wata irin murya, amman ya rasa ta inda zai fara tattara abinda Khalid ya wargaza masa, babu wasu kalamai da zasu fassara asalin abinda yake ji, bacin rai? Farin ciki? Karyewar zuciya? Rauni? Mamaki? Kowanne a cikin abubuwan ne da wasu da baisan sunayensu ba suka hade masa waje daya. Dakyar ya iya jan kafafuwan shi zuwa bandaki, ya watso ruwa ya fito, babu abinda ya bashi tsoro sai wata irin bukatar mace data taso masa saboda yanajin duminta ne kawai abinda zai kauda masa wannan hargitsin da Khalid ya jefa shi ciki.
Rurin wayarshi yaji, yana mamakin lokacin daya cireta daga silent, karasawa yayi kan gadon ya dauka. Ganin Nawfal ne ya sakashi saurin dagawa ya kara a kunne
“Bajjo…”
Ya kira, sai dai Nawfal din bai amsa ba.
“Bajjo…”
Ya sake kira, banda numfashin Nawfal din da yake juyowa ta cikin wayar da zai dauka ko kiran ya yanke ne.
“Meya faru? Kamun Magana.”
Cewar Salim yana zama gefen gadon
“Ina Hamma?”
Nawfal ya bukata ta dayan bangaren yana dorawa da
“Na kira shi bai daga ba”
Dan dafe kai Salim yayi
“Dole sai Khalid? Ba zaka iya magana dani ba?”
Jin yayi shiru yasa Salim din sauke numfashi
“Ina Daada? Ya jikinta? Yau za’ayi mata aikin ko?”
A takaice Nawfal ya amsa da
“Alhamdulillah. Eh…”
Shiru ya sake gifta musu
“Sai anjima Hamma…”
Nawfal ya fadi, kafin Salim din yace wani abu ya kashe wayar ta dayan bangaren. Karamin tsaki Salim yaja, kamar su duka sun hada baki yau, babu abinda suke so sai su dagula masa lissafi. Kaya ya sake ya dauki turaruka ya feshe jikin shi, saiya tuna baiyi ko sallar la’asar ba, da fitar zaiyi inya dawo saiya hada duka yayi
“Ya zanyi Hamma?”
Maganar Khalid da yanayin muryar shi suka dawo masa suna hana masa fita, tsaki ya kara ja ya koma bandaki ya dauro alwala, sanda ya idar har anyi isha’i, don haka ya gabatar da ita. Ya sake mikewa ya fice daga dakin. Bayason haduwa da Khalid, da ya sani yayi musanyar aikin shi na yau dana dare, tunda da yawa bason aikin daren sukeyi ba. Yana son ganin Madina, da dukkan zuciyar shi yana so ya ganta. Wayar shi da yasa aljihu ya ciro ya kirata, yayi sa’a bugun farko ta daga.
“Hamma…”
Muryarta ta daki kunnenshi, wata irin nutsuwa daya manta rabon daya sameta ta ratsa.
“Ki fito in ganki.”
Ya fada yana kasa gane muryarshi saboda yanda tayi kasa. Bata amsa ba, ta dai kashe wayar daga dayan bangaren. Sai yaga kamar ya kusa awa yana jira kafin ta fito, wandone na jeans a jikinta, sai ta saka wani takalmi mai gashi da ita kadai yake gani dashi, rigarta fara, ita dashi zasu shiga ciki saboda girmanta, ta saka farar hula akanta, sai hannunta da take kaiwa tana gyara zaman gilashinta kamar tana tsoron idan batayin hakan lokaci lokaci zai iya fadowa. Tayi masa kyau, Madina tana yi masa kyau ko me zata saka. Murmushi take masa da yake haska wajaje da dama a cikin kirjin shi. Sai da ta karaso gab dashi yaga fuskarta ta kumbura, idanuwanta sun sake kankancewa ta cikin gilashinta.
“Kuka kikayi ko?”
Murmushin ta sake fadadawa
“Tun dazun ne fa… Kuma na wanke fuskata.”
Murmushi ya tsinci kanshi dayi, in dai tana kusa, fara’a bata masa wahala, zata fadi wani abu da ko bai tanka ba zai saka shi murmushi. Yanayin da yake ciki da yanda take tsaye a gabanshi, sai ya daga hannu, nufin shi ya taba kuncinta, koya ne yaji duminta a jikin hannun shi. Saiya kare da sake tura mata gilashinta yanda takanyi.
“Ba kayi bacci ba ko Hamma?”
Dan daga mata gira yayi yana sa tayi dariyarta da yake so.
“Ya nuna a fuskarka… Girarka ta karayin sama fiye da kullum.”
Kai ya girgiza da murmushi a fuskarshi.
“Mu fita yawo.”
Dan yatsina fuska ta yi.
“Mu zauna muyi hira, kaje ka kwanta… Kana da aiki gobe da safe… Ka yi bacci.”
Yanda yake hade fuska yasa Madina dorawa da.
“Dan Allah Hamma ka yi bacci…”
Sosai yake hade mata fuska.
“Bana ganinki yanzun.”
Ya furta da wani yanayi a muryarshi.
“Kayi bacci, zaka ganni gobe In shaa Allah… Ina nan daka dawo aiki, sai muje yawon.”
Kallonta yake tana ganin musun da yake son yi shimfide cikin idanuwan shi.
“Ba gobe kawai ba, kullum idan ka dawo zaka ganni.”
Hannun shi ya mika mata, batayi musu ba ta saka nata a ciki, tana ganin kankantar nata hannun. Numfashi ya sauke mai nauyin gaske, ganinta, magana da ita, da hannunta daya rike ya samar mishi nutsuwar da yake bukata, kallon ta yake
Kallon da ba zai iya hango abinda gobe ta tanadar musu ba a cikin so.