Kwanaki biyu kenan, da Nawfal ya same shi ya mika masa wasu takardu guda biyu, kamar yaki karba, kamar ya cewa Nawfal din ya fara fada masa abinda yake cikin takardun kafin ya karba, sai yayi karfin halin mika hannu ya amsa, ya bude ya karanta, nauyin abinda yake ciki na kara danne shi tare da sauran abubuwan da yake fama dasu a cikin kwanakin nan.
“Ba zakaje Borno ba, ka sani ai ko?”
Ya fadi yana daga ido ya kalli Nawfal din.
“Idan tunanin da yake cikin kanka kenan ka fitar dashi, ba zakaje Borno ba. Waya baka wannan ma?”
Kafadu Nawfal din ya dan daga masa batare da yace komai ba, kamar babu muhimmanci a sanin wanda ya bashi, tunda dai ya rigada ya gani.
“Bajjo ba wasa nakeyi ba.”
Ya fadi yanajin wani abu yayi masa tsaye a waya da yanayin kallon da Nawfal yake yi masa.
“Idan naje Borno ta ina zan fara? Ko ina so inje bansan ta inda zan fara ba Hamma, ni Marake zanje…zamuje da Hamma Khalid…kace zakaji da Madina, mu zamuje Marake.”
Numfashi ya sauke yana jinjina ma Nawfal din kai, takardun ya karba daga hannun Salim yana juyawa batare da ya sake cewa komai ba, shima Salim din ya bude baki amman sai ya rasa abinda zaice, ya karbi duk lambobin wayar da yake bukata. Ya kuma gama shirin duk da zaiyi, asibiti ya samu wanda baiji a muryarsu sun nuna alamun ya takura su ba daya bukaci su karbar masa shift din shi, tunda ya sha yi musu nasu na dare babu adadi. Idan komai ya tafar masa yanda yake so, kwana daya ya tsara yi a garin Abuja. Duk da bai daga burin shi akan komai ya tafi yanda ya tsara ba, dan jikin shi ya gama yin sanyi da yanayin rayuwa yanzun.
Sai yasha mamaki, yanda komai yazo masa da sauki, saiya kara mamaki akan wani mamakin lokacin da idanuwan shi suka sauka akan Kabiru, kafafuwan shi suka soma yi masa barazanar kasa daukar sauran gangar jikin shi, da gaske ne, ana kama, har zakaji wasu na cewa,
“Ai kuwa idan wane ya bace to tabbas ‘yan uwan shi da dangin shi duka ba zasu taba yarda ba kai bane ko kece, saboda yanda kukayi kama.”
Shima wajen mutum nawa ya fada masa ya taba ganin me kama dashi, amman mutumin da yake tsaye a gabanshi, ko yayi rantsuwa ba zaiyi kaffara ba jinin Madina ne, da ya yi murmushi sai Salim ya ji zuciyarshi ta doka.
“Kullum ina duba hanya, a cikin fuskoki da yawa ina neman wanda zaiyi shige dana Yelwa ko zan rike shi in tambayi labarin ‘yan uwanta, in samu in hadata da ahalin dana rabata dasu, yaro nazo nan cike da taraddadi, nazo nan da zuciyata a tafin hannu na saboda bansan abinda zan gani ba. Bayan shekaru masu yawa, a tsakanin haduwa da fulani kala-kala, yau naga fuslar Yelwa a cikin taka.”
Salim ya bude bakin shi, labbanshi sun motsa,amman muryar shi bata karasa cikin kunnuwan shi ba, bai san meya tambaya ba sai da yaji amsar Kabiru.
“Neman wanda ya daura mana aure ne abu na farko da muka fara yi da Yelwa bayan motar data dauke mu daga Marake ta sauke mu.”
Kabir ya karasa maganar da wani kyalli da Salim din ba zai iya fassarawa ba kai tsaye a cikin idanuwan shi, kyallin yana masa kama da dana sani, yana masa kama da shekaru cikin wani ciwo na zuciya da babu wanda zai fahimta, yana kuma yi masa kama da firgici, kwatankwacin wanda ya dandana a ‘yan kwanakin nan. Yayi tunani kala-kala, akan abinda ya tambaya, amman ya kasa tunawa. Ya dai san amsar Kabiru ta saukaka masa wani abu daya jima kulle da zuciyar shi, ya sauke numfashin da baisan yana rike dashi ba tun randa ya karanta wasikar Yelwa a hannun Madina.
“Za muzo, zan dauko ta muzo.”
Shine kalman karshe da suka hadashi da Kabiru, suna masa yawo a cikin kanshi ya koma Kano, suna masa yawo har kwanaki uku da yayi amfani dasu wajen binne kanshi da aiki a asibiti dan ya janye hankalin shi daga kiran Kabiru, ya kuma ji dadi da Madina ma duk wayar da sukayi bata daga masa maganar ba. A safiyar kwana na ukun ne da yake jin hakurin shi yana gab da karewa Kabiru ya kirashi ya fada masa suna hanya, bai tambayi daga inda zasu taho ba, ya dai cire farar rigar jikin shi, ya kuma dauki mukullin motar shi ya fita daga asibitin.
“Ka ci abinci Hamma?”
Sakon Madina ya shiga wayar shi lokacin daya fita daga asibitin, ta saba tuna masa yaci abinci saboda tasan in dai yana aiki saiya wuni da yunwa. Yau yana da karfin cin abincin, duka a kwanakin nan zai amsata ne, amman saiya saka abincin a gabanshi yaji ko kadan bayaso ya kai shi baki, idan ya tura abinda zai iya yanayin hakan ne don jikinshi yana bukatar abincin, amman baya gane dandanon ko kadan. Sai ya rasa abinda zai siya, bayason shiga bangaren Saratu, har yanzun bai shirya ganinta ba, balle kuma abinda zai hadashi hanya daya da ganin Julde. Yana cikin wannan tunanin ne yaji alamun kira ya shigo wayar shi.
“Adee”
Ya fada bayan ya daga ya saka wayar a kunnen shi.
“Ka manta kana da kanwa ne Hamma?”
Sai murmushi ya kwace masa.
“Yanzun na fito daga asibiti, abinda zanci nake nema Adee.”
Ya furta a madadin amsa korafinta.
“Fanke zan soya ni, ka biyo ka karba mana to, ina da Zobo da kunun aya a fridge, jiya nayi, in kuma da tea zaka hada to.”
Numfashi ya sauke.
“Yanzun sai nazo har unguwarku saboda fanke Adee?”
Yanajin dariyarta.
“To me kake so sai in dafa maka? Kaji? Dan Allah kazo, kaga rannan da naje gida baka nan, banganka ba.”
Sai da yayi kamar ba zai amsa ba, saboda tunanin da yake yi, yana hango tsayin tafiyar da zai hada shi da gidan Adee daga inda ya ke.
“Bari in karbi fanken.”
Bai amsa surutun da takeyi ba ya kashe wayar. Ya danyi fama da cunkoso daya juya dayan hannun, tunda ranar aikice, ga kuma yan kasuwa da sauran al’umma da suka fito dan gudanar da uzurin ranar. Sai yaga komai ya kara kala a idanuwan shi yau, har iskar da yadan bude gilashin motar tana shigo masa jinta yakeyi daban, kamar duk wani abu da zaici karo dashi yau ya san girman abinda yake shirin faruwa dasu. Da wannan yanayin ya karasa gidan Adee, yanda duk tayi dashi ya shiga ciki yakiya, motar shima a bakin kofa yayi parking dinta bayan ya juyata hannun da zai fitar dashi daga unguwar.
“Hamma wannan ba zuwa ka yi ka ganni ba.”
Cewar Adee data fito jikinta sanye da hijab, tayi masa kyau, alamar akwai kwanciyar hankali a tattare da ita, hakan kuma yayi masa dadi, duk gidansu idan akwai wanda ya cancanci ya samu natsuwa fiye da kowa to Adee ce, saboda nagartattun halayen da take dashi.
“Baka fadamun zobo zaka sha ba ko kunun aya, na dai saka maka duka biyun.”
Karbar kwandon da ta mika masa yayi yana ajiyewa kan kujera a cikin motar.
“Na ganki, kin ganni nima ina lafiya. Ki gaishe da mijin ki.”
Ya karasa yana murza mukullin motar.
“Hamma…”
Ta kira da sauri, sai ya daga ido ya kalleta, duk ta daburce lokaci daya, kashe motar ya sakeyi yana kiran sunanta.
“Adee”
Numfashi ta ja ta fitar.
“Da naje gida, akwai abinda ya faru ko? Na tambayi Nanna tace bakomai banda Daddy da bayajin dadi kuma shima jikin da sauki, naga da sauki, har hira munyi… Daga Bajjo har Khalid sunce mun bakomai.”
Sosai ya kalleta wannan karin yana ganin sauran kalaman da bata furta ba kwance akan fuskarta.
“Akwai abinda ya faru, ki yarda dani rashin saninki yafi muhimmanci.”
Ta dauki wasu dakika, har saida ya fara tunanin musu ne abinda zai fito daga bakinta sannan ta ce,
“Abinda ya farun? Ya wuce? Komai ya koma dai-dai?”
Kai ya girgiza mata.
“Amman babu abinda lokaci baya tafiya da shi, right?”
Murmushi ta yi tana dan daga masa kai.
“Zamu yi waya.”
Kan dai ta sake daga masa, sai kuma hannunta bayan ya rigada yaja motar, ta mudubi ya hangota tana tsaye har lokacin. Babu ma’aunin da zai iya daukar girman son da yake yiwa Adee. Tun suna yara yakejin duk wani abu kafin ya sameta zai fara wucewa ne ta cikin shi, saboda ko menene zai same shi tsaye a gabanta, yana bata duk wata kariya da take karkashin ikon shi. Waje ya samu yayi parking, ya saka ruwa ya wanke hannun shi ta murfin motar, sannan ya bude robar fanken, harda soyayyen nama ta zuba masa. Yayi mamakin yanda ya kusa cinye, dakyar ya rage guda hudu, yanka nama biyu. Gida ya wuce ya watsa ruwa ya sake kaya, yadine ya saka bula, Nawfal ne ya sai musu, duk wani kaya da yake dasu masu kalar yawanci kyautar Nawfal ce, kamar a duniya babu wata kala da idanuwan shi suke gani sai ruwan sararin samaniya.
Saiya wuce gidan Daada, kamar kullum a bakin kofa ya tsaya ya kira Madina, ta fito, sai da ta zauna cikin motar tana hamma kamar bacci bai isheta ba sannan ya kula da wani takalmi mai kaza da ta sakama kafafuwanta, irin mai gashin nan, murmushi ya kwace masa.
“Ina kwana.”
Ta furta kowacce kalma a tsakanin Hammar da takeyi, tana mika hannu cikin kwandon da dauke kafin ta zauna, ta kuma ajiye shi akan cinyarta.
“Menene wannan? Ina ka samu zobo mai sanyi da safen nan?”
Yana kallo ta dauki roba daya tana juyawa, data kwance ta kurba.
“Adda ta baka?”
Ware idanuwa ya yi cikin mamaki.
“Kasan zobon Adda fa ba irin shi a garin nan, dana sha saina gane nata ne, na ce ta koyamun dame-dame take sakawa, nayi amman sai naji bai dai kai nata ba…”
Komai nata, komai na Madina yayi masa, harda surutun ta.
“Fanke? Ya naga guda hudu?”
Ta karasa tana bude robar ta dauko guda daya.
“Rage miki na yi”
Ya furta yana jingina jikin shi sosai da kujerar motar ya juyar da kai yana kallonta, yanda da yaganta duk wata gajiya da yake ji, wadda ya sani da wadda bai sani ba take danne shi yana bashi mamaki, ko bacci yakeji daya ganta saiya karu, saboda yana so yayi baccin a kusa da ita, yanajin kamar duk wani hutu nashi yana jingine ne da ita
“Kwara hudu Hamma?”
Ta fadi tana dariya
“Ya yi dadi, da kyar na rage.”
Dariya take yi sosai, ya kuwa yi mata dadin, suna da sauran shinkafa da miyar data dafa da daddare, shine ta dumama musu da safen saita dafa ruwan shayi tunda daga ita sai Daada a gidan, Murjanatu bata nan, bata tambayi inda taje ba tun jiya saboda abubuwan da take tunani sunyi mata yawan da bata da wajen kananun tambayoyi irin wannan.
“Hamma karkayi bacci a motar nan, ka fito mu shiga ciki ka kwanta a kujera, Daada ma bacci ta koma.”
Madina ta fadi tana saka shi makale mata kafada, idan cikim gidan ya shiga, ba zaiji ta a kusa dashi haka ba, tana ma iya bar masa falon da taga yayi bacci, shisa ya sake langabewa cikin kujerar, yace yana sonta, ya fada mata yana tabbatar da taga duk wani waje da son nata ya taba a tare dashi, batace komai ba, ta kalle shi, kamar ta fahimta haka ta kalle shi.
“Mug…”
Ya kira can kasan makoshi, sai da ta gyara gilashin fuskarta sannan ta kalle shi
“Bakya so na?”
Tambayar ta fito daga bakin shi tana dukanta, saboda batayi tsammaninta ba, daga wajen wani ma balle kuma shi, ya zai dora ayar tambaya akan son da takeyi masa bayan yana daya daga kalilan din mazan da suke cikin rayuwarta? Kuma kamar tunda suka hada jini bata da wani zabi akan son shi. Kafin kusanci ya gifta musu tana son shi saboda jinin shi da yake yawo a jikinta, da tasan wanene shi sai ya tabbatar mata ko basu hada jini ba zata so shi.
Amman a kalmar so na karshe daya furta mata sai taga kamar yasha bamban da wanda take tunani, a kallon da yakeyi mata yanzun sai yake tabbatar da inda tunaninta yaje anan na shi yake zaune.
“Bakya sona?”
Wannan karin ya furta cikin son tabbatar ma kanshi, saita tsinci kanta da sauran girgiza masa kai, kaifin kallon shi na ratsawa ta cikin kirjinta zuwa zuciyarta, kawai dai kamar bata shirya ba take ji, ta bude baki batare da tasan amsar da tayi niyyar bashi ba, karar wayar shi ta katse musu yanayin, daya duba sai taga yanayin shi ya canza.
“Bari yanzun zan dawo.”
Ya furta idanuwan shi na kan wayar da bai daga ba, da kyar ya rabasu da wayar yana kallonta, kai ta dan daga masa tana daukar kwandon da yake kan cinyarta, yanda jikinta yake a sanyaye sai taji dakyar ta iya fita daga motar, kafin tayi wani yunkuri ya mika hannu ya rufe murfin yaja motar yabar wajen. Cikin gida ta koma, da kwandon a hannunta, saita wuce dashi kitchen, ta dauki robobin da suka rage ta saka a fridge, harda zobon data fara sha, sai sauran fanken da guda biyu taci, ta dauko robar tana fitowa falon, suka ci karo da Daada a tsakiyar falon inda take neman zama kan kafet
“Wai Daada laifin me kujera tayi miki?”
Madina data zauna kusa da ita a kasa ta fadi
“Ke da batayiwa laifi ba me kike a kusa dani?”
Dariya tayi tana mika mata robar fanken.
“Adda ce ta ba Hamma, ci kiji Daada, yayi dadi sosai, inajin gobe idan Allah ya kaimu shi zanyi mana.”
Murmushi Daada ta yi tana daukar guda daya.
“Lallai fanke yayi dadi tunda kike tunanin yi.”
Dayan daya rage ta dauka tana ajiye robar.
“Fanken ne baya sona Daada duk son da nakeyi masa, kin manta na karshe da na yi.”
Dariya Daada takeyi, dan ba zata manta da wannan fanken da ya koma fankaso ba.
“Amman dai ba zan cika ruwa ba.”
Cewar Madina, Daada ta kasa daina dariya.
“Daada mana”
Da kyar ta iya cewa,
“Ki dai kwaba kadan dan a takaita barna.”
Tare suka yi dariyar wannan karin, labari suke danyi, kusan ma Madina ce take bata labarin, wani littafi data karanta, itama Daadar rabin hankalinta ne yake kan Madina, saboda wata irin bugawa da zuciyarta takeyi a cikin kirjinta, kamar tana son sanar da ita wani abu data kasa fahimta, shisa ita kuma zuciyar taki natsuwa waje daya, take ta kai kawo cikin neman hanyar da zata isar da sakonta, tasan muryar Salim, amman yau da yayi sallama sai bugun zuciyarta ya kara tsananta.
“Hamma ne, yace zaije ya dawo ne daman.”
Madina ta furta, amman Daada jin maganar tayi can nesa da ita, haka da Salim ya shigo dakin, ya zabi ya fara sauke idanuwan shi akanta a maimakon Madina, Salim da yakeyi kamar bayason magana da kowa, Salim da zaiyi duk wani kokari na kaucewa hada idanuwa da ita bayan ya gaisheta dan karta samu halin sakeyi masa magana, yau nashi idanuwan ne suka fara laluben nata, labbanshi suka motsa ya furta.
“Daada…”
Kafin ya matsa daga hanyar kofar kamar yana son bawa wani damar shigowa, sai idanuwanta suka bar na Salim suka koma kan kofar, inda duk wani mafarki, duk wani hasashe, duk wani tsammani a tsayin shekarun nan bai shirya zuciyarta tarbar abinda take gani yanzun ba. Kamar hudowar hasken rana ta tsakanin giza-gizai, haka shigowar Yelwa dakin ta kasance mata, sai farin mayafin da yake yane saman kanta ya shiga idanuwan Daada, tare da wani hasken da bata da kalmomin misalta shi, batare data sani ba ta kai hannu saman cikinta, inda take jin wani abu yana yamutsa mata, a lokaci daya kuma abubuwa da yawa suka soma turereniya da juna wajen dawo mata.
A cikinta, Yelwa ta kwanta.
Watanni tara harda satika uku, lissafi ba zai taba kwace mata ba ko akan yaran da suka leko dan ta amsa sunan uwa, suka koma kafin ta taka wata rawar gani a wannan matsayin da suka bata.
Nakudar ta a tsakanin kai kawon Abu da kuma mahaifiyarta.
Kyawunta.
Kyawun Yelwa da ya zama abin magana wajen duk wanda yayi tozali da ita
‘Yarta.
Tilon ‘yarta.
Sai kauna irin wadda mahaifiya ce kawai zata taba fahimta ta danneta hartana kasa fitar da numfashi yanda ya kamata, wannan kaunar da babu wani laifi da yake disashe haskenta a zuciyar mahaifiya, kaunar yaranta, kaunar da ko mahaifansu ba zasu taba fahimta ba, saboda kashin bayansu bai karye ba, kugunsu bai amsa ba, ba suyi rayuwa a tsakanin duniya da lahira ba a cikin dakin nakuda, ba suja numfashi suna tsammanin shine na karshe ba, da suka fita suka nemo don su ciyar, a cikin shekaru biyu abincin daga aljihunsu ya fito ba daga jikinsu ba, ba zasu taba fahimtar wannan soyayyar ba. Hannu ta mika, saboda shine iya motsin da zata iya.
“Daada…Daada Am.”
Muryar Yelwa da take rawa ta ratsa kunnuwan Daada data lumshe idanuwanta tana jero duk wata godiya da zata iya tunawa wajen Ubangiji, da ya kadarta fitowar Yelwa daga cikinta, ya kadarta zatayi mata nisa, ya kuma kadarta rayuwa ba zata kare mata ba sai ta sake ganinta, idanuwan ta bude lokacin da dumin hannun Yelwa ya ratsa nata.
‘Yarta.
‘Yar su ita da Datti.
Gudan jininsu.
Saura bukar
Naga har kin Kai 36 a Wattpad
Please Ina sauran