Na gode da fatan alkhairi
Na gode da tarin addu'o'inku
Wanda suka kira, sako ta whatsapp, text, wattpad harma wanda suka turo ta email dina domin tambayar lafiyata, na gani, na gode kwarai, Allah ya saka da alkhairi.
Na kuma gode da uzurin da kukeyi mun.
Shekaru goma sha bakwai ana neman hada ta sha takwas din, a cikin shekarun ta yi numfashi da sanin adadin shi sai wanda ya bata ikon yi, sai dai a tsayin lokacin, a cikin kowanne shiga da fitar numfashinta akwai kewar ahalinta, wata irin kewa da zata ce ta danne ruhinta dan. . .