Hannunta ta saka cikin na Salim, bashi bane karo na farko da hannuwansu ya shiga cikin na juna, amman yanda ya dumtsa yatsunta yau sai taji kamar an halitta musu wajen zama a cikin nashi ne, daya dan juyo ya kalleta, sai ya dago dayan hannun shi yana goge mata jambakin daya haura gefen lebenta da yatsanshi yana yawatawa da idanuwan shi kan fuskarta kamar yana neman wani abin da baiyi mishi ba ya gyara, kafin ya dan daga kai alamun komai yayi. Yaja hannunta
"Hamma bana gani sosai"
Ta fadi saboda komai yayi mata dishi dishi, ya saka gilashinta. . .