Sake gyara zaman shi yayi a cikin mota a karo na ba adadi, bacci yake ji ba dan kadan ba, saboda bai samu wadatacce ba da dare. Da ace babu hayaniya lafiya kalau zaiyi baccin shi. Tunda motar a kashe take dole ya sauke gilashin kadan dan shige da ficen iska. Amman hakan sai kwaso mishi surutan da baya bukata zuwa kunnuwan shi yakeyi. Harda yara da a lokacin ya kamata ace suna islamiyya amman sun cika unguwa da hayaniya sun hana kowa sakat. Inda unguwar su Daada yake yana da tabbacin da anyi gangami an tashe su ko da. . .