Skip to content
Part 9 of 58 in the Series Rai Da Kaddara by Lubna Sufyan

“Adee…”

Nawfal ya furta bayan sun shigo dakin ita da Khalid suna gaisawa da Daada. Wata irin kewar ta na tsirga mishi, dariyar da takeyi bai hanata hararar shi ba

“Bawani nan…”

Murmushi ya keyi yana mika mata hannun shi daga inda yake zaune, karasawa tayi ta kama tana zama gefen shi kafin ta zare hannun nata tana daka mishi duka.

“Ouchhh… Adeee”

Ya fadi yana murza wajen dan yaji zafi sosai

“Ka zo ba zaka iya kirana ba Nawfal, ba sai kazo inda nake ba in ganka…”

Har lokacin murza wajen yakeyi

“Saboda ke fa na zo, yanzun nake so in kira inji ko kin dawo…”

Tabe baki Adee tayi, Nawfal na gyara zaman shi kan kujerar yanda zai fuskance ta, fuskarta fayau take babu kwalliya, amman sai yaga har wani kyalli-kyalli takeyi mishi

“Kinyi kyau sosai”

Murmushi tayi, kowa haka yake ce mata tun bayan sati daya da fara mata gyaran jikin da bata san nawa Nanna ta kashe a kai ba. Kuma itama tana jin santsin da fatarta tayi, daman fuskarta tunda can babu kurji ko daya, tana dai gani a fuskokin mutane, ita wannan zumuncin ne bai taba tsallakowa kanta ba.

“Nagode”

Ta fadi, kai ya jinjina mata yana sata girgiza mishi nata, ita ba dan yace tayi kyau take mishi godiya ba

“Ina nufin nagode da kazo…”

Wani sauti Khalid ya fito dashi daga kasan makoshin shi yana dorawa da

“Karku fara dan Allah…”

Cikin yanayin da yasa su yin dariya

“Daada ina Madina?”

Cewar Adee

“Sallah ta shiga daki tayi. Na san yanzun zaki ga ta fito”

Ai kam Daada na rufe bakinta Madina tana fitowa daga daki

“Adda…”

Ta kira tana karasowa ta zauna daga gefen Adee

“Hamma ina wuni”

Ta gaishe da Khalid da yake daddana wayar shi

“Lafiya kalau Madina… Kwana biyu”

Kallon shi tayi

“Ina cewa Hamma ya gaishe ka fa”

Shima nashi idon ya raba da waya yana kallon ta cike da alamar tambaya

“Wanne Hamman?”

Murmushi tayi

“Hamma Salim, ko shekaranjiya na ce ya gaishe ka, kullum ma idan mun hadu ina cewa ta gaishe ka”

Wannan karin Adee ta kama Madina tana juyo da ita dan su fuskanci juna

“Hamma Salim naji kince Madina… Hamman mu… Salim na mu wanda duka muka sani?”

Yanayin da yake fuskokin su ne ya ba Madina dariya, yi suke kamar abune da ko a mafarki basu hango zai faru ba, kai ta jinjina

“Hamma Salim kike gani? Kina magana da shi, shima yayi magana da ke?”

Kai ta sake jinjina ma Adee, Khalid da ya ajiye wayar shi kan hannun kujera fuskar shi dauke da tsantsar mamaki yace

“Ya sunan bokon ki Madina?”

Har Daada sai da tayi dariya

“Da gaske nakeyi… Tafdin… Hamma fa… Bajjo kana jin ikon Allah”

Kai Nawfal ya jinjina musu, dan shi ya gama nashi mamakin tun kafin su zo

“Har daga makaranta yana dauko ta ya dawo da ita gida wasu ranakun…”

Sai da yaga hankulan Adee da Khalid sun koma kan shi tukunna ya dora da

“Suna labari da juna har suzo gida… More like Madina tana labari da shi kuma bai taba sauke ta a hanya ba.”

Baki Adee ta rike

“Ashe zanyi tsahon ran da zan ga ranar nan… Madina anya ke mutum ce?”

Dariya suke bata sosai ma

“Yanzun idan ya shigo fa?”

Daada ta fadi tana saka wani shiru ya ratsa dakin, Khalid na daukar wayar shi daya ajiye, Nawfal ya koma cikin kujera ya zauna. Adee ma gyara nata zaman tayi tana kallon Madina.

“Maganar kunshin, gobe idan Allah ya kaimu ne fa…”

Kai Madina ta jinjina mata

“Ban manta ba, wajen karfa tara In shaa Allah zan taho sai in fara ma wanda suke nan kafin sauran su zo…”

Ganin sabuwar hira zasu dasa yasa Daada cewa

“Abinci fa?”

Adee ta fara amsawa,”Ni dai ina ci, sau daya naci abinci duk yau wallahi, cikina sai kullewa yake tun dazun”

Abincin kuwa Madina ta tashi ta zuba musu banda Nawfal da ya shiga kitchen din da kan shi yana dafa ruwan zafi ya hada shayi. Kankara ya dauka a fridge ya fasa ya zuba cikin kofin yana karasa cika shi taf ya dauko ya fito. Banda Daada babu wanda yayi mishi magana tunda duk ba bakon abu bane a wajen su. Musamman Khalid da ba zaice ga rana daya da yaga Nawfal yasha shayi mai zafi ba. Sam baya so, suna nan suna hira Julde ya shigo ya same su, shima abincin aka zubo mishi suna dasa sabuwar hira kamar lokacin gari ya waye musu ba dare bane ba.

Shikam Julde hankalin shi yana kan Adee da su Khalid suka saka a gaba da tsokana. Haka yake son ganin su kullum, yaran shi, farin cikin shi. Yanda maganar auren ta ya tafar mishi batare da wata matsala ba abune da zai jima yana nutsar da shi duk idan ya tuna. Akan ce mutane na daya daga cikin Rahmar da Allah zai maka, bai kara yarda ba sai akan bikin nan na Adee, yanda abokan arziki suka mishi tsaye ta yanda wani dan uwa na shi bai taba mishi ba tunda yake. Daga tambayar auren har daurin shi da ya wakilta abokin shi ya kuma karba. Tabbas yaga halaccin mutane, a tare da dangin mijin Adee kuma yaga wautar mutane ta yarda da wani kamar yanda suka yarda da shi.

Dan shi bai basu wannan yardar ba, kaunar da yake ma Adee tasa sai da yayi cikakken bincike a kan su kafin ya amince. Ba zai dauki yar shi ya kai inda wata matsala zata biyo baya ba. Sauran maza ne, yana da tabbacin babu wani abu da zai taba su da zasu kasa dauka. Adee ce yake son karewa da dukkan kumajin shi. Kuma hankalin shi ya kwanta da kalar mijin da zata aura.

“Karfe goma da wani abu, in dai ba anan zaku kwana ba ya kamata ace kun tashi kun kama hanyar gida yanzun”

Julde ya fadi yana kallon agogo, sake shigewa cikin kujera Nawfal yayi yana dauke idon shi daga cikin na Khalid da yake kallon shi

“Da gaske Bajjo?”

Adee ta fadi bayan ta mike

“Gobe da safe zan taho, sai mu taho da Madina…”

Yace yana kin hada ido da su, su yake son gani daman, kuma ya gan su, ko da can kalar baccin da yakeyi a gidan Daada ya sha bamban da na ko ina, bacci yake batare da tunanin komai ba. Yana son ko da na yau ne kawai kar ya hadu da Nanna.

“Muje Khalid, Allah ya kaimu goben. Daddy sai da safe”

Adee ta fadi tana kallon su Daada

“Daada sai Allah ya kaimu… Madina ina jiran ki”

Kanta da yayi mata nauyi Madina ta jinjina, bacci takeji ba dan kadan ba, ba zata tuna ranar karshe da tayi wannan daren ba. Julde ma mikewa yayi

“Nima ai tafiyar zanyi”

Dan tunda aka fara hidimar bikin ya tattara ya koma hotel da zama, har fada sukayi da Saratu kan hakan

“Daman kofa kake nema, in ba haka ba ko bangaren su Khalid ai zaka iya komawa”

Shine abinda ta fadi da ko amsa bata samu ba, saboda ba sai da biki ba, idan yaga dama zai iya kwanakin shi a hotel tunda ba zamanta yakeyi ba. Sai da Nawfal yaga Julde ya mike tukunna ya raba nashi jikin da kujera, tare duk suka fita, Daada iya bakin kofar daki ta raka su, Nawfal ne ya fita har kofar gida. Sai da su Khalid suka fara sannan Julde ya kalli Nawfal

“Menene? Me kake son fada mun?”

Da mamaki Nawfal yake kallon shi, murmushi Julde yayi

“Na sanka Bajjo, kana ta kallo na da na shigo, na san akwai abinda kake son fada mun…”

Murmushi Nawfal yayi, shisa a duniyar shi gabaki daya babu kamar su, sune kawai suke kula da kananun abubuwa haka a tare da shi

“Zai iya jira Daddy, abinda nake so in fada maka din… Zai jira sai an gama hidimar Adee…”

Numfashi Julde ya sauke.

“Ka tabbata?”

Ya tambaya a idanuwan Nawfal din yaga ko wacce irin magana ce ba ta rashin dadi ba ce ba, babu damuwa ko daya a tattare da yaron na shi.

“Daddy… Allah da gaske”

Murmushin dai Julde ya karayi

“To shikenan. Ka koma ciki, sai da safe”

Kiyawa Nawfal yayi, sai da yaga tafiyar Julden tukunna ya koma yana mayar da kofar gidan ya kulle hadi sa sauke wani numfashi da baisan yana rike da shi ba. Kamar yanda ya fada ne, tashi maganar zata iya jira har a gama bikin Adee.

*****

A tsaye ta fito ta same shi, ya mika mata hannu ya karbi jakar da take rike da ita, batayi musu ba ta mika mishi tana rugawa ta shiga kitchen, numfashi kawai Nawfal ya sauke, ya kai minti talatin yana jiranta, sai yanzun ya gane me yasa Daada tace mishi

“In dai Madina ce da ka samu waje ka zauna…”

Ko Salim ya kai minti sha biyar yana tsaye kofar gida, dan da tace ma Nawfal shi zai zo ya dauketa bai yarda ba har sai da yaga zuwan na shi, ita take kara bata lokaci shi gaban shi yake faduwa saboda Salim ne, Salim ne a waje yana jiran su. Zai fara tsayawa a cikin soron gidan Daada, idan yaji Salim din baiyi fada ba saiya fita, dan bai shirya a sauke mishi hayaniya da sanyin safiya ba. Ba zaice ga abinda ta kara tsayawa yi ba, amman a tsakanin kitchen da kuma dakinta sai da ta kara bata kusan mintina goma. Sannan ta sake komawa kitchen tana dauko wata karamar roba mai murfi ta fito.

Kai kawai Nawfal ya girgiza yana sata yin dariya.

“Daada… Mun wuce”

Ta furta saboda Daada ta koma daki, daga can tayi musu Allah ya tsare tana fada musu su ja mata gidan idan sun fita. Daga baya Nawfal ya tsaya dan ya hango Salim ya jingina kanshi da kujerar motar da alamar ya gaji da jira, yana kallo Madina ta bude

gaban motar, sai da yaji gaban shi ya fadi, musamman da Salim din ya dago yana kallon ta a kasalance.

“Oh goodness”

Nawfal yace yana matsawa baya, jira kawai yake yaji Salim din ya fara fada, amman ga mamakin shi zama ya gyara yana tashin motar, juyowa Madina tayi

“Hamma ka taho”

Kai ya daga mata yana takawa, kafin tayi wani motsi ya bude bayan motar ya shiga yana mayar da murfin ya rufe, dan babu wanda zai saka shi zama gaban motar Salim, yana kallo Madinar ta shiga ta zauna ta rufo kofar. Sai da Salim ya fita da motar tukunna ta fara korar shirun da fadin

“Doya da kwai na soya, ga naka na dibo maka…”

Dan kallon ta Salim yayi yana mayar da hankalin shi kan tukin da yake yi

“Shisa kika bata mun lokaci?”

Kai ta girgiza tana dariya

“A’a Allah, inata sauri fa, ko Hamma?”

Ta karasa maganar tana dan juyawa ta kalli Nawfal da ya sadda kan shi kasa, wannan labarin ba dashi za’ayi ba. Baya son ta fara tsoma shi ciki. Baisan me yake faruwa ba ko yanda akayi ta sa bakin Salim ya bude, ko yanda maganar ta bata mishi hayaniya cikin kunnuwa, amman shi yasan yana bude idon shi zaice yana ihu. Hirar Madina ta cigaba da yiwa Salim da yake amsata dai-dai. Suna karasawa cikin gida Nawfal na budewa ya fice daga cikin motar, yana sane da ko gaisawa basuyi da Salim ba, amman Salim ne in zaku hadu ka wuce ya wuce yafi mai wata gaisuwa da zakayi mishi.

Madina ma bai mata sallama ba ya wuce abin shi. Murfin motar ta kama da nufin fita itama Salim yace

“Ina zaki?”

Kallon shi Madina tayi

“Su Adda na ta jira na nasan”

Dan daga kafadun shi yayi

“Nima na jira ki ai, ina doyar?”

Inda ta ajiye ta dauko robar tana mika mishi

“Allah suna ta jira, karfe tara nace musu…na san zan kai dare kilan ban gama ba, zan ara wayar Adda in kiraka idan na gama”

Ta karasa maganar tana bude murfin motar ta fice kafin ma yace wani abu, baya ta sake budewa ta dauki jakarta da Nawfal yabar mata. Sannan ta wuce cikin gidan, numfashi Salim ya sauke yana juyawa ya ga har ta bace ma ganin shi, yanda gajerun kafafuwanta suke da sauri har mamaki yake bashi. Haka kawai yaji ganin tan da yayi ya mishi kadan, ko hirarta baiji da kyau ba. Sake kunna motar yayi yaja ta yana kara ficewa daga gidan dan ba zai zauna ba, hayaniyar tayi yawa. Gara yaje ya samu wani hotel din ya kira wata ko zata taya shi ya rabu da yanayin kewar Madina da ya dabaibaye shi.

Ita kuwa cikin gidan ta wuce, tana shiga cikin falon da sallama, Saratu ta fara gani da ta amsa sallamar da fara’a a fuskarta. Ko a cikin yaran idan taji ana cewa Salim baya son mutane abin baya bata mamaki, itama din ba wai mutane sun dameta bane ba, kafin jinin ku ya hadu akwai aiki. Idan wani ya ce mata me yasa take son Madina zata karyata, amman yarinyar ta shiga ranta tun ba yanzun ba, bata san me yasa bata zuwa gidan ba, lokaci zuwa lokaci tunanin ta yakan fado mata. Banda su Salim babu wani da zataji alkhairi zai shiga tsakanin shi da Julde da zataji ranta bai mata bakikirin ba sai Madina.

Tana kaunar yarinyar, irin kaunar nan da bata da dalili. Share muryar da taji a cikin kanta tana tambayar ta

“Anya kuwa? Kin tabbata babu wani dalili? Kaunar da kike mata bata da alaka da Yelwa?”

Tana kokarin dishe sautin muryar da yiwa Madina Magana.

“Madina ana ganin ki daman? Adee ta jawo mana ke ko?”

Dariya Madina tayi, “Nanna… Makaranta fa. Ina kwana… Ya hidima?”

Murmushin ta Saratu ta kara fadadawa, duk da yanayin muryar Madina din na son daukar tunanin ta zuwa abubuwan da ta zabi ta adana.

“Alhamdulillah…suna ciki suna jiran ki, amman da kin fara cin wani abu, an kawo waina yanzun nan”

Kai Madina take girgizawa.

“Sai dai anjima Nanna, doya naci wallahi”

Dan har bayan wuyanta take jin ruwan shayi na taso mata, wani irin koshi tayi na ban mamaki

“To shikenan…”

Har Madina ta wuce ta dan juyo

“Daada tace a gaishe ki”

Fara’arta dake fuskar Saratu sai da ta dan ragu, kai ta jinjina kafin dakyar ta iya cewa

“Tana lafiya?”

Da murmushi Madina ta amsata tana juyawa, karancin shekarun ta bai hanata fahimtar babu wani shiri mai karfi tsakanin Daada din da Saratu ba, kawai wasu tambayoyin bata san ta inda zata fara su ba, wasu tambayoyin tsoron amsar su na sakata sake adana su a cikin kanta. Amman kam tana da tarin tambayoyi, masu yawan gaske

“Sai yanzun? Karfe tara fa mukayi dake”

Muryar Adee ta katse mata tunaninta

“Afuwan Adda, inata hidima ne ashe lokaci yana tafiya”

Cewar Madina tana ajiye jakar hannunta a kasa dan duka kayan lallen suna ciki, tsugunnawa tayi ta kwance takalman da suke kafarta da sam sai lokacin ta tuna bata cire su ba. Kafin ta dago har Adee ta daukar mata jakar

“Ki kawo Adda”

Harararta Adee tayi

“Ni dai muje, ki dauko takalmin ki kafin a dinga bi takan shi ana wucewa”

Juyawa kuwa tayi tana daukar takalman nata ta rike su a hannu tabi bayan Adee har zuwa dakinta da alamu suka nuna duk an kwashe kayan ciki an bar gado kawai, dan dakin yayi fili sosai. Yan matane kusan su sha biyar, in dai kallo ne Madina ta saba da shi tunda inta fita har ta dawo bata cin karo da mace mai kalar shigar ta. Yau ma riga da wando ne, wandon na jeans ne baki, kamar ko yaushe ta nannade kafafuwan har kusan kwaurinta sai safa baka a kafarta. Akwai farar riga kal daga ciki, ta dauki mai dogon hannu ta dora a kai, tana jan hannun baya, sai yar karamar hijab da ta saka.

Ko gilashin fuskarta abin kallo ne, waje ta samu gefe ta zauna tana karbar jakarta a hannun Adee bayan tace ma yan matan da suke cikin dakin,”Sannun ku”

Rigar saman yellow ce, ita babu yanda za’ayi ta bata ta da lalle, amman tabbas a cikin yan matan nan ko wajen wucewa ne wata na iya shafar ta. Kunshin gidan biki ba bakonta bane ba. Shisa ta mike tsaf tana cire rigar tabar farar da tayi zanzaro da ita, ganin tana neman inda zata ajiye yasa Adee karba, saida ta ninketa sannan ta fice da rigar tana barin Madina da ta zauna zata fara hada lallen ta.

*****

Sai wajen tara da rabi tukunna ta samu suka barta, shima dan Salim da yake ta kiran wayar Adee ne, ita nata kunshin sai washegari ma da sassafe idan Madina din tazo ita zata fara yiwa tunda ranar ne ya kama alhamis kuma shine za’a fara bikin gadan-gadan, za’ayi kamu. Sai dai kowa yazo ya ga kunshin wasu sai yace shima za’ayi mishi, duk ta bar su a zuwan washegari idan ta gama yiwa Adee duk sai ta samu tayi musu. Nanna ta so ta kwana anan din tace mata tabar Daada ita kadai. Tunda take a rayuwarta bata taba kwana wani waje banda gida ba, bata ma jin zata iya kwana wani wajen.

Wata babbar leda Nanna ta cika mata da kayayyakin da batasan ko meye a ciki ba. Adee ta rike ledar tana rakata har wajen motar Salim din sannan ta bata kayayyakin tana mata godiya sukayi sallama, bayan motar Salim ta bude ta saka kayan ta rufe tana kowama ta bude gaban motar da kamar jira Salim yake ta zauna.

“Ke ba zaki iya ce musu dare yayi ba? Ba zaki ce kin gaji kina so ki tafi gida ba, ko baiwar su ce ke?”

Saboda yanayin ta kawai ya nuna a gajiye take, ko wayar farko daya kira wajen karfe bakwai aka bata yanayin muryarta akwai gajiya.

“Mutanen suna da yawa ne Hamma, shisa na tsaya na kara rarragewa, kanata kira da na kara yiwa ko mutum biyar ne kafin mu tafi tunda kai zaka mayar dani gida”

Kallon ta yakeyi kawai, itama kallon shi tayi, yanayin fuskar shi na sata kai hannu ta gyara gilashin ta.

“Dan Allah kar kamun fada Hamma, nagaji sosai Allah, kaji…”

Numfashi kawai ya sauke, ba fada bane baya son yi mata, surutun ne ba zai iya ba. Yana kallo ta rufo murfin motar tana yarfe hannun ta na dama tana mikar da shi kafin ta sake yarfe shi, tsintsiyar hannun take ji kamar bata tare da hannun ta saboda yanda yayi mata sanyi, kafin tayi wani motsi sai ganin hannun tayi cikin na Salim ya rike shi yana gyara zaman shi ya saka dayan hannun shi yana murza mata dai-dai tsintsiyar hannun, kafin ya bude daga gaban motar yana dauko wani abu cikin yar roba, sai da ya dangwalo taji yajin abin har cikin idanuwanta, murza mata yayi sosai a gabaki daya hannun nata har yatsu sannan ya sakar mata hannu.

Man ya rufe ya mayar inda ya dauko, wuyan shi yana yawan rikewa idan yayi zaman karatu shisa baka raba shi da irin wannan magungunan na shafawa, sai daya tayar da motar sannan yace mata.

“Saura ki murza idon ki”

Dan yasan abinda zata iya ne, murmushi kawai tayi tana jinta wani iri, ko dan yau dinne ranar farko da hannun shi ya taba nata. A kasan zuciyar ta take jin rashin kyautuwar da yake cikin hakan duk da Salim din Yaya ne a wajen ta, amman ba muharramin ta bane ba.

“Kishirwa nake ji Allah”

Ta fadi tunda zasu fito taso ta cewa Adee zata sha ruwa sai ga Nanna kuma, sai ta manta.

“Akwai ruwa ki dudduba”

Salim ya furta yana jin muryar shi ta fito a bude. Sake rike matukin motar yayi gam ko zai samu zuciyar shi ta natsu waje daya. Mata ne kalar duk da yaso zai samu, daga lokacin daya fara binsu zuwa yanzun ba zai kirga hannuwan da ya murza ba. Ko yau hannun mata biyu ne suka shiga cikin na shi, zuciyar shi batayi tsalle irin haka ba. Baiji kamar yana murza wani abu a cikin kirjin shi ba.

“Madina ce, Madina… Madina ce”

Shine abinda yake fadi cikin kanshi, ko bai duba komai ba zai duba karancin shekarun ta. Gudun motar ya kara ko zasu karasa da wuri.

“Hamma gudu kakeyi yau, sosai”

Ta furta muryarta na dan rawa saboda bata son gudu a abin hawa ko kadan, hankalinta tashi yakeyi, yanayin yanda sautin muryarta ya fito yasa shi rage gudun motar, badon tsoron ta ba sai dan nutsuwar shi da take neman rabuwa da jikin shi. Bai taba jin dadin hango kwanar gidan Daada irin yau ba, hannuwan shi har rawa sukeyi da ya sauke ta kofar gidan, tsaye yayi ta bude bayan motar ta dauki kayanta, sai da safen da tayi mishi ma da kai ya amsa mata ita. Sai da yaga shigar ta gida tukunna ya ja motar yayi kwana yana hawan titi da wani irin yanayi da bashi da kalaman da zai fassara shi.

<< Rai Da Kaddara 8Rai Da Kaddara 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.