Skip to content
Part 2 of 4 in the Series Ranar Birthday by Abba Abubakar Yakubu

Jikinta duk a sanyaye yake, tana tunanin yadda ta rungumo wannan hidima da ba ta taɓa yin irinta ba, duk da yake ta saba shiga a taimaka wajen shirya taro a makarantar su, inda take nazarin aikin kiwon lafiyar dabbobi, kuma lokaci zuwa lokaci idan ta samu hutu tana shiga aikin taimakawa a kungiyar Da’awah ta mata masu yawon wa’azi da faɗakar da ‘yan mata da ke shiga shekarun balaga a makarantun sakandire da ba su tallafin audugar tare jinin al’ada ta mata.

Ƙarar wayarta da ke fitar da sautin addu’ar Hafiz Ahmad Suleiman Kano ce ta farkar da ita daga zurfin tunanin da ta shiga, na karambanin da ta yi da kuma irin yadda mata za su fahimce ta kuma su karɓi abin da ta yi da kyakkyawar niyya.

Ta miƙa hannu ta ɗauki wayar da ke kusa da ita, yayin da fuskarta ta cika da murmushi ganin sunan mai kiran a jikin fuskar wayar, an rubuta HUBBI, a cikin zuciyarta ta gane wanene ta sa wa wannan suna, masoyinta ne abin ƙaunarta da take da matuƙar burin aurensa nan da wani lokaci kaɗan, idan Allah ya yarda, wato Ayman.

Cikin sansanyar murya tare da lumshe idanu ta amsa wayar da fadin, “As Salamu Alaikum, amincin Allah ya tabbata gare ka, farin cikina.”

“Wa Alaikumus Salam, kwanciyar hankalina.”

“Hmm!”

Murmushinta ya sake faɗaɗa tare yin wata ‘yar dariya.

Ayman ya cigaba da magana, “Yaya shirye shirye? Ina fatan an kammala komai cikin yardar Allah.”
Ta ce, “Wallahi, Alhamdulillah. Komai ya kammala, ban jima da barin wajen ba, na dawo gida ne in shirya, sannan mu ta fi da su Ummi.”

“Lallai, buki ya yi albarka. Har da su Ummi.”
“Ai Abba ne ya ce duk su je su mara min baya, don in samu ƙwarin gwiwa.”

“Masha Allah. Abu ya yi kyau. Kin san ai ke ‘yar gatan Abba ce. Yana bai wa duk wani abu da ya shafe ki muhimmanci…Mu ne dai za a yi babu mu!” Ya ƙarasa maganar a sanyaye, kamar abin tausayi.

Ita ma ta taya shi da cewa, “Ba damuwa ai zan turo maka hotuna a waya, kuma na gaya wa Zinatu za ta ɗaukar min taron a waya, saboda in turo maka ka gani.”

“Hakan ma ya yi kyau. Allah dai ya sa a yi lafiya a gama lafiya.”

Ta ɗan yi ajiyar zuciya, sannan ta ce masa, “Ni dai bakina ba zai gaji da yi maka godiya ba. Allah ya saka da mafificin alheri. Ummi ma ta ce a yi maka godiya.”

Ya ce, “Ni ban cika son kina min godiya kan irin waɗannan ƙananan abubuwan ba. Idan ban taimaka miki ba, wa zan yi wa, kuma abu ne ki ka shirya na alheri, wanda zai ƙara wa addinin Musulunci martaba da kima, ya kuma taimaki al’umma.

Tilas in mara miki baya nima!”

Ta kara maimaitawa, “Na gode.”

“Wai ɓata lokacin me kuma ki ke yi ne a ɗaki, tun ɗazu fa ki ka fito daga wankan nan, kowa ya shirya ke ake jira.”

Muryar mahaifiyarta ta jiyo daga falo tana mitar daɗewarta a ciki tana shiryawa. Ko da yake ita dama kurarta ta daɗe da yin kuka, don kowa ya santa da nauyin jiki da nawa wajen shiri, musamman idan ta shiga wanka, sai mutum ya je kasuwa ya dawo ba ta gama wanka ko shiryawa ba.

Cikin murya mai kamar raɗa ta yi sallama da masoyinta, wanda hirarsu ta ɗauke mata hankali ta manta da masu jiranta.

Allah ya jarabci zuciyarta da son Ayman wanda suka jima tare suna soyayya tun tana aji biyu na babbar sakandire. Ya so a ce an ɗaura auren su da ita bayan ta gama makaranta, amma mahaifinta ya ƙi amincewa, kan sai ta samu akalla diploma kafin ta yi aure.

Saboda ba ya son wani abu ya katse mata karatun ta, ko kuma ta yi aure da ƙuruciya ba ta da wata madogara, a ƙarshe ta zama abin tausayi a gidan miji.

Ayman matashi ne mai kimanin shekaru 32 a duniya, yana da ilimin addini da na boko, ga sanin darajar manya da kula da addini. Fari ne mai matsakaicin tsawo, ga fara’a da sakin fuska.
Mahaifin Ayman, Alhaji Babayo Abdullahi, babban ɗan siyasa ne, ya ma taɓa riƙe muƙamin Babban Sakataren Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Filato. Yana da arziƙi da kadarori daidai gwargwado, kuma mutum ne mai kishin ya ga yara maza da mata na karatu.

Shi ya sa ko da mahaifinta ya dakatar da batun aurenta da Ayman shi ma ya goyi bayan cigaba da karatun nata, ko da yake ya so a yi auren, idan ya so sai ta cigaba da karatun daga ɗakin mijinta. Amma dai babanta ya nuna bai gamsu ba, sai dai a bari ta samu shaidar makarantar gaba da sakandire.

Ta mayar da wayar ta ajiye a wajen da take a da, sannan ta miƙe ta ɗauko wata rigar ta mai kamar alkyabba ta ɗora a kan doguwar rigar da ta sa. Ta sake kallon madubi yayin da take daidaita rigar a jikinta. Ba ta cika yin irin wannan shigar ba, saboda rashin fadin rigar sosai, domin ta lura kamar tana dan fitar mata da fasalin jikinta.
‘Amma hakan ma bai baci ba.’ Ta fada a ranta, a daidai lokacin da wayar ta sake ƙara, ta juyar da kallonta zuwa fuskar wayar.

ZINATU

“Aunty, har yanzu ba ku fito ba ne? Ku ake jira fa!”

<< Ranar Birthday 1Ranar Birthday 3 >>

1 thought on “Ranar Birthday 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×