Skip to content
Part 1 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Matashiya

Karka yi tunanin abinda ba za ka samu ba. Za ka kasance marar wadatar zuciya. Ka yi tunanin abinda ka samu, ka zama mai gode ma Allah. Karka kalli wanda ya ke gaba da kai. Ba za ka taɓa jin daɗin inda kake tsaye ba. Ka duba wanda yake ƙasa da kai, Naka matsayin zai maka daɗi. 

Karka duba baiwar wani da ba ka da ita. Ka duba wanda ba shi da kalar baiwar da kai kake da ita. Rayuwa zata zame maka da sauƙi. Allah ya datar damu. Amin. 

“Ka nutsu don girman Allah. Ba ka san wai gidan nan cike yake da mutane ba?”

Tayyab ke faɗi yana kallon Dawud da ya san kuiris yake da birkice musu. Numfashi yake ja ta hancin shi yana fitarwa ta baki. Har lokacin idanuwan Tayyab na yawo a fuskar Dawud ɗin a tsorace da abinda yake gani. 

“Bana son ganin shi Tayyab. Waya faɗa mishi yana da damar yanke min hukunci?”

Dawud ke faɗi muryarshi a dakushe. Kai Tayyab ya ɗaga cikin nuna mishi ya yarda da maganarshi tare da faɗin, 

“Na sani. Don girman Allah da matsayin Ummi za ka yi haƙuri a gama bikin nan lafiya. Ummi za…..”

Katse shi Dawud yai da faɗin, 

“Karka faɗa min abinda Ummi zata so da wanda ba zata so ba Tayyab. Kasan don ita kaɗai nake zaune a gidan nan. Don ita kaɗai nake shaƙar iska a ƙarƙashin inuwa ɗaya da Shi”.

Yadda ya faɗi kalmar ‘shi’ ɗin ya sa wani abu matsewa a ƙirjin Tayyab. Sai dai yasan furta abinda yake ji ba zai yi amfanin komai ba. Zai ma iya ƙara musu matsaloli ne. 

“Na ji dai. Yanzun ka wuce ka shirya. Ka ga lokaci na ƙurewa, ƙarfe huɗu muka so a fara program ɗin nan wallahi.”

Kallon me kake nufi Dawud yake ma Tayyab. Scowl ɗin da ke fuskarshi yana ƙara zurfafa. Da mamaki Tayyab ya ɗora da faɗin, 

“What is with the look? Kana min kamar ba ka san da maganar ba.”

“Na san da maganar. Kai ne kake yin kama ban baku amsa ta ba wata biyu da suka wuce.”

Girgiza wa Dawud kai Tayyab yake yi. 

“Kar ka ce min da gaske kake nufin maganar ka please. Ba Za ka yi mana haka ba.”

Juya idanuwanshi kawai Dawud yayi. Ya raɓa ta gefen Tayyab yana wucewa da faɗin, 

“Zan ɗan kwanta.”

Buɗe baki Tayyab ya yi da niyyar magana Dawud ya katse shi da faɗin, 

“Raina a ɓace yake. Don’t…..just don’t.”

Mayar da bakinshi yayi ya rufe yana bin Dawud ɗin da kallo har ya bar falon. Sauke numfashi Tayyab ya yi ba don abinda yai ɗin ya bashi mamaki ba. 

Sai don rasa mutum mai kalar halayya irin na Dawud ɗin. Ya ɗauka zai canza tunda bikin nashi ne wannan karan.

Yasan me zai yi. In akwai wanda yake jin zai iya lanƙwasa Dawud ya yi abinda baya so El-Labeeb ne. Wayarshi ya zaro daga cikin aljihu. 

Key ɗin jiki yake cirewa ya ji motsi. Da sauri ya ɗago ya sauke idanuwanshi kan Zulfa. Nazarinta yake yi. Idanuwanta sun zurma ciki kamar wadda tai kwanaki bata yi bacci ba. Ga wani irin haske da ya ga ta ƙara yi. Idanuwa suka haɗa tai saurin sauke nata. 

“Lafiyarki kuwa?”

Ya buƙata. A daburce ta amsa shi da,

“I am ok.”

Yanayin amsarta kawai ya sake tabbatar mishi da ƙarya take. Sai dai ba yanzun bane lokacin da ya dace ya matsa ta da jin ko menene. 

“Ya naga baki shirya ba. Kunsan huɗu har da mintina talatin Zulfa. Ya kamata ace kuna can wallahi.”

Runtsa idanuwanta ta yi . Ta buɗe su da alama sai lokacin ma ta tuna da maganar wani party. Muryarta babu alamar komai ta ce, 

“Nasan su Mardi na can. Kayana ma suna wajenta. Bara na kira Aseem in basu tafi ba su sauke ni.”

Kai kawai Tayyab ya ɗaga mata ya ci gaba da danna wayarshi bai ma ko kula da ajiyar zuciyar da Zulfa ta sauke ba kafin ta wuce tana fita daga falon. 

**** 

Yana shiga ɗakinshi ya kwanta. Rufe idanuwanshi ya yi. Wani irin zafi yake ji a ƙirjinshi. Maganganun mutumin da yake kokawar kira da mahaifinshi na mishi yawo. 

“Ko ka so ko karka so ba za ka taɓa sake matsayina a wajenka ba. Idan kana ganin rashin girmama matsayin zai canza shi ka ci gaba da ƙoƙarin yin hakan.”

Janye kanshi ya yi daga kan pillow ɗin yana amfani da shi ya toshe kunnuwan shi ko hakan zai sa ya daina jin muryar mutumin nan cikin kunnen shi. Yasan dawowa gidan nan matsala ne. Baya son ganin shi sam. Baya son jin muryarshi. Baya son yana mishi magana kamar akwai wata alaƙa a tsakaninsu. 

Ba zai iya irin haƙurin Ummi ba. Baisan yadda take manta duk abinda mutumin nan yai musu ba. Pillow ɗin ya janye yai jifa da shi yana miƙewa zaune. 

Kanshi ya saka cikin hannuwanshi. Irin matsalar da ake samu kenan da ya haɗa idanuwa da mutumin nan. Inda bai ganshi ba da yanzun yana cikin nishaɗi abinshi. 

“Yumna….”

Ya furta a fili. Wayarshi ya shiga duddubawa. In ya ji muryar Yumna zai ɗan samu nutsuwa. Wayar ya ɗauko ya kunnata don a kashe ma take. 

Tana gama loading lambar Yumna yai dialing, wayarta a kashe take. Kamar hakan zuciyarshi take jira. Ya rasa madafa, ta ɗauke shi ta watsa shi shekaru goma sha biyar da suka wuce. 

****

“Fitar min daga gida. Munafuka!”

Kuka take tana riƙe rigarshi. Hannu ya saka ya ɓanɓareta ya hankaɗata, ta faɗi ƙasa ba tare da ya duba tsohon cikin da ke jikinta ba. Wata irin ƙara ta saki tare da dafe cikinta tana kiran sunayen Allah duk wanda suka zo bakinta. 

Zufa ke tsattsafo mata saboda azaba. Dawud da ke tsaye hannunshi riƙe da Sajda da ke wani irin kuka ya ajiye ta ya ruga yana kama Ummi. 

A ruɗe yake faɗin, 

“Ummi…. Ummi tashi don Allah. Ummi sannu!”

Alhaji Haruna da ke tsaye babu alamar tausayi ko kaɗan a fuskar shi ya ce,

“Bana son ganinki. Bana son ganin su suma. Wallahi ji nake kamar in yi ihu in na ga ko da giccin ku a gidan nan. Ku fita ku bar min gida…..”

Kallonshi Dawud yake yana riƙe da hannun Ummi da har lokacin salati kawai take yi. Kafin ya mayar da hankalin shi kan matar da ta shigo rayuwarsu ta tarwatsa komai. Kamar jira take Dawud ɗin ya kalle ta ta ce,

“Alhaji na bana so kana ɗaga muryarka akan wannan banzar. Yau dai komai ya zo ƙarshe. 

In ka ce ta tafi ai dawowa zata yi, hmm wannan mayyar kuma.”

Juyawa ya yi, yadda ya yi mata fara’a za ka rantse da Allah ba shi bane ya gama rashin mutunci yanzun. 

“Wallahi kuwa Hajiyata. Bana son ganinta ko kaɗan.”

Wani murmushin nasara ta yi. Tana kallonshi ya juya da tsana da ƙyamata a muryarshi ya ce, 

“Na sake ki saki ɗaya. Ki tattara ki bar min gida. Ki nemi uban cikin da ke jikinki. Wannan yaran ma da bani da tabbas akan su ki kwashe su ku yi gaba…!”

***

Ƙwanƙwasa ƙofar da Dawud ya ji ana yi da ƙarfi ne ya katse mishi tunanin da yake. Hannu ya sa yana fifita fuskarshi saboda yadda iskar ɗakin ya ji ta kasa wadatar da shi. 

****

Gashin kan shi yake tajewa ya ji hannuwan Ateefa kan ƙugunshi. Ta kwantar da kanta a bayanshi. 

Murmushi ya ƙwace mishi. Kamo hannunta yayi yana zagayo da ita gabanshi suka fuskanci juna. 

“Tee…”

Ya kirata can ƙasan maƙoshi kamar yadda yakan yi in yana cikin yanayin ƙaunar ta da har mamaki yake bashi. 

“Na ga kana ta sauri ba tare za mu tafi ba?”

Girgiza mata kai yayi. 

“Tayyab ya kira ni. Wai Don ba za shi ba. Kin san halinshi dai. Zan je in ɗauko shi sai in same ki acan.”

Shagwaɓe fuska ta yi. Bata son shiga taro ba tare da shi ba. Bata son yin nisa da shi ko kaɗan in ba dole ba. Ta fi son shi kusa da ita ko da yaushe. 

“In ba tare muka je ba mutane ba za su bar min kai ba.”

Murmushi yayi har dimple ɗin da ke fuskarshi ya loɓa. 

“Labeeb naki ne Tee. Mutane ba kowa suke samu ba sai El-Maska. Kuma munyi ƙoƙarin making abun da mutane kaɗan.”

Duk da ta ji daɗin maganarshi bai hanata faɗin, 

“Na sani. Duk inda kake ba a iya rage yawan mutane. Ka kula da kanka don Allah.”

Sumbatar ta yai a kunci kafin ya tsugunna ya sumbaci cikinta. 

“Ki kula min da ku. Da na ɗauko Don za mu taho muma.”

Kai ta ɗaga mishi alamar ta fahimta. Kafin da wani irin sanyin murya ta ce mishi,

“Na kasa yarda mu ne a wannan matsayin Labeeb. Na kasa yarda farin cikin nan mai ɗorewa ne. Na…..”

Ɗan yatsa yasa ya rufe mata laɓɓanta. Idanuwanshi cikin nata da wani irin yanayi yake faɗin, 

“Bana so Tee. Bana son kina irin wannan maganganun. Me zai hana farin cikinmu ɗorewa?”

Ta rasa dalilin da ya sa hawaye cika mata idanuwa. Wani abu take ji a zuciyarta da ta rasa inda zata ajiye shi. Bata san meye fassarar hakan ba. Ta kasa yarda cewar zunubansu sun gama wankewa. Mintsini ta ji a kuncinta. 

Muryarshi a dake ya ce, 

“Bana so Tee. Bana son tunanin nan. Ki yarda da ni mana.”

Hannunshi da ke kuncinta ta kama tana dumtsewa cikin nata. 

“Ba daga yarda da kai matsalar take ba. Da ban yarda da kai ba da yanzun babu ajiyarka a jikina kasan hakan.”

Ta amsa shi tana tabbatar da ya karanci gaskiyar maganganunta. 

“To menene matsalar?”

Ya tambaya da gajiya a muryarshi. Ya ɗauka irin wannan maganar ta gama giftawa a zamansu. Murmushi tai mishi da yasan bai kai zuciyarta ba. 

“Mu bar maganar nan ƙar ta ɓata mana mood. Yau ranar Dawud ce ba tamu ba.”

Duk da ba hakan yaso ba. Yasan gaskiya ta faɗa mishi. Sumbatarta ya yi tare da tallabar fuskarta cikin hannayen shi yana son tabbatar mata komai zai daidaita. 

Kafin ya sake ta ya ɗauki malfar shi da ke ajiye kan gadon ya saka saman kanshi. Kallonshi Ateefa take yi, yai mata kyau. 

Suspenders ne a jikinshi. Wandon baƙi sai rigar ja. Sun matukar amsar jikinshi.

“Kayan sun maka kyau.”

Ɗaga mata girar shi yayi. 

“Kayan ne sukai min kyau ko ni naima kayan kyau?”

Tsayawa tai jim tana matse baki. Alamar tunani take. Ganin ya nufota yasa ta rugawa da gudu tana nufar ƙofa. 

“Tee ki bi made n yaro a hankali. Oh my God. Wai yaushe za ki girma ne?”

Ai ko saurarenshi bata yi ba ta buɗe ɗakin tana dariya ta fice. Girgiza kai yayi da murmushi a fuskarshi har ya ɗaura Rolex ɗin shi ya fita. 406 ya ɗauka. Gaba ɗaya gilashin jiki tinted ne. Don yasan babu wanda zai zace shi a kuaramar mota. Duk da in Ateefa ta sani rikici za su yi. 

Hakan kawai ya sa murmushin da ke fuskar shi faɗaɗa. Ya gaji da yawo da securities. Yau shi kaɗai zai fita abinshi. 

*****

Tunda yai parking cikin gidansu yake jin hayaniyar mutane. Ya lumshe idanuwanshi ya buɗe su. Malfar da ke kanshi ya sake ja ya rufe kusan rabin fuskarshi. 

Ya taka zuwa cikin gidan. Yana jin idanuwan mutane na yawo a kanshi. Ba baƙon abu bane hakan amma ya kasa sabawa. 

Bai kalli kowa ba. Asali ma idanuwanshi kafe suke a ƙasa, inda yake saka ƙafafuwanshi kawai yake kallo. 

Har ya ƙarasa part ɗin su Dawud. Kanshi tsaye ya shiga ba tare day yai sallama ba. 

“Isasshe ai na san sai kai ɗin. Babu sallama balle gaishe da mutane.”

Malfar da ke kanshi ya tura baya. Ya kalli Beeba da ke maganar. Ya tsani matar nan kamar yadda yasan ta tsane shi. Tafiya ya ci gaba da yi kamar bata yi magana ba. 

“Mai baƙin hali kawai.”

Juyowa yayi. Matar nan na da wata baiwa ɗaya. Ta iya zuwa wuyan mutane tai tsaye. Abokin tayi take nema shi kuma ba shi da lokacin biyeta. 

Lungun da zai kai shi ɓangaren Dawud ya bi. Bai damu da ya ƙwanƙwasa ba sai da ya tura ya ji shi a kulle sannan. 

Ya ƙwanƙwasa ya kai sau biyar shiru. Yasan yana cikin ɗakin. Don haka ya sake ƙwanƙwasawa da ƙarfi wannan karon. 

Ganin ana murɗa handle ɗin ƙofar ya sa shi sauke hannunshi. Buɗewa Dawud yayi fuskar shi cike da masifa. Ganin El-Labeeb ɗin ne ya sa shi jan wani numfashi yana sauke wa. 

“El. Kawai…..”

Kasa ƙarasawa Dawud yayi saboda kanshi da ke wani irin sarawa. Jiri ya ji yana ɗibar shi ya dafa ƙofar ɗakin. 

Da sauri El-Labeeb ya kama hannunshi. Janshi yai suka ƙarasa cikin ɗakin. Ya zaunar da shi kan gadon. 

“Lafiyar ka kuwa?”

Girgiza mishi kai Dawud yayi. Sai da ya ɗan ɗauki mintina kafin ya iya cewa, 

“Bana son ganin su El. Bana son jin muryarsu. Matsala za a samu idan ina ganin su.”

Cikin taushin murya El-Labeeb ya ce, 

“Kalle ni nan.”

Ba musu ya ɗago kai ya kalli El ɗin. 

“Ya muka yi da kai? Alƙawarin me ka ɗaukar min?”

Sake yatsine fuska Dawud yayi. Babu walwala a fuskar shi ya ce, 

“Ina iya ƙoƙari na. Ina gaishe da shi. Ba shi da right ɗin shigar min rayuwa ne kawai. Saboda me zai zaɓar min inda zan zauna? Na ce ina buƙatar…..”

“Ka rufe min baki a wajen nan. Yaushe za ka gane ba zaka iya canza abinda ƙaddara ta rubuta ba. Ka taɓa ganin an sake Uba?”

Ƙasa-ƙasa Dawud ya ce, 

“Za a fara ta kaina.”

A ƙufule El-Labeeb ya ce, 

“Magana ka yi?”

Girgiza kai Dawud yayi. 

“Good. Ka tashi ka shirya mu tafi. Lokaci na ƙurewa.”

Ƙafafuwanshi Dawud ya ja kan gadon yana gyara zama. 

“Ba na ce muku ni bana son yin komai banda ɗaurin aure ba? Na faɗa ma Tayyab bazan je ba.”

Miƙewa El yayi yana ƙarasawa wajen wardrobe ɗin ɗakin ya buɗe yana duba ma Dawud ɗin kaya tare da faɗin,

“Ba tambayarka na yi ko za ka je ba ai. Cewa na yi ka shirya mu tafi. Akwai banbanci.”

Duba kayan ya ci gaba da yi. Babu komai sai baƙaƙen wanduna da fararen riguna ƙal da su . Runtsa idanuwanshi El-Labeeb yayi ya buɗe su. Muryarshi a fusace ya juyo ya kalli Dawud. 

“Wai baka da wani kaya sai baƙi da fari ne?”

Kauda kai gefe yai ya amsa da, 

“I hate colors.”

El kam ya gaji. Har yau Dawud baya gajiya da bashi mamaki. 

“Koma menene. Ka tashi ka shirya mu tafi. Za ka iya sassauta fushin da ke fuskar ka tunda ya samu wajen zama. It’s your wedding party saboda Allah Don.”

Miƙewa yayi. Yanajin yadda har lokacin kanshi ke sarawa. Yasan El sarai. Za su iya kai dare a wajen nan yana maimaita magana ɗaya. 

In ba shiryawa yayi suka tafi ba ba zai sama mishi lafiya ba. Ciwon kai ma zai ƙara mishi. Can bayan kanshi ya adana zai jama Tayyab kunne.Kar ya sake mishi irin wannan. Yasan shi ya haɗo shi da El ɗin. 

****

Kuka sosai Zulfa take yi. Jikinta babu inda baya kyarma. Da ƙyar Nabila ta iya kamata ta shigar da ita mota. Sannan ta zagaya ta shiga ta turo motar. Ita kanta babu nutsuwa a tattare da ita. Ta nemi hawayen ma ta ɗan samu sauƙi ta rasa. Kanta ta jingina jikin gaban motar. 

Sai da ta tabbata ta samu nutsuwar magana ta fahimta da Zulfa sannan ta ɗago. Hannu ta kai ta dafa ƙafar Zulfa da ta ɗago fuskarta jiƙe da hawaye. 

“Na shiga ukuna Nabi. Ya zanyi? Ta ina zan fara kallon yaya da maganar nan? Nabi mutuwa nake son yi. Wallahi gara naga ranar mutuwata da in kalli fuskar yaya da maganar nan……”

Ta ƙarasa zuciyarta na mata kamar zata tarwatse. Hannu Nabila ta sa tana goge ma Zulfa fuskarta. 

“Ki daina faɗin haka Zulfa. Don Allah ki bari. Mu yi abinda na faɗa miki kawai shi ne mafita.”

Da sauri Zulfa ke girgiza kai alamar bata yarda ba. 

“Laifukan za su yi yawa Nabi…”

Ringing ɗin wayar Zulfar ya katse mata managarta. Hannu ta sa cikin jakarta ta zaro wayar ta duba. Tayyab ne. 

Kallon Nabila ta yi idanuwanta na sake cikowa da hawaye. 

“Tayyab ne. Na shiga uku na. Ya zanyi nikam?”

“Get a grip. Ki nutsu ki ɗaga ki ce mishi muna hanya. Gidanmu kika biyo muka taho tare.”

Hannu zulfa ta saka ta goge hawayen da ke fuskarta tana jin wani yana sake zubowa. Zuciyarta na wani irin dokawa. Gani take tana ɗaga wayar Tayyab zai gane halin da take ciki. 

Mayar da wayar ta yi cikin jaka tana jin kiran ya yanke wani ya sake shigowa. Da ƙwarin da bata ji a jikinta ta ce, 

“Ba saina ɗauka ba mu je kawai.”

Cike da tausayawa Nabila ta ce, 

“Ko mu biya ta gida ki ɗan nutsu tukunna?”

Girgiza mata kai Zulfa ta yi kawai tana jin wani abu tsaye a zuciyarta. Ta kauda kanta gefe kawai. Tana jin nabila ta tashi motar suka tafi. 

****

Material less ne a jikinta. Light purple. Ɗinkin doguwar riga. Don shi ne anko ɗin partyn su na yau.

Fuskarta take kallo a mudubi tana tunanin yadda dole tana buƙatar heavy make up don ɓoye yanayin da ke fuskarta. 

Sam bata son wani ya gane halin da take ciki. Foundation ta fara ɗaukowa na sleek tana juya shi a hannunta. Idanuwanta take kallo ta cikin mudubin. 

Gaba ɗaya kanta take kallo ta cikin mudubin. Ita ɗin dai ce. Babu abinda ya canza a tattare da ita daga waje. Mardiyya ce. 

Saidai tana jin daga ciki abinda ya faru da ita ya girmi ta ɗora shi kan canji kawai. Kamar ya fi ƙarfin kalmar ita kaɗai kawai. 

Mutane da yawa na faɗar cin amana. Mutane da yawa na bada labarin rashin adalci. Mutane da yawa na bada misalin zalunci. Sai dai dukkan su suna bada labarin yadda wani yai musu ne. 

Ko yadda wani yaima wani. Ita tana mamakin yadda akanta akasin hakane. Cin amanar ba kowa yai mata shi ba sai zuciyarta. Rashin adalcin ba daga ko ina ya fito ba sai zuciyarta. 

Zaluncin ba kowa yai mata shi ba sai zuciyarta. Inda za a bata zaɓin sake wata da gudu zata karɓi tayin ba tare da tunanin komai ba. 

Sai dai ko da hakan ne ya faru a yanzun zuciyar bata tare da ita. Ta mata nisa mai zurfi. Zuciyarta na wani waje inda har yanzun ta kasa daina mamakin lokacin da abin ya faru. 

Zuciyarta na inda take ja ma su biyun wulaƙanci na fitar hankali. Shekara ɗaya data wuce inda wani zai ce mata hakan zata faru da ita dariya zata sha sosai saboda hango rashin yiwuwar abin. 

Amma yanzun komai ya canza. Ta tabbata inda za a buɗe ta. Ba ƙawayenta kaɗai ba. Harta ‘yan uwanta sai sun yi mamakin Mardiyyar da za su gani. 

Rayuwa ta canza ta. Ciwon da ta kamu da shi ya canza ta gaba ɗaya. 

“Ko da mata sun ƙare a duniya babu abinda zan yi da irinki Mardiyya. Kin ga wannan da kika raina? Wallahi jin muryarta na minti ɗaya ya fiye min kallonki na shekara guda. Bana sonki ko kaɗan. Idan na ce ina jin tsanarki ma na baki muhimmanci a rayuwata. Bana jin komai a kanki. Don Allah ki fita daga rayuwata!”

Lumshe idanuwanta ta yi hawaye masu ɗumi na zubo mata. Zuciyarta na mata ciwo marar misaltuwa. 

“Ta ya zan fita rayuwarka Danish? Ta ina zan soma bayan ka zame min rayuwa da kanta?”

Ta furta a fili tana saka hannu ta goge hawayen da ke fuskarta. Tasan maganganun shi za su ci gaba da mata ciwo na tsawon lokacin da bata sani ba. 

Miƙewa ta yi ta shiga toilet ɗinta. Fuskarta ta wanke ta fito. Haƙuri take bama abinda yai saura a ƙirjinta da yai mata haƙuri har ta dawo sai ta ji da shi. 

A daddafe ta samu ta ƙarasa kwalliyar. Mayafi ba damunta yaiba. Don haka ɗankwali kawai ta ɗaura ta ɗauki ƙaramar purse dark purple. Takalmanta ma kalar purse ɗin ne, ta ɗauki wayarta ta fice. 

A falo ta samu Mummy tana zaune. Tai mata murmushi. 

“Kinyi kyau daughter.”

Kasa mayar mata Mardiyya ta yi. Cikin sanyin murya ta ce, 

“Na gode Mummy. Ki ara min motarki in babu inda za ki je.”

Babu musu Mummy ta ɗauki mukullin da ke gefenta ta cilla ma Mardiyya. 

“Have fun.”

Kai Mardiyya ta ɗaga mata ta fice daga gidan. 

****

El na yin parking za su fito daga motar wayar Dawud ta soma ruri alamun kira na shigowa. Ɗauka yayi ya duba, Yumna ce. 

Ɗagawa yai ya kara a kunnenshi. Kukan da take ya hana maganarta fitowa. Ba baƙon abu bane a wajen shi, don haka ya ce, 

“Take a deep breath Yumna. Ki nutsu ki min magana yadda zan gane. Menene?”

Kallonshi El yake yi cikin ƙoƙarin fahimtar me ke faruwa. Yanayin fuskar shi ya soma canzawa cike da wani ɓacin rai kafin ya ce, 

“What?! Karki buɗe dakin nan kina jina. Ko me za su yi karki buɗe gani nan zuwa yanzun nan.”

Sauke wayar yayi yana maida numfashi da son controlling ɗin abinda yake ji. 

“Don?”

El ya kira cike da shakku. Ƙafa Dawud yasa ha harbi gaban motar da ƙarfi. 

“Wannan matar bata da zuciya a ƙirjinta. Bansan me take so da Yumna ba kuma. Ta gayyato wasu mutane ko me za su yi mata oho.”

Tayar da motar El yayi yana janta baya. 

“No. Ka zauna anan ɗin. Inje ni kaɗai sai in taho da ita. Kun tara mutane bai kamata a barsu ba. I got this.”

Kallon baka da hankali El yake mishi.

“Kai ɗin ne zan bari ka tafi kai kaɗai? Da wannan zuciyar taka? Ina da ɗaurin aure gobe in Allah ya kaimu. Ina son duk wata nutsuwa da zan samu. Bazan iya zirga-zirga wajen ‘Yansanda ba.”

Runtsa idanuwa Dawud yayi ya buɗe su tare da faɗin, 

“Ka yarda da ni. Ba abinda zai faru. Kawai zan je in taho da ita ne. Zan kiraka idan ina buƙatarka.”

Nazarin shi yake yana tauna maganarshi. 

“Promise me za ka yi controlling ɗin kanka?”

Kai Dawud ya ɗaga mishi. Sannnan ya buɗe motar ya fita. Tsaye yayi saida ya ga barin Dawud ɗin daga wurin tukunna ya ƙara yin ƙasa da malfar kanshi yana ɓoye fuskarshi. 

****** 

Yana shiga hall ɗin ya sauke ajiyar zuciya. Kamar yadda Tayyab ya faɗa mishi haka kuwa ya samu wajen. Mutane basu wuce hamsin ba. Kowanne cikin cousins ɗin su an bashi damar inviting mutum ɗaya don a rage yawan mutanen. Duddubawa yake ko zai hango Ateefa. Yawo yake da idanuwanshi kan matan da ke wajen. Sai dai maimakon Ateefa, Zulfa ya hango tsaye da ƙawarta da ya kasa tuno sunanta. 

Kamar ta ji a jikinta yana kallonta. Tana juyo ta sauke idanuwanta a kanshi. Da gudu take tahowa ba tare da ta damu da cewar cikin mutane bane. 

“Damn….”

El ya furta don yasan abinda ke shirin faruwa. Gefe yai da kanshi ko zai hango Ateefa. Sai jin Zulfa yai a jikinshi ta zagaye hannayen ta a bayanshi ta riƙe shi dam.

Ba don ya damu da kalar kallon da mutane suke musu ba. Ko abinda suke tunani kan Zulfa da ke manne a ƙirjinshi. Kamar yadda yasan itama bata damun ba. 

Yadai damu da abinda Ateefa za ta yi tunani. Dalon haka yasa hannuwanshi kan kafaɗun Zulfa ya ɗago da ita. Ga mamakin shi hawayene a fuskarta. 

“Ya Rabb. Zulfa…. Subahanallah. Menene?”

Yake tambayarta a ruɗe yana saka hannuwanshi duka biyun ya tallabi fuskarta. Ƙaunar da yake ma Zainab daban ce. 

Amma in aka zo cikin cousins ɗin su abinda yake ji akan Zulfa ba zai taɓa fassaruwa ba. Babu wanda ya zata ba zai aure ta ba. 

Kuka take da yake wani irin ci mishi zuciya. 

“Please Zulfa ki min magana. Ki faɗa min ko menene.”

Sam baya son inda tunanin shi ke son kaishi. Ɓacin rai yake ji yana taso mishi tun daga ɗan yatsan ƙafarshi kafin ya samu wajen zama a ƙirjinshi. 

Cikin idanuwanta ya kalla sosai. 

“Damn it. Ki min magana mana.”

Da ƙyar muryata na sarkewa ta iya ce mishi,

“Komai ya ƙare…..i know…. Mistake… Na… Na….bansan ya zanyi ba.”

Ta ƙarasa wani sabon kukan na sake cin ƙarfinta. Don duk abinda take ta dannewa a satin nan ganin shi da ta yi yasa ya taso ya mata wani irin dabaibayi. Zata iya ɓoye damuwarta daga wajen kowa. Har Dawud. Amma tare da El ko wanne sirri nata a buɗe yake. 

Ta soma saka mishi ciwon kai. Zai iya karantar koma menene a fuskarta babba ne. 

“Ki min magana yadda zan fahimta. Ko mu bar wajen nan muyi magana a waje?”

Ya buƙata. Kai ta ɗaga mishi. Fuskarta ya saki. Ya kama hannunta yana janta su bar wajen kamar daga sama ya ji muryar Ateefa. 

“Ashe ka zo…”

Yana jin kishin shi a muryarta. 

“Tee…..”

Ya fara. Zulfa ta goge fuskarta tana katse shi da faɗin, 

“Kinga magana kawai za mu yi. Bana son matsala.”

Kallon ta Ateefa ta yi sannan ta mayar da dubanta zuwa hannun mijinta da yake riƙe da na Zulfa kafin ta tsayar da idanuwanta akan fuskarshi. Bata ce komai ba ta juya. Sauke numfashi yayi. Blood first ya faɗi cikin kanshi yana jan Zulfa suka fice daga hall ɗin. 

***** 

Wani abu ne kamar ƙwallo tsaye a maƙoshinta. Bata san har yaushe zata daina fuskantar matsala ta ɓangaren Zulfa ba. Farkon auren su da Labeeb ɗin ta sha mamakin dalilin daya sa ya aure ta bai auri Zulfa ba. Yana da cousins mata.

Ga su Mardiyya nan. Amma ranar farko da ta fara ganin su da Zulfa ta fuskanci ƙaunar da ke tsakanin su mai girma ce. 

Tasan bata isa ta raba su ba. Sai dai hakan baya hanata jin kishin Labeeb har ƙasan zuciyarta. Kuma daga shi har zulfar basa kunyar riƙe hannayen juna ko a gaban wa. 

Muharraminta ne. Amma babu inda ya halatta musu hakan, in har da ƙaunar da ta wuce ta ‘yan uwantaka a tsakanin su. Ya sha ƙaryatawa cewan yana jin Zulfa kamar zainab ne. 

Ta rasa dalilin daya sa ta kasa yarda. Balle yanayin da take ji yau ɗin nan. Tana ganin su tare tsoro ya sake kamata. Basu jima da samun kwanciyar hankali ba. 

Basu jima da samun ‘yar nutsuwar nan ba. Abu kaɗan zai iya birkita lissafin su. Foundation ɗin da suka gina rayuwarsu da Labeeb ba mai ƙwari bane ta sani. 

Siraran hawayen da suka zubo mata ta sa hannu ta goge. Kafin ta ji an rufe mata idanuwa ta baya. Wani kasalallen murmushi tayi. 

“Zainab yaushe za ki girma ne?”

Dariya ta yi tana sakin fuskarta ta zagaya suka fuskanci juna. 

“Ina ta nemanki tun ɗazun. Come on. Anata having fun banga favorite couples ɗina ko ina ba.”

‘Yar dariya Ateefa ta yi. Zainab ta kama hannunta tana janta. 

“Ki taho Aunty. In-Law ɗinki yake son ku gaisa shi ne na zo neman ki.”

Ba musu Ateefa ta bita. Don tana buƙatar distraction ɗin. 

***** 

Jikin wata mota ya jata ya jinginar sannan ya saki hannunta. Ranshi a ɓace ya ce, 

“Ina fatan ko menene yana da muhimmanci saboda na zaɓe shi akan matata….”

Bata yi ƙoƙarin tarbe hawayen da suka zubo mata ba.

“Matarka ta tsane ni.”

Ɗaga mata kai yayi. 

“Ki faɗa min abinda ban sani ba. Ina jinki.”

Idanuwan shin nan ya tsura mata. Fuskar shi babu alamun wasa. Wani yawu ta haɗiye. Fuskantarshi zata fi mata sauƙi akan Dawud. Rufe idanuwa ta yi tana tattaro duk wani ƙwarin gwiwar da take da shi kafin ta furta kalaman da ta san za su canza komai. Kalaman da ta san su ne ƙarshe wajen tarwatsa abinda ya rage na rayuwarta da mutanen da take da kusanci da su. 

Kafin ta buɗe idanuwanta ta tsayar da shi akan fuskar El. 

“Ciki nake ɗauke da shi, wata uku!”

Kallonta yake kamar abinda ta fada da wani irin yare da baya fahimta ta faɗe shi. Kallonta yake yi yana son gane ma’anar maganganunta. Hannuwanshi ya ɗaga ya dafe kanshi kamar yana juya mishi. Sannan ya sauke su. Gaba ɗaya so yake ya fahimci abinda take nufi. Amman kamar wani abu ya toshe mishi ɓangaren da ke da alhakin tauna maganarta. Yakai mintina biyar a hakan. Ya kai ya dawo. Ya kalleta. 

Zuciyarta wani irin dokawa take cike da tsoro da fargabar abinda zai biyo baya. Zata rantse tana jin agogon sauran lokacin da ya rage mata yana harbawa cikin kanta.

Rayuwarmu 2 >>

1 thought on “Rayuwarmu 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.