Wani numfashi ya ja ya fitar da shi a wahalce kafin ya saki handle ɗin ƙofar tukunna ya ƙarasa inda su Tayyab suke, Zulfa ta soma tasowa ta kama hannunshi.
“Yaya Ummi ta haihu?”
Kallon Tayyab yayi. Bai furta ba, amma yanayin shi ya nuna cewa shima kalar tambayar da ke bakinshi kenan. Girgiza musu kai yayi, wani abu na mishi tsaye a ƙirji.
“Ku zo mu je.”
Ya faɗi, muryarshi a dakushe. Ba musu suka bishi har ɗakin da Ummi take. Babban ɗaki ne da gadaje guda biyu a ciki. Sai kujerun zama har guda shida.
Ummi ce kaɗai a kwance kan gadon. Sai Dawud ya ga kamar cikin da ke jikinta ya ƙara wani irin girma. Su duka suka ƙarasa inda take suka ja kujeru suka zauna.
“Ummi sannu.”
Da ƙyar ta yi musu murmushi, ta wahala, bata jin ƙarfi ko kaɗan a jikinta.
“Ko kina son wani abu?”
Tayyab ya buƙata. Zulfa kuma hannun Ummi ta kama ta riƙe shi dam cikin nata, ƙoƙarin haɗiye iye kukan da yake zo mata take yi.
Tambayar Tayyab ta yi ma Ummi tsaye, abu ɗaya zuwa uku take buƙata a yanzun, na farko Auwal, tana buƙatar mijinta a kusa da ita.
Tana buƙatar kulawarshi kamar yadda ya saba a haihuwar dukkan su, tana son abinda zata haifa ya zamana addu’ar Abba ya ji cikin kunnuwanshi.
Shi ya yi mishi huduba, in da Auwal kusa da ita a yanzun zata ji kamar sun raba wahalar ne. Yau ta fi jin zuciyarta cike da wani irin kaɗaicin shi.
Cikin zuciyarta ta ce,
“Allah na yafe ma Auwal duk wani laifi da yai min, wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah Ka yafe mishi, Ka ceto shi daga halakar da ya faɗa….”
Abu na biyu da take buƙata shi ne ta ga Sajda, bata san me yasa take son saka idanuwanta akan Sajda ba. Abu na uku da take buƙata shi ne ace wani cikin kawunnanta ko wanda suka haɗa jini ya zo.
Sai dai tasan ba zai yiwuwa ba, domin ba su damu ita ko ‘ya’yanta ba ko da can ma. Bata san dalilin da zai sa su fara ba a yanzun ɗin.
“Ummi….”
Zulfa ta sake kiranta a karo na huɗu, tana katse mata tunanin da take. Cikin idanuwa ta kalli dawud.
“Ka kawo min Sajda in ganta Dawud , ka je ka faɗa ma Abban ku ko ba zai zo ba, mu sauke haƙƙin shi da yake a kanmu…….”
Ko bata furta ba yasan abinda take son faɗa amma kalaman sun maƙale mata. Kai ya ɗaga mata tare da faɗin,
“Bari in tafi yanzun Ummi, Allah ya baki lafiya.”
Su duka suka amsa da amin. Hankalinshi ya mayar kan Tayyab.
“Ka kula da zulfa”
Da kai ya amsa shi, hannun Ummi da ke cikin na Zulfa Dawud ya kama, ya sumbata yana jin ƙaunar Ummi da bai haɗata da ta kowa ba a zuciyarshi na ƙara yawaita.
Sannan ya fita daga ɗakin yana ja musu ƙofar, bayanshi ya jingina da bangon wajen. Kokawa yake da zuciyarshi. Bai ce ba zai sake ganin Abba ba. Amma bai taɓa kawo ma ranshi zai ganshi nan kusa ba.
Duk abubuwan nan da suke faruwa sun saka shi danne abinda yake ji kan Abban. Yanzun tunanin ganinshi ya mishi magana, zuciyar shi rawa take sosai.
Jikinshi babu ƙarfi yake takawa har ya fita daga gidan. Mashin ya tarba ya hau zuwa Malali.
*****
Ƙwanƙwasawa yayi. Ya kai kusan shekara ɗaya rabon da ƙafarshi ta tako gidan. Yakan kai musu ziyara lokaci zuwa lokaci saboda Ummi na jin daɗin hakan.
Tunda yake sau ɗaya ya taɓa ganin matar kawun Ummi ɗin a gidansu, shi ne ranar sunan Sajda. Daga nan kuma bai sake ganin kowa ya zo ba.
Maigadi ya buɗe mishi, da alama ya gane shi don haka ya matsa mishi, gaishe da shi Dawud yayi a mutunce sannan ya wuce. Zuwan da yaima gidan ya fi a ƙirga.
Amma ya kasa daina mamakin girman shi. Duniya kenan, kowa da yadda Allah ya tsara mishi zai yi zama a cikinta. Haka ya taka har zuwa cikin babban falon gidan da sallamar shi.
Hajiya Uwani ya samu zaune da remote a hannunta. Sallama ya ƙara yi don a zaton shi bata ji bane. Ɗan juyo kanta ta yi, sannan kamar wadda aka yi wa dole ta amsa da ƙyar.
Takaici ya cika Dawud. In akwai abinda ya tsana a rayuwarshi bai wuce wulaƙanci ba. Sai dai akan Ummi zai iya jure komai. Farin cikinta ya fi nashi muhimmanci.
Gaishe da ita yayi. Nan ma da ƙyar ta amsa. Sai da ta ɗauki ɗan lokaci kafin ta ɗora da faɗin,
“Lafiya dai ko?”
Buɗe baki dawud yayi zai yi magana, dai dai sakkowar kawun Ummi daga kafar benen da ke cikin falon. Idanuwanshi kafe kan Dawud.
Gaishe da shi dawud yayi. Shima irin tambayar da Hajiya Uwani tai mishi ya maimaita. Ran Dawud ya kai ƙarshe wajen ɓaci. Koda Ummi bata son ana tayar da maganar, yasan wannan daular da ke saka su wulaƙanci fin rabinta dukiyar Ummi ce.
Muryar Dawud a dakushe saboda ɓacin rai ya ce,
“Ba komai. Dama Ummi ce take naƙuda, za a yi mata CS shi ne na ce bari na biyo na faɗa muku.”
Wani kallo kawun ya watsa ma Dawud, a gadarance ya ce,
“Kuɗin CS ɗin ne babu ko me?”
Miƙewa Dawud yayi, yana da na sanin zuwa ya faɗa musu. Sam basu damu da Ummi ba, ballantana su tausaya mata. Bai ce komai ba ya nufi ƙofa. Yana jin suna kiran shi bai juyo ba har ya fice.
Da sassarfa ya ƙarasa gate ɗin gidan yana ficewa. Yasan zuciya zata iya saka shi faɗa musu maganar da ba zata yi ma Ummi daɗi ba in ta ji.
Zai yi komai, zai jure komai don farin cikin Ummi. Titi ya fita, saida ya tare mai mashin tukunna ya soma tunanin ina zai nufa don duba Abba.
Kasuwa zai yi ko gidan su. Gashi babu agogo a hannunshi balle yasan ko ƙarfe nawa. Yasan dai ƙila tara na safe zata yi ko ma ta wuce.
Don haka ya yanke hukunci zuwa gida, ƙila Abban bai fita ba. Aikam haka yayi. Mai mashin na sauke shi kofar gidan da ya san ba zai sake kira da nasu ba zuciyar shi tai wani irin dokawa.
Sallamar mai mashin ɗin yayi. Ya kai mintina biyar tsaye a bakin ƙofar gidan yana kokawa da zuciyarshi wajen shiga.
“Ummi, saboda ke kawai…..”
Ya faɗi yana ɗaga ƙafarshi ya taka cikin soron gidan. Danne abinda yake ta taso mishi yake kafin da sallama ya tura ƙofar ya shiga cikin gidan.
Gaba ɗaya yake ganin komai na gidan ya canza. Hatta da fentin gidan an sake shi. Yayi mishi wani duhu duhu duk da safiyar garin.
Muryarshi a sarƙe ya sake yin sallama.
“Waye?”
Ya ji muryar Hajiya Beeba tana dirar mishi cikin kunnuwa da wani sauti marar daɗi. Shiru ya yi, yai tsaye a tsakar gidan.
Ɗago labulen falon aka yi, ya sauke idanuwanshi cikin na Abba. Duk wani abu da yake ji, da yake ƙoƙarin dannewa ya samu tasowa da ganin Abba da yayi.
So yake ya ƙarasa inda yake tsaye yana kallon shi ya kama shi ya girgiza shi har sai ya faɗa mishi abinda ya canza. Sai dai kamar an dasa shi a wajen da yake.
Yana kallon Hajiya Beeba ta leƙo da kai ta bayan Abba tana faɗin,
“Wai waye?”
Ganin Dawud ya sata ware idanuwanta da mamaki. Wata tsanar shi na ziyartarta. Don yanzun in akwai abinda ta tsana bai wuce duk wani abu da zai tuna ma Auwal cewa suna raye ba ma.
Balle har ya tuna yayi wata rayuwa da su. Auwal kam kallon Dawud yake yi kanshi na sarawa kuma ya rasa dalili. Kamar akwai abinda ya kamata ya ji daban akan Dawud ɗin banda ƙyamar ganinshi, amma ya kasa tuna komenene.
Kuma ƙoƙarin tunawar na saka kanshi sarawa, hannu ya kai yana murza goshin shi. Baya son ganin Dawud sam sam. A daƙile ya ce,
“Lafiya?”
Yanayin yadda yai maganar ya ƙara tunzura abinda Dawud yake ji akanshi.
“Ummi ke kiranka….”
Dawud ya faɗi yana kasa ƙarasa maganar. Caraf Hajiya Beeba ta amshe zancen da cewa,
“Me zai mata to? Ta bar gidan ma ba zata barmu mu sake ba.”
Ko kallonta Dawud bai yi ba. Ba ita bace a gabanshi. Ba don Ummi ba babu abinda ƙafafuwanshi za su sake yi a cikin gidan nan.
Zuciyarshi zafi take sosai. Amsar Abba yake jiran ya ji.
“Me zan mata? Bana son ganinta. “
Numfashi Dawud ya ja yana yatsina fuska saboda zafin da zuciyarshi ta ƙara yi. Ya tsani duk abinda zai taɓa Ummi.
Can ƙasan maƙoshi dawud ya ce,
“Naƙuda take. CS za ai mata shi yasa take son ganinka.”
Daƙuna fuska Auwal yayi yana rasa dalilin da zai sa ta neme shi bayan abinda tai masa. Babu ruwanshi da cikin jikinta ballantana naƙudar da take yi.
Asalima tunaninta kawai da yayi ƙara mishi sarawar kai yayi da ɓacin rai da ya rasa ta inda yake tasowa.
“Banda alaƙa da cikin jikinta ballantana naƙudar ta. Karka sake shigo min gida.”
Tsanar da baya son zuciyarshi ta ambato mishi ne maganganun Abba suka tunzura ta. Ya tsani wannan mutumin da ke tsaye a gabanshi. Ya tsane shi da wani irin yanayi da bai taɓa sanin kalarshi ba. Baya son ganinshi, baya son jin abinda zai sake fitowa daga bakinshi.
In da makami ne a hannun shi, kalar yadda yake jin zuciya na tunzura shi zai iya akaita komai. Juyawa yayi yasa hannu ya buɗe ƙofar ya fita.
Tafiya kawai yake ba don yana gane inda yake saka ƙafa ba. Tafiya yake ba tare daya san abinda zai gaya ma Ummi ba.
Tun faruwar abin nan bata taɓa buɗe baki ta ce yayi mata wani abu ba. Yau da ta faɗi abinda take so ya kasa cika mata shi. Hakan kawai ya sa zuciyar shi ciwo.
Bakin wata bishiya ya samu ya zauna ƙasanta ya jingina bayanshi da bishiyar. Kanshi ya dafe da hannuwanshi. Numfashi yake fitarwa da sauri-sauri.
Gaba dayay nauyi ya mishi yawa. Baisan da wa zai raba nauyin ba ya samu sauƙi. Sai da ya ɗan ji ya samu nutsuwar da zai iya zuwa asibiti ya ɗauko Sajda sannan ya miƙe.
Ko ba komai ba zai je ma Ummi haka nan ba. Ko da ya kasa kawo mata Abba, zai kai mata Sajda. Fatanshi ɗaya ya samu Sajda cikin sauƙin da zai iya tafiya da ita ba tare da matsalar komai ba.
****
Leda ɗaya suka ɗiba ma, da ya yi magana likitan ya faɗa mishi ba su ɗiba don Ummi na buƙata ba sai don kar ta buƙaci hakan bayan an gama CS ɗin.
Hana shi tashi suka yi sai da ya samu fiye da mintina ashirin a kwance. Gajiya yai ya miƙe don yana buƙatar zuwa gida ya sake kayan da ke jikinshi.
Fitowa yayi bai ga su Tayyab ba. Yasan suna tare da Ummi, don haka ya fice kawai ya ɗauki motarshi ya jata zuwa gida.
*******
Yana shiga gida, ɓangaren shi ya wuce ya watsa ruwa ya fito, jeans ya saka blue sai polo shirt ruwan madara, ya sa comb ya ta je sumar kanshi ya feshe jikinshi da turaruka sannan ya fito zuwa falonshi.
Fridge ya buɗe ya ɗauki malt guda biyu ya shanye sannan ya fito zuwa babban falon gidan. Asad ya samu zaune ko Anees ne don wani lokaci ba gane su yake ba.
“Ina kwana.”
Kai Labeeb ya ɗan ɗaga mishi tare da faɗin,
“Ina mummy?”
“Ka san bacci take kaima.”
Ɗan dafe kai Labeeb yayi yana wucewa ɓangaren maman tasu har ya ƙarasa bedroom ɗinta. Ƙwanƙwasawa yayi shiru.
Ya ci gaba da ƙwanƙwasa ƙofar har sai da ya ji takun tafiya tukunna ya daina bugawa. Buɗe ƙofar ta yi. Banda alamun baccin da ke idanuwanta za ka rantse da Allah daga wajen wani gagarumin biki take.
Ko alama kwalliyar da ke fuskarta bata nuna cewar an kwanta akanta ba. Yatsine fuska Mummy ta yi.
“Labeeb ko meye ba zai iya jira in tashi bacci ba? Ka fi kowa sanin jiyan nan na dawo ko?”
“Sorry Mummy. Ummin Dawud ce take asibiti tana naƙuda tun jiya. CS ma za ai mata shi ne zan faɗa miki.”
Wani guntun tsaki Mummy ta ja da ya tsaya ma Labeeb a maƙoshi. Da bata da matsala da Aisha, ranar da Hajiya Beeba ta zo gidan ta ga kamar Auwal da ita ya fi dacewa ba wannan bagidajiyar ba.
“Shi ne abinda yasa ka katse min bacci na? Allah ya raba lafiya.”
Ƙofar Labeeb ya ga zata rufe ya sa hannu yana tarbewa.
“Mummy mana. Don Allah ki zo.”
Juya idanuwanta ta yi.
“Karfa ka dame ni. Zan je suna in ta haihu, Abuja zan tafi ƙarfe sha biyu. Ina da bashin baccin da zan rama.”
Tana ƙarasawa ta rufe ƙofar a fuskar Labeeb. Ya kamata ace yayi tsammanin abinda zai faru kenan. Yadda ranshi ya ɓaci ya sa shi da na sanin faɗa ea Mummy.
Su kansu matsalar su ba damunta ta yi ba. Balle ya yi tunanin zata damu da zuwa duba Ummi. Juyawa yayi abinshi.
Kan hanyar shi ta fita ya ci karo da Zainab. Raɓa shi ta yi zata wuce ya ce,
“Zeezee baki je makaranta ba?”
Kallon nan da takanyi in magana bata da muhimmanci a wajenta tai mishi tare da faɗin,
“Na ɗauka abinda kowa yake so yake yi?”
Sauke numfashi Labeeb yayi. A shekarun Zainab yana mamakin irin halin da take da shi. Bai da lokacin wannan don haka ya wuce ta kawai.
Motarshi ya buɗe ya shiga.
****
Sai da ya fara samun likitan Sajda ya faɗa mishi komai don ya ji ko ɗaukar sajda zai zama matsala. Ga mamakin shi likitan ce mishi ya yi,
“Jiya ma ta tashi. Bata duk wannan ihun, sai dai bata ce komai ba. Ko yanzun tana ɗakinta a kwance, babu ƙoƙarin da bamuyi ba amma bata yi magana ba.”
Miƙewa Dawud yayi, bai ko tsaya ya ce ma likitan komai ba. Sajda kawai yake so ya gani. Da gudu gudu ya ƙarasa ɗakinta ya tura ya shiga. Zaune take kan gadon tana ta lila ƙafafuwanta.
Kanta a ƙasa. Ko da ta ji tura ƙofarshi bata nuna alamu ba.
“Sajdaa.”
Ya kira, juyowa ta yi da sauri ta kafe idanuwanta a kanshi. Kafin ta diro daga kan gadon da gudu ta rugo ta riƙe ƙafafuwanshi tana sakin wani kuka.
“Yaya a ina nake? Tun jiya banganku ba sai wasu mutane. Ina ta jin tsoro, yaya ka kaini wajen Ummi…..”
Take faɗi tana ci gaba da kuka har jikinta na ɓari. Ɗago da ita yayi ya riƙeta sosai a jikinshi yana lumshe idanuwanshi da yima Allah godiya.
Ko da ya sa bai yi nasara kan zuwan Abba wajen Ummi ba, sai yai mishi musayar hakan da samun sauƙin sajda. Don gaba ɗaya ɓacin ran da yake ciki ya ji ya wanke.
“Yaya mu tafi daga nan. Bana son wajen nan.”
Sajda ta faɗi cikin kunnenshi tana ƙara ƙanƙame shi. Bai jira ta sake magana ba ya juya don ko ɗakin bai tsaya rufewa ba.
Da Sajda saɓe a kafaɗarshi suka fice daga asibitin. Mashin ya tare ya ɗorata sannan ya hau shima yana faɗa mishi inda zai kai su.
Saboda yadda ya ke ɗokin su ƙarasa asibitin Ummi ta ga Sajda ta ji sauƙi ya sa shi ganin gudun da mai mashin ɗin yake yi yayi kaɗan.
Kallon Sajda yake yana sake gode wa Allah da wani sabon imanin da ke shigar shi. Iko na Allah mai girma ne. Yadda sauƙi ya samu wajen Sajda ya bashi tsoro sosai.
In Allah ya so ka da rahma babu wanda ya isa ya hana hakan. Haka idan ya so ka da sauƙi, sai kai mamakin samuwar shi.
Don ka ga jinkiri wajen samun sauƙin al’amuranka baya nufin Allah ya manta da kai.
****
Da sajda a kafaɗarshi ya shiga asibitin, dudduba su Tayyab yake bai gansu ba. Don haka ya samu wata nurse ya tambayeta.
Hanyar da daƙunan tiyata suke ta nuna mishi. Yai mata godiya ya wuce. Yana ƙarasawa kuwa ya same su tsaitsaye sun zuba ma ƙofar ɗakin da yasan Ummi na ciki idanuwa.
Takun tafiyar shi suka ji, su dukkansu suka juyo. Sajda ya sauke, kallon su take kamar yadda suke kallonta. Murmushi ta yi tare da faɗin,
“Yaya Tayyab….”
Da sauri ya tako, ya tsugunna yana kama kafaɗarta. Ya rasa abinda yake ji don ya wuce farin ciki, ga nauyin da ƙirjinshi yayi da tunanin halin da take ciki kullum ya ɗauke. Wani irin light yake jinshi, rungume Sajda yayi yana jin kamar ya mayar da ita cikin jikinshi ya ɓoye ta don kar wani abu ya ƙara samunta.
“Yaya Tayyab sake ta haka….”
Zulfa ta faɗi, dariya suka yi su dukkansu. Kallon Dawud suke yi, ya daƙuna musu fuska, don sun jima basu ga dariyar shi ba.
Rungume Sajda Zulfa ta yi, ita kaɗai tasan yadda ta yi kewar ƙanwarta.
“Ina ummi?”
Sajda ta tambaya.
“Za ki ganta yanzun. Zata haifo mana baby.”
Zulfa ta ƙarasa maganar da murmushi. Ware idanuwa Sajda ta yi kafin murmushi ya mamaye fuskarta.
“Yaya da gaske wai?”
Ta tambaya tana kallon Dawud. Kai ya ɗaga mata. Hannun zulfa ta riƙe, ta kasa ɓoye daɗin da take ji. Sai dai kanta ciwo yake mata sosai.
“Yaya kaina ciwo yake sosai.”
Ta faɗi tana ɗan dafe goshinta da hannu. Kamata Tayyab yayi ya zaunar da ita yana faɗin,
“Sannu… Ko za ki sha ruwa?”
Girgiza mishi kai ta yi. Sai lokacin Dawud ya maida hankalinshi kan Labeeb da ke tsaye yana kallon su. Ɗan murmushi Labeeb yai mishi.
“Thank you.”
Ya faɗi a hankali. Girgiza mishi kai Labeeb yayi tare da harararshi. Ya ɗan yi dariya yana samu waje gefen Sajda ya zauna. Kanta ta kwantar a jikin hannunshi.
Ya sauke numfashi yana jin komai ya soma daidaita a wajenshi. Hakan shi ne sabon shi, ita ce rayuwar da ya sani tare da Sajda.
Da ta naniƙe mishi haka, ya dinga tureta kenan yana mita ta fiye son jiki. Amma yau yasan ya yi kewarta fiye da zato. Lumshe idanuwanshi yayi yana jin yadda bugun zuciyarshi yake tafiya.
Can ƙasanta yana addu’ar samun nasara da aikin da ake ma Ummi.
****
BAYAN AWA ƊAYA
Wata nurse ya fara ganin ta fito da gudu da baby a hannunta. Su dukkansu suka miƙe suna zuba ma ƙofar idanuwa. Kafin wata ma ta sake fitowa da gudu l.
Kallon da ke fassara ‘Me yake faruwa ne?’ Labeeb ya yi wa Dawud. Ware idanuwa ya ɗan yi alamar shima bai sani ba.
Hannunshi ya ji Sajda ta riƙe. Kafin ya juya ya kalleta Zulfa ta riƙe ɗayan hannunshi. Runtsa idanuwa yai ya buɗe su. Tayyab ya ji ya ɗora hannunshi kan na Sajda yana haɗawa da na dawud ɗin ya riƙe gam.
Ƙwarin gwiwa suke so daga gareshi. Tabbaci suke nema da bai san ta inda zai fara basu shi ba. Zuciyar shi rawa take amma baya son jikinshi ya nuna.
Daga baɗininshi ya gama karaya. A zahiri ne ƙannen nashi ke gani kamar yana da wani sauran ƙarfi da zai iya rabawa da su. Suna nan nurse ɗaya ta dawo.
Ta kai mintina sha biyar kafin su fito tare da likitan. Fuskarshi babu walwala yake takowa wajen su. Dawud na jin yafda Tayyab ya sake matse hannuwansu.
Shi kanshi zuciyarshi dokawa take da ƙarfin gaske. Wani irin kallo ya ga Labeeb na musu kamar yana son ɗauke musu dukkan damuwarsu. Da sauri ya ƙarasa ya tarbi yana janshi gefe.
“Me yake faruwa?”
Labeeb ya tambaya muryarshi cike da ƙaguwa da damuwa. Numfashi likitan ya ja yana fitar da shi.
“Yaronta na lafiya duk da ya wahala sosai. Hutu kawai yake buƙata da…..”
Katse shi Labeeb ya yi da faɗin,
“Ba babyn nake son jin ya yake ba.”
“An samu wasu complications ne haka. Ta samu matsala a ƙashin bayanta, kamar accident ne ko faɗuwa….”
Kallonshi Labeeb yake, ya kasa gane me yake son faɗa mishi. Don baisan Ummi ta taɓa samun wani accident ba.
“Me kake nufi wai? Bana ganewa.”
Ya faɗi yana tsura ma likitan idanuwa.
“Um ina nufin sai an sake mata wani aiki, saboda naƙudar da ta yi ya sake fama ciwon da ta samu.”
Sauke numfashi Labeeb yayi.
“Dan wannan ba matsala bane. Kome ake buƙata, ko wanne asibiti ne ka faɗa min.”
Ɗan dafa kafaɗarshi likitan yayi. Yana mishi murmushin ba da ƙwarin gwiwa kafin ya wuce.
“Zamu iya ganinta?”
Labeeb ya buƙata. Ɗan jim liki yayi.
“Sai an fito da ita tukunna. Zan sa ai muku magana.”
Ya ƙarasa yana juyawa. Wani numfashin Labeeb ya sake saukewa kafin ya tako zuwa inda su dawud suke.
Tun kafin su tambayeshi ya ce,
“Ita da babyn lafiyansu ƙalau….”
Yana kallon yadda wani irin relief ya saukar musu. Kafin Tayyab ya saki hannun Dawud yana komawa ya samu waje ya zauna. Da idanuwa Labeeb ke nuna wa Dawud yana son su yi magana.
Jan su Zulfa yayi ya zaunar da su wajen Tayyab sannan ya dawo wajen Labeeb.
“Akwai complications in ji Doctor, ya ce Ummi na da ciwo a bayanta, sai an mata wani tiyatan an gyara, but bai faɗa min ko yaushe ne ba.”
Dafe goshi Dawud yayi saboda yadda ya ji kamar ɗakin na juya mishi. Hutu yake so Ummi ta samu, farin ciki yake so ya ganta a ciki da lafiya ko da yaushe.
Damtsen shi Labeeb ya kama yana girgiza shi.
“Look at me Dawud….. Breathe in……out”
Da sauri-sauri yake jan numfashi yana fitar da shi har saida ya dai daita.
“She will be fine. Kana jina, ciwo ne kuma za a gyara.”
Kai kawai Dawud ya iya ɗaga mishi. Sai da Labeeb ya tabbatar ba zai sake samun wani panic attack ɗin ba sannan ya ce mishi yana zuwa ya bar wajen.
Bai fi mintina ashirin ba ya dawo da ledoji a hannunshi. Lemuka ne ya siyo musu masu sanyi da cake. Sai da ya matsa sannan Dawud ya ci cake ɗaya.
Don baya son saka ma cikinshi komai, Ummi yake son gani ba yunwa yake ji ba. Ita yake son gani don ya san halin da take ciki.
Yana zaune gefe yana kallon su, har suka cinye. Kallon Sajda yake har lokacin mamakin samun sauƙinta cikin ɗan lokaci ya ƙi ya sake shi.
****
Kamar jira suke nurse ta zo ta ce musu za su iya ganin Ummi. Su dukkansu suka bi bayanta. Har ɗakin da aka mayar da Ummi.
“Ummi.”
Sajda ta faɗi tana ƙarasawa inda Ummi ke kwance kan gadon da gudu. Juyowa ta yi da murmushi a fuskarta, kafin ta ɗan buɗe idanuwanta kan Sajda.
Da sauri ta ɗago ta kalli Dawud. Murmushi ya yi yana ɗaga mata kai alamar da gaske ne sajda take gani, ‘yar dariya Ummi tayi.
Dawud kam yana tsaye ne daga gefen Labeeb. Yana kallon yadda su zulfa ke ma Ummi surutu tana musu dariya. Zai iya rantsewa bai taɓa ganin fuskar Ummi tai kyau irin na yau ba.
Ya san yadda fuskarta take da tana cikin kwanciyar hankali, ya kuma san yadda take da bata ciki. Amma yau yanayin da yake gani na nutsuwa da kwanciyar hankali a fuskar ta bai taɓa sanin akwai irin shi ba.
Wata nurse ta shigo da baby cikin farin towel. Ta kai wa ummi ta ajiye mata a gefenta, ta kalle su da murmushi ta fita daga ɗakin.
Dawud na kallon yadda Ummi ta ɗan gyara kwanciyarta da ƙyar tana ɗagowa kaɗan. Hannu ta sa ta ɗauki babyn ta ƙura mishi ido.
Tana iya ganin kamar da sukayi da Auwal fiye da yadda suka yi da Sajda. Ta so ace ya zo, ta sake ganin shi ko da sau ɗaya ne. Ya riƙe ɗanshi a hannunshi kamar yadda sauran suka samu.
Idanuwanta ta ji sun ciko da hawaye. Ta samu da ƙyar ta mayar da su, sannan ta ɗago, da sauri Dawud ya ƙarasa inda take, yaron ta miƙa mishi.
“Ka yi mishi huɗuba tunda Abbanku baya nan.”
Hannunshi na rawa ya karɓi babyn, kallonshi yake shi da kanshi yana ganin kamar da suka yi da Abban, zuciyarshi ya ji ta sosu.
Kiran Sallah yai mishi cikin kunnuwa da addu’o’i kafin ya tuna yadda Ummi ke faɗa musu in da tana da wata macen sunan da take son a saka mata, in kuma namiji ne ma haka.
Miƙa wa Labeeb yayi, ya ware idanuwa yana girgiza mishi kai.
“Karɓe shi mana, gara ku fara koya tun yanzun….”
Ummi ta faɗi, dariya Labeeb yayi ya miƙa hannu Dawud ya ɗora mishi shi, kallonshi yake. Yana tunanin anya akwai abin da ya fi jariri kyau da ban mamaki kuwa.
Kafin ya miƙa ma Tayyab shi da su Zulfa suka zagaye shi kamar za su haɗiye babyn. Kallonsu Ummi take kafin ta ja numfashi tana fitar da shi da yanayin da ya sa su duka suka maida hankalinsu kanta.
Idanuwanta kafe akan hannayenta da take wasa da su, kamar wadda take wata duniya ta daban ta ce musu,
“Ku zama masu haƙuri da yafiya a rayuwarku, kar ku bari rasa wasu abubuwa ya zama sanadin farin cikinku. Kar ku bari ruɗin wani abu ko ya yake ya rabaku da imaninku, rayuwa da kuke ganinta ba komai bace ba. Ku yi haƙuri da ita a duk yadda ta zo muku saboda ba tabbas gareta ba.
Ku yi ƙoƙarin neman samun lahirarku saboda hutun duniya da kuke ganinshi babu wata nutsuwa a tattare da shi.
Babu wani abu da yake dawwamamme a rayuwar nan. Karkuce sai kun samu farin ciki ko da yaushe, ku dai ku yi ƙoƙarin amfani da lokacinku yadda ya kamata.”
Nisawa tayi ta ɗago da idanuwa tana kallonsu. Gaba ɗaya jikin kowa yai sanyi.
“Ummi bana son kina irin nasihar nan. Jikina sanyi yake yiwallahi.”
Tayyab ya faɗi muryarshi a karye.
“Ba kai kaɗai ba Tayyab.”
Labeeb ya ce yana gyara tsayuwa tare da sauke ajiyar zuciya. Dawud kam bai ce komai ba. Idanuwanshi kafe akan Ummi. Babyn da ke hannun Tayyab ya fara kuka.
Ummi ya miƙa wa shi da sauri ta karɓe shi. Kallonsu take sosai, kafin ta ce,
“Ku ɗan bamu waje.”
Miƙewa Tayyab yayi ya kama hannun su Zulfa yana nufar ƙofar kafin Dawud da Labeeb su rufa mishi baya.
“Dawud…..”
Ummi ta faɗi, juyawa yayi da faɗin
“Na’am ummi….”
Yana ƙarasawa inda take tare da jan kujera ya zauna. Yana jin ko waye ƙarshen fita ya ja ƙofar. Sosai Ummi ke kallonshi har abin ya fara tsorata shi.
Muryarshi can ƙasa ya ce,
“Ummi?”
Cike da alamar tambaya. Muryarta ɗauke da wani yanayi ta ce,
“Dawud kai min alƙawari duk ranar da Abbanku ya nemi ku koma gida za ku koma…..”
Ya rasa me yasa zuciyarshi ke dokawa da ƙarfi haka.
“Ummi ki daina magana haka, tsoratani kike yi.”
Murmushinta ta yi mishi.
“Kai dai ka yi min alƙawarin da na ce.”
Kai ya ɗan ɗaga mata ba tare da tunanin komai ba sai don yana son ta daina mishi irin maganganu haka.
“Ya sunanshi?”
Ta tambayi Dawud tana kallon babyn da ke ta kuka, tana jin yadda jikinta yake mata wani iri.
“Khateeb….”
Ya faɗi. Ɗagowa ta yi da sauri ta kalle shi. Tana ganin yadda bai manta faɗa musun da ta yi inda zata haifi namiji sunan da zata saka mishi kenan ba. Mace kuma Khadeeja.
Da murmushi a fuskarta ta maida kallonta kan Khateeb da ke hannunta, Dawud kuma kallonta yake yi ya ji ta sauke wata irin ajiyar zuciya.
Idanuwanta kafe kan Khateeb, murmushin nan yana fuskarta. Kukan da Khateeb yake yi ya ji ya tsananta, kamar zai shiɗe.
Kallon Ummi yake sosai, don ya rasa me yasa bata yi ƙoƙarin yin wani abu kan kukan da Khateeb yake yi ba.
“Ummi yana ta kuka fa….”
Dawud ya faɗi, bai ga alamar ta motsa ba. Sake kiran sunanta yayi shiru, miƙewa yayi daga kan kujerar da yake yana kai fuskarshi saitin tata.
Muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce,
“Ummi…….”
Shirun dai ya sake gani, bata ko motsa ba, hannunshi yakai ya taɓa kafaɗarta, gani yai ta tafi luuuu. Cikin hanzari ya riƙeta da hannu ɗaya, ɗayan kuma ya riƙo Khateeb da ke shirin suɓuce mata.
Gyara mata zama yai sosai sannan ya ɗauki Khateeb da har lokacin yake kuka, da gudu ya fita daga ɗakin, su Labeeb da ke bakin ƙofar tambayarshi suke lafiya.
Amma da alama bayajin su, gudu kawai yake yi, hakan yasa Labeeb binshi ya kama rigarshi ya riƙe.
“Dawud menene wai?”
Numfashi yake fitarwa da ƙyar a sarƙe yake faɗin,
“Ummi……. El… Ummi.”
Ware idanuwa Labeeb yayi, likitan da yake takowa suka nufa. Labeeb ya ce ya zo ya duba Ummin su. Da hanzari suka taka suka nufi ɗakin tare.
Su Tayyab na rufa musu baya. Hannun Ummi likitan ya taɓa, sannan ya taɓa wuyanta. Tunda ya shigo ya kalleta ya gane. Abu ɗaya ya fi tsana a aikinshi. Shi ne wannan ɓangaren.
Babu wanda zai fahimci wahalar da take cikinshi sai wanda yake aiki irin nashi. Ɗagowa yayi ya sauke idanuwanshi cikin na Labeeb tare da girgiza mishi kai.
Bai jira komai ba da sauri ya fice daga ɗakin. Riƙe baki Labeeb yayi yana jin yadda ƙafafuwanshi ke barazanar kasa ɗaukarshi.
“Ya naga ya fita? Ya zo ya duba ta mana!”
Dawud ya faɗi a razane, yana kallon Labeeb daya rufe fuskarshi da hannuwanshi biyu. Ƙarasawa yayi inda Labeeb ɗin yake.
Ya kama hannunshi yana girgiza shi. Durƙushewa Labeeb yayi, jikinshi ko ina ɓari yake yi.
“Wai menene?”
Tayyab ya faɗi yana ƙarasowa inda su Dawud ɗin suke. Girgiza musu kai Labeeb yake, yana jin hawayen da ke zuba a zuciyarshi amma sun ƙi fitowa waje ko zai samu sauƙin raɗadin da yake ji.
“Ta…..ta rasu!!!”
Ya faɗi zuciyarshi na ciwo. Ummi ita ta maye mishi gurbin da tashi mahaifiyar bata yi ba.
“Waye ya rasu?”
Tayyab ya faɗi yana kasa fahimtar me Labeeb din ke son faɗi, gyara Khateeb dawud yayi yana cire shi daga cikin towel ɗin.
Rungume shi yayi sannan yasa towel ɗin yana zagayawa da shi ta baya, maganar Labeeb na ta yawo a jikinshi da alama ta rasa wajen zama.
“Ɗaure min.”
Ya faɗa ma Tayyab, ɗaure mishi towel ɗin yayi sosai, kamar Khateeb yasan akwai wani abu babba da ya girme su yai shiru luf a ƙirjin Dawud.
Buɗe baki Dawud yayi zai yi magana, Sajda ta ce,
“Yaya Ummi ta ƙi min magana.”
Juyawa suka yi shi da Tayyab, ƙarasawa inda ummi take kwance Tayyab yayi.
“Ummi……”
Ya kira shiru, hannu yasa ya taɓata ya ji jikinta ya yi sanyi ƙarara, da sauri ya janye hannunshi yana kallon Dawud.
“Bata magana, a kira likitan.”
Ya faɗi yana juyawa.
“Ta rasu Tayyab……..”
Labeeb ya faɗi har lokacin bai ɗago da kanshi ba. Cikin tashin hankali yake kallon Dawud da yai tsaye hannunshi ɗaya tallabe da bayan Khateeb.
Da sauri Tayyab ya ƙarasa inda Ummi take, hannunshi ya kai ya kama nata yana jijjigata.
“Ummi ki tashi su ga ba da gaske bane! Ba mu yi haka da ke ba Ummi, kin manta yadda na ce zan siya miki mota in na fara aiki?
Kin ga Sajda ta warke fa, Ummi don Allah ki tashi.”
Sajda da ta kasa fahimtar me yake faruwa ta ce,
“Ya Tayyab me yasa Ummi bata magana?”
Ta ƙarasa maganar da kuka.
“Ina zuwa Sajda. Ai Ummi ba zata yi mana haka ba, yanzun zata tashi. Ita ma tasan muna buƙatarta, ga baby kuma.
Ummi don Allah ki tashi, na san ba ki rasu ba. Kin ga ba ma don mu za ki tashi ba, ga babynki ai ba za ki barshi shi kaɗai ba ko?”
Yadda ya ƙarasa maganar jikinshi na sanyi don ganin ko alamar motsi ummi batai ba dole ya baka tausayi, hannuwanshi akanta, sai dai ya bar girgizata wannan karon ya saki wani irin kuka.
Su duka ukkun kuka suke, Sajda ta dafa bayanshi tana kiran.
“Ummi… Ummi.”
Zulfa kuma ta ɗora kanta kan Ummi tana wani irin kuka, don ba zata manta ƙawarta ba ta makarantar Islamiyya da babarsu ta rasu, ƙarshe ma daina zuwa makaranta ta yi.
Takuma san in an rasu shikenan. Ba za ka ƙara ganin mutum ba, bata hango rayuwa babu Ummi a cikinta.
“Ummi don Allah ki tashi. Wallahi in kika tashi zan je in kawo miki Abba. Ki tashi ki ga zamu koma gidanmu…… Ummi karkiyi mana haka…..”
Tayyab yake faɗi yana jin zuciyarshi na barazanar daina aiki a ƙirjinshi. Komai ya kwance mishi. A hankali Dawud ya juya yana kallon su. Idanuwanshi akan su ya ce ma Labeeb.
“Me ma ka ce ya samu Ummi?”
Ɗagowa yai ya kalli Dawud ɗin. In har shi yana jin rasuwar Ummi irin haka. Ba zai soma misalta yadda su za su ji ta ba.
Cikin sanyin murya ya ce,
“Ta rasu Dawud. Ummi ta rasu…..”
Kai Dawud ya ɗaga mishi sannan kamar wanda ke tafiya kan ƙwai yake tsoron in ya taka da ƙarfi zai fashe haka yake tafiya har ya kai inda Tayyab yake.
Hannu Dawud ya kai ya kama Sajda, ta ko maƙale ƙafafuwanshi tana kuka.
“Don Allah yaya ka tashin mana Ummi.”
Runtsa idanuwanshi yayi ya buɗe su, Labeeb ne ya taso daga inda yake don yasan Dawud ya fi buƙatar taimakonshi a yanzun fiye da ko yaushe.
Zulfa Labeeb ya kama, tana tirjewa tana kuka.
“Ka sake ni, babu inda zani, in Ummi bata tashi ba bazan sake ganinta ba na sani ai…… Ka sake ni!”
Cak Labeeb ya ɗagata yana matseta a jikinshi gam, tun tana ƙoƙarin ƙwacewa har ta haƙura tai luf, sai kukan da take yi kamar ranta zai fita.
Hannu Dawud ya kai yana kamo kafaɗar Tayyab. Juyowa Tayyab yayi yana zama a ƙasa, ya tsugunnar da kanshi kan ƙafafuwan Dawud ɗin yana kuka kamar yaro ɗan shekara biyu.
“Me yasa mutuwa bata san adalci ba Yaya?…..”
Yake faɗi yana kuka, tsaye Dawud yayi, idanuwanshi kafe kan fuskar Ummi da ke ɗauke da murmushi har lokacin.
Hannunshi ya kai yana addu’a tare da rufe mata idanuwanta. Cikin zuciyarshi yake roƙon mata rahamar Allah.
“Ummi ban san yanayin mahaifiyar kowa ba, abu ɗaya na sani, ko da zaɓi aka bani na kalar mahaifiyar da nake son samu bazan taɓa zaɓar wadda ta kai ki ba. Lokaci baya jiranmu Ummi, nasan kina jina, kuma nasan inda kina da zaɓi ba za ki barmu a lokacin da muka fi buƙatarki ba.
Allah ya yafe miki, na ga kalar hutun da kike magana Yanzun Ummi, Allah ya baki shi, Allah ya baki dukkan farin ciki a lahirarki tunda baki same shi a duniya ba.
Zan kula da su Ummi, zan basu kulawa ko da ba zata kai taki ba…”
Sai lokacin Labeeb yake jin hawayen da suka kasa zubo mishi suna fitowa. Maganganun Dawud gaba ɗaya sun sa ya ji shi ɗin ba komai bane.
Sun sa shi jin gaba ɗaya rayuwa aikin banza ce. Babu tabbaci na dawwamar komai, yasan gaba ɗaya duniya babu abinda ya fi ƙaunar da ke tsakanin ɗa da mahaifanshi.
Amma gashi ita kanta ta yi kaɗan ta zaunar da Ummi a duniya. Hannunshi ɗaya ya sa ya goge fuskarshi, ɗayan na tallabe da Zulfa.
Kamo Tayyab Dawud yayi, ya ɗago fuskarshi har ta kumbura saboda kukan da yake yi. Kama hannuwan Dawud yayi ya miƙe jiri na ɗibarshi.
Kallon Ummi yake, kafin cikin kuka ya soma faɗin,
“Ummi wanne farin ciki kike faɗin kar mu rasa? Ba kya nan, babu Abba. Meye ya rage a duniyar mu banda maraici?
Zan miki addu’a ba don zuciyata na son yarda kin barmu ba, me yasa mutuwa ba zata bari ko sallama mu samu yi da ke ba?
Allah yai miki rahma, Allah ya baki kwanciyar kabari mai sauƙi…….Ummi………”
Kasa ƙarasawa yayi saboda kukan da ya sake cin ƙarfinshi. Kama hannunshi Labeeb yayi yana janshi suka fice daga ɗakin.
Inda dawud yake tsaye nan Labeeb ya dawo ya same shi, sajda ya kamo ya saɓata a kafaɗarshi ya fita da ita, mota ya kai ta itama.
Saida ya kira Mamdud cewar yazoe da wata motar tukunna ya dawo wajen Dawud ya tsaya. Har sai da Mamdud ya iso ya kira shi tukunna.
Dawud na tsaye yana kallonsu har suka kama ummi suka sakata kan wani gadon daban. Suka tura za su fice da ita, sannan Labeeb ya ce mishi.
“Muje Dawud…..”
Babu musu ya bi Labeeb suka fice.