Skip to content
Part 20 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Har a hanya tunanin yadda za a yi ace yana da yaro yake yi. Gaba ɗaya yasan ya kula da duk wani possibility na hakan. Kuma tunda ya haɗu da Ateefa rabonshi da wata mace. 

Sai da ya ƙarasa gida yai parking ɗin mota ya fito sannan ya kula ko takalmi babu a ƙafarshi. Haka ya taka yana ƙarasawa cikin gidansu. 

Da sallama ya shiga babban falonsu. Fuskar Dady kawai ya kalla zuciyarshi ta tsinke. 

“Dady…….”

Hannu ya ɗaga mishi. Ya miƙe tsaye tare da faɗin, 

“Ka kalli wannan yaron ka ce min ba ɗanka bane Labeeb.”

Dady ya ƙarasa cike da takaici. Inda ya nuna gefen Dawud Labeeb ya bi da kallo, yaro ne kwance akan kujera. Tun daga ƙafarshi yake kallo da faɗuwar gaba har ya tsaida idanuwanshi kan fuskar yaron. 

Kafin kanshi ya gama processing me yake faruwa, zuciyarshi ta gama yanke mishi hukunci, saboda ta gama ji mishi connection ɗin da ke tsakanin shi da yaron da wata irin ƙaunar shi ta shigar mishi zuciya lokaci ɗaya. 

Miyan bakinshi ya ƙafe, kamar wanda ya kwana bai sha ruwa ba, a hankali ya taka har inda yaron yake kwance ya kai hannu ya shafi kuncin yaron. A hankali kamar me yawo cikin wata duniya ta daban ya ce,

“He is mine……”

“What???”

Maganar Ateefa ta mayar da hankalin su gaba ɗaya akanta, sam basu ga shigowarta ba sai muryarta da suka ji. Zuciyar Labeeb tai wani irin dokawa. 

“No Tee….. Me kike yi a anan?”

Hannuwanta ta ɗora akan ƙugunta tana kallon Labeeb cikin idanuwa. 

“Na gaji da barina cikin duhu da kake yi. Biyoka na yi sai kai min bayanin abinda ke faruwa….. Wannan yaron waye?”

Ta ƙarasa maganar da bugun zuciya na gaske. Girgiza mata kai Labeeb yake yi. Yana kallon yadda komai ke shirin tarwatse mishi ba tare da ya shirya ko yasan yadda zai yi ya hana faruwar hakan ba. 

“Anty in bai shirya baki amsa ba ki tambayeni mana.”

Asad ya faɗi , duka hankalinsu suka mayar kan Asad. Labeeb da faɗin, 

“Asad…..”

Cike da kashedi. Dariya ma yayi. 

“Menene Yaya? Kar a faɗa mata gaskiya ko kar a faɗa mata yaron da ke kwance ɗanka ne?”

Dafe kai Labeeb yayi yana jin yadda yake sara mishi. Ateefa na jin yadda mararta ta ƙulle, zata iya rantsewa abinda ke cikinta sai da ya harmutsa. Yaron take kallo. 

Cikinta ya sake yamutsawa da wani tashin hankali marar misaltuwa ganin kamar da yaron yake da Labeeb, wasu hawaye masu zafin gaske suka zubo mata. 

Muryarta a dake ta ce, 

“Ɗanka ne?”

Ware idanuwanshi yayi akan fuskarta, roƙonta yake yi. Kai ta girgiza mishi. 

“El-labeeb ka bani amsa ɗanka ne? Ko muna buƙatar DNA kafin ka amsa ni?”

A hankali ya girgiza mata kai, muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Ɗana ne!!!”

Hannunshi ta dafa tana riƙewa gam, saboda jirin da ta ji yana ɗibarta, kuma babu abin dafawa a kusa in ba shi ba, da sauri ya riƙota. 

“Tee, kin gani ko, don Allah ki nutsu kin ga ba ke kaɗai bace ba.”

Hankaɗe shi tayi, hawaye kawai ke fita a idanuwanta. Tana nuna yaron da ke kwance da hannunta idonta na kan Labeeb. 

“Wannan ma yana cikin past ɗinka da ka so binnewa ko? Sai dai kai baka isa kai ma ƙaddara wayau ba El-labeeb!…..”

Matsawa yai da niyyar taɓa ta, da sauri ta ja baya. 

“Karka matso kusa da ni wallahi!!”

Ɗaga hannuwanshi sama yayi da sauri yana faɗin, 

“Yi haƙuri….. Just calm down don Allah. Wallahi bansan yadda aka yi ba. Ban sani ba……”

Hannuwa Ateefa ta sa ta toshe kunnuwanta. 

“Bana son ji…. Bana son ji!”

Dafe kai ya sake yi yana rasa inda zai tsoma ranshi ya ji sanyi. Dai dai sallamar Mummy. 

“Ya Allah…..”

Labeeb ya furta yana sanin yanzun komai ya soma hargitsewa. Jikinta sanye yake da shigar doguwar riga irinta mutanen Sudan. 

Ɗaya bayan ɗaya Mummy ke ƙare musu kallo. Murmushi Labeeb ya ga Ateefa ta yi tana sa hannu ta goge fuskarta. 

“Sannu da zuwa Mummy.”

Ateefa ta faɗi da wani yanayi ɗauke a muryarta. Wani mugun kallo Mummy ta watsa ma Ateefa tare da faɗin, 

“Me take yi anan? Inason magana da family ɗina. She should get lost. Bana son juyowa na sake ganinta a nan.”

Mummy ta faɗi idanuwanta kafe kan Labeeb, dariya Ateefa ta yi.

“Irina ɗin da kike ƙyamata sai kuma Allah ya fito da shi a jikanki. Gashi can kwance Mummy. Ɗan El-labeeb ne. Your precious son. 

Ina taya ki murna. A bastard in your family!!!”

Wani irin mari Mummy ta ɗauke Ateefa da shi. Amma sam bai ma Ateefa ciwo ba, ko hannu bata kai don ta taɓa kuncinta ba. 

Mummy kawai take kallo, babu abinda zata yi da zai mata ciwo, ɗanta ya riga da ya gama kula da wannan ɓangaren. Kawai ta cikinta ta mayarma Mummy. Gorin da take mata ne Allah ya nuna mata. 

“Da baki yi saurin marinta ba ai. Gaskiya ta faɗa miki, ga jika nan Labeeb ya samar miki. Akwai wani ma a jikin Zulfa.”

Dady ya faɗa. Zaka iya jin ɓacin ran da ke tattare da muryarshi, Labeeb fuskar Ateefa yake kallo. Yanayin da kalaman Abba suka jefata. 

“Zulfa? Cikinka a jikin zulfa El-labeeb?”

Dariya Asad ya sake yi, da ka ji kasan ba ta lafiya bace. 

“Oh bai faɗa miki ba kenan? Probably watan haihuwarku ɗaya.”

Da sauri Labeeb ya ce, 

“Zan miki bay……”

Bai ƙarasa ba Ateefa ta ɗauke shi da mari. 

“I hate ranar da na sanka! Na tsani wawuyar zuciya ta data amince za ka canza. 

Baka canza saboda Allah ba, saboda me banza irina zata ɗauka zaka taɓa canzawa saboda ita?!

Guess what? I am done El-labeeb Maska! Na gama da sonka! Na gama da aurenka! Ka biyoni asibiti ka karɓi ɗanka ko ‘yarka…..cikina bazai iya dakon ajiyar maƙaryaci, maha’inci ba.”

Ta ƙarasa da ihun kuka, tana jin kamar numfashin ta zai ɗauke saboda tashin hankali da ƙunar zuciya. Ji take kamar ta caka ma Labeeb wuƙa ko zai ji kalar abinda yasa take ji. 

Labeeb kam ya rasa me ya kamata yayi, ya rasa abinda zai yi, wanne piece yakamata ya fara bi cikin duniyar shi da ta gama tarwatsewa gaba ɗayanta. 

“Ateefa don Allah karki min haka……..please don’t.”

Juyawa ta yi tana nufar hanyar ƙofa. Cikin hanzari ya kamo hannunta. 

“Ki rufa min asiri banda babyna, karki kashe min baby Ateefa…….ki barni na yarda…. Amma karki taɓa min baby.”

Juyowa ta yi tana kiciniyar ƙwace hannunta da Labeeb ya riƙe dam. 

“Ka sakemun hannu! Me za ka yi da babyn jikina, ga wani can kwance, ga wani a jikin zulfa. Na faɗa maka, na faɗa maka if you cheat on me shikenan……ka sake ni!”

Kallon Mummy Labeeb yake yi. 

“Mumy don Allah ki bata haƙuri.”

Harara Mummy ta watsa musu su biyu. 

“Matsalarka taka ce Labeeb. Bayan ɓata sunan family ɗina da ka yi me ya rage a tsakanin mu? 

Ka nuna mana iyakarmu….. Ka je kawai!”

Kallon Mummy yake cikin tashin hankali ba shiri ya saki Ateefa. 

“Na shiga uku, Mummy karki min baki don Allah……”

Ya faɗi yana ƙarasawa ya tsugunna gabanta yana kama ƙafafuwanta ya riƙe dam. 

“Mummy please……..ki rufa min asiri……zunubaina sun isheni karki haɗa min da fushin ki.”

“Labeeb ka sakeni. Wallahi ranka zai ɓaci, ba ka lalace ba? Ɗan shege ne a zuri’ata saboda kai? Ko na ce ‘ya’yan shegu? 

Bayan shegiyar suruka da ka sa dole na kauda kai sai ka ajiye min jikoki Labeeb? Bana son ganinka cikin gidan nan.”

Kan Labeeb a ƙasa ya ce, 

“Mummy karki yi haka, karki ɗora ayar tambaya akan tarbiyata, karki taɓa nan, karki fara nuna kin damu saboda baki damu ba.

Baki bani tarbiyar da zan ɓata ba, kome na zama ke ce.”

Da tashin hankali Mummy ke kallon Labeeb. 

“Me kake nufi?”

Ta tambaya muryarta na rawa. Anees da sai lokacin yayi magana ya ce, 

“Ki godema Allah Mummy….. Jikoki biyu kika samu, ta wajen Yaya kawai. Bakya nan all the time…..karki ɗora laifin akan shi kawai. 

Tarbiyar da zai ma kanshi ce yai mana…..”

Yana rufe baki ya juya ya bar falon. Asad na rufa mishi baya. Dady Mummy kawai ya kalla ya bi bayan ‘ya’yan shi. Dawud kallon su kawai yake yi. 

Shi kaɗai ya kula da Ateefa da ke dafe da bango tana maida numfashi. Kafin Labeeb ya miƙe daga gaban Mummy da ta rasa bakin magana. 

Juyawa yayi. Dai-dai lokacin da Ateefa ta durƙushe ƙasa tana yarfe hannuwa tare da kiran sunan Allah. Da gudu Labeeb ya ƙarasa inda take ya kamata. 

“Tee menene? Me ya sameki?”

Yake faɗi. Yana jin yadda take riƙe hannunshi tana jan numfashi. Dawud yai niyyar share su saboda haushin labeeb amman ya kasa. 

Tashi yayi ya ƙarasa wajensu.

“Meke miki ciwo?”

Ya tambaya, da ƙyar ta iya nuna mishi mararta. Kallon Labeeb yayi. 

“Ɗaukota mu tafi asibiti…..”

Ba musu, cak Labeeb ya ɗaga Ateefa kamar bata da nauyin komai ya tallabeta a jikinshi suka fita tare da Dawud ɗin har wajen motar shi. 

“Ina key ɗin?”

Dawud ya buƙata. 

“Yana aljihuna….”

Zagayawa Dawud yayi, yasa hannu a cikin aljihun Labeeb ɗin ya buɗe masa bayan motar. Ya saka Ateefa. Cikin tashin hankali yakalli gaban farar shaddarshi da hannayenshi. 

“O. M. G she is bleeding! Me ya sameta? Ateefa….. Tee…..”

Labeeb ke faɗi yana saka jikinshi cikin motar. Ƙarasa turashi Dawud yayi. Yasan da wahala in cikin jikinta bai zube ba. Da sauri ya rufe musu ƙofar. Ya zagaya ya shiga gaba. 

Sanin Dialogue Labeeb yake zuwa yasa Dawud nufar can ɗin. Suna isa da sauri aka zo aka karɓi Ateefa aka wuce da ita. Hana Labeeb din shiga suka y. 

Dawud ya riƙe shi. 

“Ka barsu su yi aikin su.”

Kai kawai ya ɗaga ma Dawud. 

BAYAN AWA ƊAYA 

Tare suka shiga ofishin Likitan da Dawud. 

“Mun yi saving baby ɗin. Amma ta rasa jini da yawa, so zamu riƙe ta sati biyu ko fiye da haka. 

Tana buƙatar hutu.”

Wani numfashi Labeeb ya sauke, yana ɗaga ma Likitan kai. Dawud ne yai mishi godiya kafin su fice daga office ɗin. Su koma waiting area na wajen ɗakin da Ateefa take don ance ba zasu iya shiga ba sai ta farka. 

“Thank you.”

Labeeb ya ce ma Dawud, ɗan ɗaga mishi kafaɗa yayi. 

“I am mad at you. Ina jin kamar in haɗa kanka da bangon wajen nan…….so ka barni kawai.”

“Na sani. Ka yi haƙuri.”

Shi ne kawai abinda Labeeb ya iya faɗi. Yana gyara zamanshi ya jingina bayashi da kujerar, kanshi da bangon wajen yana lumshe idanuwanshi. 

Fuskar yaron nan na mishi yawo, yaron da baya buƙatar DNA ya tabbatar mishi da cewar ɗanshi ne. Jininshi ne. Yadda aka same shi da ko daga jikin wa ya fito shi ne abinda yake ɗaure mishi kai.

Zai kula da wannan, ya fi damuwa da Ateefa a yanzun. Yana kallo kamar lokacin abin ya faru. Suna kwance kan kujera.

“Ina son yara Tee, yara daga jikin ki.”

Dariya ta yi kawai. Hakan yasa shi faɗin, 

“Ba wasa nake ba. Da gaske yara nake so.”

Juya kwanciyarta ta yi a jikinshi saboda kujerar ta musu kaɗan tana kallon fuskar shi. 

“Ba yara bane bana so tare da kai. Ina tsoron abinda zai ƙulleni tare da kai, zaman mu bashi da tabbaci.”

Haɗe fuska yayi. 

“Me ya hana shi rashin tabbas?”

“Akwai Mumynka. Kai da kanka, ranar da duk ka bi wata mace na gama zaman aure da kai. Bana son haɗa yara da kai kar su hanani tafiya.”

Buɗe idanuwa Labeeb yayi. Sam baya son wannan tunanin. Baida amfani, yanzun yasan ba zai bar Ateefa ta kubce mishi ba, balle babyn dake jikinta. 

Kamar an ce ya ɗaga kanshi. Ateefa ya gani ta fito daga ɗakin tana dafa bango. Da ƙyar take iya ɗaga idanuwanta. Da sauri ya tashi ya nufi wajen.

“Me kike yi haka? Za ki kashe kanki ne ko me? Wane irin rashin hankali ne wannan?”

Ƙoƙarin ture hannunshi take bata da ƙarfi, cak ya ɗauke ta ya shiga ɗakin da ita, Dawud na ganin haka ya tashi ya bi bayansu. Mukullan motar Labeeb ya shiga ya ajiye mishi akan gadon ya fice abinshi. 

Labeeb ya bishi da kallo har saida ya ja musu ɗakin. Kan gadon ya sauke Ateefa. Ya tallabi fuskarta.

“Ki kalleni Ateefa! Me kike so nayi? Hauka ko me?”

Hawaye ne suka zubo mata. 

“Bazan haɗa jini da mazinaci ba, bazan zauna da kai ba!”

Sakin fuskarta yayi. 

“Ni nai maki laifi, ki hukunta ni. Wallahi zan baki mamaki kika sake ƙoƙarin kashe min baby. Zaki san wanene El-Maska. Aurenki a hannuna yake aiko? Nake jin ba zaki saki kanki ba.”

Buɗe baki ta yi zata yi magana, cikin zafin nama ya haɗa bakinta da nashi. Tuna mata yadda yake sonta yake yi, tuna mata alƙawuransu yake yi. 

Kafin ya saketa yana maida numfashi.

“Don Allah ki bar min babyna. Ina sonku ku duka. Wallahi ina son ku.”

Ya ƙarasa maganar yana sauke muryarshi. Yana jin yadda hawaye ke taruwa cikin ƙwayar idanuwanshi. Gaba ɗaya komai ya birkice mishi. 

Yanajin fitowar ɗigon hawaye ɗaya da ya faɗo kan hannunshi, kallon hawayen yake. Ta cikinsu komai yake dawo mishi. 

Ta cikinsu yake ganin abinda El-Maska ya ja musu.

**** 

 RAYUWAR EL-LABEEB MASKA 

Kamar yadda mukaji a baya. Alhaji Ibrahim shi kaɗai ya ci gaba da harkar kasuwancin da yayi gado na mahaifin shi. Inda bai tsaya iya cikin garin Kaduna ba. 

Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin shi da matarshi Hajiya Habiba. Inda ‘yan uwanta suke ganin ta kowanne fanni Alhaji Ibrahim bai dace da ita ba. Bai kai ajin namijin da zata aura ba. 

Saboda masu kuɗi ne na gaske, a lokacin babanta shi ne minister mai ci, sannan mamanta lawyer ce babba, su bakwai ne a gidansu. Maza huɗu, mata uku, ita ce ta biyar.

Gaba ɗaya gidansu, daga Doctor, Engineer sai ɗaya daga cikin yayyenta babban Producer ne a Kannywood.

Aurensu da Alhaji Ibrahim ya fuskanci matsaloli da barazana daga danginta. Amma rubutaccen al’amari baya fasuwa. Da kuma ƙaunar ita kanta Hajiya Habiba. Haka suka haƙura bayan kafa mishi sharuɗɗa kala-kala. 

Na cewar zata ci gaba da aikinta da kuma business ɗinta da take yi. Ana kawo mata kaya daga dubai da Italy tana siyarwa gari-gari. Haka wasu cikin manyan kamfanoni na garuruwa takan haɗa hannun jari da su. 

Soyayyar da Alhaji Ibrahim yake mata yasa ya amince da duk wani sharaɗi na ahalinta. Don burin shi ya sameta kawai. Hakan akayi. Allah ya azurta su da ‘ya’ya biyar. 

El-labeeb shi ne na farko, Anees da Asad ‘yan biyu ne, Zainab sai autansu Arif. Wanda daga Alhaji Ibrahim har Hajiya Habiba babu mai lokacin kula da su.

El-labeeb shi ne ɗansu na farko, kuma shi Hajiya Habiba ta ɗora duk wani burinta akai, tana so ta ga ya shahara ya zama wani abu a rayuwa. Yana da shekara shida a duniya ta ɗauke shi ta miƙa ma yayanta da ya saka shi a harkar fim. 

Hakan bai yi wahala ba, kasancewar tun yarintar El labeeb abinda yake so bai wuce ya ga ya burge Mumnyn mshi ba. Don yana ganin in yai abinda zata yi alfahari da shi zai sa ta rage tafiye-tafiyen da takeyi ta bashi lokacinta. 

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar musu, Hajiya Habiba bata bada tazara tsakanin haihuwarta ba. Don kawai so take ta ga ta huta, yara biyar take ganin sun isheta, don da ƙyar ta yarda ta haifi Arif bayan Zainab. 

Asalin labarinsu zai fara ne a lokacin da Labeeb ya cika shekaru goma sha biyar a duniya yake aji biyar a Secondary school. 

**** 

Zaune yake cikin aji amma gaba ɗaya hankalinshi na gida. Yana kan Arif da ya bari hannun ‘yan aiki ga kuma Zainab da bata je makaranta ba, bata da lafiya. 

Miƙewa yayi, Abdul dake kusa da shi ya kalle shi. 

“Ina za ka je?”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa Labeeb yayi. 

“Gida, bazan iya zaman makarantar nan ba, beside gobe zan bar garin.”

Kallon shi Abdul yake kamar yana son suyi musayar matsayi. Girgiza kai Labeeb yayi. 

“Meye kake kallona haka?”

Murmushi yayi.

“You are so lucky, ka haɗa duka, kuɗi, popularity”

“Baka so ka zama ni Abdul, ka yarda da ni ba abu bane mai sauƙi kasan…….”

Kallon da Abdul yake mishi yasa shi ɗaukar jakar shi da ke ajiye. 

“Forget it.”

Ya faɗi yana ficewa daga ajin. Yana jin yadda idanuwan sauran ‘yan ajin ke binshi har ya fice daga ajin ya nufi office ɗin principal ya karɓo permit kafin ya fice daga makarantar. 

Ba driving bane bai iyaba. Ɗauko motar ne yake ƙara janyo mishi attention shi yasa yake biyo mashin duk ranakun da zai zo makaranta.

Gaba ɗaya a gajiye yake, shooting ɗin da suka yi a Kano sam bai huta ba. Haka ya dawo gida ya samu su Zainab shima bai hutan ba. 

Wani shago ya gani gefenshi, ya taka ya ƙarasa zai siya drink. Wani matashi ya gani zaune akan bencin da ke gefen shagon, yasan zasu zo shekaru ɗaya koma bai kaishi ba. 

Kamar an ce ya kalli ƙafarshi, jini ne ke ɗiga daga wani irin yanka dake jikin babban ɗan yatsan shi. 

“Ba zaka je a duba ƙafarka ba, sai ka kwashi infection a jiki.”

Lemon daya siya aka miƙo mishi, sannan saurayin da yai ma magana ya ɗago ya kalle shi. 

“Zai warke, karka damu.”

Labeeb baisan me yasa ya damu ba, girgiza kai yayi. 

“Ka je gida a rakaka asibiti.”

Murmushi yayi ma Labeeb dake tattare da emotions da yawa da ya kasa fahimta. 

“Ba makaranta zaka koma ba? Karka damu dani.”

Dafa kafaɗarshi Labeeb yayi. 

“Taso muje a duba maka, i think akwai chemist anan kusa.”

Babu musu ya bari Labeeb ɗin ya taimaka mishi ya miƙe. 

“Bansan me yasa ka damu ba, baka ma sanni ba.”

Kallonshi Labeeb yayi, gaskiya ya faɗi, bai sanshi ba, ya kuma rasa me yasa ya damun, bai cika damuwa da mutanen da basu haɗa jini ba. Sai dai yadda yake kallonshi ba tare da tsammanin wani abu ba, da kuma yana jin har da rashin wani aboki bayan ƙannenshi. Ba zai ce baida abokai ba,kusan kowa so yake yai mishi magana saboda kuɗin da zai iya basu ko saboda ace sun sanshi. 

“Ka cika surutu, muje kawai.”

Dariya saurayin yayi. 

“Daga sanina minti nawa kenan? Har ka gane ina da surutu.”

Murmushi Labeeb yayi, yana gyara zaman jakar makarantar shi a kafaɗarshi, lemon robar da ke hannunshi ya buɗe, ya kai bakinshi yasha sannan ya miƙa mishi. 

“El-labeeb Maska.”

Karɓar lemon yayi, yana daƙuna fuska kamar yana son tuna wani abu game da sunan Labeeb ɗin. 

“Mamdud…….”

Jinjina kai Labeeb yayi, haka suka ci gaba da tafiya ba tare da sun ce wa komai ba, har suka ƙarasa chemist ɗin da Labeeb ke faɗa. 

Ciki suka shiga, daga mai chemist ɗin sai wasu samari da zasu girmi su Labeeb ɗin. Magana Labeeb yayi mishi kan ya duba ƙafar Mamdud ɗin. Ɗaya daga cikin samarin da ke wajen a ɗan tsorace ya ce, 

“El-Maska?”

Cike da kasa yarda cewar Labeeb ɗin ne a gabanshi, murmushin daya saba ɗorawa a fuskarshi ya ɗora ya gaisa da su biyun, suna faɗa mishi yanda suke jiran fim ɗin da ya fito a ciki mai suna ‘A dalilina’.

Godiya yayi musu, suka fice, Mamdud da ake ma dressing ya ce, 

“Nasan akwai inda na taɓa ganinka ko na ji sunanka, amma na kasa tunawa sai yanzun, actor ne kai ko?”

Kai kawai Labeeb ya ɗaga mishi, Mamdud ne mutum na farko bayan family ɗinshi da ya haɗu da shi yake ganin abin da yake dashi da matsayin shi bai dame su ba. 

Ko mintina sha biyar bai yi ba da sanin Mamdud amma ya karanci hakan. Tsaf aka gama mishi dressing ɗin, ya bashi magunguna kala uku, Labeeb ya biya kuɗin suka fito. 

“Na gode.”

Mamdud ya faɗi. 

“Bakomai, mu sami mashin in sauke ka a gida sai in wuce….”

Murmushin da yayi ɗazun mai cike da fassara kala-kala shi ya sake yi. Gyara tsayuwa Labeeb yayi, a rayuwarshi baya son ɓoye-ɓoye. Bai iya ba, bakuma yaso ai mishi. 

“Ka ga, nasan baka san ni ba, but maganarmu ta farko na ji ina son mu zama abokai, ba don bani da su ba, ina buƙatar wanda matsayina da abinda nake da shi basa gabanshi. 

Wanda zai zauna da ni saboda ni ba don abinda zan iya bashi ba. So i will be honest, na faɗa maka sunana, ina da ƙannai guda huɗu.

Ajina biyar, sai me? Ina da sana’a ka sani, ina da kuɗi da bazan iya lissafawa ba….. So ina son sanin waye kai, in ba zai yiwu ba zan tsallaka titi in hau mashin.”

Kallonshi Mamdud yake yi, tunda ya fara magana kallonshi kawai yake yi, kafin ya ja isk ya fitar da ita ta bakinshi. 

“Na faɗa maka sunana Mamdud, bansan ko shi ne asalin sunana ba, banda kowa, a gidan marayu na buɗe idanuwa.

Bazance na yarda da kai ba, saboda abune da yake da wahala a wajena. Zan iya zama abokinka saboda ina buƙatar wanda zasu kalleni babu ƙyamata, wanda zasu zauna da ni bayan sunsan banda asali. 

In zan zauna da kai babu wulaƙanci…….”

Da sauri Labeeb ya ce, 

“Yes…. Ni bazan taɓa wulakanta ka ba. Mu je gidanmu.”

Kai Mamdud ya ɗan jinjina mishi, nan suka tsaya gefen titi, ba tare da wani ya sake cewa komai ba, har Labeeb ya tare musu mashin, suka hau guda ɗaya tare.

***** 

Tare suka shiga gida da Mamdud, tun daga falo yake jiyo kukan Arif, jakar makarantar ya ajiye kan kujera, da sauri ya ƙarasa cikin ɗakin Arif ya samu ‘yar aikin da ke kula da shi. 

Wadda ko sunanta bai sani ba, zaune hankalinta a kwance tana shan ice cream, ga Arif ɗin zaune yana ta kuka kamar zai shiɗe. 

Ta kuwa tsorata da ganin Labeeb, da sauri ta miƙe tana ajiye robar ice cream ɗin. Hannu ta kai zata ɗauki Arif. 

“Karki sake ki taɓa shi……”

Labeeb ya faɗi ranshi a ɓace yana ƙarasawa inda Arif yake ya sa hannu ya ɗauke shi, tun kayan da ya bari ne da safe, ko wanka ba ai mishi ba. 

“Fita…. Fita ba daga ɗakin ba, daga gidan gaba ɗaya. Karki sake dawowa.”

Baki ta buɗe zata yi magana, cikin tsawa Labeeb ya katse ta da faɗin. 

“Get out!”

Ba shiri ta fice, ya ja tsaki yana rocking Arif da ke ta kuka, juyawa yayi, ya ga Mamdud a tsaye. Hannu ya miƙa mishi. 

“Kawo shi ka gani.”

“Ba zai yi shiru ba, in ya fara kuka….. I dunno ƙila yunwa yake ji, ko wanka ne da ba ai mishi ba…..”

Ƙarasawa Mamdud yayi. 

“Ka yarda da ni, inda na ta so, mu muke duk wannan. Ka kawo shi.”

Kamar baya so, haka ya miƙa ma Mamdud Arif. Ya saɓe shi a kafaɗa, yana rocking ɗinshi a hankali. 

“Ina za ai mishi wanka?”

Mamdud ya buƙata, da sauri Labeeb ya ƙarasa toilet ɗin da ke cikin ɗakin Arif ya tura shi, ruwa ya gani a robar wankan Arif ɗin, ya sa hannu ciki, da ɗumi sosai. 

Da hannu ya nuna ma Mamdud da ya shigo, ƙarasawa yayi, ya sauke Arif da yayi shiru, ya cire mishi kaya, shi yayi mishi wanka, Labeeb na tsaye yana kallo. 

Ya gama suka fito tare, Labeeb ya ɗauko baby lotion ɗin Arif da kayan da za a canza mishi. Mamdud ɗin ya shirya shi tsaf, ya sabe shi a kafaɗarshi yana ɗan rocking ɗinshi. 

Magana Labeeb zai yi, da hannu Mamdud ya nuna mishi da yayi shiru. Shirun yayi, sun kai mintina sha biyar a wajen kafin Arif yayi bacci. A hankali Mamdud ya kwantar da shi kan gadonshi ya lulluɓe shi suka fito daga ɗakin . 

“Na gode, da baka nan bansan yadda zan yi da shi ba.”

Labeeb ya ƙarasa yana ɗan murza goshin shi da hannu. 

“Karka da mu.”

“Ka zauna, bari in dubo ƙanwata in zo in samo mana abinda za mu ci.”

Zama Mamdud yayi kan ɗaya daga cikin kujerun ɗakin. Labeeb kuma ya wuce ɗakin Zainab. da sallama ya tura, tana kwance kan gado ya ƙarasa ya zauna gefe. 

“Zeezee? Zee….”

Ɗago kai ta yi da ƙyar ta kalle shi, hannu ya kai ya taɓa fuskarta da wuyanta, zazzaɓi ne ruf jikinta har lokacin. 

“Sannu, kin sha magungunanki?”

Kai ta ɗan ɗaga mishi. 

“Zaki ci wani abu? Name it, ko me kike so zan siyo miki.”

“Ni Mummy nake so, yaushe zata dawo?”

Ɗan jim Labeeb yayi, shi kanshi buƙatar Mummyn yake, ƙila gara su, ya kai wata ɗaya rabon da ya ganta. Cikin sanyin murya yace. 

“Ban sani ba Zeezee, amma zata dawo soon.”

“Ohhhh…..”

Zainab ta faɗi, tana jan mayafinta ta rufe har fuskarta. 

“Zeezee mana, zata dawo fa.”

Daga cikin mayafin ta ce, 

“Ni ka tafi, bana son maganaaa”

Mikewa labeeb yayi, yasan zata iya saka mishi kukan da bai shirya ba, ya ja mata ƙofar, inda ya bar Mamdud ya same shi zaune. Kitchen ya wuce, ya tsani abincin restaurants ko na hotels. 

Abinci yake so ya ci da aka dafa a gida, ba zai ce abincin da Mummy ta dafa ba, don tunda yake bai taɓa sanin ya taste ɗin girkin da ta yi yake ba. Na ‘yan aiki kaɗai ya sani. 

Baya son barin Zainab ita kaɗai tunda ya kori ‘yar aikin da ta rage musu, sai kuma ya sa an nemo wata, da ya ɗauki Arif da Mamdud sun tafi gidansu Dawud wajen Ummi sun ci abinci. 

Tukunyar da ya gani a saman gas ya buɗe, ya lumshe idanuwanshi ya buɗe su ganin miya ce, ‘yar aikin nan ta ɗan yi abin arziƙi. Sauke tukunyar yayi, ya kunna gas ɗin ya ɗora ruwa. 

Lockers ya buɗe yana tunanin me ya fi saurin dahuwa, macaroni ya ɗauko leda ɗaya, ya jira ruwan ya tafasa, ya zuba ciki, yana dahuwa ya tace a basket ya ɗauki plates guda biyu ya zuba musu shi da Mamdud ya saka cokali ciki ya ɗauka ya fita falo da shi. 

Gaban Mamdud ya ajiye plate ɗaya, ƙasa ya zauna ya soma cin nashi yana faɗin, 

“Yunwa nake ji, in samu in gama kafin Arif ya farka, in haɗa mishi abinda zai ci.”

Mamdud baisan me zai ce ba, don haka ya ɗauki plate ɗin abincin ya ɗora kan cinyarshi ya soma ci, rabon cikinshi da wani abu tun jiya da rana. Wajen aikin da zai yi ya samu abinci yau ya ji ciwon da ke ƙafarshi. 

Yama riga Labeeb gamawa, tas ya cinye. 

“In ƙaro maka?”

Girgiza kai Mamdud yayi a kunyace. 

“Come on, akwai fa, in ƙaro maka?”

“Ruwa kawai zaka bani, Na gode.”

Miƙewa Labeeb yayi, ya ɗauko musu ruwa roba ɗaya da kofuna biyu ya zuba ya miƙa ma Mamdud. Karɓa yayi ya sha yana ƙara kallon gidan da kyawun shi. 

Ba sai an faɗa maka yanayin wadatar da suke ciki ba. Sai dai ya wuce kalar gidajen a hanya, bai taɓa shiga cikin irin su ba. 

Plates ɗin Labeeb ya ɗauka ya wuce kitchen ya ajiye, yana fitowa Asad da Anees na shigowa. 

“O. M. G……”

Labeeb ya faɗi yana ƙarasawa ya kama ɗaya daga cikinsu da yake tunanin Asad ne yana duba goshin shi da yake da plaster. 

“Waya ji maka ciwo?”

“Agogon Asad ya maƙale kan bishiya, na hau in ɗauko mishi na faɗo.”

Sauke numfashi Labeeb yayi. 

“Sau nawa zan hana ku hawa bishiya? Anees kaima ka fara rashin ji ko?”

“Mummy bata taɓa hanamu ba.”

Asad da ke tsaye ya faɗi, yana kallon Labeeb cike da rashin fahimtar dalilin da yasa yake hana su abinda ko Mummy bata hana su. 

“Ina ka ga Mummy ɗin?”

Anees ya tambaya yana hararar ɗan uwan nashi kafin ya kalli Labeeb da ke tsaye ya rasa me zai ce musu. 

“Ka yi hakuri, mun daina hawa.”

Kai ya ɗan ɗaga, Asad ya wuce yana nufar ɗakinsu. 

“Ina zeezee? Ta warke? Wai yaushe Mummy zata dawo? Ni kaina ciwo yake yi.”

Anees ya jero ma Labeeb tambayoyin, bai kuma jira amsarshi ba ya wuce yana bin bayan Asad. Juyawa yayi. 

“Ya kuke gane su? Kamarsu ta ɓaci.”

Mamdud ya tambaya cike da mamaki da burge shin da su Asad suka yi. 

“Ɗaya ya fi ɗaya surutu, da faɗa, in ba haka ba bana gane su, sai tabon da goshin Anees zai yi in bai ɓace ba kenan.”

Jinjina kai Mamdud yayi, kitchen Labeeb ya koma ya samu plate guda ɗaya ya zuba ma su Asad abinci a ciki ya saka cokali ya wuce ɗakinsu ya kai musu. 

Anees har ya cire uniform, Asad kam yana zaune kan gado da game a hannunshi. 

“Ka tashi ka cire uniform ka zo ku ci abinci.”

Game ɗin ya ajiye yana saukowa daga kan gadon. A shekaru sha uku har mamakin tsayi da girmansu Labeeb yake yi, don da kaɗan ya fisu, shi yasa Asad ya raina shi. 

In ba dole ba, ba son dukansu yake ba. Bar musu ɗakin yayi ya fito ya sake komawa kitchen ya dafa ma Arif ruwan tea ya sa a flask. Don yasan da ya tashi zai ji yunwa sannan ya dawo falo suka zauna da Mamdud suna kallo. 

**** 

Tun da ya taso a rayuwar shi yau ce rana ta farko da ya gane menene abokantaka. Tare da Mamdud suka shiga kitchen suka wanke duka kwanonin da suka ɓata, suka yi abincin da za su ci da dare. 

Akwai wani abu tattare da Mamdud mai shiga rai lokaci ɗaya, hatta Anees da surutu bai dame shi ba sai da suka yi hira da Mamdud ɗin. Zainab ce ma ko kallonshi bata yi ba da ta fito. 

Ta sake komawa ɗaki abinta, miskilancinta ko ‘yan gidan ba ko yaushe take kula su ba. 

“Fim ɗin da zamu tafi yi a Kano gobe babbane, sai dai Zainab bata da lafiya, ga Mummy bata nan. Samun ‘yar aiki zuwa gobe zai yi wahala.”

Labeeb ya faɗi yana jingina da bangon ɗakin shi da Mamdud ya gama taya shi gyarawa. 

“In nine zan zauna.”

Kallonshi Labeeb yayi, da idanuwa yake tambayar shi dalili. 

“Ka gode ma Allah, kana da ‘yan uwa, kana da wanda zaka kira naka, zan ajiye komai na kasance da ‘yan uwana in ina da su.”

Zama Labeeb yayi a gefen gadon shi kusa da Mamdud. 

“Ka kwana anan in babu wanda zai neme ka.”

‘Yar dariya Mamdud yayi. 

“Na tabbata babu wanda zai kula bana nan, balle har a neme ni.”

Duk magana ɗaya da zata fito daga bakin Mamdud tsaye take ma Labeeb a zuciyarshi. Kwata-kwata ya kasa hango kalar rayuwar Mamdud.

Baisan ko shi waye ba, in babu su Asad. ‘Yan uwanshi ne komai nashi, ko ya zai gaji, ko ya zai ji kamar idanuwan duniya gaba ɗaya na Kallonshi. In ya tuna zai dawo gida cikinsu sai ya ji komai ya dai-daita. 

“Kana zuwa makaranta?”

Ɗan ɗaga kafaɗarshi Mamdud yayi tare da faɗin, 

“Na gama aji uku, ban ci gaba ba.”

“Me yasa? Da karatu ne zaka zama wani abu a rayuwar ka.”

Dariya Mamdud yayi. 

“Me yasa na daina zuwa makaranta? Saboda babu mai siya min uniform, litattafai, lokacin da zan je makaranta ina yawon neman sana’ar da zan yi in ci abinci. Har yanzun kana son zama abokina? Da ka ga ciwo a ƙafata ɗazu, kasuwa na shiga inda muke sauke kaya a bamu kuɗi ƙarfe ya faɗo min. 

Kayan da ke jikina su kaɗai nake da su a yanzun, sai na cire na wanke sun bushe nake mayarwa. Har yanzun kakana son zama abokina?”

Shiru Labeeb yayi na tsawon mintina sama da biyar, wani irin shiru ya ziyarci ɗakin, kafin muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Kana faɗa min ne don in ƙyamace ka ko me? Ba rayuwarka bace kaɗai take da matsala, na sani bazan haɗa kaina da kai ba. Abinci ko sutura basu taɓa zama matsala a wajena ba. 

Baka san iyayenka ba, nasan nawa, sai dai ba su da lokacina balle sanin matsalata, shekara biyu ne tsakanina da su Asaad da ka gani, zan iya cewa a hannuna suka girma. 

Bansan yadda muka yi rayuwa ba, amma da wahala sosai a cikinta, haka Zainab, ga Arif yanzun. Ban taɓa saka kalar abincin Mamana a cikina ba. 

Kasan meye matsalarta? In zama wani abu, bata damu ko ina son acting ba ko bana so, bata bari na yi girman da zan zaɓa ba. 

Kuɗi ne suke min karatu a makaranta, saboda a wata uku da wuya in je na sati ɗaya. Zagaye nake da mutane da suke tare dani saboda abinda nake da shi. 

Kana faɗa min rayuwarka don in guje ka ne Mamdud? In na faɗa maka abubuwan da masu aikin da Mummy ta barni da su suka yi min da ƙafarka za ka gudu ka barni. 

Rayuwata ba kalar wadda ka saba da ita bace ba, ba abin so bace, ka zama abokina, zan tabbata taka ta zama irin wadda zan ba su Asad. 

Zaka yi karatu Mamdud, zan zame maka ɗan uwan da baka da shi. Abinci ya gama zama matsala a wajenka, kayan sawa sun daina zame maka damuwa…”

Fuskarshi Mamdud ya haɗe cikin hannayenshi. Kuka yake yi, hawaye ke zubar mishi da ya kasa tsayar da su. Baya tunanin akwai wata rayuwa da zata kai tashi muni. 

Duk lokacin nan, tun da ya fara gane bambacin abubuwa ya gane tashi rayuwar ba irin ta sauran yaran da yake gani a makaranta bane ba. 

In ba gidan marayun da suke bane, inda dubban yara suke ajiye batare da wani ya damu dasu ba, babu abinda zai kai wannan muni, ka kwanta kunnuwanka basa jin komai sai kukan yaran da wanda suka fisu girma suka zalinta. 

A baka abinci wanda ya fika girma ya ƙwace, kayi rashin lafiya kamar zaka mutu da ƙyar a dubaka sau biyu. Labeeb ba zai taɓa gane kalar rayuwar shi ba. 

Ko sau ɗaya yake so ya ga kalar iyayenshi, ya tambaye su me yai musu zasu yarda shi, ya tambayi mahaifiyarshi shege ne shi ko da ubanshi, ya tambayeta me yasa bata zubar da cikinshi ba. 

Sai dai yau ne karo na farko da wani ya taɓa mishi alkawari, alƙawari mai girma haka. Yau ne karo na farko da aka bashi abinci cikin girmamawa. 

Yau ne karo na farko da duk matsayin Labeeb bai nuna mishi ƙyamata ba, bai nuna mishi shi ɗin bakomai bane. Ya miƙo mishi igiya yana so ya fito dashi daga rijiyar da yake ciki. 

Ya kasa tsaida hawayen da ke zubo mishi, saboda su kaɗai ne sauƙin da yake samu daga raɗaɗin da ke zuciyarshi. Dafa kafaɗarshi ya ji Labeeb yayi. 

Hakan yasa shi ɗago fuskarshi, ya sa hannuwa yana goge hawayen da suka zubo mishi. Kaya ne a linke riga da wando na shadda da Mamdud yasan tana da tsadar gaske. 

“Ka sake na jikinka. Ba kayan kaɗai ba Mamdud, har rayuwarka gaba ɗaya.”

Karɓa yayi. Muryarshi na rawa ya ce, 

“Na gode.”

“Babu godiya a tsakanin abokai, babu godiya a tsakanin ‘yan uwa. Karka bani dalilin da zanyi da na sanin yau Mamdud.”

“Bazan taɓa baka ba, ba zaka taɓa da na sanin zama abokina ba, zanyi komai saboda ɗan uwana.”

Murmushi Labeeb yayi, ya nuna mishi ɗakin da zai shiga ya sake kaya. Ya miƙe ya shiga, sauke numfashi labeeb yayi. Yana jin maganar da suka yi da Mamdud kamar ta rage mishi nauyin da ke ƙirjinshi kaɗan. 

Bashi da wanda yake tunkara da damuwarshi. Yana jin tare da Mamdud ya sami wannan. Fitowa yayi, ya ɗan fi Labeeb tsayi, amma kayan sun mishi dai dai. 

Ba labeeb kaɗai ya ga ya canza ba. Har shi kanshi Mamdud ɗin yana jin yadda ya canza duk da baya ganin fuskarshi. 

“Mamdud Ibrahim Maska.”

Labeeb ya faɗi, yanajin sunan yayi mishi. Dariya Mamdud yayi, duk da hawayen da suka zubo mishi. Yau shine da sunan Uba. Muryarshi cike da shakku yace. 

“Abbanku? Ba zai yi faɗa ba, sunan shi……”

Dariya Labeeb yayi. 

“Daddy muke kiranshi, ba zai yi faɗa ba. Ni zan yi accepting ɗinka . Kuma na yi, kana da asali Mamdud, kai ɗan gidan Maska ne!”

Kai kawai mamdud yake ɗaga ma labeeb saboda ba shi da bakin magana, ba shi da abinda zaice akan karamcin Labeeb. 

*

Tare suka fita sallar Isha’i. A hanyar dawowa Mamdud yake ce ma Labeeb, 

“Me ‘yan aiki suka yi maka?”

Ɗan jim yayi, kafin ya girgiza kai. 

“Baida amfani, ko menene ya canza ni ta ɓangare marar kyau, ban kuma san yadda zan gyara ba. 

Abu mai amfani yanzun shi ne ganin hakan bai faru da su Asaad ba. Za ka iya fara makaranta daga aji huɗu?”

Hirar makaranta suka shiga yi har suka kai gida. Daren ranar Mamdud yai ma Arif wankan dare, shi ya bashi tea ya kuma riƙe shi har yai bacci. 

“Anan zai kwana shi kaɗai?”

Dariya Labeeb yayi. 

“Nan ne ɗakin shi ai”

“Na gani, amma ban ɗauka a nan zai kwana ba. Shekararshi nawa?”

“Biyu da wata huɗu, in yai kuka zanji har ɗakina”

“uhmmm.”

Kawai Mamdud ya faɗa yana ganin tasu kalar rayuwar, don ba ruwanshi, haka suka saba, amma gani yake arif yai ƙanƙantar abarshi a wannan ƙaton ɗakin shi kaɗai. 

Haka suka fita, Labeeb ya kashe mishi fitila ya ja ɗakin a hankali. 

“Ka wuce ɗakina, zan duba su Asad, akwai kayan kallo ka kunna in kana so.”

Wucewa Mamdud yayi, shi kuma ya nufi ɗakin su Asad. Suna zaune sun baje litattafai akan kafet ɗin ɗakinsu. 

“Me ake yi haka?”

“Note nake taya Asad.”

Anees ya bashi amsa, zama yayi a tsakiyarsu, ya ɗauki ɗaya daga cikin litattafan yana dubawa yana jansu da hira, a hankali yake jin kome ke tafiya a rayuwar su da ya yi missing kwana takwas ɗin da yayi baya gida. 

“Cikunku wanda bai wuce 3rd position ba, sai ya zaɓi kalar abinda yake so, ina nufin har Islamiyya. “

Murmushi Asad yayi.

“Zan fi Anees ƙoƙari wannan time ɗin Yaya.”

Dariya Anees yayi, kamar cewar maganar da Asad ɗin ya faɗa abune mai wahala. 

“Ku dai kwanta da wuri, banda game, kar in dawo in ga baku kwanta ba. Me za ku ci da safe?”

“Anees ya faɗa, ni komai ma ina ci.”

“Irish da tea, kar a soya eggs ɗin a dafa mana.”

Kai Labeeb ya ɗaga musu, ya miƙe yana faɗin, 

“Saida safenku. Love you.”

“We love you more.”

Suka fada a tare, ya fita ya bar musu ƙofar a buɗe kamar yadda ya ganta, ɗakin Zainab ya nufa, tana zaune tana kallo da ice cream a gabanta sa’adda ya tura ɗakin. 

“Yaya baka yi min knocking ba.”

Dariya ta bashi, komawa yayi, ya ƙwanƙwasa.

“Shigo…”

Ta ce sannan ya buɗe ƙofar ya shiga, ya zauna a gefenta. Hannu yasa ya taɓa wuyanta da fuskarta, zazzaɓin ya sauka. 

“Babu fever ɗin ko?”

Kai ta ɗaga mishi. 

“Ma shaa Allah. Zaki iya zuwa makaranta gobe ko a barki ki ƙara hutawa?”

“No zanje, na haɗa school bag ɗina ma, da komai duka.”

“That is my little sister.”

“Ni ba little bace fa. ‘Yan mata zaka ce Yaya.”

Dariya yayi sosai, itama kuma abin ya bata dariya. 

“Good night.”

“Zeezee korata kike yau?”

“Ni bacci nake ji, ice cream ɗina kawai zan shanye, akwai school gobe.”

Miƙewa yayi, ya sumbaci goshinta. 

“Sweet dreams, love you.”

“Me too.”

Ta amsa tana sumbatar kuncin shi. Zai fice ta ce. 

“Yaya kashe min TV ɗin.”

Kashe mata yayi, sannan ya ja mata ƙofar. Ya nufi ɗakinshi. Duk da ya ga ta ji sauƙi zai haƙura da tafiya Kano goben nan. 

Zai je da safe ya faɗa ma Uncle a ƙara mishi kwana biyu. In ya samu ‘yar aikin da zata zauna da su sai ya je. Ga mamakin shi bacci ya samu Mamdud yayi akan kafet. 

Ƙarasawa yayi ya ɗan bubbuga shi. 

“Mamdud bacci a ƙasa, ka tashi ka hau gado.”

Cikin bacci ya ce, 

“Nan ma yayi…”

“Ka tashi mana, sai ka ɓata min rai da daren nan. Meye haka ɗin wai?”

Saida Mamdud ya ga da gaske ran Labeeb ɗin zai ɓaci tukunna ya tashi ya koma kan gadon. Da alama ya gaji sosai don ko minti biyar bai yi ba da komawa kan gadon bacci ya ɗauke shi. 

Labeeb kam wanka yayi sannan ya fito, ya sake kayan jikinshi ya mayar da na bacci, drawer ɗin gefen gadonshi ya janyo, kuɗin da ya samu na wata biyu sune a ciki da yawa. 

Sai kuma wanda Mummy ta bashi na makarantar su Asad da kuɗin hidima da ko taɓa su bai yi ba. Mayarwa yayi ya rufe ya kwanta gefen Mamdud, bai ji ya takura ba saboda gadon na da girma. 

Kuma ya saba sharing ɗin wajen kwana wasu lokutan in suna location shooting ɗin fim. A haka bacci ya ɗauke shi cike da tunani barkatai. 

<< Rayuwarmu 19Rayuwarmu 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.