Bai koma gida ba ranar, wani irin party suka yi da ya jima bai yi irin shi ba, kwana yayi da mata har huɗu, runtsa bai runtsa ba ranar.
In ranshi na ɓace baisan wata hanya ta mantawa da ya wuce shaye shayenshi da mata ba. Da safe ya samu yayi bacci har wajen sha biyu. Sannan ya sake yin wanka.
Ciwon kai yake ji kamar ya cire ya ajiye shi a gefe. Mamdud ne ya shigo.
“Yau saukar su Sajda fa, ka samu waje ka zauna.”
Da ƙyar Labeeb ya buɗe idanuwanshi akan Mamdud.
“Ku yi gaba, zan taho nima, kaina kamar zai rabe biyu nake ji.”
“You drink too much jiya”
“Ohhh ka tafi Mamdud, kana min ihu a saman kai.”
Dariya Mamdud yayi yana ficewa daga ɗakin. Labeeb ya koma ya kwanta kan bayanshi yana dafe ekanshi. Yadda yake jin nan bashi da energy ɗin fada da Zulfa.
Ba don bata da matsayi ko muhimmanci ba a idanuwanshi. Auren ne baya hango ma kanshi, tunanin shi da mata a yanzun har amai yake ji.
Yana hango ma kanshi aure har ma da yara wata rana. In ya bar wannan rayuwar, ya ji da kula da su Asad a yanzun. Bai fita daga gidan ba sai da yayi sallar Azahar tukunna.
Yana shiga da sallama bai ga kowa ba ma a falo, kanshi tsaye ya wuce ɗakin Zulfa, ya ƙwanƙwasa ya ji shiru, a hankali ya tura yana zura kai.
Tana zaune a gaban mudubi tana kwalliya. Sauke numfashi yayi.
“Kina ciki ashe.”
Shiru ta yi tana gyara girarta kamar bata ji shigowarshi ba ma balle maganar da yai mata, zama yayi kan kujerar dake ɗakin.
“Zulfa…”
Bata ce komai ba. Kwalliyarta take yi kawai. Mikewa yayi ya ƙarasa ya tsaya a bayanta suka haɗa ido ta cikin mudubin. Zuciyarta tai wata irin dokawa, don tun jiya duk wani tunaninta ya canza akanshi.
Duk wani yanayi da take ji wanda ta kasa fahimta ta gama gane shi, sai yanzun take jin yadda zuciyarta ke bugawa da sonshi. Kominshi dabanne.
Idanuwanshi cikin nata ta mudubin ya ce,
“Ni nake magana kike shareni ko?”
Ya ƙarasa yana ɗaga mata gira, bakinta ne ya bushe babu yawu ko kaɗan a ciki. Sauke idanuwanta ta yi, ta kai hannu ta ɗauki sarƙarta zata saka.
Hannunta ya kama ya karɓe sarƙar, da kanshi ya saka mata. Hakan ya ƙara tsananta bugun da zuciyarta take yi.
“I am sorry. Muhimmanci da matsayinki a wajena mai girma ne. Zanyi aure, amma ba yanzun ba. Zunubaina masu yawane, bansan ko auren zai iya danne wildness ɗin dake cikina ba Zulfa. Bana son cutar da ‘yar mutane, bana son ƙara cutar da kaina.”
Miƙewa Zulfa tayi ta kama kitson da ke kanta ta tattara gashin waje daya tana ƙullewa da abin ɗaure gashi.
“Ba mu da maganar da za mu yi kenan. Ka je abinka kawai. Kai da kanka ka ce aure kawai bai isa ya hanaka komai ba. Ballantana kuma ni.”
“Ba haka nake nufi ba. Kin ga ni yunwa nake ji, ga kaina na ciwo. Bana son yin faɗa yanzun.
Bari in shirya mu tafi tare.”
Haka kawai tun jiya sai hawaye yaita ciko mata idanuwa ko ya tayi tunanin shi da abinda ta gani da kishin abinda take so yayi.
“Ni kaɗai zan tafi….bazan iya zama mota ɗaya da….da kai ba.”
Wani abu ne ya taso mishi tun daga ƙafarshi yana tsayawa a ƙirjinshi. space ɗin da ke tsakaninsu da Zulfa ya haɗe, ya kamata yana juyo da ita, hannunshi yasa bayan kanta ya riƙe abinda ta ƙulle kitsonta da kitson duka a hannunshi.
Bai riƙe da ƙarfi ba, amma yadda zuciyarta ke dokawa da kuma kallon da yake mata tasan ba zata iya ƙwacewa ba. Banda ita ɗin babu macen da zai faɗa tana faɗa.
Balle har ta gaya mishi abinda take so.
“Me kike son cewa. Ba zaki iya shiga mota daya da wa ba? Ki ƙarasa maganar da kika yi niyya kafin ki canza ta. “
Idanuwanta cike taf da hawaye. Muryata can ƙasa ta ce,
“Ba abin da zance. Ka ƙyaleni Yaya Labeeb.”
Sosai yake kallonta kafin ya ce,
“Matsayinki ba zai bari isata tai aiki akanki ba. Karki ɓata min rai, ki jira ni in shirya mu tafi tare.
Ba buƙatar hakan na yi ba. Umarni ne!”
Yana ƙarasa maganar ya sake mata gashi ya fice daga ɗakin yana doko ƙofar da ƙarfin gaske. Ƙasa ta zauna ta ɗora kanta kan gadon tare da sakin wani irin kuka.
Komai ya dagule mata, ta sha ganin wani fraction na ɓacin ranshi amma ba irin na yau ba. Yau kala dabanne ta gani kuma bata son shi ko kaɗan.
Sai da tayi mai isarta, zuciyarta kamar zata fito, ta sake komawa toilet ta wanke fuskarta don ta dame kwalliyar gaba ɗaya ta fito ta sake sabuwa sannan ta zauna tana jiran Labeeb.
Bata son sake ɓata mishi rai fiye da wanda tayi babu jimawar nan. Ita kanta ta gaji da rigimar. Kanta ciwo yake, don babu abinda ta ci tunda ta tashi. Ta kuma nemi yunwar ta rasa.
*****
Yana shiga ɗaki ya wuce banɗaki. Ko kayan da suke jikinshi bai cire ba ya sakar ma kanshi shower. Tsoro yake ji har ƙasan zuciyarshi.
Tsoro yake ji sosai, tunda yake a wajen gidansu yake barin komai da ke tattare da El-Maska ya shigo a El-Labeeb ɗinshi. Yana jin tsoro yadda ɓangarenshi da yake ɓoyewa yake son rinjayar wanda yake son ƙannen shi su gani.
Mutumin da yake son ya zame musu, wanda za su so suyi alfahari da shi, baisan abinda ya sashi yi ma Zulfa abinda yai mata ba.
Sai da ya baro ɗakin sannan hankakinshi ya fara dawowa jikinshi, nutsuwa ta fara dawo mishi. Zulfa ce ba wata ba, dole ya bata haƙuri.
Kayan jikinshi ya cire ya bar su nan yai wanka sosai ya fito ya gama shiryawa, kamar ko da yaushe suspenders ne a jikinshi. Yana ƙarasa shiryawa ya fito daga ɗaki ya ci karo da Zainab.
Kallo ɗaya tai mishi ta ce,
“Meke damunka?”
Ɗan ɗaga mata kafaɗa yayi.
“Babu komai.”
“Ka ce ba za ka iya faɗa min ba Yaya. Kasan yadda nake ji in akai min ƙarya.”
“I am sorry. Abubuwa ne suka yi min yawa, amma ba wani na damuwa bane. Har da stress.”
“Ka huta mana, ko na sati biyu Yaya”
Dan jim yayi kafin ya ce,
“Da mun ƙarasa wannan fim ɗin, zan huta fiye da sati biyu ma.”
“Ka tabbata?”
Murmushi yayi.
“Ni zan kula da ku. Kin manta? Not the other way.”
Dariya tayi.
“Kaima kana son kulawa Yaya. Mun kusan fixing ɗinka da wata tunda ka ƙi samo mana Anty.”
Ware idanuwa Labeeb yayi.
“Kun gaji da ni ba Zee Zee? Seriously meye damuwar kowa da in yi aure ne?”
Murmushi Zainab tayi tana ɗan ɗaga mishi kafaɗa.
“Na tafi wankin kai, daga nan zan wuce wajen saukar Sajda.”
“Banda gudu dai. Allah ya tsare.”
Ta amsa da amin tana ficewa. Ɗakin zulfa zai nufa ta fito, ta yi wani irin kyau da baya gajiya da bashi mamaki. Sai dai ta ƙi haɗa idanuwa da shi.
Wuce wa yayi gaba ta bishi a baya har motarshi. Ta gama haɗa abinda zata ba sajda ta kai gida ta ɓoye tun sauran sati biyu.
Saida suka hau hanya sannan Labeeb ya ɗan kalleta ya mayar da hankalin shi kan tuƙin da yake sannan ya ce,
“I am sorry, abinda nai bai kamata inyi ba. Kina da muhimmanci a rayuwata Zulfa. Fushinki wani abune da bana so. Kiyi haƙuri.”
Ba tare da ta kalle shi ba ta ce,
“Banda shi kam, tunda ban isa kai aure ka cire kanka daga halaka ba. Ka daina bani haƙuri, ni ce zan baka haƙuri da nai maka Shisshigi cikin rayuwar ka.”
“Me yasa ba za ki fahimce ni ba? Me yasa ba za ki gane aure ba shi bane solution a rayuwata?”
Bata ce komai ba har suka ƙarasa islamiyyar su Sajda inda yake cike da taron mutane, ko parking zulfa bata bari ya gama ba ta buɗe motar ta fito.
Da sauri Labeeb ya ƙarasa parking. Ya fito, ranshi a ɓace yake kallon Zulfa.
“Baki da hankali ashe? Inda gudu nake kuma fa? Zulfa kina zuwa min wuya wallahi. Kina son ɓata min rai ne na ga alama.”
“Meye na damuwa kuma? Duk abinda zai sameni iya duniya ne, baka damu da abinda zai samu lahirarka ba ma.”
Ta faɗi tana ɗan ware mishi idanuwa. Maganganunta sun mishi zafi sosai da sosai. Wata irin zuciya gare shi, shi yasa baya bari mutane su shiga jikinshi. Wanda suke da muhimmanci ne kawai suke iya ɓata mishi rai ya jure.
Yana kallonta ta taka ta kƙarasa inda su Dawud suke. Murmushi ya nema da ƙyar ya ɗora kan fuskarshi ya ƙarasa. Ba wani daɗewa yai ba.
Yai musu sallama. Ya so magana da Zulfa ta share shi kamar bata gani ba. Da nauyin zuciya ya koma gida. Yana jiran ta dawo suyi magana. Faɗan nan ya ishe shi haka.
****
Kwananshi huɗu a garin Kaduna amma Zulfa bata dawo gidan ba. In ya kira wayarta ma kashewa take yi. Daga ƙarshe gaba ɗaya wayar ta kashe.
Wannan shi ne karo na farko a rayuwarshi da yake cikin garin Kaduna Zulfa tai kwana biyu bata kwana ƙarƙashin inuwar gida ɗaya da shi ba.
Koda bai kwana gida ba sanin kowanne lokaci ya dawo zai sameta kawai yakan saka mishi wata nutsuwa da baisan da ita ba sai yanzun da bata nan.
Party biyu aka gayyace shi amma ko ɗaya bai je ba. Ko na gidanshi da ya je kasa yin komai yayi, bai sha wani abu ba, don tunanin Zulfa kaɗai yake da shi baya son ya sha abinda zai mantar da shi ko na minti ɗaya ne.
Sau biyar yana zuwa hanyar gidansu, iyakacin shi titi, zuciya ta hana shi ya ƙarasa, don gani yake bai mata laifin da zata zaɓi tai mishi nisa har haka ba.
Saboda me ba zata fahimci uzurinshi na guje wa aure ba. Wunin ranar kwance yayi shi a gida. Sallah kaɗai ke fitar da shi. Yanzun hakan ma kwance yake ya dawo sallar Magariba.
Zainab ta shigo gidan da ledojin Rich bites a hannunta ta baje su a tsakar ɗakin. Sam bai ji sallamar ta ba, sai da ta ɗan taɓa mishi hannu.
“Yaya! Meke damunka haka?”
Tashi yayi zaune ya dafe kanshi yana sauke wani numfashi mai nauyi.
“Bana jin daɗin jikina ne Zee Zee.”
“Me yasa ba za ka je a dubaka ba?”
Ɗan murmushi yayi kawai baice komai ba.
“Zulfa ce ko?”
Tambayar ta mishi bazata, kuma zai rantse Zainab ta karanci amsar shi a fuskarshi kafin ya furtata. Don haka baice komai ba.
“Ka je kai mata magana mana.”
Zainab ta faɗi.
“Ki barta kawai. Beside gobe in Allah ya kaimu zan bar garin.”
“Shi ne dalilin da zai sa kaje kai mata magana ai.”
Girgiza kai yayi, yadda Zainab bata son takura haka bata son takura ma wani. Don haka ta kwashe ledojinta ta nufi ɓangaren su Asad ta kai musu nasu ta kai ma Arif nashi ta wuce ɗakinta.
Miƙewa Labeeb yayi, kanshi da ke ciwo ne kawai alamar da yaji jikinshi na nunawa ta cewar yana buƙatar abinci. Duk ranar bai ci komai ba.
Kitchen ya nufa ya ɗauki strawberry yogurt ya sha ya koma ɗakinshi ya kwanta. Yana nan Mamdud ya shigo.
“Wai kai me yake damunka?”
“Shine sallamar ka kenan?”
Labeeb ya buƙata.
“Da gaske nake. Wani abu na damunka.”
Nisawa Labeeb yayi kafin ya ce,
“Zulfa ce Mamdud. Bamu taɓa faɗa irin wannan ba, gaba ɗaya a takure nake ji na.”
Kwashewa da dariya Mamdud yayi.
“Soyayyar ku na bani mamaki.”
Kallonshi Labeeb yayi daga inda yake kwance.
“Me kake nufi?”
“Ka ce mata kana sonta, duk mu huta.”
Tsaki labeeb yayi.
“Matsalar baka da hankali lokuta da dama. Bansan sau nawa zance maka babu wannan soyayyar a tsakanin mu ba ka yarda.”
Rigarshi da ya cire ya jefa ma Labeeb a fuska.
“Babu rana. Kallon da kuke ma juna babu wanda baya kula.”
Rigar Labeeb ya cire daga fuskarshi yana jefar da ita gefe ɗaya. Tsautsayi ne yasa yaima Mamdud maganar Zulfa. Baisan me yasa kowa yake ɗauka kalar soyayyar dake tsakanin su kenan ba.
Gyara kwanciya yayi, ya lumshe idanuwanshi, bacci ko ɓarawo bai sace shi ba. Kan kunnen shi akai kiran sallar Asuba, ya tashi Mamdud.
Wajen bakwai na safe ya gama shirya komai, wannan karon banda Mamdud don suna ta test a makaranta, saboda exams ya ƙarato.
Shi kaɗai ya tafi garin kano.
*****
In yace ga yanda satika ukun da yagi a Kano suka wuce mishi ƙarya yake, zai iya cewa akwai party da mata dabai san adadin su ba, wanda ko na minti ɗaya basu mantar da shi ciwon da ƙirjinshi yake ba.
Har abokan aiki sai da suka tambaye shi ko lafiya, saboda tun da ya fara fim wannan shi ne karo na farko da ya manta lines ɗinshi.
A daddafe suka ƙarasa aiki ya dawo gida, kallo ɗaya za ka yi mishi ka ga duhu da ramar da yayi. Bai kira Zulfa ba text ya tura mata.
‘Na dawo. Ina gida.’
Bata yi reply ba, bai zaci ɗaya ba dama. Abinda ya sani shine ba zai iya jure yanayin da yake ji ba. Damunshi da su Asad suke kan yaje asibiti yasa shi ɗibar mukullin mota ya fice daga gidan.
Gidanshi ya nufa. Yana shiga kitchen ya nufa, ya buɗe inda yasan yana ajiya abinshi, ƙwayoyine ya ɗauko, yasan ɗaya ma in ya sha ta wadatar, amma biyu ya sha ya kulle gidan daga ciki, ya kashe wayarshi sannan ya nufi bedroom ya rage kayan jikinshi ya kwanta.
Ko minti biyar bai yi ba ƙwayoyin da ya sha suka soma aiki, bacci mai nauyin gaske ya ɗauke shi. Bai tashi ba sai bayan Magariba.
Banɗaki ya shiga ya watsa ruwa yana jin yanda jikinshi gaba ɗaya yai nauyi, sannan yayo alwala, yana jin duk babu daɗi don ba sabon shi bane haɗa salloli har haka.
Yana idarwa ana kiran sallar isha’i don haka ya fita masallaci yayo ya dawo ya ɗauki wayarshi da mukullai ya kulle gidan. Naf Club ya nufa. Waje kawai ya samu ya zauna ko mutane da suke mishi magana da ƙyar ya dinga amsa su.
Sha ɗaya da wani abu ya bar Naf Club ya nufi gida, don yasan ko su Asad ba suyi bacci ba babu kowa a falo. Kanshi tsaye ba tare da tunanin komai ba ya danna kai falon.
Sai da zuciyarshi tai wani irin dokawa ganin Mummy zaune a falon, hannun ta riƙe da kofi da juice a ciki. Kamar ba dare bane ba, zai iya rantsewa bai taɓa ganin fuskar Mummynsu babu kwalliya ba.
Ko da yaushe sanye take da shiga ta alfarma, da basu kaɗai ‘ya’yanta ba har mutanen waje kallo ɗaya za su uyi mata su san kuɗi ba matsala bane a wajenta.
Takalmanshi ya cire ya ƙarasa ya zauna akan kujera.
“Mumy ban zaci samun ki a gida ba.”
Labeeb ya faɗi, idanuwanta da suke sak irin nashi ta sauke kanshi.
“Shi yasa kake shigowa gida yanzun kenan? Magana nake so muyi shi yasa nake jiranka, zamu tafi Dubai jibi da su Hajiya.”
Yasan kakarsu take nufi da Hajiya. Ganin shi Mummy take jira ya amsa ta yasa shi faɗin,
“Da kin kwanta ko da safe sai muyi magana.”
Kallon Labeeb tayi kama yayi suggesting wani abu mai girma.
“Banda lokaci, za a sauke min kaya gobe in Allah ya kaimu. Anyway akwai yarinyar Hajiya Jamila. Ina so kaje Ka ganta.
Na maka text ɗin address ɗin.”
Sosai labeeb yake kallon Mummy, sai dai sam ya kasa mamakin abinda tayi, saboda ba baƙon abu bane. Bata nan a rayuwar su, bata damu da yadda suke kwana suke tashi ba.
Amma ta damu da yadda take so rayuwar su ta kasance. Perfect life, kamar yadda take ganin rayuwarta take a tsare.
Wani abu ne ya sake danne mishi ƙirji kan damuwar Zulfa da yake ji. Ya kai mintina biyar yana tauna maganar Mummy. Faɗa mishi da ta yi yaje ya ga yarinyar baya nufi koda yace batai mishi ba zata saurare shi.
In don ta Mummy ne da wahala in basu gama maganar har da Dadyn su ba. Son da Dady yake mata baya barinshi ya ga kuskuren hukuncin da duk zata yanke akansu koda akwai shi.
Gani yai kusan ma mafita ce Mummy ta samar mishi, in ɗaya daga cikin yaran ƙawayenta ne ya tabbatar ‘ya’yan masu kudiene da zasu amince da aurenshi da matsayi da abinda ya tara.
Duk da sam ba haka ya hango auren shi ba, ya hango samun matar da zai iya haɗa iyali da ita, wadda zata so shi ɗin da kanshi. Kafin zuciyarshi ta hana shi yace ma Mummy,
“Ba sai na ganta ba Mummy. In ta miki ta min, ki ƙarasa komai kawai.”
Murmushi Mummy tayi.
“Really?”
Kai ya ɗaga mata.
“That is my son. Na san ba za ka bani kunya ba. Suma ba wani lokaci suke so a ɗauka ba. Mun gama maganar komai, sati ɗaya nace. Don nasan ba lokaci gare ka ba.”
Dama ya sani, kanshi yaji yana juya mishi. Da gaske auren zai yi, can ƙasan zuciyarshi wani ɓangare ke faɗa mishi hankalin Zulfa saiya kwanta.
Sai dai abinda zuciyarshi ke ji kawai ya tabbatar mishi babu abinda auren nan zai canza, already ya riga ya tsani yarinyar tun kafin yaganta.
Miƙewa Mummy tayi.
“Sai da safe. Love you.”
“Bana son wani babban biki, just family, bana son hayaniyar komai.”
Wata ‘yar dariya Mummy tayi.
“Believe me bani ma lokacin, nan da sati ɗaya ina Dubai ma.”
Ware idanuwa Labeeb yayi.
“Mumy. Kina nufin ba kya nan za a yi auren nawa?”
Girgiza kai Mummy tayi da murmushi a fuskar ta, tana wucewa ta ce,
“How old are you? Sixteen? Bacci nake ji Labeeb.”
Ta ƙarasa tana wucewa abinta. Labeeb ya bita da kallo har ta ɓace mishi. Sauke numfashi yayi.
“Great!!!”
Ya faɗi yana sa ƙafa ya ture center table ɗin sake gabanshi. Abinda Mummy za ta yi mishi bayan fixing ɗin auren shi shi ne ace tana nan.
Miƙewa yayi, komai na jikinshi ce mishi yake ya koma Naf club ko gidanshi ya sha giya ko ƙwaya har saiya manta abinda ya faru yanzun.
Har ya juya muryar Anees ko Asad da ba tantancewa yake ba in ba zaune suke tare ba ta daki kunnen shi.
“Yaya?”
Lumshe idanuwanshi Labeeb yayi, ya buɗe su yana juyawa. Takowa yai ya ƙaraso inda yake.
“Munata kiranka. Ina kaje haka? Ya jikinka?”
Kasa magana yayi, gaba ɗaya abinda yake faruwa da rayuwarshi ya ishe shi. Gaba ɗaya rayuwa da kanta ta ishe shi. Komai dawo mishi yake kamae lokacin ya faru.
Yana jin ƙirjinshi kamar zai buɗe, yana jin rashin uwa da yake fama da shi ba don ta rasu ba. Yanayin fuskarshi kaɗai ya isa ta gane baya son auren nan.
Wata irin kewar Ummin su Dawud yake ji da tunda ta rasu bai ji kalarta ba. Ba sai ya faɗa ma Ummi damuwarshi ba. Data kalle shi take ganewa.
Nasihunta da kalamanta kan sa ya ji komai yai mishi sauƙi. Zulfa kuma da zai gani ya ɗan samu nutsuwa ita ma bata nan. Runtse idanuwanshi yayi, amma me baya ganin komai sai fuskar ‘yar aikin da ta yi sanadin lalacewar rayuwarshi.
Wani irin numfashi ya ja da yasa Asad dafa mishi kafaɗa.
“Yaya…yaya…”
Buɗe idanuwa Labeeb yayi yana jin komai ya mishi zafi. Muryarshi a sarƙe ya ce,
“Aure zan yi next week.”
Sakinshi Asad yayi yana kallonshi kafin ya kwashe da dariya. Ganin yanayin fuskar Labeeb yasa shi faɗin,
“No da wasa kake Yaya.”
Girgiza mishi kai labeeb yayi.
“Da gaske nake, Mummy tayi fixing komai.”
Fuskar Asaad ɗauke da wani irin ɓacin rai ya ce,
“Sai kuma ka yarda? Yaya yaushe zaka fara ce ma Mummy A’a ne? Saboda me zata dinga zaɓar maka yadda zaka yi rayuwa bayan bata cikin ta? Kasan me, in ba zaka iya ce mata baka so ba bari in je in faɗa mata…”
Asad ya ƙarasa yana juyawa, riƙo shi Labeeb yayi. Yanayin shi ne yasa ya gane Asad ne.
“Asad….”
Fisge hannun shi yayi.
“No yaya! Gaba ɗaya rayuwarka ta ƙare ne a kula damu, you deserve matar da kake so. Zulfa fa?”
Ƙirjin labeeb ne yaji ya ƙara mishi nauyi da kiran Zulfa da Asad yayi.
“Itama ta damu in yi aure. I guess lokaci yayi. Me nake jira? Ina da gida, ina da kuɗin da zan riƙe mata huɗu ba biyu ba”
“Wa kake so kai convincing? Ni ko kai? Kasan me? Am done…!!!”
Asad ya faɗi ya wuce ranshi a ɓace. Sauke numfashi Labeeb yayi, idan akwai abu ɗaya da zuciyarshi take da rauni akai shi ne family ɗinshi.
Zai iya komai domin su. In auren nan zai sa Mummy farin ciki, zai yi. Dama mafarki yake na cewar wata rana rayuwa zata juya mishi yadda yake so. Kuma ya farka yanzun.
Juyawa yayi ya fice daga gidan, ya shiga motar shi ya koma Naf club. Yarinyar daya fara cin karo da ita ya ɗauka suka fito zuwa gidanshi.
Suna shiga bedroom ɗin gidan ta soma rage kayan jikinta. Muryar Labeeb a dishe yace mata,
“Ba abinda yasa na ɗauko ki kenan ba.”
Ware idanuwanta tayi tana kallon shi cike da rashin fahimtar abinda yake nufi. Zama tayi gefen gadon ta zuba mishi idanuwanta har ya cire kayan jikinshi daga shi sai boxers da singlet yahau kan gadon ya kwanta.
Hannu ya miƙa mata ta saka nata cikin nashi, ya jata ta kwanta kusa dashi, cikin idanuwa yake kallonta, wani yake so yai comforting ɗinshi ko na minti biyar ne.
Wani yake so a karo na farko ya damu da damuwarshi, ya fahimce shi, ya gane yana son kulawa amma baisan inda zai juya ya samu hakan ba.
“Hug me…”
Ya ce ma yarinyar, buɗe baki tayi za ta yi magana yasa hannunshi ya rufe mata baki tare da girgiza mata kai, baya son surutu, shiru yake son ji cikin kanshi.
Yau kuma bayason shan komai don ya gaji da gujema reality ɗin rayuwarshi. Zai fuskanci komai da yake faruwa na yau kawai. Zai yi duk abinda zai mantar da shi nan da sati ɗaya wani nauyin zai sake hawa kanshi.
Nauyin kula da ‘yar mutane da Mummy ta ɗauko zuwa rayuwar shi da take cike da hargitsi. Daga yau zai yi duk wani abu da zai ɗauke mishi hankali daga kanta.
Hugging ɗinshi yarinyar tayi kamar yadda yace. Ya lumshe idanuwanshi yana jin ƙamshin turarukan da ke jikinta da ɗuminta da babu abinda ya rage mishi, saima zafin da ke ƙirjinshi da ya ƙaru.
Idanuwanshi biyu har ya ji yanayin numfashinta ya canza alamar tayi bacci, sosai ta sake manne wa a jikinshi. Sauke ajiyar zuciya yayi kawai yana sake buɗe mata waje a ƙirjinshi.
****
Yana dawowa sallar Asuba ya sallami yarinyar da ya ɗauko ya kwanta, sai lokacin ya ɗan samu bacci, don bai farka ba sai wajen goma.
Anan yai wanka ya sake kaya. Classy buggers ya fara tsayawa ya sakama cikinshi wani abu ba don yana da appetite ko kaɗan ba. Sannan ya wuce gida.
Bai yi tsammanin ganin mumy ba, bai kuma same ta ba. Zainab ce zaune a falon, ƙarasawa yai ya zauna kusa da ita. Yi tai kamar bai shigo ba.
“Zeezee…”
Ya kira sunanta a hankali. Juyowa tayi ta sauke mishi idanuwanta cikin fuska, yana ganin yadda ranta yake a ɓace, yasan Zainab sarai, ta fi kowa rigima cikin gidan. Hannunta ya kama, ba zai iya auren nan babu yardar dukkan su ba.
“Ku dukan ku ne ƙarfina, ya kuke so inyi? Bani na ce Mummy ta nemo min yarinyar da zan aura ba, ba kuma zan iya ce mata bazan yi ba, saboda bamu taɓa hakan ba.
Dady, ni, ku dukan ku duk wani abu da Mummy zata buƙata amsa kala ɗaya ce. Me ya canza yanzun?”
Fisge hannunta Zainab tayi.
“Abinda ya canza shi ne Mummy ta wuce inda ya kamata wannan karon…saboda me ba za ka ce mata Zulfa kake so ba?”
Dafe kai Labeeb ya ɗan yi, kafin ya sake kallon Zainab.
“Wai wa ya ce muku akwai wannan soyayyar a tsakanin mu?”
“Kuskure kake yi babba Yaya, in ba za ka auri Zulfa ba fine, ka jira right girl ta zo duk da bana jin zata wuce zulfa ɗin…”
Wani kallo Labeeb ya watsa mata. Kai ta jinjina.
“Fine na bar maganar Zulfa, ban ma san me yasa na damu ba, rayuwarka ce, in ka zaɓi ka bari Mummy ta zaɓar maka yadda za ka yi farin ciki su waye mu da zamu ce wani abu…”
Ta ƙarasa tana miƙewa, hannunta ya kamo ya zaunar da ita, ƙafarshi ɗaya ya ɗora kan kujerar yana fuskantar Zainab sosai kafin ya ce,
“Ku ne komai nawa Zee Zee kinsan haka. Kuna da damar kuyi magana in kunga zan yi kuskure a rayuwata, kamar yadda nake da ikon yi a taku.
Amma nasan Mummy ba zata taɓa zaɓo abinda zai cutar da ni ba. In akwai wani abu da Mummy take so bai wuce komai namu ya zama perfect ba. Saidai damuwar ku babu abinda zata ƙaramin sai damuwa. I need you to be okay da auren nan saboda ke za ki yi handling komai na bikin.
Family kawai, i want a very simple and normal wedding.”
Sauke numfashi Zainab tayi tana jin duk tausayin Yayan nata ya kamata, gashi yayi duhu, yai zuru zuru kamar wanda yai jinya.
Rungume shi tayi, tare da sumbatar kuncin shi.
“I love you, everything is going to be ok.”
Ta faɗi sannan ta sake shi ta miƙe. Binta yai da kallo, kamar tasan yana buƙatar hug ɗin. Dawud ya dinga kira bai yi picking ba.
Kawai miƙewa yayi, yasan Mamdud na makaranta, kuma yasan Asad ya faɗa musu maganar bikin. Miƙewa yai ya fice, gidan su Jarood ya fara biyawa.
Ya ko yi sa’a yana gida, faɗa mishi maganar bikin yayi, shi kanshi Jarood mamaki yake da Labeeb ya ce mishi wata yarinya ce daban ba Zulfa ba.
Yana hanyar gidansu Dawud ne yake tunanin ko me yasa dukkan family ɗinsu suka ɗaga burinsu kan Zulfa zai aura. Ko me yasa suke tunanin akwai kalar soyayyar aure a tsakaninsu.
Sake kiran Dawud yayi suka yi magana. Gidan yaje ya faɗa musu maganar auren, sosai suke mamakin aure haka daga sama.
Gida ya dawo, yanayin fuskar Zulfa manne a ƙirjinshi, itama ta rame tai zuru zuru, su dukansu take bama wahala. Ɗakinshi ya shiga ya kwanta ba don yana jin bacci ba.
Yana nan kwance Mamdud ya dawo daga makaranta.
“Ango ka sha ƙamshi.
Cewar Mamdud.
“Bana son iskanci Mamdud.”
Zama Mamdud yayi gefen gadon.
“Meye kake kamar baka son auren?”
Miƙewa zaune Labeeb yayi.
“Bana so, ban shirya yin aure ba yanzun.”
Wani murmushi Mamdud yayi ya miƙe yana ficewa daga falon kawai, gani yake Labeeb ya raina mishi hankali. Rannan ya ce mishi baya son Zulfa, yanzun yana gaya mishi bayason auren nan.
Ya samu komai da kowanne namiji zai yi burin samu a rayuwa amma yana nuna kamar inda za a bashi zaɓi da gudu zai bar rayuwar da yake da ita. Ƙaramin tsaki Mamdud ya ja.
In za’a haɗa abinda yake ji da hassada bai damu ba. Zai yi komai don ya samu rayuwa irin ta Labeeb, komai da sauƙi yake zo mishi. Baisan wata wahala ba a rayuwarshi.
Kitchen Mamdud ya shiga ya zubo abinci ya ɗauko lemo ya fito ya zauna falo ya ci. Nan yabar komai ya kwanta don gaba ɗaya a gajiye ya dawo daga makaranta, da ƙyar ya iya tsayawa yai sallar Asr.
Yana nan kwance Zulfa ta shigo. Da murmushi ya miƙe.
“Ina Yaya labeeb?”
Ta buƙata cikin muryar da ke nuna babu wani abu a yanzun dake da muhimmanci a wajenta da ya wuce sanin inda Labeeb yake. Baisan me yasa hakan ya ɓata mishi rai ba.
Ganin ba shi da shirin amsata ne yasata wucewa kawai ta nufi ɗakin Labeeb ɗin. Ƙwanƙwasawa tayi.
“Shigo.”
Ya faɗi, muryarshi kawai yasa zuciyarta dokawa. A hankali ta tura ƙofar ta shiga, ganinta yasa shi sakkowa daga kan gadon yana faɗin.
“Zulfa… Thank goodness”
Muryarshi a gajiye, idanuwanshi cike da abinda yake ji. Ƙarasowa yayi inda take yai hugging ɗinta a jikinshi yana jin ƙamshinta da kala ɗaya ne da nashi. Don duk turarukan da yake amfani da su ne yake siya mata.
Yana jin yafda jikinta ke ɓari, da hawayen ta da ke jiƙa mishi riga. Sosai ta zagaya hannuwanta ta bayanshi ta riƙe shi don ji take kamar tana sakin shi ya kubce mata kenan.
Jin riƙon da tai mishi yasa shi ɗan rocking ɗinsu.
“Hey, it’s ok. Bana son kukan nan. Abinda kike so ne zan yi Zulfa, auren zan yi ba shikenan ba?”
Kai kawai take ɗaga mishi, har ƙasan zuciyarta ba abinda take so bane. Bata son ta ganshi da wata balle kuma mata, matar aure.
Tunda ya bar gidansu take ji kamar zuciyarta zata tarwatse saboda zafin da take yi. Inda zata yi ta samu sauƙi take nema ta rasa.
Ɗago ta yayi daga jikin shi yasa hannu yana goge mata fuska, kafin ya tallabi fuskarta cikin hannuwan shi yana saka idanuwanshi cikin nata.
“Karki sake guje min, kome zan miki karki sake yin nisa dani, i can’t… I can’t stay sane ba tare da ke ba.”
Kai ta iya ɗaga mishi don abinda take ji ya tsaya mata a wuyanta ya hanata magana. Sake riƙe fuskarta yayi cikin hannun shi.
“Ki min magana in ji don Allah.”
Ya faɗi muryar shi can ƙasa, jin komai yake ya mishi sauƙi da ganinta, babu abinda zuciyar shi take so a yanzun sai ya ji muryarta. Da ƙyar Zulfa ta iya samo muryarta ta ce,
“Allah ya sanya alkhairi…”
Goshin shi ya haɗa da nata murmushi na ƙwace mishi, ba abinda ta faɗa bane ya sa hakan. Muryarta da ya ji ce ta bayyana murmushin da ke fuskarshi.
Dariya ta yi ta ture shi tana goge fuskarta da hannunta, bata san ya za ta yi da ganin shi da wata ba. Amma wannan moment ɗin, muhimmancin ta da take gani a idanuwanshi tasan duk macen da zata shigo rayuwarshi tana da aiki.
Shima dariyar yayi, abinda ya kwana biyu baiyi ba.
“In kika sake min haka har gida zanzo, believe me a kafaɗa zan ɗauke ki in taho da ke.”
Sosai take dariya duk da tana jin hawayen dake sake taruwa a idanuwanta da kishin shi da ke damunta.
“Yaushe zamu je wajenta?”
Ta buƙata muryarta a dakushe tana jin zuciyarta na wani tsalle tsalle, da murmushi Labeeb ya ɗan ware idanuwan shi.
“Wacece?”
“Matar ka. “
Wani murmushi yayi mai sauti ya juya ya ɗauko mukullin motar shi da ke kan drawer ɗin gado ya ce ma Zulfa,
“Kina jin yunwa?”
Kai ta ɗaga mishi a hankali tana fadin.
“Yaya am serious fa”
“Naji ki ai.”
Ya amsata yana nufar ɗakin canza kayanshi ya ɗauko takalma ya fito dasu.
“Baka ce komai ba kuma.”
“Saboda bata da muhimmancin komai a wajena. Kuma kin fi kowa sani abinda yake da muhimmanci a wajena ne kawai nake magana akanshi. “
Dariya Zulfa tayi tana jin ranta ƙal, sai dai wani waje can ƙasan zuciyar ta yana tausayawa koma wacece wannan da zata aure shi. Don tasan yadda yake yi da mutanen da basu da wani waje a rayuwar shi.
Takalmanshi ya saka, ya ɗauki turaruka kala biyu ya fesa a jikinshi ya fesa ma Zulfa. Mayarwa yayi ya ajiye ya dawo ya kama hannunta yana janta zuwa ƙofa.
“Yaya kabari in gyara fuskata.”
Juyowa yayi ya kalleta a kasalance, duk da fuskarta tayi ja dan kukan da tayi, idanuwanta sun ɗan kumbura wani kalar kyau tai mishi da ba zai misalta ba.
Sumbatar goshinta yayi tare da faɗin,
“You are ok yadda kike, yunwa nake ji.”
Dariya tayi tana bin bayanshi. Dai dai lokacin da cikinshi yai wani ƙugi. Dariya suka yi gaba ɗaya har sukaje falo suna dariya.
“Ya isheki, yunwa nake ji shi yasa.”
“Na ce wani abu ne?”
Zulfa ta tambaya tana ƙarasa maganar da dariya da yasa Mamdud juyowa ya kalle su.
“Zo mu tafi yawo.”
Labeeb ya ce mishi. Girgiza kai yayi yana taɓe baki.
“Test nake da shi gobe, karatu zan yi.”
“Uhm… Yaushe ka fara karatu ma test? I envy kalan ƙwaƙwalwarka.”
Zulfa ta fadi.
“Hmmm.”
Kawai Mamdud ya faɗi yana kallon su suka wuce. Gaskiya Zulfa ta faɗa, baida matsala da karatu, indai zai duba sau ɗaya yaygama da koma menene.
Wannan baiwa ce da Allah yai mishi. Ba zai bisu bane ba, yanayin su kawai ɓata mishi rai yake yi, sun wani riƙo hannun juna, a hakanne Labeeb yake raina mishi hankali, don anyi magana ya ce babu soyayya a tsakanin su.
Ba ma wannan ba, yanzun ko fita suka yi duk wani attention kan Labeeb yake, shi kam ko a jikinshi. Gyara kwanciya Mamdud yayi yana jan ƙaramin tsaki.