Skip to content
Part 35 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Ya ga text ɗin Ateefa da ta ce ya ɗibo mata kaya a gida da darduma, don haka daga wajen party ɗin gida ya nufa ya yi sallar Magariba ya ɗauko abinda ta ce tukunna ya sake fitowa. 

Parking ya yi gefen hanya, ya yi zamanshi a cikin motar. Baisan inda zai nufa ba, karo na farko a rayuwarshi da bai san inda zai je ba, gidan shi ba gida bane babu Ateefa a ciki. 

Gidan su, ba zai jure yanayin da ke fuskokinsu ba, ɗanshi yake son sake gani, yake son ya sa hannu ya riƙe a jikinshi ko zai san daga inda ya fito. 

Amma yana tsoron haka, kamar yadda yake tsoron ƙarasawa asibiti ya sake kallon idanuwan Ateefa, baya jin yana da ƙarfin ci gaba da faɗan da basu gama ba. 

Baida ƙarfin sake yi mata wata ƙaryar da yasan dole ne, don za ta buƙaci sanin sa’adda abinda bai faru tsakanin shi da Zulfa ba ya faru. 

A gefe ɗaya kuma yana son fahimtar abinda ya gani a fuskar Mamdud, yana son fassara meye ma’anarshi, yana son hango abinda Mamdud ɗin zai mishi next ya kasa.

Ba zai iya kare Zulfa ba in ‘yan gidansu suka san ba cikinshi bane a jikin Zulfa. Jikinshi babu ƙarfi ya tayar da motar ya hau titi yana nufar hanyar asibitin. 

Sai da ya tsaya akan hanya ya siya wa Ateefa take away da drinks tukunna, yana shiga asibitin ana kiran Isha’i. Ya tsaya nan ya yi sallah tukunna ya ɗauki ledojin ya ƙarasa ciki. 

Zuciyarshi cike da takarcen tunani kala-kala. Da sallama ya tura ɗakin, ta amsa mishi ba tare da ta kalle shi ba. Ƙarasawa ya yi ya ja kujera ya zauna. 

Yana kallon yadda ta ƙara wani irin haske, sai dai baya son ramar da ke cikin idanuwanta. 

“Bana son ramar na Tee…”

Sai lokacin ta ɗago ta kalli fuskarshi. 

“Tun yaushe ne ba ka son ramata? Kafin ko bayan ka wa Zulfa ciki?”

Maganarta ta mishi zafi sosai, bai ce komai ba. Ya ɗora mata ledojin hannunshi akan gadon. 

“Ki ci wani abu…”

Ya faɗi maimakon amsa mata tambayar da ta yi mishi, kallon shi take, duk ya fita hayyacin shi, gaba ɗaya ya firgice ya yi zuru zuru. 

Haushin shi da take ji bai hanata jin tausayin shi ba, tasan shima bai ci wani abu ba, ba don tana jin yunwa ba, sai don ta damu da lafiyarshi. 

Hakan ya sa ta buɗe take away ɗin guda ɗaya, ta ɗauki cokalin da ke cikin ledar, ta saka cikin fried rice ɗin, zamanta ta gyara yadda za ta fuskance shi sosai kafin ta ɗibo abincin. 

Miƙa mishi ta yi, ya riƙe hannunta yana girgiza mata kai, idanuwanshi taf da hawaye da ya rasa ko me ke damunshi duk yau. Sai ka ce mai famfo a cikin idanuwa. 

“Banda lafiya… Bazan iya ci ba.”

“Ba koyaushe muke cin abinci dan muna so ba…”

Ateefa ta faɗi itama nata idanuwan da hawaye, buɗe bakinshi yayi yana sakin hannunta ta saka mishi abincin daya haɗiye ba tare da ya tauna ba. Haka ta ci gaba da bashi har sai da ta kusan ba shi rabi. 

Ya girgiza mata kai da faɗin, 

“Zan yi amai idan na ƙara…”

Bata ce komai ba, ta ƙarasa cinye sauran wanda ya rage ɗin, saboda babyn da ke cikinta, saboda su duka suna buƙatar abincin ko da bakinta baya so. 

Da ƙyar ta iya sakkowa daga gadon, mararta na mata ciwo har lokacin, da idanuwa Labeeb yake binta ta ɗauki jakar kayan da ya ajiye mata ta ɗora akan gadon. 

Kaya ta ɗauka ta nufi toilet ɗin da ke cikin ɗakin. Yana nan zaune ya ji tana wanka, har ta gama ta fito ta yi sallah duk yana kallonta. Ta idar ta dawo kan gadon ta kwanta. 

“Ki yafe min Tee…”

Ya faɗi muryarshi can ƙasa, bata amsa shi ba. Saboda har yanzun zuciyarta na jin haushin shi, bata kuma daina son shi ba. 

Zafin cin amanar da ya yi mata bai je ko ina ba, ba za ta iya barin shi saboda hakan bane kawai, son shi ya riga da ya mata illa. Rufe idanuwanta ta yi ba tare da ta amsa shi ba. 

Tana jinshi yana jan kujerarshi, kafin ta ji laɓɓanshi kan kuncinta ya sumbata. 

“Bazan gaji da baki haƙuri ba…na miki laifi mai girma. Zan gyara komai… I love you.”

Badai ta bashi amsar ba, komawa ya yi ya jingina bayanshi sosai da kujerar. Idanuwanshi ƙyar akanta, don yasan baida nutsuwar da zai iya bacci को ya kwanta. 

Yanzun damuwar yaron shi da ko sunanshi bai sani ba take addabarshi. Yanzun zuciyarshi ke ciwo da son sanin ɗayan ɓangaren da yaron ya fito. 

Tsoro na daban na ziyartar shi, wani abu ya soki zuciyarshi da ciwo kala daban da wanda yake ji. Da wanne idanuwa zai kalli yaron ya faɗa mishi ta son zuciya suka same shi. 

Wanne irin ciwo zai ji duk lokacin da wani ya kalli yaron ya goranta mishi, yai mishi gori mafi ciwo. Duk lokacin da Mummy za ta jefi Ateefa da kalmar asalinta ji yake kamar ya rusa ihu. 

Kamar Ateefa tasan abinda yake tunani kenan ta buɗe idanuwanta ta sauke su akan shi ta ce, 

“Yaron nan fa? Duk lokacin nan El-labeeb ina tausayin yaran da aka samu ta kalar hanyar da aka same ni…ina tausayawa yadda rayuwar su take kasancewa a duk inda suke. 

Na ɗauka da ka aure ni ka fahimta… Na ɗauka ni kaɗai na isa ka guji cutar da yaran da za su fito daga jikinka. 

Sai ga guda ɗaya yana yawo a duniya ba tare da saninka ba Sai ga wani a jikin Zulfa da saninka. Ƙarya nake idan na ce maka baka karya min zuciya ba… Kanka da yaranka ka ha’inta amma tare muke jin ciwon. 

Kai za ka yi wa yaranka bayani amma ni nake tayaka jin kunya. Wace irin rayuwa ce wannan?”

Ta ƙarasa hawaye masu ɗumi na zubo mata. Ya kasa cewa komai, duk kalmar da za ta fito daga bakinta yankar mishi zuciya take, tsoron da yake ji take ƙara mishi. 

“Ɗan Adam bashi da dabara… Bashi da wayau sai wanda Allah ya hore mishi… Kullum sai ka jefa kokwankwanto a cikin tubanka… Ka kasa tubarwa Allah da dukkan zuciyarka…. Wataƙila hakan ne ya sa abinda kake ƙoƙarin binnewa yake ta fitowa…”

Da ƙyar ya iya buɗe bakinshi ya ce, 

“Don Allah…. Don Allah ki barni haka…”

Yake roƙonta, ji yake kamar kanshi zai tarwatse saboda tashin hankali, hannu ta sa ta goge hawayenta. Saida ta ce, 

“Zunubina ɗaya ne… Da sonka ya sa na rufe idona da ganin laifukanka…”

Sannan ta juya mishi baya. Tun yana jin sautin kukanta da babu abinda yake mishi face ƙara mishi sabon tashin hankali har ya daina ji. Nan kan kujerar ya zauna yana jiran gari ya waye. 

Yana jiran ya ga da me awannin wayewar garin za su zo mishi da shi. Har wajen fatar ƙirjinshi yake jin zafin da zuciyar shi take yi. 

******* 

Kuka take a jikin Ishaq a kwance, ya sake gyara mata waje a ƙirjinshi, kukanta na ci mishi zuciya. Da wani nisantaccen yanayi a muryarshi ya ce, 

“Bansan El-Maska yadda kika san shi ba…Na gansu shi da Zulfa…a hotuna, na gansu a fili… Ba wanda ya faɗa min… Soyayyar da ke tsakanin su mai ƙarfi ce. Zuciyata ta kasa yarda cewar son da El yake mata zai bari yai mata wannan abin.”

A ƙirjinshi Zainab ta sake tura fuskarta, muryarta a dakushe ta ce, 

“In da bai faɗa maka n da bakin shi ba bazan yarda ba… Har yanzun akwai ɓangaren zuciyata da ya kasa yarda… Amma yaron shi fa? Yaron da na gani kuma fa?”

Sauke numfashi Ishaq ya yi yana ranƙwafo da kanshi ya sumbaci kanta, abin ya ɗaure mishi kai. 

“Bana son kukan nan… Har raina nake jinshi… Sai ya sa miki ciwon kai ko?”

“ƙirjina zafi yake min… In ni ina jin haka bansan me Zulfa take ji ba…ba…”

Bai bari ta ƙarasa ba ya janyota yana haɗa bakin su. Cikin nutsuwa yake nuna mata soyayyarshi mai wahalar mantawa. Da kalar ƙaunarshi yake lallashin ta. 

Da ƙyar ya samu ta bar kukan da take yi, sai dai yafda bata yi bacci ba, shi ma haka ya kwanta yana kallonta, damuwarta na damun shi har Asuba tayi. 

*****

Tun bakwai Dadyn Labeeb ya sa aka kira mishi Abban su Dawud, baban su Jarood, Labeeb, sai kuma Dawud. Duka ya tattara su a babban falon gidan. 

Daga Labeeb har Dawud kallo ɗaya za ka yi musu kasan babu wanda ya runtsa a cikinsu, kayan da kowannen su ya kwana da shi a asibiti ne a jikin su. 

Sai da kowa ya zauna tukunna Dady ya kalle su ya ce, 

“Idan na ce zuciyata bata ciwo ko bana fushi da Labeeb akan abinda ya faru ƙarya nake… Wallahi ina kunyar cewar sanadin shi ne wannan abin yake faruwa….”

Jin Dady ya kasa ƙarasawa ya sa baban su Jarood karɓe zancen da faɗin, 

“Dukkanmu Musulmi ne… Babu wanda baisan ƙaddara ba… Tunda Labeeb ya tara mu ya faɗa kunsan yana son gyara kuskuren shi ne.

Alhamdulillah da basu sake wani shirmen ba suka fito da maganar. Yaya fushinka ba zai ƙara mishi komai ba sai sabuwar fitina. 

Kowa yasan abinda ya kamata, zamu jira ta haihu, sai a ɗaura musu aure…”

“Hmm…”

Kawai Dady ya ce. Abba kam kallon su yake, tun shekaranjiya yake jin canji a jikinshi da ya kasa fahimta. Ji yake kamar ƙofofi kanana suna buɗewa a cikin kanshi inda yake dunɗum da wani irin duhu. 

Ba komai yake fahimta ba, don haka ya zaɓi da yai shiru, hankalinshi baban su Jarood ya mayar kan Abba. 

“Auwalu ba ka ce komai ba.”

Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Kuma ‘yarku ce… Abinda duk kuka yanke…”

“To Alhamdulillah. Shikenan sai mu jira haihuwarta tukunna…. Kai kuma Labeeb bansan me zan ce maka ba… Laifinka tsakaninka da Ubangiji ne. 

Saika roƙe shi gafara, da iyayenka da suka yi fushi da kai.”

Sakkowa Labeeb ya yi daga inda yake zaune kan gwiwoyin shi ya durƙusa kanshi a ƙasa. 

“Dady na yi kuskure…. Don Allah ku yafe min… Banda wani sauƙi da fushin ku akaina…”

Miƙewa Dady ya yi ya bar falon, su Abba suna binshi da kallo, sosai baban su Jarood ya sake yi wa Labeeb nasiha da bashi haƙuri kan cewar Dady zai sauko. 

Don yaron tausayi yake bashi, kafin shima da Abba su fita su bar falon. Har lokacin Dawud na zaune inda yake ba tare da ya ɗago ba. 

Babu komai a ranshi sai tunanin yadda zai dinga kallon zulfa a kullum da cikin da ke girma a jikinta. Yadda za ta yi ɗawainiya da wahala da ƙaddarar da ta same ta. 

“Bazan roƙi ka yafe min ba saboda ban cancanci yafiyar ka ba Dawud… Zan auri Zulfa… Wallahi zan aureta….zan gyara komai…”

Girgiza mishi kai Dawud yayi, yana ɗago kai ya sauke idanuwanshi akan Labeeb , har lokacin yana jin kamar yaita haɗa mishi kai da bango sai ya faɗa mishi dalilin da ya sa yai musu abinda yai musu. 

“Ka daina magana… Do n Allah in dai ba za ka faɗa min me yasa kai mana haka ba… Karka sake cewa komai…”

Duk yanda Labeeb ya so ya sa kanshi a halin da Dawud yake ciki don ya fahimta ya kasa. 

“Ka yi haƙuri…”

Ya furta da sanyin murya… Miƙewa Dawud ya yi ya bar mishi falon yana ficewa. Zama Labeeb ya yi akan kafet ɗin ɗakin ya jingina kanshi da kujerar wajen yana maida numfashi a hankali. 

*****

Sallar Asuba kaɗai ta tasar da shi ya sake dawowa kan gadon ya kwanta, kanshi kamar zai faɗo ƙasa saboda ciwon da yake mishi. 

Ga rashin bacci, ga kukan da ya yi har ya saukar mishi da zazzaɓi mai zafi. Can wajen ƙarfe sha ɗaya ya samu da ƙyar ya raba kanshi da gadon ya shiga banɗaki. 

Wanka yayi ya fito, ya ɗauko wani three quarter blue da riga baƙ ya saka a jikinshi. Ya ma manta da wani abu wai shi taje kai balle kuma shafa mai. 

Haka ya ɗauki mukullan motar shi ya fito waje. Da ƙyar yai parking ya dawo ya kulle gate ɗin. Awanni biyu ne banbancin lokacin da ke tsakanin Nigeria da Jordan. 

In har ƙwaƙwalwarshi na lissafi yadda ya kamata wajen sha ɗaya da wani abu ya kamata a ce Arif ya iso. Don haka ya ƙarasa airport ɗin ya samu waje yai parking ya fito ya tsaya. 

Bai fi mintina ashirin ba ya hango Arif yana jan akwatin shi, ƙafafuwanshi sun yi wani nauyi, ya kasa ƙarasawa ya tarbo shi, har sai da ya ƙaraso. 

Kallon Mamdud ya yi yana nazarin fuskarshi da take a kumbure, abinka da farar fata, ta yi wani ja.

“You look good.”

Arif ya faɗi, neman murmushi Mamdud yayi ya kasa samu. 

“Sannu da hanya…”

Ya ce yana rasa abinda ya kamata ya fara faɗi. Handle ɗin akwatin Arif ya saki ya rungume ƙafafuwan Mamdud ɗin. 

“Komai zai yi dai-dai… Ka daina damuwa.”

Hannu ya sa kan bayan Arif yana karɓar comfort ɗin da rungumar da Arif ɗin yai mishi take saukar mishi. Sun ɗan jima tsaye a haka kafin Mamdud ya ɗago da Arif daga jikinshi. 

Murfin motar ya buɗe mishi ya shiga, sannan ya ɗauki akwatin Arif ɗin ya saka bayan mota. Ya zagaya shima ya shiga… Babu wanda ke magana a cikin su. 

Mamdud ji yake yana buɗe bakin shi kuka zai sake, musamman da ya ga Arif ɗin. Yake ganin yadda ko yaushe zai iya rasa shi, a hankali yake tuƙin saboda ba ya gani sosai har suka kai ƙofar gidan. 

Parking ya yi ba tare da ya shiga ciki ba, ya ja numfashi yana fitarwa. Sai da ya tabbatar zai iya magana ba tare da ya yi kuka ba tukunna ya ce, 

“Nan zan barka Arif… Bazan iya shiga ba.”

Girgiza mishi kai Arif yake yi tunda ya soma magana. 

“Tare za mu shiga ko mu koma inda za ka je har sai ka shirya fuskantar su…”

Runtsa idanuwa Mamdud ya yi yana buɗewa. Shi zai faɗa wa wani halayyar Arif. Babu inda zai fita in ba tare suka shiga ɗin ba… Dole ya sake kunna motar ya yi baya da ita yana ɗan juyata. 

Sannan Maigadi ya buɗe mishi gate ɗin, lokacin da yake parking zai rantse yana ɗanɗana zuciyar shi da ta yi tsalle tun daga ƙirjin shi ta dawo kan harshen shi. 

Hannunshi na kyarma, wata zufa na fito mishi ya buɗe motar ya fito. Ya zagaya ya buɗe bayan motar ya fito ma Arif da akwatin shi. 

Hannun shi Arif yasa cikin na Mamdud ɗin yana janshi suna nufar hanyar da za ta kai su ɓangaren su Labeeb. 

Yana shiga ɓangarensu ɗakin shi ya wuce. Sai da ya kai bakin ƙofa tukunna ya tuna yadda ya birkita komai na ciki. Lumshe idanuwanshi yayi, baisan meke damun shi haka ba in ranshi ya ɓaci. 

***** 

A hankali ya sa hannu kan handle ɗin ƙofar ya tura, kayanshi kawai zai ɗauka ya wuce ɗakin Tayyab ya sake yin wanka ya canza. 

Ga mamakin shi ɗakin ya gani fayau, duk abinda ya hargitsa an mayar da na mayarwa. Wanda ya fasa an kwashe, komai ya yi fes. Ƙamshin room freshner din dake dakin yasa shi sanin Tayyab ne ya yi gyaran. 

Numfashi ya ja mai nauyi yana sauke shi, ya cire takalmanshi sannan ya tura ƙofar yana shiga cikin ɗakin sosai, toilet ya nufa ya sake yin wanka ya fito. 

Jeans ya ɗauka baki da farar riga ya saka, turaruka kawai ya iya fesa wa jikinshi ya koma kan gado ya zauna. Ya rasa yadda zai yi, kewar Ummi da yake ji tun jiya tai mishi sauƙi. 

Balle kuma Abba da ya yi mishi tsaye a wuya da wani irin yanayi. Miƙewa ya yi ya fito daga ɗakin. A karo na farko tun dawowar su gidan da ƙafafuwan shi suka ɗauke shi zuwa ɓangarensu Abba. 

Zuciyar shi ke dokawa kamar za ta fito daga ƙirjinshi har ya ƙarasa. Yai tsaye a bakin ƙofar yana maida numfashi kamar wanda ya ci gudu na tsawon lokaci. 

Duka jikinshi ya mishi nauyi. Baisan iya lokacin da ya ɗauka tsaye a ƙofar ɗakin ba, yana shirin juyawa aka buɗe ɗakin. Idanuwa Abba ya sauke kan Dawud, fuskarshi na nuna mamakin da yake ji na ganin Dawud ɗin. 

Akwai wani abu tattare da Dawud ɗin, yanayi ne da Abba ya kasa fassarawa. Wani abu na ɗaukar zafi cikin kanshi. 

“Dawud lafiya dai ko?”

Sosai Dawud ɗin yake kallon shi, abubuwa kala-kala na mishi yawo cikin kanshi. Searching yake yana neman Abbanshi da ya sani, Abbanshi da zai kalle shi yasan yana cikin damuwa tun kafin ya furta. 

Abbanshi da yake zama tare da shi su warware duk wata matsala. Abbanshi da shi ne ƙarfin gwiwar shi, Abbanshi da yake nuna mishi yadda zai yi da kome ya taso mishi.

Zuciyar shi ta sake buɗewa wajajen duk da babu ciwuka suka samu nasu ganin babu Abbanshi. Wannan mutumin tsaye a gabanshi wani ne daban. 

Muryarshi a dakushe ya ce, 

“Abu na zo nema kuma ban gani ba.”

Kafin Abba ya ce wani abu Dawud ya juya ya tafi. Hannu Abba ya sa yana dafe kanshi da yake sarawa kamar ana buga mishi wani abu. Dole ya koma ɗaki yana fasa fitar da ya yi niyyar yi. 

Bakin ƙofar ɗakin shi ya tsaya yana ɗan dafe kai, bai ma san abinda ya ɗauke shi yakai shi ɓangaren Abba ba. Baisan me yake nema ba. 

Ya riga da ya binne Abbanshi shekaru masu yawa tun kafin ya ga gawarshi, ya kamata har zuciyar shi ya haƙura da shi kamar yadda ya haƙura da dawowar Ummi. 

Su duka sun barsu a duniya mai cike da rikici, sun barsu ba tare da sun san yadda za su yi da rayuwa ba. 

“Yaya…”

Kamar daga sama muryar Zulfa ta katse mishi tunanin da yake yi, da sauri ya juyo yana ƙarasawa inda take tsaye. Hannunshi ya fara sakawa ya taɓa fuskarta ya ji babu zazzaɓi a jikinta. Tukunna ya kalleta sosai yace

“Ya jikinki?”

Cikin sanyin murya ta amsa shi da

“Naji sauƙi. Ina kwana.”

Yanayin sanyin maganarta na taɓa shi, har zuciyarshi yake jin ƙaddararta, da yana da dama da ya cire abinda ke jikinta ya dawo da shi nashi ko za ta samu sauƙi 

“Ya zan yi in sauƙaƙa miki abinda kike ji? Zulfa bansan me zan yi ba… Komai baya min daɗi… Damuwarki… Ƙaddarar ki…”

Idanuwanta da ke cike taf da hawaye ta saka cikin nashi. 

“Ka yi haƙuri na zame muku matsala… Na ja muku damuwa mai yawa… Za ka sauƙaƙa min komai in ka haƙura… In na san ba kwa fushi da ni zan ji sauƙi…”

Ta ƙarasa hawaye na zubo mata, da sauri yasa hannuwanshi yana goge mata fuska tare da girgiza mata kai, muryarshi na rawa yake faɗin, 

“Ba ma fushi… Ba mu yi fushi da ke ba… Dadyn su El ya ce a bari…”

Shiru ya ɗan yi yana kokawa da sauran kalaman saboda dacin su da yake ji

“A bari ki haihu tukunna ai aurenku da El…”

Kallon shi Zulfa take yi, sai da ya ɗauke idanuwan shi daga fuskarta tukunna ya iya faɗar maganar. Tun daga zuciyarta take son faɗa mishi abinda ya faru. 

Sai dai ta kasa motsa harshenta balle kalaman su fito. Bata san ko zai iya kallonta in yasan abinda ke jikinta ba laifin Labeeb bane ba. Bata san me za su ce ba. 

Tsoro take ji har ƙasan zuciyarta. Kai kawai ta iya ɗaga mishi wasu hawayen na sake zubo mata. 

“Kukan nan ƙara ɗaga min hankali yake yi… Ki rage damuwa don Allah. Kin ci abinci?”

Kai ta girgiza mishi, bai ce komai ba ya kama hannunta suka nufi ɓangaren Mami, da sallama ya tura ɗakin ya shiga. 

“Mami ina kwana”

Ya faɗi bayan ta amsa sallamar. 

“Lafiya ƙalau, ya mai jiki? Anjima za mu je in sha Allah. “

“Da sauƙi…ina abin karin mu?”

Da murmushin ƙarfin hali Mami ta miƙe tana fita daga ɗakin, Dawud bai jira ba ya bita kitchen ɗin. 

“Khateeb fa?”

“Ya tafi makaranta..”

Dawud bai ce komai ba ya karɓi plate ɗin da Mami ta zuba dankali a ciki. 

“Haɗa mana waje ɗaya kawai.”

Haɗa musu komai ta yi, tana taya shi ɗaukar kayan suka kai ɗakinta. Yana ajiye na hannun shi ya sake fita ya nufi ɗakin Tayyab. 

Kwance ya same shi. 

“Fito mu karya”

“Ban jin yunwa Yaya. Ina kwana.”

“Lafiya ƙalau… Kowa ma baya jin yunwa. Ka taso…”

Gyara kwanciya Tayyab ya sake yi da faɗin, 

“Zan ci anjima.”

“Bana son gardama. Ka sani kuma.”

Miƙewa Tayyab ya yi ya sauko daga kan gadon yana turo bakin shi, kamannin shi da Ummi na fitowa sosai, da sai da Dawud ya ji zuciyarshi ta matse waje ɗaya. 

“Sannu da gyaran ɗaki.”

Tayyab bai amsa shi ba, ya ɗauki riga ya saka kan singlet ɗin da ke jikinshi ya zo ya raɓa shi ya wuce. Idan ya barsu ba za su ci abincin ba. 

Da kanshi ya haɗa wa kowa tea a kofi har Mami ya mimmiƙa musu. Kallon su kawai za ka yi kasan babu mai jin daɗin abinda yake ci.

Da suka gama Dawud ya kwashe kayan duka ya mayar kitchen sannan ya dawo. Zulfa ya kalla ta yi wani so cool da ita. 

“Zulfa… Ya dai?”

Bata ɗago kanta ba, tunanin makarantarta take yi, zangon ta na ƙarshe ne a shekara ta uku. Satuka kawai ya rage musu su fara exams. 

“KaratunaYaya…”

Shiru Dawud ya yi yana rasa ko me zai ce mata, yana jin ɗacin da yake dannewa akan El na sake taso mishi. Ba don shi ba Zulfa ba za ta san ranar nan ba. 

Ba za ta damu da wani abu banda karatunta ba. Tayyab ya ɗan kalle shi ganin ya rasa me zai ce ya sa shi maida hankalinshi kan zulfa ya ce 

“Deferring semester ɗin za ki yi.”

Kallon Tayyab ta yi idanuwanta cike taf da hawaye. Da sauri ya matsa daf da ita yana riƙe hannunta. 

“Kina gani ai mutane na deferring…ba sabon abu bane ba. Baya nufin karatun ki zai tsaya gabak ɗaya. Kawai na ɗan lokaci ne… Mu gama da wata matsalar tukunna.”

Kai ta ɗaga mishi. 

“Yauwa… Kar hawayen nan su zubo don Allah.”

Kai ta sake ɗaga mishi tana ƙoƙarin tarbe hawayenta ko don farin cikinsu. Ko don su rage damuwar da take gani a fuskokin su. 

Sai da Tayyab ya tabbatar da ba za ta yi kuka ba tukunna ya miƙe yana barin ɗakin. Kan gado Zulfa ta koma ta kwanta, Mami ta kalli Dawud. 

Robar Swan ta miƙa mishi da ke gefenta.

“Ka zuba a duk wani abu na ci da zaka iya gani a gidan nan. Ko ruwa, kome ka samu indai zai shiga ciki ka zuba.”

Karɓa Dawud ya yi, yana jujjuya robar, a idanuwanshi ruwa yake gani babu komai kuma a ciki. 

“A gidanmu na karɓo, zam zam ne da addu’oi. Komai ya kusan zuwa ƙarshe In sha Allah.”

Jinjina kai dawud yayi yana miƙewa da robar a hannunshi. Ko bata mishi bayanin menene ba zai yi yadda ta ce, saboda ya yarda da Mami kamar yadda ya yarda da Ummi. 

Ɗakinshi ya wuce ya ajiye robar a gefe yana kwanciya kan gadon shi, rufe idanuwan shi yayi ko Allah zai taimake shi ya samu bacci ko na minti talatin ne. 

*****

Ko ina jikinshi ɓari yake, ga zufa da yake ji har cikin tafin ƙafarshi, bugun zuciyarshi ya ƙara tsananta ne da ganin su a baƙin ƙofar da za ta shigar da su cikin gidan su Labeeb ɗin. 

“Just relax…”

Arif ya ce mishi yana jan hannun shi, ƙafarshi ɗaya ta fara taka cikin gidan. Abubuwa da yawa na dawo mishi, shigowar shi ta farko cikin gidan ba tare da kowa ba, ba tare da komai ba. 

Shigowar shi gidan da tarin burika da Labeeb ya taimaka mishi wajen ganin ya cika su, Arif ya kalla da sauri, kafin ya maida hankalin shi yana kallon ko ina da ina da idanuwan shi za su iya ɗora kansu akai. 

Kafin jerin abubuwan da ya yi wa Labeeb su soma dawo mishi suna giftawa ta cikin idanuwan shi kamar walƙiya. Girgiza kanshi yake yi. 

“Me na yi haka?”

Ya faɗi yana tsayawa cik, hakan ya sa Arif tsayawa ya ɗan ɗaga kanshi yana kallon Mamdud da yake a firgice. Kamar wanda yake ganin abubuwan tsoron da babu mai ganinsu sai shi. 

Kamar yadda shi kaɗai yake ganin abubuwan da yayi da babu damar komawa ya gyarasu. Yana kallon ranar farko da Labeeb ya miƙo mishi Arif ya riƙe shi a hannun shi. 

Yana kallon ranar farko da Labeeb ya bashi kayan sawa masu tsada ba tare da nuna damuwar komai a fuskar shi ba. Ire iren ranakun yake gani wani sabon zazzaɓi na riƙe shi. 

“No… No… Bazan iya ba…”

Yake faɗi, hannunshi da ke riƙe cikin na Arif ya ji Arif ɗin ya jijjiga. 

“Don Allah mu je Yaya Mamdud… Ina buƙatarka a rayuwata… Yaya Asad, Yaya Anees, Anty zeezee, har Yaya ma…karka barmu don Allah…”

Kallon Arif ɗin yake yana jin kamar ya fashe da kuka, ba zai gane ba. Bazai fahimci abinda yake faruwa ba. Baisan da idanuwan da zai kalli Labeeb ba. 

Janshi Arif yake yi, da baisan yadda akai yake binshi ba, sai ganin shi ya yi a bakin ƙofar falon a tsaye. Idanuwanshi ya sauke kan Labeeb da ke zaune ya haɗe kanshi da kujerar wajen. 

Ba sai wani ya faɗa mishi ba, yasan Labeeb kama yadda yasan kanshi, yasan damuwa ce fal cikin shi. Damuwar da shi ne ya jaza mishi. 

Da gudu Arif ya ƙarasa cikin falon ko takalman shi bai cire ba. 

“Yaya…”

Da mamaki ƙarara a fuskar Labeeb ya dago yana kallon Arif ɗin, murmushin da ya yi tattare yake da damuwa da wani abu da ba zai fassaru ba. 

“Arif… How?…Ta yaya ka zo… I mean yaushe?”

Murmushi Arif yake yi sosai. Don dukkan su basu san da zuwan shi ba, yana kuma jin daɗin mamakin da ya basu. 

“Suprise?”

Ya tambaya yana buɗe hannayenshi, murmushin da yake har haƙoranshi sai da suka bayyana. Hannu Labeeb ya miƙa mishi, Arif ɗin ta kama. 

“Mun yi kewar ka sosai…”

Labeeb ɗin ya faɗi yana jin yadda yai kewar ɗan ƙanin nashi, musamman yanzun da ya ganshi. Suna waya kusan kullum, tunda ya tafi sau ɗaya labeeb yagan shi. 

Shi ya je Jordan ɗin. Zama kusa da shi arif ya yi. 

“Mummy ta biya maka kuɗin dawowa ko?”

Labeeb ya buƙata yana kallon shi, har lokacin yana jin zuwan shi kamar a mafarki, ganin Arif ɗin na ɗan rage mishi kaɗan daga cikin damuwar da yake ji. Girgiza kai Arif ya yi. 

“Yaya Mamdud ne…”

Ya amsa mishi, sunan Mamdud na dira kunnuwan Labeeb da wani yanayi marar daɗi. Ta gefen idon shi ya ga kamar mutum a tsaye. Da sauri ya juya kanshi gaba ɗaya. 

Sai lokacin ya ga Mamdud, duka idanuwansu kan junansu. Labeeb bai taɓa ganin Mamdud a yadda yake ganin shi yanzun ba.

Fuskar shi ta kumbure, babu nutsuwa balle alamar kwanciyar hankali a tare da shi. Miƙewa Labeeb ya yi, a hankali yake takawa yana ƙarasawa inda Mamdud yake. 

Kanshi ya sadda ƙasa, yana jin takun tafiyar Labeeb kamar a cikin zuciyar shi yake yin shi, har ya ƙaraso daf da shi, hannun shi Labeeb ya ɗora akan kafaɗar Mamdud. 

Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“In gawata kake son gani karka damu Mamdud…ba zai ɗauki lokaci ba. In kuma ba za ka iya jira ba… Kowa na ciki, ka faɗa musu ko me yake faruwa kawai…”

Har lokacin idanuwan Mamdud na kafe a ƙasa, yana jin duk abinda Labeeb yake faɗi cikin kunnuwan shi, maganganun shi na zauna mishi a wajaje da dama. 

Nazarin shi Labeeb ke yi, in ba zuwa yai ya hargitsa musu komai ba, baisan me ya kawo shi ba. Tun jiya yake tsoron faruwar hakan. 

Sai dai ya rasa me yake ji tun yau da safe, wata irin nutsuwa ce zuciyar shi ta yi. Yana jin kamar ko me yake shirin sake taɓa shi a yau ba zai iya kauce mishi ba. 

Baisan abinda zai faru ba in aka gane cikin jikin Zulfa na Mamdud ne, ya rasa me yake ji haka, yanayi ne da ya kasa gane daga inda yake fitowa. 

“Ka faɗa musu kawai… In damuwar da nake ciki bata kashe ni ba… Zullumin me za ka yi nan gaba zai sa min ciwon zuciya.”

Labeeb ya faɗi yana sauke hannunshi daga kafaɗar Mamdud, ya tsaya tare da zuba wa Mamdud ɗin idanuwa don ya ga ko me zai yi. 

In har haka kake ji in kayi laifin da ba zai taɓa gyaruwa ba, in ka ɓata rayuwar mutanen da basu yi maka komai ba banda alkhairi, Mamdud na mamakin yadda ya kasa kokawa da zuciyar shi. 

Zafin da yake ji yanzun ya girmi hassadar da ta baibaye zuciyarshi har ta kawo shi inda yake tsaye yanzun. Ya kasa ɗaga idanuwan shi ya kalli Labeeb. 

Ya kasa yin komai banda tsayuwa yana jin labeeb na faɗin kalaman da ke ƙarasa wargaza mishi zuciya. Da baya baya ya soma tafiya yana fita daga gidan. 

“Yaya Mamdud! Don Allah karka tafi…”

Arif ke faɗi da ƙarfi yana miƙewa, juyawa Mamdud yayi ya fita daga ɗakin da sauri, ba zai iya tsayawa ba. Ba zai iya ganin abinda yai musu ba. 

Labeeb na kallon Arif ya bi Mamdud da gudu.

“Arif! Arif!! Arif!!!”

Ganin ko alamar ya ji shi bai nuna ba balle ma ya dawo yasa shi ƙarasawa inda takalmanshi suke ya saka yana bin bayan su. 

Kusancin su da shi babu abinda ya ja musu sai ɓacin rai da tabon da ba zai gogu ba. In har ganin Labeeb da ya yi ya sa shi jin kamar numfashin shi zai ɗauke. 

Ba zai iya kallon fuskokin su Asad ba, ba zai iya kallon tsanar shi a idanuwan su ba, gara ciwon rasa su yai mishi abinda zai mishi. 

Gara ya rufe idanuwanshi na ƙarshe a duniya, zuciyarshi na ganin murmushin su da ƙaunar su da bai dace su yi mishi ita ba. Hawaye masu zafi ne suka zubo mishi. 

Bayan hannun shi yasa yana goge su tare da jan numfashin da ya soma tsaitsaya mishi. 

“Yaya Mamdud…”

Ya ji muryar Arif, sauri ya ƙara, kafin ya soma gudu yana nufar gate ɗin gidan. Yana jin Arif na bin shi a baya. Yana jin yadda in ƙafarshi ta bar cikin gidan ya gama rasa su. 

Zai musu nisa sosai, wasu hawayen ne ke ƙara zubo mishi lokacin da ƙafarshi ta taka gate ɗin gidan, ya manta yana da wata mota balle ya tuna da ita ya zo gidan.

Kawai so yake yai musu nisa, so yake ya fita daga gidan kafin ya ga abinda ba zuciyarshi bace zata sake tarwatsewa ba wannan karon, tsayawa za ta iya yi gaba ɗaya. 

In da yana da tabbacin abinda zai tarar a lahirarshi mai kyau ne, ba zai damu da mutuwar shi ba sosai. Yana da zunuban da baisan ta inda zai fara wanke su ba. 

Iskar da ya shaƙa sai da tai mishi daban da ta cikin gidan, da gudu ya tsallaka ɗaya gefen yana maida numfashi kafin ya soma tafiya da sauri sosai. 

“Saboda me yasa ba zaka tsaya ba?! Kai ka faɗa min in muna gudu daga abinda muke tsoro ba zai barmu ba har abada!”

Arif ke faɗi yana jin wasu hawaye masu zafi na zubo mishi. Ya kula da yanayin Mamdud ɗin, barinsu yake son yi gaba ɗaya. Yanzun ɗin ma bai tsaya ba, sauri ma yake ƙarawa. 

Ya ƙi ko juyowa. Ganin hakan yasa Arif takawa zai tsallaka babbar hanyar da ta raba tsakanin shi da Mamdud ɗin.

“Arif!!!”

Labeeb daya biyo bayanshi ya kira, ganin ko kaɗan bai kula da motar da ta tunkaro shi da gudu ba. A zuciyarshi Mamdud ya fara jin wani abu zai faru kafin yanayin kiran da Labeeb yai ma Arif cikin tashin hankali yasa shi juyowa. 

Kamar a wata duniya ta daban daga shi har Labeeb suke kallon yadda da alama control ɗin motar ya ƙwace wa mai ita, saboda da gudu direbobi kan shigo hanyar sanin da wuya ka ga mutane na zirga-zirga da ƙafafuwan su. 

Juyowa Arif ya yi saboda kiran da ya ji Labeeb ya mishi, kamar a mafarki, sai dai ganin motar yayi daf da shi, kafn wani abu da ba zai kira bacci ba ya ɗauke shi. 

Komai yai mishi nauyi, yana jin yadda motar ta dake shi da ƙarfi, wata irin iska ta wuce ta cikin kunnuwanshi, kafin ya ji duka jikin shi a wani irin yanayi da ba zai misaltu ba. 

Wani abu ya ji yana mishi yawo a ko ina na jikin shi, kafin ya ji shi a ƙasa da wata irin buguwa da zafinta yake shigar shi a hankali a hankali. 

Tsaye Labeeb ya yi kamar an dasa shi, ya ɗauka ya gama sanin tashin hankali, abinda yake ji yanzun da gaban idanshi mota tai sama da Arif ta jefa shi can gefe ya girmi tashin hankali.

Zuciyar shi tai tsaye cik da wani irin shiru a ƙirjin shi kamar yadda yake jin duka duniyar ta tsaya, can nesa yake jin ƙarar motar da inda ta doka. Amma idanuwan shi na kafe kan Arif da ke kwance. 

Ƙafafuwan Mamdud yake ji kamar ba nashi ba saboda nauyin da suka mishi, sauri yake so ya yi ya ƙarasa inda Arif yake kwance amma da ƙyar yake cira ƙafafuwan shi. 

Abinda duk yake ji ɗazu shafar ruwa ne akan yanzun. Da ƙyar ya samu ya ƙarasa inda Arif yake kwance, tsugunnawa Mamdud yayi yana yawata idanuwanshi kan Arif ɗin, 

Baisan iya ina jini yake a jikin Arif ɗin ba ko daga ina yake fitowa, amma gani yake ko ina na jikin shi da rigarshi jinin ne. 

“Arif…arif…”

Mamdud ke kiran sunanshi muryarshi cike da tashin hankali, hannuwan shi sun kasa ƙarasawa su taɓa Arif ɗin su ga ko yana motsi ko baya yi. 

Zuciyarshi yawo take yi, yana jin bugunta har cikin idanuwan shi da ke kallon Arif a kwance, har cikin hannuwan shi da sun kasa ƙarasawa jikin Arif ɗin. 

Kamar an sa wani abu an tura shi, jikinshi Labeeb yake ji kamar ba nashi ba da yake takawa yana tsallakawa, haka da yake takawa inda Mamdud da Arif ɗin suke. 

Gani yake kamar wani mummunan mafarki ne da In ya yi ƙoƙari ya ƙi ƙarasawa inda su Mamdud ɗin suke zai farka. Amma ina, gaskiyar abinda yake faruwa ya ƙara tabbatar mishi da ya ƙarasa inda Arif yake kwance. 

Tsugunnawa ya yi ya sa hannuwanshi duka biyun ya ɗago da Arif, yana kallon jinin da ya wanke mishi fuska, a jikinshi ya riƙe Arif ɗin ya sa hannun shi yana shafar fuskar shi. 

Yana jin jinin da ke fuskar Arif ɗin a hannunshi da wani yanayi da ya zauna daram a zuciyarshi. Buɗe bakin shi ya yi, amma ya kasa fito da kalma ko ɗaya. 

Sai da ya buɗe bakin shi yana rufewa ya fi a ƙirga kafij can ƙasan maƙoshi ya samu cewa, 

“A.. Arif..”

Wani numfashi Arif ya ja jini na sake fitowa ta hancin shi, Mamdud ya kai hannu yana dafa Arif ɗin, hannu Arif ya ɗago yana kama na Mamdud da ke jikin shi. 

“Yaya… Ka yafe mishi… Duka rayuwar mu muna da kai… Kana nuna mana abinda ya kamata da wanda bai kamata ba… Ba shi da kowa… Please…”

Wasu hawaye ne masu ɗumi suka tarar wa Mamdud a idanuwa, da ka ga yanayin da Arif yake maganar kasan a wahalce yake yinta. Abinda yake ji bai hana shi roƙar mishi gafarar su Labeeb ba. 

Bayan baisan me ya yi ba, wannan ƙaunar son zuciya ya ja mishi rasawa. Ƙaunar da yake da yaƙinin ko ‘yan uwan da suka haɗa jini da shi ba kowa zai so shi kamar Arif ba. 

Hannu labeeb yasa yana shafa gefen fuskar Arif ɗin, bai damu da jinin da ke ɓata mishi hannu ba. 

“Shhh… Ka yi shiru mu tafi asibiti… Ka daina magana…”

Bai sake cewa komai ba, sai tari da ya yi, wani jinin na sake fito mishi ta hanci, shaƙuwa ya soma yi, ya yi guda biyu zuwa uku, a ta huɗun ya ja wani numfashi da Labeeb bai ga sa’adda ya fito da shi ba. 

“Arif…”

Mamdud ya kira yana kallon shi cikin tashin hankali.

“Don… Dawud…”

Labeeb ya faɗi yana miƙewa da arif a hannun shi, da gudu bai damu da mutanen da suka fara taruwa kan motar da ta bige Arif ba. 

Ya nufi cikin gida da shi, Mamdud na bin bayanshi, ɓangaren su Dawud ya shiga, kanshi tsaye ɗakin Dawud ya wuce, ya sa ƙafa ya tura ƙofar. 

Ƙarar buɗe ƙofar ya sa Dawud da ke kwance tashi babu shiri, ganin Labeeb da yaro a hannu, sai kuma Mamdud kamar daga sama ya sa shi saukowa. 

“El? Lafiya?”

Arif ya sauke mishi kan gado.

“Ban sani ba… Mota ta buge shi… He is bleeding… Yanzun ya zo… Wallahi yanzun ya zo…”

Ganin Labeeb ba cikin hayyacin shi yake ba ya sa dawud faɗin, 

“Zauna… Bari in fara duba shi sai mu tafi asibiti…”

Girgiza mishi kai Labeeb ya yi. 

“Kawai ka duba shi ya tashi!”

Ya faɗi cikin ɗaga murya, Mamdud kam idanuwan shi na kafe kan Arif, zuciyarshi ta yi wani sanyi na ban mamaki. Da ƙyar Labeeb yake fitar da numfashi yana maida shi saboda tashin hankali. 

Duka komai kamar a fim yake ganin shi, zuwan Arif, fitar su, bigewar da mota tai mishi. Har yanzun zuciyar shi bata gama yarda da faruwar abin ba. 

Hannun shi Dawud ya fara kamawa ya ɗanyi jim, kafin ya taɓa wuyanshi. Sai da zuciyarshi tai wani tsalle, juyowa yayi ya sauke idanuwan shi cikin na Labeeb. 

Haushin shi da yake ji bai hana shi tausaya mishi ba. Saboda ya fi kowa sanin abinda Labeeb ke shirin ji. Jarabawa ce da ta fi kowacce zafi da wahalar jurewa. 

A hankali ya girgiza mishi kai, ɗakin Mamdud ya ji yana jujjuya mishi. Ƙwaƙwalwar shi na son fahimtar abinda Dawud yake nufi da girgiza kan da ya yi. 

Dariya Labeeb ya yi wadda da ka ji ta kasan ba ta lafiya bace ba. Ya kalli arif da ke kwance kan gadon Dawud kafin ya sake kallon Dawud ɗin. 

“Don Allah in saboda Zulfa ne kake min wasan nan ka daina. Ka yi haƙuri ka tashe shi…don Allah karka hora ni ta haka…Ka yi haƙuri…”

Wani abu ne ya tsaya wa Dawud a wuya da maganganun Labeeb ɗin. Ciwon kanshi na dawowa sabo, duk da cewa ba sosai ya shaƙu da Arif ba, hakan ba ya nufin baya ƙaunar shi shima. 

Wannan part ɗin shi yake ta addu’a akai kullum. Kar ya taɓa faɗa wa wani rashin wani nashi. Sai gashi zai fara da ɗan uwanshi. 

“Ka yi haƙuri El… Ya rasu.”

Wata iska Labeeb ya ji ta fara cika mishi kunnuwa kafin kalaman Dawud ɗin su ƙarasa iso mishi. Komai ya ji ya sake tsaya mishi cik. 

Fahimtar komai ta tsaya mishi, baya gane komai, baya jin komai banda kalaman Dawud da abinda suke mishi. Bai ma kula da Mamdud ba balle ya ga ya fita daga ɗakin da gudu. 

Ranƙwafawa ya yi yana ɗaukar Arif kan kafaɗarshi, gida zai je don ya ga alamar Dawud rama abinda ya faru da zulfa yake son yi. 

Da kallo Dawud ya bi shi har ya fice daga ɗakin , ji ya yi ba zai iya ba ya miƙe ya bi bayanshi. Faɗan su ba zai hana yai mishi abinda ya kamata ba. 

Har ya nufi gida ya fasa. Aljihunshi ya taɓa. Mukullan motarshi na ciki da ya zo da ita, don haka ya koma ya buɗe bayan motar ya saka Arif ya rufe ya zagayo ya ga Dawud a tsaye. 

“Ina zaka kaishi?”

“Asibiti.”

Labeeb ya bashi amsa yana buɗe murfin motar ya shiga. Dawud bai ce komai ba ya zagaya ya buɗe ɗayan ɓangaren ya shiga shima. 

Kowa da yadda yake ɗaukar mutuwa in ta zo mishi. Labeeb na son samun tabbacin wani ba shi ba. In sun je asibitin ma labarin ba canzawa zai yi ba. Motar Labeeb ya kunna yana fita daga gidan ya nufi hanyar asibiti. 

<< Rayuwarmu 34Rayuwarmu 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.