Skip to content
Part 36 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Zip ɗin doguwar rigar da ke jikinta Ishaq ya zage mata yana ɗora hannuwanshi akan kafaɗarta. 

“Mene ne?”

“Kawai bana jin daɗi ne. Ina jin wani irin abu da ban taɓa ji ba.”

Juyo da ita Ishaq ya yi yana kallon fuskarta. 

“In sha Allah alkhairi ne… Ki zo ki sa ma cikinki wani abu.”

Girgiza mishi kai ta yi. 

“Don Allah ka kaini gida kawai. Bana jin yunwa.”

“Ba fa zaki fita daga gidan nan ba ki ci wani abu ba.”

Fuskarshi ta kalla babu alamar wasa a cikinta. Dole ta nufi ɓangaren dining ɗin ta haɗa musu tea ɗin ta miƙa mishi nashi. 

Daga ruwan tea sai farfesun kayan ciki da ta ɗan ci. Ta jira shi ya gama cin nashi, miƙewa ta yi, zuciyarta tai wani irin dokawa. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”

Ta faɗi da ya maida hankalin Ishaq kanta. 

“Lafiya Zainab?”

Idanuwanta cike da hawaye ta ce, 

“Nima ban sani ba… Wani abu ya faru… Don Allah ka kaini gida…”

Yadda ya ga jikinta na ɓari ya sa shi miƙewa ya zo ya kamata yana hugging ɗinta. Kuka take yi. 

“Ka kaini gida…”

“Yanzun nan… Don Allah ki ɗan nutsu. Babu abinda ya faru… Ki kwantar da hankalin ki…”

Jinshi kawai take, ita ta san abinda ta ji a jikinta, da zuciyarta. Ta san wani abu ya faru da su. Sai dai ta rasa ko menene. Sai da ya ga ta ɗan nutsu tukunna ya goge mata fuskarta. 

Shi ya ɗauko mata mayafinta ya bata, yana ja mata hanci, ta ture mishi hannu, bata cikin yanayin biye wa tsokanar shi. Gida take son zuwa kawai. 

****** 

Har cikin gida suka shiga da Ishaq. Jin babu wanda ya amsa sallamar da suke yasa shi ce mata, 

“Kin ga duk bacci suke ko? Ki zo mu koma in sun tashi sai mu zo.”

Daƙuna fuska ta yi da ya sa ta ƙara mishi kyau. 

“Ka zauna please…za su tashi yanzun… Zauna in ɗauko maka ruwa.”

“Ki ɗauko mana ruwa dai.”

Ya amsa yana murmushi. 

“Kai ne baƙo.”

“Baƙi mu duka. Kin bar gidan remember? Kina da naki gidan yanzun.”

Harararshi ta yi ta wuce kitchen. Bama ya jin ƙishi, murmushi yake so ya ga ta yi ko yaya ne shi yasa yake janta da tsokana. Ruwa da kofi ta dawo da shi ta zauna a gefen shi. Karɓa kawai ya yi ya ajiye yana ɗan janta da hira. 

**** 

Suna ƙarasawa asibitin Labeeb ko mukullin motar bai cire ba ya fito, sai dai Dawud ya cire mishi key ɗin. Haka murfin da ya buɗe ya ɗauki Arif ma shi ya rufe. 

Ya bi bayanshi, ganin yadda suka riƙo Arif ya sa aka zo don kawo musu taimako, hannun shi kawai wata nurse ta kama, ta kalli likitan da ya taho. 

Bama su shiga da Arif ko ina ba, a nan likitan ya dudduba shi. Ya kalle su yana faɗin, 

“Wannan ai ya rasu.”

Shiru Labeeb ya yi na wasu ‘yan lokuta, hannu Dawud ya kai zai taɓa shi ya janye jikin shi. Arif ya ɗauka yana nufar hanyar da suka bi suka shigo. 

Sauke numfashi Dawud ya yi yana bin shi. Bayan motar Labeeb ya shiga ya zauna, yana rungume da arif a jikinsh. Dawud ya rufe ƙofar. Ya zagaya ya shiga ya ja motar yana nufar hanyar gida. 

Labeeb ya kasa ɗauke idanuwanshi daga kan Arif da ke kwance a jikin shi. Ya kasa gane me yake faruwa da su haka. Ya kasa yarda Arif ya rasu. 

Ta yaya za a ce mishi Arif ya rasu bayan ko daɗewa bai yi ba da zuwa ƙasar. Ta yaya ma za a ce mishi Arif ya rasu bayan gasu nan manya da tasu rayuwar. 

Babu kalar tunanin da bai zo wa Labeeb ba, cikin su babu ɗaya na yarda Arif ya rasu. Wani abin ne dai yake faruwa da ya kasa fahimta. In suka je gida wajen su Mummy da su Anees za su faɗa mishi ko me ke faruwa. 

Baisan sun zo gida ba sai dai ya ji Dawud ya buɗe murfin motar. Sakkowa ya yi da Arif riƙe a jikin shi. 

“El…”

Hannu Labeeb ya ɗaga mishi. 

“No… Karka ce min ya rasu…kai ma baka fahimci me ke faruwa ba… Abinda ke damun Zulfa kawai ya isheni… Ga yaro na can a gida shi ma…ban san ya zan faɗa mishi ta hanyar da ya fito ba… Now sai ka ce min Arif ya rasu? No…”

Ya ƙarasa maganar yana nufar hanyar gidan su kamar wanda ya samu matsalar ƙwaƙwalwa. Dawud bai bi bayan shi ba ya nufi nasu ɓangaren don ya faɗa wa su Mami abinda yake faruwa. 

Sauri Labeeb yake amma gani yake kamar gidan ya ƙara tsayi, ko sallama bai yi ba ya sa kai falon, Zainab da Ishaq ya gani a zaune. 

Yana kallon Zainab ta miƙe da sauri tana nufo shi. 

“Yaya…”

Ta kira cikin tashin hankali, janye fuskar Arif ya yi daga inda za ta gani yana faɗin, 

“Karki ƙaraso Zee Zee… Karki ƙaraso don Allah…”

Baya son ta ga Arif tukunna, sai Mummy ta ganshi ta faɗa mishi ko me yake faruwa da su. Baya son Zainab ta shiga irin tashin hankalin da yake ji bayan Arif ba rasuwa yayi ba. 

“Mummy! Mummy!!”

Labeeb yake kira, sake matsawa kusa da shi Zainab ta yi tana son ganin waye yake riƙe da shi haka amma ya ɓoye fuskar a ƙirjin shi. Hannun Arif da yake a sake Zainab ta kama. 

Yatsun shi ta gani, zuciyarta da ke dokawa tai wani tsalle kamar tana neman hanyar fitowa, kafin ta ji wani abu ya yamutsa a cikinta.

“Arif…”

Ta faɗi muryarta can ƙasa, sosai ta riƙe hannun Arif da take jin ya mata sanyi ƙarara. Matsawa ta yi ta kama hannun shi ta ɗora a fuskarta. 

Wani abu ya tsirga mata tun daga yatsan ƙafarta har cikin kanta. Bata son ta fara yawo da tunaninta akan abinda ya samu Arif. Za ta tsayar da tunanin ta a mamakin me Arif yake yi a Nigeria. 

Me Arif yake a jikin Labeeb. Ko shekaranjiya sun daɗe suna waya da shi. Kuma yana Jordan. Tashin hankali yasa ta manta bata kira shi ba jiya. 

Tana shirin buɗe bakinta Mummy ta fito. 

“Labeeb lafiya?”

Ta tambaya, Zainab ta juya tana sauke idanuwanta kan Mummy da kallo ɗaya za kai mata kasan ita ma ba cikin kwanciyar hankali take ba. 

Karo na farko da Zainab ta ga fuskar Mummy babu kwalliya. Ko bacci take sai ka ga kwalliya a fuskarta. Sai ta ga ta mata wani fayau. 

Da sauri Labeeb ya ƙarasa inda Mummy take tsaye, tsugunnawa yayi a hankali ya sauke Arif akan kafet. Mummy ta ja wani numfashi tana dafe ƙirjinta inda zuciyarta tai wani irin tsalle. 

Da sauri Zainab ta durƙushe a wajen ganin jini dake fuskar Arif da jikinshi tana riƙoshi jikinta. Cikin wani irin kuka take kallon Labeeb tana faɗin, 

“Me ya same shi Yaya? Arif… Arif ka kalle ni… Arif… Yaya me ya same shi?”

Idanuwan Labeeb kafe akan Arif, akwai wani yanayi na nutsuwa a fuskar Arif ɗin da bai taɓa gani ba. Jinin da ke jiki bai hana shi ganinta ba. 

Da wani abu a muryar shi, ba tare da ya ɗauke idanuwan shi daga kan Arif ɗin ba ya ce, 

“Ya rasu!”

Yamutsa fuska mummy ta yi, kafin ta soma fifita fuskarta da hannunta tana jin iskar wajen ta mata kaɗan. Kamar saukar jirgi haka ta ji maganar Labeeb. 

Ya za a yi ya ce mata Arif ya rasu. Ta yaya? Me ya same shi? Babu yadda za a yi ya rasu. Duka lokacin rayuwar shi nawa ta samu? Bata ma san abincin da ya fi so ba, ba za ta tuna sa’adda suka yi maganar awa ɗaya da Arif ba. 

Ba ta gama sanin ɗanta ba. Ba ta ko samu lokacin da za ta so shi yadda ya kamata ba. Ba yanzun ba, Arif ba zai barta yanzun ba ta nuna mishi kalar ƙaunar da take mishi ba. 

Arif zainab ta sake kallo, tukunna ta maida duka hankalinta akan labeeb. 

“Yaya me ka ce?”

“Ya rasu!”

Ya sake faɗi ba tare da ya kalle ta ba, ita yake faɗa ww, amma kanshi yake son tabbatar wa da maganar. Girgiza mishi kai Zainab take. 

Rabonta da ganin Arif tun ranar daren aurenta. Sai kuma a hotuna, ba zai yiwu ace shi ne gani na ƙarshe da za ta yi mishi da rayuwar shi ba. 

Anees ne ya fito ɗaukar ruwa don na ɗakinsu ya ƙare, ya ga Mummy tsaye, Labeeb a zaune kan kafet da Zainab. Ƙafafuwan Arif da ke sanye da takalma ya fara kallo. 

Juyawa Zainab ta yi tana son wani ya ƙaryata maganar da Labeeb yayi. 

“Yaya Anees…Yaya Anees zo ka ji… Arif ya rasu wai!”

Ware idanuwa Anees ya yi, Maganarta na zo mishi kamar daga sama. Ya ma kasa fahimtar me take cewa, ya kuma kasa ƙarasawa. 

Asad ne shi ma ya fito, daga shi sai singlet da dogon wando, fuskar Anees da ta canza kala yake kallo. 

“Arif ya rasu!”

Ya maimaita yana ɗanɗana kalaman a harshen shi ɗacinsu na zauna mishi, hannu Asad ya sa ya hankaɗe shi. 

“Wanne hauka ne wannan?”

Ya tambaya rai a ɓace yana juya idanuwan shi kan Mummy da Ishaq da ke gefe kafin ya mayar da shi kan su Labeeb, da sauri ya ƙarasa inda suke. 

Arif da rabin jikin shi ke kan Zainab rabi a ƙasa ya kalla. Baisan sa’adda ƙafafuwanshi suka yi ƙasa ba, hannu ya kai yana janyo Arif daga jikin Zainab da hawaye ke zubar ma kamar an buɗe wani abu. 

Hannun shi na rawa ya kai shi yana rasa inda zai taɓa a fuskar Arif ɗin. Wani irin tsoro na shigar shi. Babu abinda yake gani a idanuwan shi sai fuskar Sajda. 

Sai tashin hankalin da ya gani na mutuwar sajda. Muryarshi na rawa ya ce, 

“Arif bansan me ma kake a gida ba…ko me ka zo yi ka tashi… Ka faɗa min wannan mafarki ne mummuna da zan farka in ƙara sonka saboda bazan iya rasa ka ba…”

Ko motsi bai ga Arif ya yi ba. Hannunshi ya ɗora akan ƙirjin Arif ɗin ya ji wani irin shiru da bai taɓa ji ba a rayuwarshi. Wani yanayi yake ji da ba zai faɗu ba. Da sauri ya juya ya kalli Anees da fuskarshi ta yi kaman babu jini. 

“Ya rasu…Anees ya rasu…”

Ƙarasowa Anees ya yi ya zauna kusa da Asad, hannun shi Asad ya kamo ya ɗora akan ƙirjin Arif ɗin 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Anees ya faɗi yana jin wani abu da ya buɗe a ƙirjin shi. Asad ya sake maimaita abin da Anees ya faɗi kafin Zainab da ke wani irin kuka mai cin rai ta fara. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Wadda Anees ya sake yi tare suka yi ta su ukkun, hannu Zainab ta miƙa ta kamo hannun Labeeb da ke girgiza mata kai, ya kasa faɗar kalmar da ita kaɗai zai furta ya samu sauƙi. 

Da ƙarfi suke faɗa, muryar Anees ita ta fara karyewa da alamar kuka. Arif yake kallo a kwance da idanuwanshi, a zuciyarshi yanayin shi yake kallo da rayuwar shi. 

Shiru-shirun shi, murmushin shi, yanayin maganar shi. Cikin kunnuwan shi yake jin yadda yakan kira sunan shi, yanayin yadda yakan saka su dariya in har yai magana. 

Hawaye masu ɗumi ne suka zubo mishi yana tunanin meye sanadin wannan lokacin, me ya yi sanadin rabuwar su da ƙaninsu da basu samu lokaci mai tsawo tare da shi ba. 

Jin kukan da Anees yake shi ya buɗe wa Asad hanyar nashi. Ji yake kamar ya cire Zuciyarshi ya ajiye ta gefe saboda raɗaɗin da take mishi. Ya yi kukan mutuwar Sajda. 

Sai yanzun da gawar Arif ke kwance a jikinshi yasan taya su Dawud kuka kawai ya yi a wancan lokacin. Yau ne yasan asalin abinda suka ji. Sam ko ɗigon hawaye bai zubo wa Labeeb ba. 

Ya kuma kasa motsa bakin shi. Kallon su yake yadda suke kuka suna maimaita

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Ɗacin mutuwar Arif da kukan su na samun waje daban-daban suna zauna mishi. Baisan ta ina zai fara ba. Mummy kam a tsaye take kamar an dasata har lokacin. 

Tana ganin gaskiyar abinda yake faruwa. Tana ganin da gaske Arif ne ya rasu, da gaske yaron da ko tsayawa ta shayar ba ta yi ba. Yaron da duk cikin ‘ya’ yanta shi ne bai samu kulawarta ko ta yarinta ba. 

Saboda daga kanshi ta tsayar da haihuwa. Ta gama tsara rayuwarta, ta gama hango lokacin da za ta ajiye kasuwancinta ta zauna da yaranta. 

Lokacin da za ta ƙaunace su, ta ɗauka tana da dukkan lokacin da take buƙata a hannunta. Tun shekaranjiya ta gane ita ba komai bace ba. 

Ba ta isa ta tsara rayuwa yadda take so ba. Saboda tun kafin a halicceta komai yake a tsare. Sai ga gawar Arif an shigo mata da ita. 

Ɗakin ta ji yana jujjuya mata, kafin wani duhu ya rufe mata ido, ta yi ƙasa luu, da zafin nama Labeeb ya tarbeta ta faɗa hannun shi. Su Zainab yake kallo da babu wanda ya motsa daga inda yake. 

Ya rasa me zai yi, Ishaq da ke tsaye yana kallon su, yana kallon yadda mutane ke asarar lokacin su wajen neman duniyar da ba za su dawwama a cikinta ba. Tausayin su na cika mishi zuciya. 

Ya zagaya ya ɗauko ruwan da Zainab ta kawo mishi da bai sha ba, ya buɗe yana miƙa wa Labeeb, ya karɓa ya zuba a hannun shi yana shafa wa Mummy a fuskarta. 

Buɗe idanuwanta ta yi ta tashi daga jikin Labeeb. 

“Don Allah ku ce mon ɗana bai rasu ba, kuce min gwadani kuke don in gane muhimmancin ku…”

Kallon ta Zainab ta yi. 

“Ya rasu Mummy… Ko kin gane muhimmancin shi ba zai dawo ba… Arif ya rasu… Ya rasu…”

Zainab ta ƙarasa cikin kuka, Ishaq ne ya zagayo ya kama hannunta, zame hannunta ta yi daga cikin nashi. 

“Ba zai rage mu

In komai ba… Ka barni na yi kukan rashin ƙanina…”

Kai kawai ya ɗaga mata, bai taɓa rasa kowa ba, baisan abinda take ji ba. Miƙewa Labeeb ya yi yana nufar ƙofa. Wannan ba ita bace soyayyar da za su nuna wa Arif. 

Yana zuwa ƙofa ya ci karo da Dawud da Tayyab har da Mami. Kallon su ya yi. 

“A zo a kaishi…”

Kai Dawud ya ɗaga mishi.

“Ka kira mutane, zan siyo komai…”

Labeeb bai ce komai ba, yana kallon Mami ta wuce cikin gida. Tayyab yake kallo. 

“Allah ya baku dangana… Allah ya baku juriya Yaya Labeeb.”

Tayyab ya faɗi yana juyawa shi ma dan n ya faɗa wa ‘yan gidan su Jarood. Yasan abinda suke ji, har yanzun zafin mutuwar Ummi da Sajda na mai raɗaɗi. 

Tsaye Labeeb ya yi yana rasa abinda yake ji, maida numfashi yake a hankali a hankali kafin ya koma cikin falon. Kusa da Mummy ya tsugunna da ke wani irin kuka. 

“Ina Dady?”

Ya tambaya muryarshi a dishe. Hanyar ɗaki Mummy ta nuna mishi, ya miƙe yana nufar ɓangaren Dady. A bakin ƙofa ya tsaya ya ƙwanƙwasa. 

Ya kai mintina biyu yana ƙwanƙwasa ƙofar kafin ya ji alamar motsi, Dady ya zo ya buɗe ƙofar. Kallo ɗaya yai wa Labeeb yasan ba lafiya ba. 

“Arif ne ya rasu…”

Ya faɗi yana juyawa ba tare da ya tsaya ya ga me abinda ya faɗa yai ma Dady ba. Falon ya koma yana zaro wayarshi daga aljihun shi. Ya rasa wanda ya kamata ya fara kira. 

Text ya yi ya sanar da rasuwar Arif ɗin yana marking duka contacts ɗinshi ya tura ya mayar da wayar a aljihunshi. Ya dawo wajen da su Zainab suke. 

Yana kallon Zainab na kuka ta zame Arif a hankali daga jikinta zuwa kan kafet ɗin. Tana kallon su Asad. 

“Wa zai mishi wanka?”

Ta buƙata, matsawa Asad ya yi kusa da Anees yana girgiza wa Zainab kai, shi kam ba zai iya ba. Abinda ke fuskar shi iri ɗaya ne da na Asad shi ma ba zai iya ba. 

Dukkan su matsawa suka yi kusa da Mummy da ke kuka kamar za ta shiɗe. Ɗaga kai Zainab ta yi ta kalli Mami, kai Mami ta ɗan ɗaga mata. 

Miƙewa Zainab ta yi tana goge hawayen da ke fuskarta. Dawud ya shigo da farin zawwati a hannun shi, zare da kuma allura, Mami ta karɓa. 

Zainab ta tsugunna ta ɗauki Arif a kafaɗarta, tana jin yadda ya yi wani irin nauyi. Ɗakinshi ta nufa da shi Mami na bin bayanta. 

Ita da Mami suka haɗo ruwa suka ɗauko, Mami ta auna Arif da farin zawwatin da ta yanka ta fita ta ba wa Dawud don a haƙa kabari, ta dawo ɗakin. 

Zainab ba ta fara kuka ba sai da suka soma yi wa Arif wanka. Ta ga ƙugun shi ba zaune yake dai dai ba. Ko da ya rayu zai yi jinya mai tsayin gaske kafin ya samu sauƙi. 

Haka ƙafarshi guda ɗaya a karye take, sai ciwukan da ke hannunshi. Da kanshi waje biyu da ya fashe. Tsaf ita da Mami suka gama haɗa Arif. 

Su dukkansu hawaye suke. Zainab na rashin ɗan uwanta take. Mami kuma na tausayawa kanta take. Na rashin sanin yadda tata rayuwar za ta ƙare. 

Kafin a rufe shi har fuska, Zainab ta ranƙwafa ta sumbaci goshin shi. 

“Allah ya sadaka da Rahma Arif… Allah ya haskaka kabarinka… Ƙaunar mu bata isa ta tsayar da mutuwarka ba… Allah ya bamu jure rashin ka….”

Ta ƙarasa kuka marar sauti na ƙwace mata, miƙewa ta yi ta fito daga ɗakin. 

“Ku zo ku yi mishi bankwana…”

Ta ce wa su labeeb, ba musu suka bi bayanta zuwa ɗakin Arif ɗin, Labeeb ya fara tsugunnawa kan gawar Arif ya sumbaci goshin shi da kuncin shi. 

Yana jin kamar su yi musayar matsayi, sai dai ina. Shi kanshi lokaci yake jira, Arif ɗin da ya tafi ba sauri yayi ba. Shi ma da yake jiran lokaci bai yi jinkiri ba. 

“Allah ya jiƙanka Arif… Mutuwarka ta dawo da kai…ajali ne yake kiranka…”

Labeeb ya faɗi yana jin wani irin ɗaci, ya matsa gefe don Anees ya samu dama. Shi ma sumbatar Arif ɗin ya yi hawayen shi na ɗgowa har kan fuskar Arif. 

Kasa furta addu’arshi ya yi a fili. Asad suke kallo, kuka yake yana girgiza musu kai. 

“Ta yaya zan yi bankwana da shi? Ku faɗa min ya kake bankwana da ɗan uwanka sanin ba zai taɓa dawowa ba? Bazan iya ba… Don Allah ku bar ni…”

Kama hannun shi Anees ya yi, su dukkan su kuka suke yi. 

“ƙaunar da za ka yi mishi kenan Asad… Yau ne farkon soyayyar… Yanzun ne zai san muhimmancin shi a wajen mu…”

Kai Asad yake ɗaga mishi kafin ya tsugunna, da ƙyar ya iya sumbatar Arif ɗin, ya kasa ɗagowa daga kan gawar. Ji yake kamar a ƙara mishi ko da mintina biyar ne tare da Arif ɗin. 

Ko bankwana su yi, mintina biyar, sai da Anees ya kamashi ya ɗagoshi. Mummy kam ta kasa ƙarasawa. Tsoro mai girma ne yake ƙara shigarta. 

Lokutan da ta yi asara a neman duniya take gani. Yanzun in Allah ya so ita ma sai ta bi Arif ɗin. Ƙaunar shi tsakanin shi da ‘yan uwan shi take kallo. 

Tasan suna da tarin memories ɗinshi tare da su. Ita kam bata da shi. Ba komai na Arif zata iya tunawa ba. Abinda take da shi kaɗan ne. 

Gashi ya tafi. Cikin lokutan da ta yi asara har da ƙaunar ɗanta. Dady ne da Dawud suka shigo da makara. Tana kallo Zainab ta ɗaga kan Arif, Mami ta sa wani farin zawwatin ta naɗo daga bayan kanshi har goshin shi. 

Sannan suka ja wancan suka rufe mishi fuska, Mami ta ɗaure ƙarshen. Tana jin yadda suka rufe da wata ƙofa a zuciyarta. Wannan shi ne gani na ƙarshe da za ta yi wa ɗan da bata nuna wa ƙaunarta ba. 

Dady da Dawud suka kama Arif suka saka a cikin makarar. Sannan suka ɗauke shi za su fita da shi. Jikin Mami Zainab ta faɗa tana rufe idonta. 

Ɗacin a take ji wanda yasan mutuwar makusanci ne kawai zai fahimta. Makarar Mummy ta riƙe. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… Ku tsaya… Don Allah ku tsaya… Minti biyar in roƙe shi ya yafe min… Don Allah karku tafi da shi ban faɗa mishi yadda nake ƙaunar shi ba…”

Hannunta Dady ya kama ya cire daga jikin makarar, ya ɗan tallabi fuskarta kafin ya sakar wa Dawud da Labeeb makarar suks fita da ita. 

Sai da Mami ta taso ta kama Mummy saboda kukan da take yi. Shi kanshi Dady har lokacin mamakin mutuwar Arif ɗin yake yi, zuciyar shi na zafi da sanin yadda mutuwar ɗa take. 

**** 

Da ƙyar ya kawo kanshi waje saboda jirin da yake. Maganar Dawud ta taɓa wani abu a rayuwar shi da ba zai taɓa komawa dai dai ba. 

Motar shi ya buɗe ya shiga, ko ina a jikinshi ɓari yake, da ƙyar ya saka mukullin ya tayar da motar yana fita daga gidan. 

Sai dai ko hanya baya gani, hakan ya sa shi parking a tsallaken gidan ya haɗe kanshi da steering ɗin motar yana jin kamar ƙirjinshi zai fito. 

‘Yaya Mamdud yunwa nake ji. Na zo kitchen babu abinci..’

‘Yaya Mamdud sabon takalmin school nake so.’

‘Yaya Mamdud kayan zane.’

‘Yaya Mamdud ina ƙaunarka sosai…kasan hakan ko?’

Maganganun Arif suke dawo mishi kamar yana cikin motar tare da shi. Wani irin gunjin kuka ya saki, ya ɗauka rasa sun da ya yi jiya yana da ciwo. 

Sai yanzun da ya san ya rasa Arif har abada. Ko rashin sanin iyayen shi bai kai wannan abin da yake ji yanzun ba. Kuka yake kamar ƙaramin yaro. 

Ba ƙani bane kawai a wajen shi. Kamar ɗan da baisan ranar samun shi bane ba. Kamar ɗan uwan da bai da shi ne. Ba ƙaramin girgiza shi mutuwar Arif ta yi ba. 

Juyawa kawai zai yi, kiran da Arif yake mishi, tsayawa kawai zai yi. Inda ya tsaya… Inda ya juya… Kasa ƙarasawa yayi ko a tunanin shi saboda nauyin kalaman. 

Ƙaddara ba ta kautuwa, rufe idanuwanshi ya yi, babu abinda yake gani sai lokacin da motar nan tai sama da Arif, sai fuskar Arif da maganganun shi na ƙarshe. 

Baisan iya lokacin da ya ɗauka a haka yana kukan da yake ba. Sai ɗago kai ya yi, ya ga layin maƙil da mutane. Fitowa ya yi daga cikin motarshi yana kutsa tsakanin mutane yana wucewa. 

Sai da Zuciyarshi tai wani tsalle ganin makarar da ke ajiye ta gawar Arif. Ana mishi sallah hawaye na zubo wa Mamdud. Haka aka idar aka ɗauki gawar, da ƙyar Mamdud yake taka ƙafarshi. 

Hannunshi ya ji an kama, ya juya ya kalli Asad, rigar shadda ce a jikinshi, sai sweatpants, yanayin shigar kawai za ka gani kasan ba a nutshe yake ba. 

Fuskarshi ta kumbura suntum.  

“Ka ce min ciwon nan zai rage Yaya Mamdud… Ta ina za mu fara da rashin Arif a rayuwarmu?”

Hannunshi kawai Mamdud ya dumtse din ba zai iya magana ba. Ɗacin da yake ji ya wuce misali. Hankalin shi bai ƙara tashi ba sai da ya ga an saka Arif a kabari. 

Anees, Asad, Labeeb da Dady sun ɗibi ƙasa sun zuba, ɗan tura shi Dady ya yi, yana jin yadda suka ɗauke shi a matsayin ɗan ahalinsu shima. Tsugunnawa ya yi ya ɗibi ƙasar shi ma ya zuba. 

Sai da Dady ya kama shi ya ɗago da shi, tsayawa suka yi har aka gama rufe kabarin Arif ɗin, duk mutane suka juya suna barin maƙabartar. Su kaɗai aka bari. 

Labeeb Mamdud ya kalla, yanayin fuskarshi yasa shi jin son ya rungume sh ya bashi comfort ko ya yake, duk da shi ma abin da yake buƙata kenan.

Tsugunnawa Mamdud ya yi ya ɗora hannunshi akan kabarin Arif ɗin yana ɗago da hannun ya sumbata. 

“Ba ƙani bane kai a wajena Arif… Allah kaɗai yasan ƙaunar da nake maka don Shi kaɗai yake ganin zuciyata… Allah Ya fini sonka… Allah ya jiƙanka Arif…”

Yana ƙarasawa ya miƙe yana juyawa. Tafiya kawai yake yana haɗe hanya. In ya ce ga yadda akai ya maida kanshi inda motarshi take ƙarya yake. 

Shiga yayi ya tayar da ita, tuƙi yake yana wani irin kuka da ko hanya baya gani, a zuciyarshi yake jin yadda zai yi nisa da su Labeeb. Zaman shi da su bai amfane su da komai ba. 

Ya cutar da su da yawa, zai cire kanshi daga rayuwar su ko za su samu sauƙi, steering motar ya saki yana saka hannuwan shi duka biyun yana goge fuskar shi don sam ya manta cewar tuƙi yake. 

Sa’adda ya sauke hannuwanshi ya ji motar ta yi sama, juyi uku ya ji ta yi da shi yana barin kujerarshi saboda bai ɗaura seat belt ɗinshi ba. 

Yana jin yadda yake buguwa da ko ina da ina na motar da yadda take haɗuwa da ƙasa tana ƙara juyawa, kafin wani duhu ya rufe mishi idanuwa. 

***** 

Suna dawowa Labeeb cikin gidan su ya shiga, cike yake da mata, bai bi takan su ba ya wuce ɗakin Arif, ya tura yana shiga. Zainab ya samu a ciki zaune ta haɗe kanta da gwiwarta. 

Bai bi ta kanta ba ita ma, kan gadon Arif ɗin ya zauna. Ya sa hannun shi kan pillow ɗin da ke kai, ya ɗaga kanshi ya kalli ƙaton hotonsu su dukkansu da aka yi ranar baikon Zainab. 

Sai na Arif ɗin shi kaɗai yana dariya, da brush ɗin zanen shi a hannu, Labeeb na tuna lokacin ya ɗauke shi hoton, wani abu ya tsaya mishi a ƙirji. 

Wannan shi ne abinda yai saura tsakanin su da Arif. A tunanin su da zuciyarsu kawai ya rage. Ba za su sake ganin shi ba sai dai hoton shi. 

Duk yadda suke son jin muryarshi ba za su samu ba, sai dai su tuna ta, hannuwan shi yake kallo, duk da ya wanke jinin Arif ɗin lokacin sa yake alwala bai hana shi ganin kamar har lokacin akwai su a hannun shi ba. 

Ya kasa kuka balle ya ɗan samu sauƙi, turo ƙofar ya ji an yi. Anees ne da Asad suka shigo. Zama suka yi a kasa suna haɗa kawunansu da jikin shi suna sakin wani irin kuka. 

“Ta ya zamu koma dai-dai?”

Asad yake tambaya don yadda yake ji baya zaton za su taɓa komawa normal. 

“Yaya haka su zulfa suka ji? Haka ɗacin mutuwa yake?”

Anees yake faɗi yana jin ƙirjin shi kamar an zuba garwashi. Kuka suke Sosai, ƙasa Labeeb ya sakko yana kama su, a jikinshi suka kwanta suna kuka, hannu ya kai yana kamo hannun Zainab. 

Ɗagowa ta yi da idanuwanta da suka rine tana kuka sosai. Yadda ta ji zuciyarta ta yi ɗazu shi ta sake ji yanzun ma. 

“Ina Yata Mamdud? Ku kira Yaya Mamdud…”

Zainab ke faɗi, zuciyarta na ci gaba da dokawa, dukkan su suna nan, tasan lafiyar su ƙalau. Amma abinda take ji tasan wani abin ya sake faruwa da su. 

Tana jin ƙaunar da take musu ne yasa take ji a jikinta in suna cikin matsala mai girma. Magana Labeeb zai yi ya ji wayarshi na zuuu a cikin aljihunshi. 

Sa’adda ya fiddo ta missed calls 44. Gabanshi ya faɗi, ya buɗe ya duba, Ateefa ce take ta kiran shi. Sai na baƙuwar lamba guda ɗaya. 

Zai kira Ateefa aka sake kiran shi da baƙuwar lambar. Ɗagawa ya yi ya kara a kunnenshi. 

“Assalamu alaikum. Ka zo asibitin Harmony. Mun ga lambarka ne a wayar wanda ya samu hatsarin. Ba zamu iya kiranka da wayar ba saboda ta samu matsala. Kuyi sauri don Allah…”

Kasa amsawa Labeeb ya yi, da ƙyar ya iya sauke wayar daga kunnen shi. Ba zai iya ɗaukar wani rashin ba. A zuciyarshi ya rasa Mamdud ya sani. Amma sanin yana raye ya rage wani abin. 

Yanzun kam, tunanin…

“Yaya menene?”

Zainab ta katse mishi tunanin shi, ya san Mamdud ne ya samu hatsari, don ‘yan gidan su kaɗai ke da lambar da aka kira shi da ita. 

“Mamdud ne… Yana harmony…”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Zainab ta faɗi tana jin kamar su kaɗai duniya tai wa zafi haka. Miƙewa suka yi su dukkansu. 

“Yau ƙaddara ta juyo kanmu…”

Anees ya faɗi yana goge fuskarshi. Tare suka fito daga ɗakin su dukkan su, basu damu da mutanen da ke kallon su ba suka fice daga gidan. 

Hango su Dawud ya yi yasan ba lafiya ba, ya taso daga inda suke zaune suna karɓar gaisuwa. 

“Lafiya?”

Ya buƙata, Zainab na kuka ta girgiza mishi kai. 

“Yaya Mamdud…”

“Ya Rabb…”

Dawud ya faɗi, har lokacin Mukullin motar Labeeb na hannun shi. Kallon su yayi su duka bai ga mai nutsuwar tuƙi ba. 

“Mu je… Wanne asibiti ne?”

Ya buƙata. Labeeb ya faɗa mishi, motar Labeeb ɗin suka nufa suka shiga. Dawud ya ja motar zuwa Harmony. Yana jin shirun su har ranshi.

**** 

A hargitse suka shiga Harmony. Cikin su babu wanda yake iya cewa komai. Dawud ne yai wa ɗaya daga cikin ma’aikatan magana aka faɗa mishi ɗakin da Mamdud ɗin yake. 

Suka nufi hanyar, suna zuwa gaba ɗayansu suka nufi ƙofar, Likitan ya fito, ganin su har su biyar ya sa shi janyo ƙofar yana dakatar da su. 

“Ina ‘yan uwanshi?”

“Mu dukkanmu.”

Anees ya bashi amsa, Asad na karɓewa da faɗin, 

“Ya yake? Za mu iya shiga?”

Sauke numfashi Likitan ya yi, da Dawud ne kawai ya fahimci cewar akwai matsala babba. Dawud ya kalla ganin duk ya fisu nutsuwa ya ce 

“Ka biyoni office”

“Abinda duk za ka faɗa mishi dole zamu sani. Ko mu bika office ɗin mu duka. Ko kuma ka faɗa mana anan…”

Zainab ta faɗi da muryarta da ke fita da ƙyar saboda kukan da ta yi. Sosai yake kallon su, yana ganin abinda Zainab ta faɗa a fuskokin su ba tare da sun furta ba. 

Hanyar office ɗin ya nufa suka rufa mishi baya. Cikin su babu wanda ya zauna, duka idanuwa suka zuba mishi cike da tashin hankali. Sai da ya nisa tukunna ya soma bayani a nutse. 

“Ya ji raunuka sosai, ya karye har waje biyu a hannu ɗaya… Sai karaya ɗaya a ƙafarshi… Ba zamu iya tsaida magana akan buguwar da yayi a kanshi ba in ba farkawa yayi ba…”

Girgiza kai Asad yake yana jin sabbin hawaye na tarar mishi cikin idanuwan shi. Zainab kam tunda ya buɗe bakin shi ya soma magana hawaye ke zubar mata. 

Sai dai ta sa bayan hannunta ta goge su. Wani abu ne tsaye a wuyan Labeeb ya ƙi wucewa. Ga ƙirjin shi da ke zafi kamar zai faɗo. Da ƙyar ya buɗe bakin shi ya ce, 

“Babu wani permanent ciwo?”

Idanuwan shi likitan ya sauke cikin na Labeeb cike da alamun tambaya ko zai iya faɗar maganar a gaban su Zainab. 

“Ko meye ka faɗa kawai…suna da haƙƙin sani kamar yafda nake da shi…”

Kai ya ɗan ɗaga wa Labeeb ɗin. 

“Iya yanzun abinda zan iya kira permanent a raunukan daya samu shi ne. Ba zai taɓa samun yara ba…”

“A’a… No… Banda wannan…”

Labeeb yake faɗi yana girgiza kai. Ba zai yiwu ba. Har a ranshi yana da niyyar ɗaukar mataki akan Mamdud. Baisan Ko wanne kala ba, amma ya gama tsara wa zuciyarshi koma ta yaya zai ɗauki mataki. 

Mamdud ya cancanci hukunci mai yawa. Yasan ƙaunar da ke tsakanin shi da Arif. Rasuwar Arif kawai ta ishe shi tashin hankali, zuciyar shi ta kasa yarda cewa wannan ƙaddarar ce za ta samu Mamdud. 

“No… Ka faɗa min wani abu banda wannan… Don Allah kai fixing ɗin wannan… Kowanne ka sa… Ko nawa ne zan biya. Ka faɗi wani abu banda wannan…”

Labeeb yake roƙon likitan. Cike da tausayawa ya kalli Labeeb. 

“Babu abinda za a iya yi akai… Ku yi haƙuri Allah ya bashi lafiya”

Hawayen da ke shirin zubowa daga idanuwan Zainab kansu ji tai sun yi tsaye cik, tare da bugun da zuciyarta take yi. Ta san Mamdud, tasan shi tana zaton fiye da Labeeb. 

Cikin idanuwanta take kallon su shekarun baya.

<< Rayuwarmu 35Rayuwarmu 37 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×