Skip to content
Part 39 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Kanshi yake jin ya mishi nauyi kamar an ɗora mishi ƙaton dutse. Ga idanuwanshi da abubuwan da yake gani suna mishi yawo a cikin su. 

Abubuwan da yake gani tamkar mafarki mai firgicin gaske. Mafarkin da zuciyar shi ta ƙi amincewa da shi balle ya samu damar fahimtar shi a cikin kanshi. 

Mafarki ne da yake jin za a yanke mishi duk wani abu na jikinshi kafin ya bari ya faru. Abubuwa ne da suka girmi tunanin shi. Ya kuma kasa buɗe idanuwanshi balle ya kauce wa faruwar ko ma menene yake gani. 

Tayyab da ke zaune ya kula da yadda Abba ke zabura kamar wanda yake firgita a cikin baccin shi.

“Mami…Mami kin ga abinda yake yi.”

Tayyab ya faɗi a kiɗime, matsowa Mami ta yi ta kalli Abban da yadda yake zabura. 

“Ka yi addu’a ka tofa mishi…”

Kai Tayyab ya ɗaga mata yana soma karanto duk wani abu da ya zo mishi yana tofa wa Abban da cikin idanuwan shi yake ganin rayuwa mai firgicin gaske. 

Cikin idanuwanshi yake ganin yadda ya sa hannu ya hankaɗe Aisha da tsohon ciki a jikinta. Miƙewa ya yi gaba ɗaya tare buɗe idanuwanshi da kiran,

“Aisha!!!”

Da ƙarfin gaske. Kallon shi su Tayyab kawai suke yi, yadda yake kallon ɗakin yana son fahimtar abinda yake faruwa da shi haka. Yadda duk fankar da ke ɗakin bata hana shi zufa ba. 

“Aisha!”

Ya sake kira wannan karon a hankali yana duba hannayenshi kafin ya fisge ƙarin ruwan dake jikinshi yana girgiza kai. 

“Aisha…!”

Ya sake kira yana ɗagowa ya tsaida idanuwanshi akan Tayyab. Abubuwan da ya dinga gani suna dawo mishi da sauri da sauri. Matsowa ya yi sosai ya sakko da ƙafafuwan shi daga kan gadon. 

Ko ina na jikinshi ɓari yake, hannuwanshi ya ɗaga yana nufar fuskar Tayyab da su. A zuciyarshi yake roƙon Allah yasa wannan shi ne farkon mafarkin shi. Allah yasa yana kai hannunshi kan fuskar Tayyab zai koma ɗan yaron daya sani. 

Yaron shi kafin faruwar mugun abin da ke mishi tsaye cikin zuciya yana tattakawa da yanayin da ke barazana da ɗaukewar numfashin shi. 

A tsorace Tayyab yake kallon shi. Zuciyarshi na mishi rawa tana ganin kamar yaudara ce abinda idanuwanshi suke gani a fuskar Abbansu. 

Yanayi ne da zuciyarshi ta daɗe da haƙura da sake gani. Ba zai yiwu a ce shi yake gani ba yanzun. Ƙaunarshi a idanuwan Abba. Shaƙuwar da ke tsakanin su. 

Hannu Abba ya saukar kan fuskar Tayyab yana jin yanayin girmanta, yana jin yanayin ɗanshi a cikin hannuwanshi zuwa zuciyarshi. A hankali yake girgiza kanshi yana son Tayyab ya koma yaron da ya sani. 

Ko shekarun da yake da tabbacin za su tarwatsa zuciyar shi su zamana sun faru. Hannuwanshi rawa suke a fuskar Tayyab da dukkan jikinshi. 

“Ta..ta.. Tayyab..”

Ya faɗi, muryarshi na rawa. Wani irin dokawa zuciyar Tayyab take, dokawa ce ta tashin hankali, dokawa ce mai cike da tsoro da firgici. 

Hannu Tayyab yake so ya kai kan ƙiirjinshi kar bugun da zuciyar shi take yi ya ja yanayin da yake gani a fuskar Abba ya ɓace. 

“Tayyab…”

Abba ya sake kira wannan karon da ɗan ƙarfi-ƙarfi cikin muryar tashi, abinda ke tsaye a wuyan Tayyab yake so ya haɗiye, ya ɗan juya fuskar shi dake cikin hannu Abba ya kalli Mami ta tabbatar mishi da gaske ne abinda yake gani a fuskar Abban. 

Cikin ƙarfin hali da sanyin jiki Tayyab ya ɗago da hannuwanshi ya ɗora su kan na Abba da ke fuskarshi. 

“Ya Allah!”

Ya furta yana lumshe idanuwanshi. Kewar mahaifin shi da ya binne wata kan wata na tasowa gaba ɗaya tana sa numfashin shi yin sama.

Tayyab bayajin bayan ƙaunar Allah da Manzon shi an halicci wata ƙauna mai girman ta ‘ya’ya tsakanin su da iyayen su. Ƙauna ce da bata da farko ba ta da ƙarshe. 

Ƙauna ce da ba ta da waje, ƙauna ce da take yawo sama da ko ina na jikinka. Da sauri-sauri Tayyab ke fitar da numfashi kamar wanda ya sha gudu na tsawon lokaci ya samu wajen da zai ɗan huta na lokaci ƙanƙani. 

Magana yake son yi, zuciyarshi ta hana. Zuciyarshi na tsoro kar maganar ta kori abinda yake faruwa. Cikin idanuwa yake kallon Abba da nashi idanuwan ke cike da tambayoyi kala-kala. 

“Mafarki nake… Mafarki nake Tayyab… Wani ya tasheni don Allah.”

Abba ya faɗi yana zame hannuwanshi daga fuskar Tayyab da yake kallon abin yana jin kamar hannun Abba ya bar fuskarshi da wani ɓangare na jikinshi. Dafe kai Abba yayi yana girgiza shi. 

Ya rasa ko me yasa wani ba zai tashe shi daga wannan rikitaccen mafarkin rayuwar da yake yi ba. Kamar Dawud yasan abinda yake faruwa ya turo ɗakin ya shigo da sallama. 

Sallamar da tasa Abba ɗagowa da kanshi yana sauke idanuwanshi kan fuskar Dawud da wani yanayi da ya sa numfashin Dawud tsayawa na wasu ‘yan daƙiƙu kafin ya ci gaba da zuwa mishi yadda ya kamata. 

Runtsa idanuwanshi yayi ya buɗe, yanayin da ke fuskar Abba na mishi gizo tun Ummi na raye kafin ya gama haƙura da shi gaba ɗaya. Me yasa abin zai dawo mishi yanzun. 

Tura ƙofar da ya shigo yayi yana tsayawa a jikinta. Yana kallon yadda Abba ya sauko daga kan gadon gaba ɗaya yana nufo shi. Ja da baya Dawud yake har ya matse jikinshi da ƙofar ɗakin. 

Ya ɗan juya a firgice kafin ya sake juyowa yana kallo da gaske Abba ne ya nufo shi da yanayin nan. Runtsa idanuwa Dawud ya yi. Abinda yake faruwa ya ishe shi, ba sai abinda ya jima da haƙura da shi ya dawo yana mishi gizo ba. 

Tsaye Abba ya yi gab da Dawud yana kallon yadda ya haɗe jikinshi da ƙyauren ɗakin ya runtse idanuwan shi. Bai ga laifin Dawud ba, shi kanshi tsoron kanshi yake, tsoron a ce abubuwan da ke mishi yawo sun faru yake yi. 

A hankali Dawud ya buɗe idanuwanshi ya sauke su kan Abba da ke tsaye gab da shi yana kallon shi da wani yanayi da ya kasa fassarawa.

Hannu Abba yakai zai taɓa fuskar Dawud ɗin, ya janye yana matsawa gefe da sauri tare da ɗago hannun shi kamar yana so ya kare kanshi daga Abban. 

“A’a… Don Allah ka barni. Abubuwa sun min yawa a halin da nake ciki… Karka ƙara min wani sabo…”

Mami kam zaune take tana kallon su kamar ba ta ɗakin. Iko da girman hanyoyin saukar rahmar Allah take kallo, imaninta na ƙaruwa. 

Sosai Abba ya girgiza kanshi, ko dai ya maƙale a duniyar mafarki ko abinda yake tsoro ne ya faru, don tunanin shi iya inda ya hankaɗe Aisha ya tsaya mishi. Kuma su Dawud basu

yi wannan girman ba. 

“Ina Aisha?”

Ya tambaya zuciyarshi cike da tsoron amsar da zai samu. Kallon shi Dawud yayi kamar ya samu taɓin hankali kafin ya kwashe da dariyar da ko sautinta ka ji kasan bata lafiya bace ba. 

Sosai Dawud yake dariya har da dafa bango. Daya juyo ya kalli Abba sai ya ci gaba da wata dariyar. 

“Tambayar ka na yi Dawud ka tsaya kana ta min dariya kamar wanda ya samu matsala.”

Da sauri Dawud ya ƙarasa ya dafa kafaɗar Tayyab da ke zaune kamar an dasa shi. Yana dariya yake faɗin, 

“Tayyab ka ji…ni ne na samu matsala. Wai ina Ummi… Ummi yake tambaya, Mami kuma ni ne mai matsala…”

Dawud ya ƙarasa maganar yana tsayar da kallon shi kan Abba da wani yanayi da ba zai fassaru ba. Bayan duk abinda yai musu, duk abinda ya faru. Baisan me Abba yake nema da su ba kuma. 

Da zai yi kamari baisan inda ummi take ba. Kamar ba tare da shi suka rufe Ummi ba. Don baya tare da su ummi ta rasu baya nufin zai ce ya manta inda take. 

Kallon Abba yake ya ga da gaske yake nufin tambayar da ya yi musu ko wasa yake yi. 

“Don Allah ku min magana… Ina Aisha?”

Abba ya sake faɗi muryarshi na rawa wannan karon, yana ɗago hannuwanshi da ya sa ya hankaɗe Aisha da su yana kallo. Me zatai mishi a rayuwar shi dazai mata wannan abin da tsohon ciki a jikin ta. 

So yake yaji inda take, ya ganta, ta faɗa mishi me ya faru da su haka, ta faɗa mishi wani abu bai sameta ba da yanayin faɗuwar da ta yi. Ta tashe shi daga mafarkin nan da yake yi mai cike da ruɗani. 

‘Ya’yan shi ba su yi wannan girman ba. Baisan sa’adda suka yi wannan girman ba. Dawud ɗinshi ko shekara sha bakwai bai cika ba, balle Tayyab.

“Tana makwancinta… Tana kabarinta a kwance… Tuni kake so nai maka ko me?”

Dawud ya faɗi muryarshi can ƙasa da yanayin da yake ji a zuciyarshi. Wata shaƙuwa Abba ya ji yayi. Kanshi ya soma jujjuya mishi. Babu shiri ya lalubi bango ya zauna. 

Runtse idanuwanshi yayi maganganun Dawud na ƙara wa tunanin shi gudu, yanzun yake ganin missing parts ɗin. Yanzun komai da ya faru yake dawo mishi dalla-dalla ɓangare-ɓangare. 

Hajiya Beeba. Hajiya Beeba da ta zama tushen komai. Sai dai ya kasa gane abinda ya shiga kanshi ya aikata abinda ya aikata ɗin. Yana jin yadda bugun zuciyarshi yake rage ƙarfi.

Runtse idanuwanshi ya yi yana tsaida tunanin shi kan rasuwar Aisha. Jikinshi na amsar saƙo na daban. Saƙo mai wahalar ɗauka a wajenshi. Buɗe idanuwanshi yayi yana kokawa da numfashin shi. 

Miƙewa tsaye yayi. Aisha ta rasu! Aisha matarshi ta rasu!! Aisha rayuwarshi babu ita!!! Wani irin haske ya gilma ta cikin idanuwanshi kafin ya yanke jiki ya faɗi. 

Da gudu Tayyab ya miƙe yayo kanshi ya ɗago shi jikinshi. Mami ta ɗauko ruwan da ke cikin roba tana buɗewa. Tsaye Dawud ya yi yana kallon su suna shafa wa Abban ruwa. 

Baisan me ya kamata ya yi ba. Ya kasa fahimtar komai. Ya kuma kasa yarda da abinda yake faruwa a gaban idanuwanshi. Yadda Abba yake nuna kamar yanzun ya san da mutuwar ummi. 

Bayan Mintina Sha Biyar 

Yana kallon yadda su Tayyab ke ƙoƙarin tashin Abba har lokacin bai ko motsa ba. Ko da Abba yai wata ajiyar zuciya yana miƙewa zaune daga jikin Tayyab Dawud bai motsa daga inda yake ba. 

Kallon su Abba yake. Yanzun kam ba mutuwar Aisha bace kawai take mishi yawo har da ta Sajda. Jikinshi ko ina ɓari yake. 

“Sajda…Sajda…”

Yake kiran sunanta kamar hakan zai dawo mishi da ‘yarshi da ya fi ƙauna duk a cikinsu. Zuciyarshi ke tsagewa, zafin na yi wa numfashin shi barazana. 

Ba zai taɓa iya misalta abinda yake ji a yanzun ba. Yanayi ne da ba zai faɗu ba. Yanayi ne da wanda ya taɓa shiga irin ruɗanin da ya shiga ne kawai zai gane hakan. 

Aisha ta rasu, babu abinda yake dawo mishi sai watannin su na ƙarshe. Watannin da ya ɗauka ba ya mata komai sai wulaƙanci. Bayan shekarun da ta bashi na biyayya da ƙaunarta. 

Bayan dukkan farin cikin da Aisha ta bashi a rayuwarshi, wankan ta na ƙarshe ma bai samu ba. Ba shi yai mata shi ba. Ba a cikin gidansu da suka gina tare tun ba shi da komai ta rasu ba. 

Ba a kusa da shi ba, bankwanan ta na ƙarshe da shi wulaƙanci ne da yake jin yana neman waje a cikin jikinshi yana yi mishi tambari da har mutuwarshi ba zai mantu ba. 

Baya son yin da na sani, baya son yin nadama saboda bai cancanci hakan ba. Ciwon rashin Aisha da na Sajda da yake ji sun mishi kaɗan. Halin da yake ciki yayi kaɗan da tarin abubuwan da ya aikata. 

Akwai hutu a cikin mutuwa, da sai ya ce mutuwarshi a yanzun ta fi mishi daga idanuwa ya haɗa su da na ‘ya’yan shi. Me zai ce musu? Wane bayani zai yi? Ta ina zai fara? 

Zai tuna kamar yanzun abin ya faru zuwan Dawud da ya faɗa mishi an yi wa Aisha tiyata, kamar yadda zai tuna Khateeb, yaron da baisan menene mahaifi a tsawon rayuwarshi ba. 

Ƙasa Abba ya dafa yana miƙewa, kanshi a ƙasa, yana kokawa da numfashin shi, Tayyab ne yai ƙoƙarin kama hannun shi ganin yadda yake shirin sake faɗuwa. 

Matsawa ya yi da sauri, bai cancanci damuwa ko kulawa daga gare su ba. Zuciyarshi tsaye take kan abu ɗaya a yanzun. Da ƙyar ya nufi ƙofa yana shirin buɗewa, Tayyab da ya ƙaraso ya rigashi kai hannu kan handle ɗin ƙofar. 

“Ina za ka je? Baka ga yanayin da kake ciki ba? Yaya kai mishi magana…”

Tayyab ya ƙarasa maganar yana kallon Dawud. 

“Gida zanje…”

Abba ya amsa shi har lokacin ya ƙi ɗago kanshi don ba zai iya haɗa idanuwa da su ba. Dawud bai ce komai ba, sai takawa yayi ya ƙarasa inda Mami take tsugunne ya sa hannuwanshi ya ɗago da ita. 

“Ki kula da kanki da Zulfa… Bari in kaishi gida in dawo.”

Kai kawai Mami ta iya ɗaga mishi, baisan me yasa yake son yi wa Abban abinda ya ce yana so ba. Ƙila halin da ya ga ya shiga ne. Koma dai menene gidan da Abba yake son zuwa zai kai shi. 

Ƙarasowa ya yi ya kama hannun Abban, sannan ya buɗe ƙofar yana janshi suka fice tare. Ɗan dafe kai Tayyab ya yi yana binsu a baya. Har suka fice daga asibitin suka nufi motar Dawud ɗin. 

Tayyab ya buɗe gaban motar, Abba ya shiga, ya zagaya mazaunin driver don mukullin na hannun shi. Dawud bayan motar ya buɗe ya shiga. 

Ya rasa inda ya kamata ya tsayar da tunanin shi. Yana jin Tayyab ya kunna motar ya ja su duka fita daga asibitin. 

******

Suna ƙarasawa Tayyab yai parking suka fito su ukun suka nufi ɓangaren su. Abba ne a gaba saboda saurin da yake yi. Ji yake komai na duniyar ya haɗe mishi waje ɗaya. 

Da sauri ya taka ƙofar gidan yana tura ƙofar babu ko sallama, don itace ƙarshen abinda ke zuciyarshi a yanzun. Kamar ta san ita ya zo wa gidan sai gata ta fito. Tsaye yayi yana kallonta. 

Inda za a ajiye mishi dorinar ruwa kusa da ita, tsaf zai ga ta fi mishi kyau sau goma akan Hajiya Beeba. Akan matar nan da take mishi wani murmushi, haƙoranta na zuwa cikin fuskarshi kamar na kada. 

Wata irin tsana marar misaltuwa ce ta cika mishi zuciya. Tsanar da bai taɓa sanin an halitta wa ɗan Adam irin ta ba. Ita yake ji akan Hajiya Beeba a yanzun. 

Ƙarasowa ta yi tana wata rangwaɗa ta zo ta dora hannunta kan kafaɗarshi ba tare da ta damu da su Dawud da Tayyab da suke wajen ba. 

“Ina ka je haka? Na dawo na samu an yi amai a ɗakin nan sai da na kira aka gyara. Ina ta neman…”

Ba ta ƙarasa ba, kalaman suka yi tsaye a maƙoshinta saboda wani irin mari da Abba ya ɗauke ta da shi, marin da Hajiya Beeba za ta rantse sai da walƙiya ta gifta ta cikin idanuwanta. 

Wani gishiri-gishiri take ji a cikin bakinta da bata san daga inda yake fitowa ba. Kafin ta gama mamakin da take ya sake ɗauke ta da wani marin da sai da ta durƙushe. 

Kallon juna Dawud da Tayyab suke kafin su maida hankalin su kan Abba da Hajiya Beeba, fuskokin su ɗauke da mamaki. 

Ita kanta Hajiya Beeba sa’adda ta ɗago mamakin ne ƙarara a fuskarta

“Alhaji Auw…”

“Idan bakinki ya furta sunana sai na cire miki haƙora wallahi! Annoba… Baƙar ƙaddara… Munafuka da ba za ta gama da duniya lafiya ba!”

Ware idanuwa Hajiya Beeba ta yi tana kallonshi tana mamakin abinda yake faruwa. Hannu Abba ya ɗaga yana nuna mata su Dawud da ke tsaye. 

“Kalle su… Ki kalli girman da suka yi… Ki kalli shekarun da kika yi min asara tare da ‘ya’yana!”

Ya ƙarasa yana kai mata gabza sai da ta faɗi ƙasa, ƙafarshi ya sa ya taka mata ciki tai wata irin ƙara. 

“Ki kalli abinda kika ja min… Matata ta mutu kamar ba ta da kowa…”

Yai maganar yana harbata saida ta juya. 

“Bansan ya suka yi rayuwa babu Umminsu babu ni ba…”

Abba ke faɗi yana tsugunnawa ya shaƙo rigar Hajiya Beeba da ke zunduma ihu tana neman taimako ya sa ɗayan hannun shi yana gabza wa bakinta duka har sai da haƙorinta yai tsalle ya fita, jini na wanke bakin. 

“Kin tarwatsa rayuwarmu, kin min sanadin komai… Duk mazan da ke duniyar nan me yasa ni zan zama zaɓinki! Me ya sa?!”

Abba ya tambaya cikin hargowa yana jijjiga Hajiya Beeba da ta gama laushi a hannunshi. Ganin yadda ya shaƙe mata wuya yana shirin kasheta yasa Tayyab rugowa yana riƙe hannunshi

“Za ka kasheta…”

Ƙara shaƙeta Abba ya yi gam, sai tari take ko ihu ta kasa yi. 

“Gara in kasheta in ƙare rayuwata a gidan yari… Zamanta a duniya ba zai ƙari mutane da komai ba banda bala’i…”

Ganin da gasken kasheta Abba yake son yi ya sa Dawud ƙarasowa ya taimaka wa Tayyab, da ƙyar suka ɓamɓare Hajiya Beeba daga hannun Abba, faɗuwa ta yi ƙasa tana wani wahaltaccen tari. 

Ba dukan da Abba yai mata ba ne babban tashin hankalinta. Maganganun malam ne suke dawo mata. 

‘Wannan maganin muddin ya shiga cikin shi sai abinda kika ce. Amma yana da hatsarin gaske. Don duk ranar da ya karye komai zai iya faruwa da ke.’

Girgiza kai take tana wani irin kuka. 

“Asirin nan bai karye ba…babu yadda za a yi ya karye!”

Ta Faɗi cikin ihu. Ƙwacewa Abba ya yi daga hannun su Dawud yana yin kan Hajiya Beeba da take jan jiki tana faɗin, 

“Na shiga uku… Wayyo Allah na… Wallahi kasheni zai yi in kuka barshi…”

Riƙe shi suka yi dam. 

“Na sake ki saki uku!!! Wallahi in baki fita daga gidan nan ba sai na kashe ki… Tsinanniya… Annoba! A gaban Allah zamu tsaya yai mana hisabi ni da ke da Aisha!”

Abba yake faɗi zuciyarshi kamar za ta faɗo ta fito daga ƙirjinshi saboda ciwon da take mishi. Kamar zai mutu haka yake ji da ganin Hajiya Beeba. 

Tunanin sun haɗa gado da ita kawai na shirin sake sashi sabon amai, ƙwacewa yake ƙoƙarin yi daga hannun su Dawud. 

“Ba dukanta zan yi ba…ku sake ni.”

Sakin shi ɗin suka yi. Da sauri ya nufi ɓangaren su, dawowa yayi da kayanta a hannunshi ya watsa mata saman jiki, ya sake komawa haka ya dinga ɗibo kaya yana fitowa da su har da na shafawa kamar wanda ya samu taɓin hankali. 

Sai da ya gama fito da komai nata. 

“Ki bar min gida! Ki bar min rayuwa! Kin gama lalata abinda za ki lalata… Wallahi… Wallahi kusa kusa da ni kika ƙara nufowa sai na kashe ki Beeba!”

Ya faɗi yana juyawa tare da komawa ɗakinshi, suna jin doko ƙofar da ya yi da ƙarfi. Hannun Dawud Tayyab ya ja suka nufi nasu ɓangaren suna barin Hajiya Beeba nan cikin falon. 

Motsin da ta ji yasa ta miƙewa da sauri, ko Auwal ne ya sake fitowa. Ta gani cikin idanuwanshi. Ta gani da gaske yake yi kashetan zai yi in ya fito yaganta. 

Kamar Mahaukaciya ta tattara iya abinda za ta iya ɗauka ta fita ta tura cikin motarta ta shiga. A gigice ta figi motar ta fice daga gidan. 

***** 

“Ka ce min abinda ya faru a falo ba mafarki nake ba.”

Tayyab ya faɗi yana kawo fuskarshi dai-dai ta Dawud. Wata irin dariya Dawud ya yi, mamakin da yake bai sake shi ba. 

“Da gaske ne Tayyab… Da gaske ya kore ta.”

Dawud yake faɗi yana son tabbatar wa kanshi da Tayyab abinda ya faru ɗin. Hugging ɗinshi Tayyab ya yi, Dawud ya ture shi suna dariya gaba ɗayansu. 

“Alhamdulillah… Kai… Wallahi na kasa yarda…”

Tayyab ya faɗi farin ciki fal a muryarshi. 

“Mu je mu faɗa wa Mami…”

Cewar Tayyab. Murmushi Dawud ya yi, yana jin shi har zuciyarshi, abinda ya kwana biyu bai yi ba. Ƙofa ya nufa

“Yaya ko kai za ka je… Kar mu barshi shi kaɗai.”

Girgiza mishi kai Dawud ya yi. Ya ce, 

“Baida wata matsala… Zo mu tafi.”

Dawud na jin gaskiyar maganar da ya faɗa tana zauna mishi. Bai sake yarda da ita ba sai da suka fito falo basu ga Hajiya Beeba ba. Suka ƙarasa waje babu motarta. 

Dariya suke har suka shiga mota, dariya suke har suka hau hanyar asibiti. Cikin shekaru masu yawa. Abu ɗaya ya soma dai-dai ta a rayuwar su. 

Haƙiƙa sun ƙara imani da cewa in ka riƙi Allah, sai dai jinkiri da babu komai sai alkhairi a cikinshi. Allah yai wa bawanshi alƙawarin sauƙi a cikin tsanani. Ba sau ɗaya ba har sau biyu. 

******* 

Ana gama ɗibar jininshi, aka gama faɗa mishi ƙa’idojin abubuwan da zai dinga ci har sati ɗaya ya miƙe. 

“Sai fa ka huta.”

Wata nurse ta faɗa mishi. Da ka ganta ba wata babba bace ba. Ko za ta girmi Zainab da kaɗan ne. Girgiza mata kai yayi. Yana zira ƙafafuwanshi cikin takalman shi. 

A kunyace nurse ɗin ta kalle shi. 

“In ba za ka damu ba ina so mu yi hoto.”

Wani murmushi Labeeb ya yi, ita kuma tata damuwar kenan. Yin hoto da shi, da tasan tarin damuwar da ke tattare da shi, da ta ƙyale shi ya bar ɗakin nan. Ganin yayi shiru yasa kunya ƙara rufeta. 

“Sure… In dai za ki yi hoto da ni haka jigi-jigi”

Dariya ta yi, ta ɗaga camera ɗin wayarta tana musu selfie da Labeeb da ya ware idanuwanshi yana ɗaga girarshi duka biyun. 

“Na gode sosai. Allah ya ƙara ɗaukaka.”

Ta Faɗi, kai kawai ya ɗan ɗaga mata yana saukowa daga kan gadon. Kanshi na ɗan jujjuya mishi. Haka ya lallaɓa ya fita daga ɗakin, yana dafa bango har ya ƙarasa ɗakin da zulfa take. 

Daga ita sai mami, jinin shi ya bi da kallo, yana saukowa da idanuwanshi inda yake shiga jikin Zulfa. Murmushi ya ɗan ƙwace mishi. Yasan jinin dake yawo a jikinta shi ne a jikinshi. 

Sai dai baisan tagwaye bane sai yanzun. Kamar yadda Dawud ya faɗi, sanadin shi Zulfa take kwance a asibitin nan. Sanadin shi take cikin wahalar nan. In sha Allah sanadin shi za ta fita daga cikinta. 

Zai gyara komai a rayuwarta. 

“Sannu Labeeb…”

Mami ta faɗi tana kallon shi. 

“Ke ce da sannu Mami…Allah ya bata lafiya. Dan Allah da ta tashi a kirani… Zan tafi yanzun.”

“In sha Allah…”

Mami ta amsa shi, tana kallon yadda yake dafa bango har ya fice daga ɗakin. Da ƙyar ya lallaɓa ya fita daga cikin asibitin zuwa motarshi. Wata gajiya yake ji kamar ya kwana yana aikin ƙarfi. 

Zama yai cikin mota yana maida numfashi. Wayarshi ya zaro ya kira Ateefa , ringing ɗin farko ta ɗaga. 

“Tee…”

Ya kira yanajin kewarta can ƙasan zuciyarshi. 

“Na’am… me ya sameka na ji muryarka ta yi wani iri?”

Baya gajiya da mamakin yadda take gane ba dai-dai yake ba da yanayin muryarshi. 

“Gajiya ce kawai… sai kewarki.”

“Hmm…”

“Da ina kusa da baki amsamin magana da humming ba… ya jikinki? Ya kuke?”

Sai da ta ɗan yi jim kafin ta amsa shi da, 

“Muna lafiya. jikina ya yi sauƙi.”

“Allah ya ƙaro sauƙi… bazan zo ba sai can da yamma. Na tura su Asad gida su huta… basa samun bacci. Ina wajen Mamdud da sun dawo zan taho… ba matsala aiko?”

“Babu matsalar komai…bacci ma zanyi. Karka zauna da yunwa…”

“In sha Allah. Ki yi bacci mai daɗi… da mafarkina. “

‘Yar dariya ta yi da ya ji har zuciyar shi, ya kwana biyu bai ji dariyarta ba. 

“Sai anjima.”

Ta Faɗi kafin ya ce wani abu ta kashe wayar, da gangan ta yi, tasan baya so a kashe mishi waya cikin kunne. Inda wasu satuka ne da suka wuce rigima zai mata. Yau kam ko ƙarfin jin haushinta baida shi balle na rigima. Wayar ya saka a key ya mayar da ita inda ya ɗauko ta. 

Tukunna ya ja motar yana lallaɓawa ya fita daga asibitin. Sai da ya tsaya ya siya takeway da siya lemuka, wanda zai ci da wanda zai ajiye wa Asad don da wahala su ci wani abin tukunna ya koma Harmony. 

****** 

Labeeb bai fi mintina goma da fita ba Dawud da Tayyab suka shigo ɗakin da sallamar su. Mami ta amsa, Tayyab ne ya ƙarasa inda take yana sumbatarta a goshi. 

“Mami Abba ya saki Hajiya Beeba… Ya mata duka ya watso mata kayanta waje… Ta bar gidan yanzun haka… Saki uku yai mata Mami.”

Tayyab yake faɗa ba tare da ya tsaya ya maida numfashi ba, fuskarshi bayyane da tsantsar farin ciki. Murmushi Mami ta yi tare da yin hamdala. 

“Cikin jikin Zulfa ya fita.”

Mami ta faɗa musu. Da gudu Tayyab ya ƙarasa gefen gadon da Zulfa take yana zaunawa. Ya ranƙwafa ita ma yana sumbatar goshinta. 

“Ya Rabb… Alhamdulillah… Mami kinga juriyan haƙuri ko?”

Tayyab ya faɗi yana kallon Zulfa. Yana so ta tashi ya zama na farko wajen gaya mata Allah ya rabata da ƙaddarar da ke jikinta. Ya faɗa mata zata iya komawa makaranta abinta. 

Hannunshi ya miƙa wa Dawud yana so ya ƙaraso su zauna, su raba farin cikin nan tare, su raba farkon dai-daituwar al’amurran su. 

Dawud bai musu ba ya ƙarasa, Tayyab ya matsa mishi shi ma ya zauna. Abubuwan duk da suke faruwa na mishi wahalar processing. Farin cikin na mishi wuyar ɗauka shi kaɗai. 

Banda auren Yumna ya manta rabon shi da farin ciki mai yawan wannan. Ya kasa sakin jikinshi, gani yake da ya saki jiki komai zai iya faruwa. Wayarshi ya zaro daga aljihun wandon shi. 

Labeeb ya zama mutumin da ya raba wahalarsu, yana tare da su a lokacin rashi da samun su. A ko ina na rayuwar su akwai shi. Dawud na jin duk abinda ya faru tsakaninsu da Zulfa, halaccin da Labeeb yai musu ba zai sa ya ɓoye mishi farin cikin su ba. 

‘An saki Hajiya Beeba. Ta bar gidanmu… Ina asibiti yanzun… Zulfa.. Cikin jikinta ya fita…’

Sai da ya sake karanta text ɗin tukunna ya tura wa labeeb. Ya mayar da wayar cikin aljihunshi da murmushi a fuskarshi yake kallon su Mami. 

Miƙewa ya yi. 

“Ina za ka je?”

“Sallah zan yi in gode wa Allah… Farin cikin ya min yawa Tayyab…”

‘Yar dariya Mami ta yi. 

“Ka je… In ka gode wa Allah zai ƙara maka wani.”

Murmushin ya sake yi, sannan ya fita daga ɗakin, yana jin daɗin yadda yake zuwa mishi babu wata wahala.

***** 

Yana zaune ya tusa Mamdud a gaba yana kallon shi ya ji ƙarar shigowar text a wayarshi, ɗaukowa yayi ya cire key ɗin, yana buɗewa ya ga Dawud ne. 

Idanuwanshi suka yi tsaye kan layi ɗaya:

‘Cikin da ke jikin Zulfa ya fita…’

Ba abinda hakan yake nufi a wajenshi da Zulfa yake dubawa ba. Abinda hakan yake nufi a rayuwar Mamdud yake gani. Kallon Mamdud da ke kwance baisan duniyar da yake ba balle abinda yake faruwa da shi yake yi. 

‘Ni fa in matata bata haihu bayan wata tara ba, bazan jira ba zan ƙaro aure.’

‘Wallahi duk idan na ga almajirai kamar in sa ihu nake ji. Seriously yazan iya bacci sanin yarona na cikin irin halin nan.’

‘Kasan me? In bazan iya kula da yara ba. Bazan taɓa yarda in haife su ba. Ina son zama wanda za su yi alfahari da shi.’

Maganganun Mamdud ne suka dawo ma Labeeb. Duk wannan burin.. Duk wannan ƙaunar tashi akan yara ashe baida rabon ganin su. In zai ce don abinda ya aikata wa Zulfa ne, in labeeb zai ce don zunuban da Mamdud ya aikata ne yake girba ta wannan fannin da yanzun Ateefa ba ta da cikinshi a jikinta. 

Da ba a kawo mishi yaron da aka kawo ba. Don baya jin ɓarnar da Mamdud ya yi ta kai tashi. In ba bayan rabuwar su ba, iya sanin shi Mamdud bai taɓa yi wa kowa ciki ba balle a zubar. 

Shi kam ba zai iya ƙirga yaran da ya zubar ba, ji ya yi zuciyarshi na wata irin rawa cike da tsoro. Idan shi ma iya yaran da aka gama rubuta mishi kenan fa? 

Wanda ya zubda a baya, wanda aka kawo mishi sai na cikin Ateefa da ba shi da tabbas akan shi fa? Jikinshi ne ya kama ɓari. 

“Allah ka yafe min… Allah ka jarabce ni ta wani fannin…”

Labeeb ke faɗi da sauri, yana sa hannuwanshi yana goge zufar da take fito mishi, yana son yara shi ma. Sai ma da ya ji cewar akwai shi a cikin Ateefa tukunna ya san kalar ƙaunar da yake musu. 

Sosai ya ƙara tsorata da al’amarin duniya da yadda komai zai iya sauya maka lokaci ɗaya. Yadda ba ka da iko akan komai na rayuwarka da ta mutanen da suke da kusanci da kai. 

Yasan ko yanzun da cikin Zulfa ya fita, sauƙi ne ta samu ta wani fannin, kuma yasan Dady ba zai janye maganarshi kan ya auri Zulfa ba. Ko ma ya janye shi zai aureta. 

Abinda ya mallaka kaf zai ƙare wajen tabbatar da an kulle mijin duk da Zulfa ta aura yai mata gori don bai sameta a budurwa ba. Ba zai iya ɗaukar wani abu ya sake samun ta ba. 

Kamar yafda yai wa kanshi alƙawari, zai kula da ita, daga yanzun har zuwa ƙarshen rayuwar shi. Baisan iya lokacin da ya ɗauka yana saƙe-saƙe kala-kala ba. 

A nan yai sallar Azahar, ya samu da ƙyar ya tura wa cikin shi abincin da ya siyo, ya sha malt guda biyu. Ya sake zama yana ɓacewa cikin duniyar tunani har akai sallar La’asar. 

Yana shigowa daga masallaci su Asad na zuwa. 

“Yaran nan… Bance sai da yamma nake son ganin ku ba?”

“Anyi Asr fa… Yamma ta yi.”

Asad ya faɗi yana neman waje ya zauna. Sauke numfashi Labeeb ya yi, gardama da su a yanzun babu wata riba. Tunda sun saurare shi ɗazu, ba zai ƙure ikon shi akan su ba. 

“Kun ci abinci?”

Kai Anees ua ɗaga mishi tare da cewa, 

“Har bacci ma mun yi.”

Kai Labeeb ya ɗan ɗaga musu. 

“Ku kula da kanku. Ku kira ni in kuna buƙatar wani abu.”

“Kaima ka kula da kanka.”

Suka faɗi a tare, tukunna Labeeb ya fita daga ɗakin. Sai da ya tsaya kan hanya ya siya duk abinda yasan Ateefa tana so tukunna ya ƙarasa Dialogue. 

A hankali ya tura ɗakin tare da yin sallama. A kwance ya sameta, ta juya bayanta, shiga ya yi cikin ɗakin yana kulle ƙofar. Ya samu waje ya ajiye ledojin tukunna ya hau kan gadon tare da zame takalmanshi yana hawa da ƙafafuwan shi saman gadon. 

Kamo Ateefa ya yi da ta buɗe idanuwanta babu shiri jin yadda Labeeb ɗin ya ɗago da ita gaba ɗaya zuwa jikinshi. Kwanciya ya yi akan gadon sannan ya kwantar da ita kan ƙirjinshi yana gyara musu kwanciyar 

A shagwaɓe Ateefa ta ce, 

“Ka tasheni daga baccina.”

Hannunshi ya sa ya ja mata hanci. Ta ture hannunshi tana yamutsa fuska. 

“Dama kin yi niyyan tashi… Beside Asr ta wuce….in kika tashi ji za ki yi duk ba kya jin daɗin jikin ki…”

Ɗan yatsa Ateefa ta saka tana zagaye ramar da ke cikin idanuwanshi, muryarta cike da damuwa ta ce, 

“Ka rame sosai…”

“Tunanin za ki barni zai sani ramewa fiye da haka…”

“Hmm…”

Hannunshi ta gani, kafin ta janye fuskarta ya matse mata laɓɓa. 

“Da zafi fa…”

Ta faɗi tana murza laɓɓanta. 

“Bana son kina amsa min magana haka… Kin sani kuma.”

“Ba damuwata bace ta sa ka rama El-labeeb…damu…”

Kafin ta ƙarasa ya sa hannu ya rufe mata bakinta. 

“Yau kawai… Iya yau Tee…ki taimaka min mu bar maganar komai banda tamu… Iya yau please…”

Kai ta ɗan ɗaga mishi, ita kanta bata son ƙara mishi damuwa. Kishin shi ne yake mata yawa a lokuta da dama. Tunanin shi da Zulfa na tsaya mata da wani irin ciwo. 

“Na gode Tee… I love you.”

“Na sani…”

Ta amsa shi. Kallonta yake cikin idanuwanta. Yana jiran ya ji ta amsa tana son shi itama. Sai da ta gama mishi yangarta tukunna ta ce, 

“Nima ina sonka…”

Sumbatar goshinta yayi, yana riƙeta a jikinshi sosai. Yana jin wata nutsuwa da kusancinta da shi ne kawai yake bashi. Damuwar da ke ci mishi rai bai wuce ƙaddarar Mamdud ba. Ita kuma bazai iya faɗa mata ba. 

Faɗa mata na nufin sanin komai da bai shirya ba a yanzun. Don haka yai shiru kawai yana shaƙar ƙamshinta da ɗuminta da ke saukar mishi da nutsuwa. 

**** 

Ya kasa zama, ya kuma kasa tsayuwa a cikin ɗakin. Ya rasa abinda yake ji, ko abinda ya kamata ya ji, abinda yake danne da ƙirjinshi shekaru da dama yana furta sakin Hajiya Beeba ya ji ya neme shi ya rasa. 

Mukullanshi ya ɗauka ya duba, hannunshi har kyarma yake da ya ga mukullin tsohon gidansu. Gidan su shi da Aisha. Da sauri ya ɗibi mukullan yana fitowa daga gidan. 

Motar shi ya shiga, kalar gudun da yake, Allah ne kaɗai ya kai shi gidan lafiya. Yai parking ya fito, zuciyarshi kamar za ta bar ƙirjinshi saboda dokawar da take yi. 

Ya sa mukulli ya buɗe gidan. Ya shiga cikin soron yana nufar ƙofar da za ta kaishi tsakar gidan. Ya kama yana turawa, idanuwanshi yake yawo da su a tsakar gidan da ya tara ƙura. 

Sai dai sam abinda idanuwanshi suke gani dabanne. Shi ba ƙurar yake gani ba. Aisha yake gani zaune inda ta saba zama ta yi karatun Ƙur’ani da yammaci. 

Inda ta saba zama ita da yaranta su yi karatu, su yi hidimar su ta yau da kullum, duk inda ya ɗora idanuwanshi cikin gidan baya ganin komai sai Aisha da yaranshi.

Yaran da a yanzun bai da tabbas da sake samun yardar su ballantana ƙaunar su. Kamar an doka mishi wani abu yake jin

‘Ciki ne a jikin Zulfa wata uku Dady… Cikina ne a jikin zulfa…’

Maganganun Labeeb na satikan da suka wuce na dawo mishi da ƙarfin da ke shirin kai gwiwoyin shi ƙasa. Ƙirjinshi ke zafi kamar ana hura mishi wuta a ciki. 

Da ƙyar ya ƙarasa cikin gidan yana jin komai ya mishi tsaye cik. Ta ina zai fara, me yake har ‘yarshi tai cikin banza? Yana wanne aikin ya kasa kula da tarbiyar su dukkan su?

Ƙarasawa ya yi yana rasa ɗakin da ya kamata ya fara shiga, ɗakin su Zulfa da Sajda ya nufa, ya tura ɗakin, wata irin ƙura a ciki da sai da ta saka shi tari ta taso. Sai da ya samu tarin ya lafa mishi tukunna ya ƙarasa shiga ɗakin. 

Katifun yaran yake kallo, da ƙanƙantar su, da girman da Sajda ta yi kafin rasuwarta, da girman Zulfa a yanzun. Da yadda duk ya rasa shekarun da yasan sun fi buƙatarshi a cikinsu fiye da ko yaushe. 

Fitowa ya yi daga ɗakin yana nufar na Aisha. Yana gode wa Allah da Hajiya Beeba ta ce ba zata koma ɗakin ba bayan barin Aisha. Ya ji daɗin yadda ba ta cakuɗa mishi memories ɗin da ke ɗakin da nata ba. 

Hannunshi na ɓari ya tura ɗakin, kujerun su da suka canza launi saboda ƙura yake kallo. Ƙarasa shiga cikin ɗakin ya yi yana kallon wajen da ya hankaɗe Aisha kamar lokacin abin ya faru. 

Yana kallon inda da bakinshi ya furta kalmar da ta datse igiyar auren su. Ta datse ƙauna da yardarsu. Cikin rashin ƙarfin jiki ya nufi bedroom ɗinsu, idanuwanshi ya sauke kan ƙaton hoton Aisha da ke ɗakin. 

Hoton ta kwanaki kaɗan da aurensu, da sauri ya ƙarasa ya sauko da shi yana ajiye shi ƙasa ya tsugunna cikin ƙurar, hannunshi yasa yana goge ƙurar jiki yana son sake ganin fuskarta. 

Har saida ya samu ta fara fitowa ta cikin frame ɗin , kallonta yake da murmushin nan nata manne a fuskarta. 

“Aisha… Aisha…”

Yake faɗi yana shafa hannuwanshi akan hoton yana jin da zai ganta a lahira a yanzun zai yi fatan mutuwa ta riske shi ya je ya nemi gafararta. Aisha mutuniyar kirki, Aisha mace mai kauda kai da haƙuri. 

Hoton ya ɗago da shi yana hadey fuskarshi da ta Aisha wani gunjin kuka na ƙwace mishi. Ba kukan mutuwar Aisha yake ba. Kukan yadda rabuwar su ta kasance yake yi. 

Kukan yadda bata jishi a ƙarshen tafiyarta daga duniya ba. Kukan yadda saƙon addu’arshi ko ɗaya bai risketa ba. Kukan yadda ƙaddarar su ta kasance yake yi. 

“Aisha da wanne ido zan kalle ki? Ta ina zan fara? Aisha mutuwarki hutu ce a gareki ni zan yi wannan shaidar… Ta ina zan sauke haƙƙin ki da na ɗauka?”

Abba ke faɗi yana wani irin kuka tamkar yaro ɗan shekara biyu. Ya rasa iyayenshi, sai dai wannan ɗacin mutuwar daban yake a wajenshi, a gigice ya miƙe yana ƙara sauko wani hoto da suke. 

Ita da shi, Dawud, Tayyab, Zulfa da Sajda tana jaririya, hannu ya sa hawaye na zubar mishi ya goge ƙurar da ke jikin hoton yana kallon su. 

Farin cikin da suke da shi kafin su fito a ɗauki hoton. Abin na mishi yawo kamar lokacin ya faru. 

*

Ta baya ya rungume Aisha da ke tsaye tana ɗaura ɗankwalinta, ta ɗora hannunta kan nashi da ke zagaye da ƙugunta. 

“Abban Sajda in yara suka shigo fa?”

Dariya ya yi. 

“Har na koma Abban Sajda ko?”

Ya tambaya cikin kunnenta, ƙaunarta na mamaye shi. 

“Dole ai, ko bacci ba ka yi, uhm Sajda ta ce sai ka farka. Na tabbata da zai yiwu da ita za ka dinga fita office.”

Dariya ta bashi sosai. Ya sumbaci gefen kuncinta. 

“Ina ƙaunarku ku duka… Wajen Sajda daban yake. Bansan me yasa ba…ƙaunarta kala daban take.”

Kwantar da kanta Aisha ta yi akan ƙirjinshi. Ƙamshin turarukanta na dukan hancin shi. 

“Ance ko cikin ‘ya’ya za ka ji ka fi son wani. Ni dai duka kala ɗaya nake jin su.”

Sake matse ta ya yi a jikinshi. 

“Ki faɗi gaskiya. Ko abu kike ci sai kin fara ba Dawud kike miƙo min.”

Ware idanuwanta ta yi tana juyawa cikin hannunshi suka fuskanci juna. 

“Banda sharri…”

Dariya ya yi, ta kamo hannunshi ɗaya tana ɗorawa a ƙirjinta. Yana jin bugun zuciyarta cikin tafin hannunshi. 

“ƙaunar ka daban take anan. Ban haɗa ta da komai ba. Idanuwanta kai suka fara gani kafin su Dawud…”

Rungumeta yai tsam a jikinshi. 

“Banda bakin musu kan kalaman ki Aisha. Ke ta dabance…”

**** 

Yana jin sautin dariyarta cikin kunnuwanshi kafin ya maye gurbi da sautin kukanta bayan ya datse igiyar auren su. 

Kukan shi ya ji ya tsananta, ajiye hoton yayi a ƙasa yana kifa kanshi akai tare da buɗe sabon shafin kuka. Kukan da ba zai dawo mishi da Aisha ba balle Sajda. 

Kukan da bazai canza abinda ya aikata a idanuwan ‘ya’yan shi ba.

<< Rayuwarmu 38Rayuwarmu 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×