Ɗif ta ɗauke wuta, zubewa ta yi ƙasa, ba ta da sauran ƙarfin ɗaga ko da yatsa ɗaya ne, ihu take son yi amma ba hali, azabar zafin ƙunarta na shiga duk wani ɓargonta.
Dishi-dishi take ganin tsirarun mutanen da ke ƙoƙarin kashe wutar da ke cin gidanta, Chak numfashinta ya tsaya, a hankali idanuwanta suka rufe ba ta ƙara sanin inda kanta yake ba.
Ruwan kumfa aka ɗebo ana watsa wa gidan, amma kamar ana ƙara hura mai wuta, ci take ba ƙaƙƙautawa, sun tabbata ko sun kira Fire Brigade kafin zuwansu Gidan ya mutu murus, don a hakan ma gidan ya ƙone ƙurmus, hatta motarta ta ƙone ba ka ganin komai sai hayaƙi.
Daga gefe suka lura da Beeba, suka ƙarasa gunta a guje.
“A kaita asibiti.”
cewar wani mutumi, haka aka samu a daidaita sahu a ka kaita wani asibiti da ke kusa da gidan, da ƙyar suka amsheta emergency, don sun ga alama ba family ɗinta balle wani kuɗin magunguna kasancewar shi private.
Kwananta biyu a asibitin ba tare da ta san wanda ke kanta ba. Sa’adda ta buɗe idanuwanta, azabar ƙunar da ke fuskarta shi ya fara kaiwa zuciyarta kafin ƙwaƙwalwarta ta ɗauka da tuna abinda ya faru.
Wasu hawaye masu zafi ne suka biyo gefen fuskarta. Musamman da Huzai ta faɗo mata a rai. Bala’in da Malam ya kira mata ne in har asirib ya karye shi ne ta fara gani da gobarar da ta faru.
Babu abinda ya fi ɗaga mata hankali face irin kuɗaɗenta da ke cikin gidan. Tunda ta samu Auwal duk wani kuɗi da take da shi ta adana a gidanta. Kamar jaraba son da take wa Auwal ya hanata bin wasu mazan don haka suma suka watsar da ita.
Bata damu ba, don in ba wajen malam za ta je ba duk abinda take so tana samu. Shi ma wajen malam ɗin da kuɗaɗen Auwal take zuwan shi. Cikinta ya soma ƙara saboda wata irin yunwa da ke addabarta.
Wata Nurse ce ta shigo ɗakin. Ganin ta farfaɗo ne ya sa take tambayarta ina ‘yan uwanta, don kusan kwana biyu kenan ba wanda ya zo nemanta, kuma mutanen da suka kawota ba su sake zuwa ba, kuma yanzu ana buƙatar kuɗin gado da magungunan da aka yi amfani da su don treating ciwukanta, ga kuma ƙafarta ta fara ruwa, ana buƙatar bandages da wasu magungunan don gudun samun infection .
Hawayen ƙunci ke sauka kan kuncin Beeba, sanin cewa duk wata kadara da ta mallaka tana cikin gidan nan, duk wani arziƙinta na ciki, komai ɗinta ya ƙone tare da gidan nan, ba ta da wani sauran Gata, ba ta da dangi, ba ta da kowa, shes on her own. Huzai ce kawai kuma ita ma ba ta nan. Sai Auwal da tasan a yanzun ko hauka yake tsanar da ta gani cikin idanuwansa ba zai barta nufar shi ba.
Nurse ta ce,
“Hajiya ki yi magana, ki kawo lambar wani a kirashi a sanar da shi halin da kike ciki, mu kuma a biya mu haƙƙinmu.
Beeba na kuka ta sanar mata da cewa bata da kowa, Nurse ta ce,
“Taɓɗijam, lallai ba abinda za mu sake yi miki, kiyi gaggawar barin asibitin nan tun kafin a wulaƙanta ki.”
Beeba ta kalli ƙafafuwanta da ke fidda ruwa ga sauran ƙunar da ke hannunta, ta yadda za ta taka ƙafar ma tashin hankali ne balle nurse ɗin nan da ke mata kallon wulaƙanci babu tausayawa tai tunanin za ta iya fita daga asibitin.
Murya na rawa Beeba ta ce,
“Ki taimake ni, banda kowa banda komai.”
Sai da ta kalli Beeba tsaf ta ga bleaching ɗin da ke fuskarta da rashin annuri. Ita kama da karuwai ma tai mata. Tsaki ta ja, wata tsawa Nurse ɗin ta daka mata, ta ce
“Ki san inda dare ya miki tun wuri, kafin na sa securities su wurgar da ke a incinerator, daga ganinki ba ta ƙwarai bace, irin ku ne ake taimaka kuke saka wa mutum da sharri, treating ɗinki da muka yi na kwana biyu Allah bamu lada, kar ki bari in dawo in sameki a ɗakin nan.”
Fuuuu ta fice ta bar Beeba zaune kan Gado tana matse ƙwalla.
“Ina zan dosa? Wa nake da shi? Na shiga uku. Ashe rayuwa zata min irin wanan juyin?”
Beeba ta faɗa a bayyane, ba ta da kowa, Huzai da take taƙama da ita ta mutu, kuma ta tabbata in ta sake nuna kanta a gaban Auwal sai ya harbeta, ko ta koma Ningi? Ƙauyensu kenan da ta watsar shekaru sunfi 20, in taje ko wa zai kalleta? Nadama ce ke shigarta a hankali.
Ba ta gama tunaninta ba ta ji an banko ƙofa, Nurse ce da securities guda biyu, kafin Beeba ta gane me suka zo yi ta ji sun damƙeta, ba su direta ko ina ba sai can nesa da gate ɗin asibitin suka yasar da ita kamar wata bola, ga rana ga yunwa ga azabar da ƙunarta ke mata. Wani irin kuka ta fashe da shi.
****
Zaune take cikin ɗakin. Ta rasa me take ji, zafi-zafi ko sanyi-sanyi. Zuciyarta dokawa take kamar za ta fito daga ƙirjinta, sai dai yau babu komawa baya.
In akwai abinda ta gaji da shi bai wuce ganin kallon da ke giftawa tsakanin Labeeb da su Tayyab ba. In akwai abinda yake ci mata zuciya dai-dai da ƙaddarar da ta faru da ita bai wuce ganin rama da damuwar dake idanuwan Labeeb ba.
Ji take kamar ta karɓar mishi duka, za ta iya jure komai in har akwai farin ciki a fuskarshi. Numfashi ta ja tana fitarwa a hankali. Tayyab ne ya shigo.
“Taso ga su can… Na kira yaya ma ya taho.”
Zuciyarta ta ci gaba da dokawa da ƙarfi fiye da yadda take dokawa kafin ya shigo. Idanuwanta cike da tsoro take kallon shi. Ƙarasawa ya yi cikin ɗakin ya tsugunna a gabanta.
“Ko menene za ki yi… Zan iya ce musu kin fasa.”
Da sauri ta girgiza masa kai.
“Kin kuwa ga yadda fuskarki take? Bana so… Bana so ko kaɗan.”
Tayyab ya ƙarasa maganar yana kallonta. Baya son tsoron da yake gani shimfiɗe a fuskarta. Miƙewa ta yi har lokacin ta kasa ce mishi komai, ta ɗauko hijabinta ta saka. A bakin ƙofa suka ci karo da Mami.
“Mami ki taho mu je…”
Murmushi ta ɗan yi.
“Taronku ne na family.”
Sosai Tayyab ya haɗe fuska.
“Ke mece ce Mami? Kema family ɗinmu ce ai… Ko don Yaya baya nan shi yasa… Dama kin fi sonshi… Kome yake so kina mishi…”
Ganin rigima Tayyab yake son yi mata yasa ta katse shi da faɗin,
“Bari in ɗauko hijabina.”
Jiran Mami suka yi ta ɗauko hijabinta suka fita daga gidan tare. Zulfa bata sake ji wani abu ya ƙulle a cikinta ba sai da ta taka ƙafarta cikin gidan su Labeeb taga Mummy da Dadynsu a zaune.
Hannun Tayyab ta kama tana riƙewa dam, ko yaya take neman ƙwarin gwiwar yin abinda za ta yi ɗin yanzun. Da sallama suka shiga, Mami da Tayyab na gaisawa da su Dady. Sam zulfa ta ji harshenta ya ƙi motsi cikin bakinta saboda nauyin da ya yi.
Suna zama Dawud na shigowa. Kallo ɗaya za kai mishi kasan a hargitse yake don ko sallama bai yi ba, idanuwanshi yake yawatawa cikin ɗakin har sai da ya ga Zulfa tukunna.
Takalmanshi ya cire ya ƙarasa da sauri yana zama kusa da ita, fuskarta yake kallo yana son ganin ko lafiyarta ƙalau, don bai yarda da maganar Tayyab ba. Yasan ƙanwarshi, ba halinta bane neman su da gaggawa haka.
“Ki kalleni Zulfa… Lafiyarki ƙalau ko?”
Idanuwanta ta saka cikin nashi, tana jin hawaye na tarar mata, kafin su zubo kan kuncinta, girgiza mishi kai tayi alamar a’a, wani sabon tsoron na sake cika mata zuciya. Ta ina za ta fara faɗa musu abinda ya faru da ita.
Ta ina za ta fara komawa ranar da take son mantawa har ƙarshen rayuwarta? Tallabar fuskarta ya yi cikin hannunshi, baya son abinda zai sake taɓata ko mene ne.
Wannan karin zai yi yaƙi da shi da duk wani ƙarfi da yake da shi.
“Ina nan zulfa… Ina nan babu abinda zai sake samun ki in sha Allah.”
Kai take ɗaga mishi kawai, ta ɗora hannuwanta kan nashi da ke fuskarta sabbin hawaye na zubar mata. Ba ta son ganin damuwar da ta saka shi a ciki, sai dai ba ta san yadda za ta tsaida hawayenta ba.
Jarood yai sallama yana shigowa. Gaishe da kowa ya yi ya samu waje kusa da Tayyab ya zauna fuskarshi ɗauke da alamun son fahimtar ko me yake faruwa amma ya rasa.
Yanayin shigowar Labeeb ya sa su maida dubansu kanshi, don da gudu ya shigo bai samu tsayawa ba sai tsakiyar falon da takalmanshi a ƙafarshi yana maida numfashi.
“No zulfa… Ba haka muka yi da ke ba…”
Labeeb yake faɗi yana girgiza mata kai.
“Labeeb lafiyarka kuwa?”
Mummy take tambaya, hannu ya ɗan ɗaga mata yana faɗin,
“Ba lafiyata ƙalau ba Mummy… Ku ce mata ba kwa son ji… Ko menene za ta faɗa ba kwa son ji.”
Labeeb ya faɗi idanuwanshi kan Zulfa da kukanta ya sake tsananta. Kallon ya za ki yi min haka yake mata, zuciyarshi cike da fargaba. Bata san yadda komai da ya faru ya gama gajiyar da shi ba.
Yadda komai ya cinye sauran ƙarfin da yake da shi. Ba zai iya jure wani abu ya sake samun shi ba, in yana tunanin rasa Ateefa zai daskarar mishi da zuciya, in wani abu ya sake samun ta zuciyar shi tarwatsewa za ta yi.
Itama Zulfa kallon shi take yi, shi ne komai nata, tun kafin ta yi hankali tasan Labeeb na da muhimmanci a rayuwarta, da ta yi hankali ta gane zuciyarta gaba ɗaya na tare da shi.
Ɓangare mai girma cikin farin cikinta yana wajen shi. Ta jima da sanin ko wa za ta aura har abada ɓangare mai girma na zuciyarta zai zauna tare da Labeeb ne.
Halin da take ciki bai hana zuciyarta matsewa da tunanin zai aureta ba, ko da auren zai faru ne sanadin ƙaddarar da ta same ta. Yanzun haka tunanin hakan ba zai faru ba kamar sake rasa Labeeb ne a zuciyarta a karo na uku.
Sai dai ba zata iya barin shi ya ci gaba da ɗaukar laifin da ba nashi ba, wani kallo Dawud yai mishi mai cike da fassara kala-kala. Kafin Labeeb ya rusa mata ƙwarin gwiwar da take da shi ta buɗe bakinta da faɗin,
“Ba shi bane ba!”
Kamar saukar hadari maganarta ta isa kunnuwan kowa. Sai dai babu wanda ya fahimta. Kowa kallonta yake yana neman ƙarin bayani, hannuwan Dawud ta sauke daga fuskarta tana riƙe su gam cikin nata.
Numfashinta har wani sama-sama yake yi saboda gani take kamar lokacin abin yake faruwa. Za ta iya rantsewa har a jikinta tana jin hannuwan Mamdud. A ko ina nata.
Kuka take kamar za ta mutu, Dawud ya sake riƙeta.
“Zulfa…”
Ya ma rasa abinda zai ce ko abinda ya kamata yai mata ta samu sauƙin koma menene. Kuka take tana faɗin,
“Ba shi bane ba Yaya… Ba shi ya min ciki ba! Fyaɗe aka yi min!”
Ta ƙarasa tana sakin wani kuka da ya fito daga zuciyarta. Iskar da ke ɗakin kanta sai da ta canza launi da girman abinda maganar Zulfa tai musu gaba ɗayansu.
Mummy, Dady, Mami, Jarood, Tayyab dukkan su Labeeb da ke tsaye suke kallo da wani abu a fuskokin su da ya girmi mamaki. Abubuwa ne da cikin su babu wanda ya gama fahimta.
Dawud kam duk wani abu da ke jikinshi ya yi wani irin sanyi. Musamman zuciyarshi. Emotions sun mishi yawa ya rasa wanne ya kamata ya fara ji. Yana ƙaunar Zulfa, ƙaunar da babu shakku ko kokwanto a cikinta.
Sai dai in akwai abinda ya fahimta a yanzun nan da kalamanta shi ne ba zai taɓa sonta da irin son da Labeeb yake mata ba. Ba kuma zai taɓa fahimtar girman ƙauna irin wannan ba.
Ko wuyanshi ya kasa motsawa saboda baisan ta yadda zai haɗa idanuwanshi da na Labeeb ba. Kunya da girmanshi da kuma ƙaunarshi da suka haɗe mishi waje ɗaya sun yi yawa ya iya ɗaukar su a yanzun.
Gefe suka yi, kalaman Zulfa guda biyu na shigarshi da wani irin girma ‘Fyaɗe aka min!’ komai da ke cikin kanshi shiru yayi yana ba wa kalaman wajen zama daram.
Zuciyarshi na dokawa da ƙarfi kafin wani irin ɓacin rai ya cika ta yana zagaye ko ina na jikinshi. Duk wani abu da yake son yi kan abinda ya faru da Zulfa ƙarfin jinin da ke tsakanin su da Labeeb ya hana yana dawo mishi.
Shi ya fara korar shirun da ke ɗakin da faɗin,
“Waye!?”
Can ƙasan maƙoshi hannuwanshi na mishi ƙaiƙayi ya fasa wani abu. Ɓoye kanta Zulfa ta yi a jikin Dawud tana ci gaba da kuka har sama sama numfashinta yake yi.
“Ya… Yaya Mamdud!!!”
Ta faɗi wani kukan na sake ƙwace mata. Miƙewa Dawud ya yi, Tayyab ma miƙewa ya yi. Mummy kam da Dady salati kawai suke yi. Mami ta kasa cewa komai kuma, wani abin in ya fi ƙarfin tunaninka sai ka rasa ta cewa.
Balle Jarood da idanuwa kawai yake binsu da shi. Labeeb har lokacin yana tsaye, abinda yake gudu ne, abinda yake son karewa shi ne yake faruwa a gaban idanuwanshi babu abinda zai iya yi a kai kuma.
Hanyar ƙofa da ya ga Dawud ya nufa ne yasa shi kamo hannunshi yana janyoshi ya dawo da shi baya. Murya a dishe ya ce
“Ina za ka je?”
Numfashi Dawud yake ja yana fitarwa a hankali sam ya kasa ɗaga fuskarshi balle idanuwanshi su yi kuskuren sauka cikin na Labeeb. Muryarshi ɗauke da abinda yake ji ya amsa da faɗin,
“Asibiti…”
“Me za ka yi?”
“Mamdud zan tasa… Bansan ko ta yaya ba amma zan samu hanyar da zan taso shi daga duk inda yake! Sannan zan mishi wani dukan da zai sake mayar da shi! Zan kuma samu wata hanyar in sake tashin shi… Haka zan ci gaba da dukanshi har sai ya zaɓi inda ya fi mishi sauƙi… Duniyar da nake ciki ko inda nake aika shi!”
Dawud ya ƙarasa da ɗaga murya. Girgiza mishi kai Labeeb yake yi, minti ɗaya zuwa biyu yake buƙata ya ɗan samu ko zai yi clearing kanshi ya gane hanyar da zai gyara ɓarnar nan da Zulfa ta yi mishi bai shirya ba.
Kafin ya samu mintinan da yake buƙata cike da ɓacin rai Mummy ta ce
“Me na faɗa maka? Tsintacciyar mage ba ta mage dama… Wanda ka tsamo daga rana zuwa inuwa gashi nan ya turaka tsakiyar rana har wuta ya kunna maka!”
Kallon Mummy Labeeb yake yi da mamaki a fuskarshi, yana sake maida dubanshi kan Dady da fuskarshi ke ɗauke da yarda da abinda Mummy ta faɗa ɗin. Wata dariya ya yi da ta sa su kallon shi.
“Da gaske Mummy? Bakin ki ya buɗe da kalaman nan saboda laifin ya tashi daga kaina ko?”
Ya tambaya yana tsaida idanuwanshi a kanta kafin ya mayar kan fuskar dady, sannan ya mayar da hankalinshi kan Dawud da ke son ƙwace hannunshi daga riƙon da yai mishi.
Hannu labeeb yasa da duk ƙarfin shi ya tura Dawud ɗin yana mayar da shi baya. Cikin hargowa ya ce
“Ku kalli abinda kuke shirin yi! Me yasa kun cika son kanku da yawa ne? Me yasa kuka riƙe kalaman ku a baya? Saboda ni ne?! Ni naku ne bari a rufa min asiri… Bari a ɗora komai akan ƙaddara! Saboda me zai sauya yanzun don an ce Mamdud ne?
Saboda me?! Mummy ki kalleni.. Ki ce min tunda Mamdud ya zo gidan nan baya miki biyayya kamar yanda nake miki! Dawud kalle ni…ba ya baka respect? Ba ya zama da Khateeb kamar ƙanin shi?
Me yake damun ku?”
Kallon su Labeeb yake da wani irin yanayi. Ba don bai tsani abinda Mamdud ya yi ba, sai don ganin yadda suke a shirye da su watsar da zamantakewar shekaru cikin ƙaramin lokaci.
Sai don ganin yadda idanuwansu yake shirin rufewa da duk wani karamci da ya taɓa shiga tsakanin su da Mamdud saboda laifin da yai musu. Sai don ganin yadda akanshi suka fahimta akan Mamdud suka rufe idanuwansu saboda jininsu baya yawo a jikinshi.
Ba duniya bace take ba shi tsoro yanzun. Mutanen cikinta ne suke tsorata shi. Sosai suke ba shi tsoro da halayen su da son kansu da yai yawa. Dawud ya kalla sosai.
“Gudun abinda za ku yi yanzun ya sa na karɓi cikin… Ba kwa tunaninta. Ba kwa tunanin abinda ɗaga maganar zai iya yiwa rayuwarta… Ya riga ya faru Dawud. Ko ajiye maka Mamdud aka yi ka yanka shi ka ƙona gawar ba zai taɓa canza mata komai ba.
Kamar yadda babu abinda ya canza… Zan aureta saboda za a ɗauki gawata kafin in bari wani namiji yai mata gori akan abinda ba ta da laifi akanshi!”
A hankali Dawud ya ɗago idanuwanshi ya sauke su cikin na Labeeb. Kallon Labeeb yake zuciyarshi na karyewa. Baisan wace kalar ƙauna ya cancanta yai mishi ba. Duk wani fushi da son ɗaukar mataki akan Mamdud ya gama ruguza mishi.
“Why? Saboda me zai mana haka? Saboda me zai mata haka? Wane irin so ne wannan El? Wanne irin so kake mata?”
Ɗan ɗaga kafaɗa kawai Labeeb yayi. Ko ɗaya baida amsar tambayoyin Dawud ɗin. Son da yake wa Zulfa baida kalaman da zai dora su a kai. Dalilin da ya sa Mamdud ya yi abinda yai ya girmi duk wani tunani nashi.
Zulfa kanta maganganun Labeeb sun taɓata ta yadda ba za ta taɓa fahimta ba. Hannu ta sa tana goge fuskarta, sai dai hakan bai hana wasu sabbin hawayen fito mata ba. Muryarta a dakushe, fuskarta ɗauke da nisantaccen yanayi ta ce,
“Ba a cikin hankalin shi yake ba… Duk da hakan ba zai taɓa zama excuse ba a wajena. Amma zai canza wani abu a wajenku… Baisan ni bace ba Yaya… Bai sani ba…”
Ta ƙarasa cikin kuka, jikinta ko ina ɓari yake, su dukansu kallonta suke, Labeeb na jin yadda maganganunta ke warware wani abu da baisan yana ɗaure da zuciyarshi ba.
Ya rasa kalar tunanin da ya kamata ya yi. Su Mummy kansu an rasa wanda zai yi magana. Kallon labeeb kawai Dady yake yi yana jinjina wa ƙaunar da yake wa Zulfa.
Wucewa Dawud ya yi ya kamo hannun Zulfa ya ɗago ta, miƙewa ta yi tana binshi inda yake janta har sai da ya zo gaban Labeeb tukunna ya kamo hannun Labeeb ya haɗa da na zulfa da yake riƙe da shi, ya zuba musu idanuwa.
Wani abu yai mishi tsaye a zuciyarshi. Me zai ce wa Labeeb, babu kalar wata godiya da zai mishi, babu kalar karamcin da zai kai rabin nashi. In zai shafe sauran shekarun da yake da su yana wa Labeeb addu’a a duk sujudar da zai yi ba ya jin zai taɓa iya biyanshi karamcin da yai musu.
Muryarshi na rawa ya ce
“I hit you El… Me yasa ba ka faɗa min ba? Kana kallon yadda na tsane a lokacin… Kana kallo…”
Kasa ƙarasawa Dawud ya yi saboda wani abu da ya tokare mishi wuya. Idanuwanshi cike taf da hawaye ya ce,
“Ga ta nan… In dai nine na baka ita… Saboda nasan bazan taɓa sonta kamar yadda kake sonta ba… I just… I just…Ya Rabb…”
Dawud yake faɗi yana kokawa da kalaman da yake son faɗi suna kubce mishi. Sakin hannun Zulfa ya yi da ke cikin na El yana wucewa ya fita daga ɗakin saboda abubuwan da yake ji sun mishi yawa.
Iskar da ke wajen ta mishi kaɗan. Jan hannun Zulfa Labeeb ya yi yana ƙarasawa da su dukkansu gaban Mummy da Dady ya tsugunna, ita ma tsugunnawan ta yi tana kuka.
Kan Labeeb sadde a ƙasa ya ce
“Mummy karku hana ni aurenta… Don Allah karku hana ni…”
Kasa tsaida hawayenta Mummy ta yi, wace ce ita da za ta raba tsakanin wannan ƙaunar da bata san tun lokacin da ta fara ba. Da ƙyar Daddy ya ce
“Labeeb saboda me za mu ce karka aure ta?”
Jinjina kai Labeeb ya yi ya ɗago yana sauke idanuwanshi cikin na Mummy.
“Mamdud… Don Allah karku riƙe shi… Ban ce कर ku hukunta shi ba… Ku hukunta shi kamar yadda za ku yi min…”
Labeeb ya faɗi muryarshi na karyewa. Kai kawai Mummy take ɗaga mishi, har Dady ɗin ma haka. Hannu Tayyab ya sa yana goge hawayen da suka zubo mishi. Zuciyarshi ta yi wani irin nauyi don haka ya kama hanya ya fice daga ɗakin shima.
Jarood gaba ɗaya sun kashe mishi jiki, sun sa shi yin addu’ar Allah ya bashi abokiyar rayuwa da za ta soshi tsakani da Allah haka. Don hakan na da wahalar samu ba kaɗan ba.
“Assalamu alaikum…”
Aka faɗi da ya maida hankalin su zuwa ƙofar gaba ɗayansu. Ware idanuwa Labeeb ya yi cike da mamaki. Taɓe baki Zafira ta yi tana watsa mishi wani kallo kafin ta ƙarasa cikin falon ta samu waje ta zauna.
“Ina wuninku… Kuna mamakin ganina ko?”
Ta buƙata tana ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya. Labeeb yasan amsar tambayar ta na shimfiɗe kan fuskarshi. Sai ya ga bata canza mishi ba, tana nan yadda ya santa shekaru uku da ɗoriya da suka wuce.
Jin kowa ya kasa amsata yasa ta faɗin,
“Well… Abinda ya kawoni ba mai yawa bane ba. Nasan an kawo maka ɗanka. Zan yi aure wannan satin kuma ƙasar za mu bari da mijin da zan aura…”
“What???”
Labeeb ya faɗi yana son ta maimaita abinda kunnuwanshi suka ji don ya tabbatar da ko gaskiya ne.
“Ban yi niyyar kawo maka shi ba… Nai niyyar tafiya da yarona don na san ba ka san da shi ba.. Sai dai ƙaunar da nake mishi na da yawa.
Na san yana buƙatarka a rayuwarshi kamar yafda yake buƙatata. Haushinka ya sa na hana mishi ƙaunarka na shekarun nan… Nasan da cikinshi satin da ka sake ni…”
Fuskarshi Labeeb ya sa cikin hannuwan shi yana maida wani irin numfashi tare da gode wa Allah da ya sa zunubanshi ba su taɓa ɗanshi ba. Da ya sa ya fito ta hanya mai kyau.
“Bazan nema da yawa ba… Ina son duk hutunshi na ƙarshen shekara ya yi tare da ni…”
Da sauri Labeeb ya buɗe fuskarshi yana ɗaga mata kai, hawayen farin ciki na cika mishi idanuwanshi. Murmushi Zafira ta yi tana miƙewa, kati ta zaro cikin jakarta ta miƙa wa Labeeb ɗin.
“Na gode…”
Sai lokacin ya samu faɗin,
“Allah ya tabbatar miki da dukkan alkhairi… Bazan iya janye abinda ya faru tsakanin mu ba… Ki yafe min in har na ɓata miki.”
“Nima haka… Ka yafe mon duk abinda nai maka.”
“Allah ya yafe mana… Ba za ki ganshi ba..”
Girgiza wa Labeeb kai ta yi. Idanuwanta na cika da hawaye.
“Ba ƙaramin ƙarfin zuciya na yi ba da zan barshi…ganin shi zai wargaza min komai…”
Hawaye na zubo wa Mummy ta ce
“Ki zo ki ga ɗanki… Karki bari ɗan ciwon da za ki ji ya hana miki farin cikin da ganinshi zai samar miki. Lokaci baya jiran mu… Ki ga yaron ki.”
Kallon Mummy Labeeb ya yi, yasan me yasa tai maganar da ta yi. Miƙewa ta yi Zafira na binta a baya suka nufi ɓangarenta. Ba su jima ba suka fito, sallama tai musu ta fice.
Labeeb na binta da kallo, ko tashin hankalin fuskantar… Bai ƙarasa tunanin ba ya tashi da gudu yana nufar ƙofa.
“ZaFira!”
Juyowa ta yi tana kallonshi fuskarta ɗauke da alamar tambaya.
“Ya sunanshi?”
Murmushi ta yi.
“El-labeeb… Junior El.”
Kai ya ɗaga mata.
“Na gode … Na gode da komai.”
Murmushi kawai ta yi ta nufi wajen motarta. Dawowa Labeeb ya yi cikin gidan, Mami ta miƙe tana kama hannun zulfa. Murya a sanyaye ta ce
“Bari mu tafi…”
“Allah ya tabbatar mana da alkhairi…”
Mummy ta amsata. Wucewa suka yi suka fice suma, Jarood na bin bayansu. Buɗe baki Labeeb ya yi zai yi magana wayarshi da ta yi ringing ta katse shi.
Zarowa yayi, sai da zuciyarshi ta doka ganin Anees rubuce a jiki. Ɗagawa ya yi da sauri yana karawa a kunnenshi.
“Yaya Mamdud ya tashi!”
Baisan sa’adda dariya ta ƙwace mishi ba.
“Gani nan…”
Ya amsa Anees yana kashe wayar. Mummy da Dady ya kalla.
“Mamdud ya farka…”
Ya faɗi yana juyawa ya fita daga falon da gudu. Mummy da Dady suka haɗa idanuwa cike da mamakin kalar ƙaunar nan da ke tsakanin Mamdud da ‘ya’yan nasu.
****
Idan ta ce ga yadda ta iya fitowa daga gidan su Labeeb ta shiga motarta take tuƙin ba za ta ce ba. Dishi-dishi take gani saboda hawayen da ke cike da idanuwanta. Babu abinda ke mata yawo sai maganganun Zulfa.
‘Ba shi yai min ciki ba! Ba shi bane yaya!’
Shi ne kawai abinda ta ji ta juya kamar yanda babu wanda ya ganta. Kuma shi ne abinda ke mata yawo cikin kanta yana sokar mata zuciya da wuƙaƙe masu ciwon gaske.
Waje ta samu a gefen hanya tai parking ta haɗa kanta da steering wheel ɗin motar tana sakin gunjin kuka. Ta ɗauka babu abinda zai zo dai-dai da ciwon da ta ji lokacin da ta ji Labeeb ya wa Zulfa ciki.
Sai yanzun da ta ji cewar ba shi bane ba. Sai yanzun da ta ga girman matsayin Zulfa a wajen shi, sai da ta tuna yadda ya ɗauki laifin da ba nashi ba saboda Zulfa. Yadda ya jure tsanar ‘yan uwanshi da fushin iyayenshi saboda kare mutuncinta.
Yadda yake a shirye da ya rasata da abinda ke cikinta saboda Zulfa. Raɗaɗi take ji har cikin tsokar jikinta, zuciyarta kamar an buɗe sabbin raunuka an zuba mata gishiri a jiki.
Labeeb shi ne komai na rayuwarta, Zulfa ba komai na rayuwar Labeeb bace ita, ba ta da kalaman da za ta ɗora matsayinta a wajen Labeeb, abu ɗaya ta sani ba za ta taɓa kaiwa rabin Zulfa a wajen shi ba.
Ba kishi bane kaɗai yake turnuƙe da ita har da tsoro da fargaba mai tsanani. Saboda tana jin yadda Labeeb ke suɓuce mata, a yanzun babu abinda ke mata yawo sai ranar da aka kaita gidanshi a matsayin mata.
****
“Na kasa yarda ba mafarkin yau nake yi ba…”
A kunyace ta sadda kanta ƙasa, farin ciki fal ranta, Labeeb alheri ne a rayuwarta, ya canza komai da shigowarshi, har su Anty ne ke nuna mata ƙauna, kuma duk don kwaɗayin abin hannun Labeeb ɗin ne ba don komai ba.
Hannu yasa yana ɗago mata fuska.
“Karki ɓoye min ganinki… Shi ne nutsuwar zuciyata…”
Hannunshi ta riƙe, tana jin shi har ranta.
“Kar ka guje ni… Kar ka barni…”
Da sauri ya matsa yana haɗe space ɗin da ke tsakanin su, tana jin hucin numfashin shi a saman fuskarta, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce,
“Ke zan roƙa kar ki barni Tee, mutuwa ce kaɗai za ta rabani da ke in sha Allah…”
Hawaye cike taf da idanuwanta ta ce,
“Mummy ba ta sona.”
Riƙe fuskarta ya yi cikin hannuwanshi.
“Ki kalli idanuwana… Ki kalli fuskata. Son da nake miki ya ishemu a yanzun, za mu lallaɓa da wannan…sai mu haɗa da son da Mummy take min, mu raba.”
Dan ware idanuwa tayi, hawayen da take tarbewa suna zubo mata.
“Ya za ka yi ka raba soyayyarka da Mummy da ni?”
Ɗan shiru yayi ya sa yatsunshi yana goge mata hawayenta.
“Nima ban sani ba… Kawai bana son kina damuwa ne… Ina son ganin ki cikin farin ciki duk da banda tabbas kullum zan iya baki shi.”
Hannuwanta ta ɗora akan nashi.
“Na gode da ƙaunar da ka nuna min…”
Sumbatarta yayi kafin ya ce,
“Shhh… Ni ne da godiya da kika amince da aurena bayan ko ta ina halayyata bata dace da ke ba.”
Jim ta ɗan yi.
“Karka koma tsohuwar rayuwarka… Karka koma don Allah, sabo da ni, sabo da kai.”
Goshin shi ya haɗa da nata.
“Kin sani Tee… Bana shan komai yanzun… Soyayyarki ta nutsar da wannan ɓangaren a tare da ni, shigowarki rayuwata ya kwantar da El-Maska gaba ɗaya. Ni kaɗai ne… Inajin hakan har zuciyata.”
Sauke numfashi ta yi tana lumshe idanuwanta, tana jin hucin ɗuminshi da kusancin shi a ko ina na jikinta.
“Ina sonka sosai…”
Ta furta.
“Na sani… Har na gaji da faɗar ina sonki… Na gaji da faɗar kina da muhimmanci a rayuwata… Zan fara nuna miki gaskiyar hakan a aikace daga yau…”
*****
Wani kukan ne ya sake ƙwace wa Ateefa, tun daga zuciyarta yake fitowa, ba ta da haufi akan son da Labeeb yake mata, ko kusa dai ba zai taɓa kaiwa na Zulfa ba ne.
Ya tabbatar mata da hakan a aikace, ba tare da ya furta ba ya nuna mata yadda Mummy take har abada a rayuwarshi haka Zulfa za ta kasance. Bai rabu da ita ba ko da Mummy ta nuna son hakan.
Rana ɗaya akan Zulfa ya shirya sallama da ita da duk wata soyayya da suke wa junansu. Ƙarya take in ta ce hakan ba ya ba ta tsoro ba kuma ya ɗaga mata hankali.
Tana tuna ranar farko da suka fara samun saɓani akan Zulfa.
*****
Zaune take a ƙasa kan kafet ɗin falon su, shi kuma ya yi pillow da cinyarta suna hira.
“Yau babu aiki kenan?”
Kallonta ya yi.
“Kin gaji da ganina ne a cikin gidan in tashi in fita?”
Dariya ta yi.
“Ni bance ba… Kawai dai na tambaya ne.”
“Um um babu inda zanje. Jikina ciwo yake min…”
Wayarshi da ke ajiye gefe ta soma ringing. Hannu ya miƙa ya ɗauko yana ɗagawa tare da kai wayar kunnenshi.
“Hello Zulfa…”
Dama saida ta kawo ma ranta Zulfa ce. Don ya fi waya da ita akan kowa ta kula da hakan. Ko wayarshi ya cika dannawa da ita yake hira. Tun wayarsu ta safe da take ƙa’ida da ta dare ba ta damunta har ta fara yanzun.
Sai dai ba ta nuna mishi tana kishi da Zulfar nan musamman da tasan akwai aure a tsakanin su. Tana kallon gudun ruwan shi ne kawai.
Da sauri ta ga ya tashi.
“Me ke damun ki?”
Ya tambaya. Ba ta jin abinda ake cewa daga ɗayan ɓangaren.
“Ban yarda ba. Na ce in sai miki mota, tsoron tsiya ba zai barki ki koyi tuƙi ba… Ki jirani a school ɗin gani nan zuwa.”
Miƙewa tsaye yayi da wayar a kunnenshi.
“Ki saurareni! Ki jira ni na ce …Bana son gardama.”
Sauke wayar ya yi yana sakawa a aljihunshi ya bar Ateefa nan zaune ya hau sama. Bai jima ba ya sauko ya kalleta.
“Bari in ɗauko Zulfa daga makaranta.”
Tsura mishi idanuwanta ta yi, akwai direban da ke kaita unguwa in Labeeb ba ya nan. Da kanshi yake koya mata tuƙi, hannunta bai gama faɗawa bane kawai.
“Ka sa driver ya ɗauko ta mana.”
Girgiza mata kai ya yi
“Ina son inga jikinta. Muryarta yayi wani iri… Ta ce ciwon kai ne, amma na san halinta.”
Ya faɗi.
“Hmm…”
Daƙuna fuska ya yi.
“Menene?”
Kallon shi ta yi sosai. Wani irin kishi na turnuƙe ta.
“Na rasa gane tsakaninku da Zulfa. Kuma a haka ka ce min ba sonta kake ba. Komai a kanta daban ka ke yi, kullum da safe da ita kake fara waya. Ba ka kwanciya baka yi mata bankwana ba… Text sai ku yi ma juna sau nawa…”
Yadda yake kallonta yasa ta yin shiru.
“Ki ƙarasa mana…”
Shirun ta sake yi. Rai a ɓace ya ce,
“Na faɗa miki iya abinda yake tsakanina da ita. Bansan me yake miki wahalar fahimta a ciki ba… Meye don na yi waya da ƙanwata? Meye don na mata sai da safe ko mun wa juna text?
Ba kya ganin kullum da safe sai na gaisa da har su Asad? In kina da matsala da Zulfa daban ki faɗa min Tee…”
Ba ta ce komai ba ta miƙe tana shirin bar mishi falon. Da sauri ya sha gabanta
“Ki faɗa min matsalarki da ƙanwata in ji…”
Ba ta da amsar da za ta bashi, kamar yadda kishin shi ba laifinta ba ne, na zuciyarta ne.
“Akwai shaƙuwa a tsakanina da Zulfa…zan sake maimaita miki Tee… Matsayin ki a wajena daban. Nata daban… Bansan me zan yi ki fahimci hakan ba…kina son ɓata min rai ne kawai.”
Ya ƙarasa yana juyawa ya bar gidan. Tana jin siraran hawayen da suka biyo mata fuska. Yau ne rana na farko da ya taɓa cewa tana son ɓata mishi rai, kuma a dalilin Zulfa.
*****
Ta jima a wajen tana wani irin kuka. Sai da ta tabbatar tana da nutsuwar da za ta yi tuƙi tukunna ta ja motar tana jin zazzaɓin da ya rufe mata jiki.