Skip to content
Part 46 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Ko da ya yi sallar Asuba ya gama Azkar ɗinshi na safe bacci ya koma don ba wani na kirki ya samu ba da dare. Bai san iya lokacin da ya ɗauka yana bacci ba. Ringing ɗin wayarshi ya tashe shi. 

Da ƙyar ya kai hannu ya lalubo wayar, ba tare da ya tsaya duba ko waye ba ya ɗaga yana karawa a kunne, jin muryar Dady ce ya sa shi miƙewa babu shiri, muryarshi ɗauke da yanayin bacci ya amsa sallamar dady yana ɗorawa da,

“Ina kwana…”

“Lafiya ƙalau… Bacci ma kake ko?”

Gyara murya Labeeb ya yi. 

“Ai na tashi Dady… Ya su Mummy?”

“Duk suna lafiya. Ya kwanan iyali?”

“Alhamdulillah.”

“Madalla… Mun yi magana ne da Auwal. Tunda ba wani abu ake jira ba. Ranar Asabar ɗin nan za a ɗaura auren ku da zulfa. In akwai shirye-shiryen da za ku yi sai ku fara…”

Tunda ya ji an ambaci sunan Abban su Zulfa zuciyarshi ta fara dokawa. Cikin kanshi yake lissafin yaushe ne Asabar. Sosai zuciyarshi ta ci gaba da dokawa da ya lissafa yau Alhamis, juma’a. Kwana biyu kenan. 

“Labeeb?”

Daddy ya kira jin shirun yayi yawa. A ɗan daburce ya amsa da, 

“Um.. Asabar.. Dady… Kwana biyu kenan ko?”

“Eh kwana biyu… Akwai matsala ne? Ko ba ka shirya ba?”

Da sauri Labeeb ya girgiza kai kamar Dady na ganinshi. 

“Na shirya… Allah ya kai mu.”

“Amin… Allah ya yi muku albarka.”

Dady bai jira ya amsa ba ya kashe wayar daga ɗayan ɓangaren. Hakan ya sa Labeeb sauke wayar daga kunnenshi yana jin yadda ya nemi baccin da ke idanuwanshi ya rasa. 

Ya ma rasa ko me yake ji, wata dariya mai sauti ce ta ƙwace mishi. Sakkowa ya yi daga kan gadon yana nufar banɗaki. Har ya yi wanka wani sama-sama yake jinshi. Da ƙyar ya lalubo jeans da T-shirt ja ya sa a jikinshi ya fita daga ɗakin. 

A falon su na sama ya samu Ateefa tana kallo, jin takun tafiyarshi ya sa ta juyawa. Murmushi ta yi, za ta iya ƙirga lokutan da ta taɓa ganinshi da shiga irin haka, suspenders ya fi sakawa ko da yaushe. 

“Ka yi kyau…”

Murmushi yayi

“Na gode… Ya kuka tashi?”

Sai da ta ɗauke idanuwanta daga kanshi ta ɗan kalli cikinta kafin ta amsa da, 

“Alhamdulillah… Kaifa? Ya gajiya?”

Ɗan ɗaga kafaɗarshi ya yi, yana jin yadda cikinshi ke ƙara. 

“Babu… Sai yunwa kawai.”

Miƙewa Ateefa ta yi.

“Mu je mu karya to… Nima kai nake jira ka tashi dama.”

Bai musa ba ya bita, Tea ta haɗa musu. Ta zuba musu dankalin turawa da farfesun nama. Ita tea ɗin ma kawai ta iya sha, don ƙamshin abincin ma ji ta yi yana neman ɗaga mata hankali. 

“Nufin ki Tea kawai za ki sha?”

“Babynka ko ƙamshin farfesun bai son ji.”

Ɗan ware idanuwa Labeeb ya yi yana haɗiye abinda ke bakinshi kafin yace

“Baby ya taimaka… Kar ya sa yunwa ta kama mom.”

Dariya Ateefa ta yi. 

“Wake da shinkafa da mai nake so… Na sa a dafa min.”

“Allah ya shirya min ke Tee… Ko ba baby kwaɗayin ki sai addu’a balle kuma yanzun.”

“Sharri dai… Duk kwaɗayina na kai ka ne?”

Ya ci dankalin da farfesun sosai, a nutse yake kurɓar tea ɗinshi, baya son abinda zai faɗa mata, abinda ya zama dole ta sani saboda ba ya son ɓacin ranta. Yana jin daɗin farin cikin da yake gani a fuskarta yau ɗin nan. 

“Ina jinka…”

Ateefa ta faɗi a sanyaye, yadda ya ware idanuwa ya sa ta faɗin, 

“Na san wani abu kake son faɗa min tun ɗazun… Fuskarka ta nuna.”

Daƙuna fuska ya yi. 

“Ki daina karanta ni kamar littafi.”

Girarta ta ɗaga mishi duka biyun, kofin hannunshi ya ajiye yana sauke numfashi. 

“Daddy ne ya kira ni. Ranar asabar ɗaurin aurena da Zulfa.”

Hannu Ateefa ta sa ta dafe kanta tana lumshe idanuwanta tare da soma jero duk wata addu’a da ta zo cikin kanta saboda yadda wani tuƙuƙin kishi ya taso yana neman lulluɓe ta. 

Da maganar aurenshi da Zulfa Ateefa take kwana take tashi tun lokacin da ta ji tana ɗauke da cikin nan, har zuwa yanzun. Sai dai ba ta ɗauka za ta ji abinda take ji yanzun ɗin ba. Ta ɗauka ta gama shirya wa zuciyarta ƙara auren Labeeb. 

Ashe ƙarya ne, ƙarya take in ta ce ta shirya jin zafin nan a zuciyarta. Ta shirya raba soyayyar Labeeb da Zulfa. Numfashi take ja tana fitarwa a hankali. 

“Don Allah ki ce wani abu…”

Labeeb ya faɗi, muryarshi cike da tsoron ganin yanayin fuskarta. Sai da ta tabbatar za ta iya magana tukunna ta buɗe idanuwanta da suka canza launi saboda kishi ta ce mishi. 

“Allah ya kai mu… Allah ya sanya alkhairi.”

“Bana son hurting ɗinki wallahi… Bana son damuwarki.”

Cikin idanuwa ta kalle shi.

“Idan na ce ka fasa aurenta za ka fasa?”

Sai da ya yi jim yana kallonta kafin ya girgiza kai a hankali. Murmushi ta ƙaƙaro ta ɗora akan fuskarta. 

“Haka nima bansan yadda zan daina kishinka ba… Ka taya ni addu’ar Allah ya rage min.”

“In sha Allah…”

Ya faɗi yana jan kujera ya matsa dab da ita, hannunta ya kama ya sumbata.

“Ina ƙaunar ki.”

Ba ta iya amsa shi ba. Kawai so take ta miƙe ta je ɗaki ko kuka ta yi ƙila ta samu sauƙin abinda take ji. Wani irin tausayinta Labeeb yake ji har bayan zuciyarshi. Ya san dauriya kawai take yi, ya san zafin kishinta. 

“Zan je asibiti… Ba kya sha’awar komai in siyo miki?”

Girgiza mishi kai ta yi alamar A’a. 

“Tee… Bana so kin sani kuma.”

“Yi haƙuri… Bana sha’awar komai.”

Kai ya ɗan ɗaga mata yana miƙewa. Ranƙwafawa ya yi ya sumbaci kuncinta tare da faɗin, 

“Ki kula min da kanku. Sai na dawo…”

“Allah ya kiyaye ya dawo da kai lafiya.”

Ta amsa shi zuciyarta kamar za ta fasa ƙirjinta ta faɗo saboda zafin kishi. Sai da ya amsata da amin tukunna ya koma ɗakin shi ya ɗauko mukullin mota da wayarshi ya fito ya nufi hanya yana sauka daga benen. 

Kifa kai Ateefa ta yi a jikin table ɗin wajen wasu siraran hawaye na zubo mata. 

“Allah ka yaye min kishin nan ko zan huta da wahala…”

Ta ƙarasa maganar wasu hawayen na sake zubo mata. Musamman da zuciyarta ta raya mata Labeeb ɗin zai iya biyawa wajen Zulfa kafin ya wuce asibiti ko kuma in ya dawo. Tun kafin maganar aure ta shiga tsakanin su ma basa iya haƙuri da ganin juna ina ga yanzun. 

**** 

Fitowa ta zo yi daga ɗaki ta ji Abba na waya yana faɗin jibi ɗaurin aurenta. Wani irin tsalle zuciyarta ta yi kamar za ta fito daga ƙirjinta. A hankali kamar wadda aka zarewa laka ta tura ƙofar tana zamewa a jikinta ta zauna ƙasa kan tiles ɗin ɗakin. 

A mafarki, a ido biyu ta sha hasko kanta a matsayin da take yanzun. Burin rayuwarta bai wuce Labeeb ya zama mallakinta ba. Mafarkinta bai wuce ta zama mata a wajen shi ba. Sai dai ba ta taɓa hango ko da wasa kasancewar hakan cikin irin wannan yanayin ba. 

Ta sha hango bikinta, har ranta tana da ra’ayin yin shagali sosai da bikinta, ta tsara komai, ta yi gwargwadon ƙarfin gidansu. Ko da ta haƙura da auren Labeeb hakan bai hana mata ci gaba da tsara bikinta ba. 

Jikinta ne ya ɗauki ɓari, ko ina rawa yake. Sanin tausayi ne zai sa Labeeb aurenta ba don yana sonta yadda ita take son shi ba bai dameta ba. Ba ta da abinda kowacce macce ke tinƙahon kaiwa gidan aurenta.

Jinta take daban, jinta take wani iri. Ta rasa abinda ya kamata ta ji, farinciki, baƙin ciki ko tashin hankali? Numfashi take ja tana mayarwa da sauri-sauri. Kafin wasu hawaye su soma zubar mata. 

Haɗe kanta da gwiwa ta yi, ta rufe idanuwanta, babu abinda take ji banda hannayen Mamdud a ko ina na jikinta. Fentin da ya yi mata take ji a zuciyarta da ba ta san ranar da zai goge ba. 

Kuka take sosai, ba haka take son je wa Labeeb ba. Ba haka ta hango rayuwa a tare da shi ba. Ba haka ta hango aurenta cikin hanzari kamar ana ɗokin rabuwa da ita ba. 

Da duk wani tunani da zai zo mata da yadda kukanta yake tsananta. Kewar Ummi na danneta, da tana kusa ƙila da ta faɗa mata kalaman da ranta zai ɗan yi sanyi. 

******

Text din Dawud ya sa shi baro makaranta, kanshi tsaye gida ya yo. Da sallamarshi ya shigo yana ɗorawa da, 

“Mami! Mami!!”

Fitowa ta yi daga ɗaki. 

“Tayyab lafiya?”

Ta tambaya a razane, tana kula da murmushin dake kan fuskarshi, hararar shi ta yi kafin ya amsa ta ɗora da, 

“Ban hanaka yi min kiran nan ba? Ka sa zuciyata na ta dokawa.”

Dariya ya yi. 

“Yaya yai min text wai jibi ɗaurin auren Zulfa.”

“Na sani ai… Ba ma wai bane… Jibi In sha Allah. Shi ne ka baro makaranta ka taho?”

Ɗan sosa kai Tayyab ya yi. 

“Na san akwai shirye-shirye shi ya sa. Kuma ba wani abin kirki ake ba.”

Tsare shi Mami ta yi da idanuwa. Shagwaɓe fuska ya yi. 

“Mami don Allah kar ki sa in koma. Kin ga fa akwai aike. Yayan ma yanzun zai zo.”

Sauke numfashi Mami ta yi, akwai wani abu tattare da Tayyab da yake sa ka kasa mishi musu wasu lokutan. 

“Ai sai ka zauna tunda ka riga da ka sa wa ranka ƙin zaman makarantar.”

Wucewa yayi yana wa Mami dariya. Wayarshi, mukullin mota da handout ya cilla kan gadon ɗakin shi yana janyo ƙofar. Ya nufi ɓangaren su Mami in da ya san Zulfa take.

Ƙwanƙwasa ƙofar ya yi yana ɗan dakatawa. Kafin ya ga an ɗan buɗe ƙofar, ƙarasa turawa ya yi yana shiga da sallama, ganin Zulfa zaune a gefen ƙofar da fuskarta da ta kumbura saboda kuka ya sa shi saurin sakin ƙofar da yake riƙe da ita. 

“Subhanallah…”

Ya furta yana zama a gefenta. Sosai yake kallon fuskarta. 

“Zulfa… Lafiya? Mene ne? Me aka yi miki?”

Ya tambaya damuwa bayyane a fuskarshi, kanta ta kwantar kan ƙafafuwanshi wani kukan na ƙwace mata. 

“Don Allah Zulfa ki min magana… Mene ne?”

Ya tambaya kamar zai yi kuka don gaba ɗaya ta dagula mishi lissafi. Ɗago da jikinta ta yi tana wani irin jan numfashi da ya sa Tayyab riƙe fuskarta cikin hannuwanshi. 

“Zulfa… Kin ga… Babu abinda zai sameki… Ina nan.”

Cikin kuka tace

“Yaya Tayyab ba…ba haka na hango aurena ba… Ba cikin hanzari haka ba… Ba don na taɓa yin ciki ba… Ba…”

Hannu yasa yana rufe mata baki tare da girgiza mata kai. Idanuwanshi cike taf da hawaye shi ma. Ba zai taɓa misalta yadda take ji ba. In har ‘yan cikinshi na yamutsawa duk idan ya tuna abinda ya faru da ita, ba zai taɓa misalta yadda take ji ba. 

Sai da ya tabbatar muryarshi ba za ta yi rawa ba in ya yi magana tukunna ya ce, 

“Wa ya ce miki auren ki ba zai kasance yadda kike son shi ba? Wa ya ce miki don abinda ya sameki ya sa za ki yi aure?”

Murmushi ta yi da bai da alaƙa da jin daɗi, hawaye masu ɗumi na zubo mata. 

“Yaya Labeeb ba sona yake ba… Tausayina zai sa ya aure ni… Bana son takura wa kowa Yaya Tayyab… Na jure son da nake mishi duk shekarun nan… Zan iya ci gaba da jurewa… Amma bazan iya jure takura Shi..”

Kallon mamakin da Tayyab yake mata ya sa ta fahimtar suɓul da bakan da ta yi. 

“Kina son Yaya Labeeb? Zulfa tun yaushe?”

Tayyab ya fadi muryarshi a sanyaye, cikin kanshi yana kallon duk wasu alamu da bai gani ba a da. Yanayin ramewarta lokacin auren shi na farko. Damuwarta da ƙarin rashin maganarta a lokacin auren shi na biyu. 

Runtsa idanuwanshi ya yi ya buɗe su. 

“Ya Allah…”

Ya faɗi don ya rasa me zai ce. Ya rasa me zai yi wa Zulfa ta samu sauƙin abinda take ji. Bai taɓa ganin mace mai ɗaukar yanayoyi da dama haka irinta ba. Mata na da rauni, sai dai akan Zulfa ya ga cewa suna da ƙarfin gwiwar da su kansu basu san da shi ba. 

Akwai juriya a tattare da mata da babu namijin da Allah ya hore wa. Akwai haƙuri a tattare da su da ba kowa ne zai fahimta ba. Hannuwanta ta ɗora akan na Tayyab da yake jikin fuskarta. Sirrinta ya riga da ya fito fili. 

Ba ta ga amfanin ci gaba da riƙe shi ba. 

“Idan na ce ga tun sa’adda nake son shi ƙarya nake. Na girma da son shi ne Yaya Tayyab… Wallahi ina son shi fiye da yadda ya kamata mutum ya so wani…ban faɗa mishi ba saboda baya sona irin haka… In ya sani zai aure ni… Bazan iya takura shi ba… Bazan iya ba…”

“Shhhhh…. Ya isa…”

Tayyab ya faɗi yana jan numfashi da fitar da shi a nutse yana neman kalaman da zai yi amfani dasu ya rasa. Don haka ya bar ƙaunar da yake wa ƙanwar tashi ta taya shi tsara abinda ya kamata. Buɗe bakin shi ya yi tare da zuciyarshi. 

“Ƙila Yaya Labeeb baya sonki da irin yadda kike zato… Ƙila yana son ki yadda kike zato. Ba lallai ba ne ki fahimci girman son da yake miki Zulfa… Ko shi bana jin ya san girman son da yake miki. 

Ni zan ce miki… Zan rantse miki wanda duk ya yi miki abinda Yaya Labeeb yai miki… Wanda ya kareki daga idanuwan duniya yadda ya yi… Ƙaunar mai girma ce. 

Ki daina kokwanto akan son da yake miki. Ko da ba irin wanda kike so ba ne ba. Na tabbata irin wanda zai ishe ki ne don ba zai taɓa barin wani abu ya sameki ba in har zai iya kareki daga hakan. 

Irin wannan ƙaunar… Irin wannan son nake son a yi wa ƙanwar da ita kaɗai ta rage min a duniya… Daga nan zan fita in faɗa wa su Abba a janye auren nan in har zuciyarki ba ta so. 

Wallahi za mu baki goyon baya a duk zaɓin da kika yi…”

Kallon cikin idanuwan Tayyab ta yi, tana karantar gaskiyar maganganu sa. Tana ganin yadda zai ɗauki duniya ya matsar mata da ita duk inda take so in har yana da ikon yin hakan. Tana ganin yadda zai miƙa rayuwar shi don farin cikin ta. Girma na ‘yan uwantaka ba abu ba ne ƙarami. 

Hawayenta ta mayar, ba ta san ko fentin da Mamdud yai mata zai taɓa gogewa ba, abu ɗaya take da tabbas akai yanzun. ‘Yan uwanta za su tayata wankin shi har ƙarshen rayuwarta ko da wankin ba zai canza kalar shi ba, ba za su taɓa gajiyawa ba. 

“Me ka zaɓa min? Ka tayani zaɓe Yaya Tayyab.”

Zulfa ta faɗi, tana sa Tayyab jin yadda ta miƙa mishi alƙalamin da zai iya canza duk wani abu na rayuwarta. Yana jin nauyin girman da ta bashi na son danne shi. Yana ƙaunarta fiye da rayuwa da kanta. Sai dai wannan zaɓi ne da ita za ta zauna da shi. 

Hurumi ne da shawara ce kawai abinda zai iya ba ta. Hannunta kawai zai iya kamawa ya sa ta a hanya ba wai ya yanke mata hukunci ba. Fuskarta ya saki yana kama hannuwanta. 

“Ki nutsar da zuciyarki… Za ki iya zama da Yaya Labeeb a matsayin miji? Za ki iya ƙarasa rayuwarki tare da shi? Za ki iya canzawa…ki girma tare da shi? Ki tsufa tare da shi ? Zakii iya raba farin ciki da duk wata ƙaddara da ta taso miki kowace iri ce tare da shi? 

Amsarki na zuciyarki. Ba kya buƙatar hukuncina ko na kowa… Akwai alkhairi da rashin shi a cikin komai. Rayuwa ta aure ba abu ba ne mai sauƙi. Ba abu ba ne na wasa. 

Duka rayuwarki za ki canza… Kar ki yi sauri.”

Lumshe idanuwanta Zulfa ta yi. Kalaman Tayyab na mata wani irin tasiri. Za ta iya rantsewa kusancin Ummi a zuciyarta ya ƙaru fiye da ko da yaushe. Kafin fuskar Labeeb ta soma yi mata yawo a idanuwanta da zuciyarta. 

Dariyarshi, ɓacin ranshi, kukan shi, farin cikin shi. Komai nashi ne yake dawo mata, ba tun yanzun tasan cewa duk wani farin ciki da ake samu a rayuwar aure nata na tattare da kasancewa da Labeeb ba. Za ta rantse tana jin hannuwan shi a jikinta a yanzun. 

Tana kallon yanayin idanuwanshi lokacin da ta faɗa mishi tana da ciki. Tana ganin yanayin shi lokacin da ya kalli dukka dangin su ya faɗa musu cikin jikinta nashi ne. Tana kallon yadda komai ya tarwatse mishi da ganin tsanar da suka yi mishi. 

Ba za ta manta yadda ya kalleta ba, yadda ya nuna mata zai iya ɗaukar komai in har hakan na nufin kariya a gareta. Da wannan yanayin na fuskar Labeeb komai nata take jin yana faɗa mata auren shi ne dai-dai. 

Buɗe idanuwanta ta yi, da ƙwarin gwiwa irin wanda ba ta taɓa jin irin shi ba ta ce, 

“Zan aure shi Yaya Tayyab… Zan aure shi ko baya sona yadda nake son shi… Zan aure shi…”

Murmushi Tayyab ya yi. 

“Allah ya sanya miki alkhairi da albarka a cikin hakan…”

Murmushi ta yi ita ma tana zame hannunta daga cikin na Tayyab tare da goge fuskarta. 

“Now… Faɗa min yanda kike mafarkin aurenki ya kasance… Ni… Yaya… Mami…Abba za mu kwatanta cika mafarkin ki yadda Allah ya bamu iko…”

Dariya ta yi tana miƙewa. 

“Bari ina wanko fuskata in zo…”

Ta ƙarasa tana tura ƙofar banɗaki. Sauke numfashi Tayyab ya yi. Damuwar ɗayansu damuwar dukkan su ce. Farin cikin ɗayansu farin cikin dukkan su ne. Babu abinda ya kai zumunci daɗi. Babu abinda ya kai ƙauna ta tsakanin ‘yan uwa tabbas da nutsuwa. 

**** 

Zainab ya samu zaune kan kujera a gefen gadon Mamdud. Shi kuma yana kan gadon a kishingiɗe da mug a hannunshi. Da murmushi Zainab ta amsa sallamar shi. 

Ɗan ɗaga mata gira Labeeb ya yi. 

“Um… Kuna hutawa fa. Me ake yi haka?”

Ya ƙarasa yana jan kujera ya zauna. Har lokacin da murmushi a fuskar Zainab. 

“Ina kwana… Su Yaya Asad ne suka je gida. Sun barmu mu kaɗai… Shi ne nake karanta wa Yaya Mamdud wani littafi na Ayna dimples NI DA ƊIYATA.”

“Lafiya ƙalau… Ya kuka tashi? Iyye! lallai. Mamdud ya jikinka?”

Sai da ya ƙara kurɓar ko meye ke cikin mug ɗin hannun shi kafin ya amsa da faɗin, 

“Alhamdulillah. Ya kuka tashi?”

“Alhamdulillah…”

Zainab Mamdud ya kalla don littafin da take karantawa ya mishi daɗi. Yana kuma rage mishi damuwar da yake ciki. 

“Sis ci gaba…littafin da daɗi.”

“Sai dai a sake daga farko.”

Labeeb ya faɗi yana kallon su ɗaya bayan ɗaya. 

“Taɓɗi… Yaya Mamdud ka ji fa. Wallahi mun yi nisa.”

Ɗan ɗaga kafaɗa Labeeb ya yi 

“Ni dai a sake daga farko.”

“Ko kuma a tura maka ka karanta da kanka ba.”

“Son kanku ya yi yawa fa… Zee Zee ki tura min Tee sai ta karanta min…”

Kallon juna Mamdud da Zainab suka yi suna taɓe baki. Dariya Labeeb ya yi yana jin daɗin yadda Mamdud ke ƙoƙarin komawa dai-dai. Duk da yasan ƙarfin hali kawai yake yi. 

“Dady ya kira ni yanzun kafin in fito. Ranar Asabar za a ɗaura aurena da Zulfa…”

Tea ɗin da ke bakin Mamdud ya ji ya mishi sanyi ƙarara kafin ya bi ta maƙoshin shi ya dira cikin shi. Ambaton sunan Zulfa kawai ya jefa shi yanayin da ba zai faɗu ba. 

Gurgunta mata Rayuwa da ya yi ya fi komai ci mishi zuciya. Ya fi ƙaddarar rashin samun ɗa tsaya mishi. Don wannan iya rayuwar shi abin ya tsaya. Wannan kuwa ya haɗa da Zulfa. 

Idanuwan shi ya tsayar cikin na Labeeb. Muryarshi na rawa ya ce, 

“Ban san me zance ba.”

“Addu’a da fatan alkhairi za ka yi.”

“Hmm… Ba zai canza abinda nai mata ba… Ba zai canza fentin da na yi wa rayuwarta ba.”

Sauke numfashi Labeeb ya yi baya son ganin raɗaɗin da Mamdud ɗin yake ciki. Har a wajen Allah laifin shi mai yafuwa ne gaba ɗayanshi in har Zulfa ta yafe mishi. 

“Ka daina magana kan abinda ba ka da ikon canzawa…damuwar ka za ta ƙara yawa in kana hakan. Addu’a ba za ta canza abinda kai mata ba… Sai dai za ta canza wani abu daga sabuwar rayuwar da za ta fara…”

Wani abu ne Mamdud yake ji tsaye a wuyanshi da ya kasa haɗiyewa. Har lokacin muryarshi na rawa ya ke faɗin,

“Allah ya sa aurenka ya zame mata alkhairi… Allah ya ba ka ikon riƙe ta da amana…”

Ɗan murmushin ƙwarin gwiwa Labeeb ya yi mishi. 

“Amin… Ko kai fa.”

Gyaran murya Zainab ta yi da ya sa Labeeb kallon ta. 

“Yaya an kusan zama ango.. Shi ya sa kake ta ƙyalli tun da ka shigo.”

Idanuwanshi da suke cike da kunya ya ware kan Zainab. 

“Gidanku Zee Zee… Ke ko?”

Dariya take mishi sosai. Juye-juye yake yana neman abinda zai jefa mata. 

“Karka taɓa min ƙanwa wallahi… Ƙarya ta yi? Ni ma na ga ƙyallin ai.”

Cewar Mamdud da wani kasalallen murmushi a fuskarshi. Dafe kanshi Labeeb ya yi cikin hannuwanshi. Baisan me ya sa yake jin kunyar da yake ji ba. Kunya ba ta cika damunshi ba. Musamman tsakanin shi da su Zainab. 

“Ku sama min lafiya…”

Labeeb ya faɗi, yana rufe bakin shi su Asad na turo ƙofar da sallamar da ko amsata basu bari an yi ba. Asad ya ƙarasa inda Labeeb yake yana sa hannu ya hargitsa mishi sumar dake kanshi. 

“Ango…”

Ture shi Labeeb ya yi. 

“Yaran nan… Ni sa’anku ne wai? Kun raina ni ko?”

Dariya Anees ya yi. 

“O. M. G Yaya… You are blushing. Har cikin idanuwanka kunya.”

Miƙewa Labeeb ya yi yana nufar ƙofa, da sauri Asad ya riƙo hannunshi yana dariya

“Yi haƙuri…mun daina.”

Su duka dariya suke mishi, hararar su ya yi yana wani tsuke fuska kafin ya koma ya zauna. Asad ya kalla sosai yana son nazarin abinda ke fuskarshi. Kai Asad ya ɗan daga mishi alamar karya damu. Komai ya wuce a wajen shi. 

Da gaske har zuciyarshi yake jin yadda ya haƙura da zulfa gaba ɗaya.Farin cikin Labeeb na nufin komai a wajenshi. Ko da ba zai auri Zulfa ba shi ba zai iya zama da ita ba bayan ya ga kalar ƙaunar da Labeeb ɗin yake mata. 

Sauke numfashin da Labeeb baisan yana riƙe da shi ba ya yi. 

“Da tsokanar nan da kuke da zama kuka yi muka yi shawara. Akwai ayyuka fa… Ga su haɗa lefe kuma… Kwana biyu muke da shi.”

“Ni da Zee Zee za mu haɗa lefe.”

Mamdud ya faɗi da sauri. Kallon shi Labeeb ya yi da hannunshi ɗaya da ƙafa nannaɗe da bandeji. 

“Really Mamdud? No, na hutar da ku.”

Shi ma Mamdud ɗin kanshi ya kalla kafin ya sake kallon Labeeb ɗin. 

“Ba za su hana komai ba. Da gaske. Kuma ƙila zuwa gobe a kwance min hannuna haka Doctor ya faɗi.”

Magana Labeeb zai yi, Zainab ta karɓe da faɗin, 

“Za mu iya. Kuma ka taɓa ganin ni da Yaya Mamdud mun kasa yin wani abu?”

“Yaya ka basu kawai ko za su barmu mu yi maganar wani abin. Kasan halin su biyun nan…”

Sauke numfashi Labeeb ya yi.

“Na ji… Zeezee da Mamdud za su haɗa lefe. Asad kayan duk da zamu sa suna hannunka… Anees ka ji da wajen da za a yi dinner da walima kawai… Abinda za a da komai dai…ko kai inviting mutane ni in yi wancan ɗin…”

Girgiza kai Mamdud ya yi. 

“Kai ɗin? Ka yi abinda ka saba. Ka ji da kuɗin da za a kashe. Ina buƙatar waya… Tab ɗina tana gidana… Ɗayar wayar bansan inda take ba. 

Sai ɗayar wayarka. Zan ji da gayyatar mutane daga nan inda nake.”

Sauke ajiyar zuciya Labeeb ya yi. Ya yi kewar hakan sosai. Ɗayar wayarshi ya zaro ya miƙa wa Mamdud don har wani nauyi-nauyi take mishi. Duk sa’adda zai ɗaga business call ko na jama’a sai ya yi kewar Mamdud ɗin. 

Hannu Mamdud ya sa yana karɓar wayar tare da jujjuya ta cikin hannunshi. 

“Ka yi haƙuri… Don Allah ka yi haƙuri.”

Ya faɗi muryarshi na karyewa. Shi kanshi ya yi kewarsu. Murmushi Labeeb ya yi. 

“Ka gyara komai…don Allah karka sake dawo min da ita…sai ta yi kwanaki a kashe. Bansan yadda zan yi da abinda ya danganci El-Maska babu Mamdud a ciki ba…”

Kai Mamdud ya jinjina mishi don ya kasa magana. 

“Asad wayar Mamdud da mukullanshi na hannunka ko? Ka biya gidanshi ka ɗauko mishi Tab ɗin. A siyo wata wayar a saka sim ɗin cikin wadda ta fashe…”

Dama Asad da Anees ɗin babu wanda ya zauna tun shigowar su. Kai kawai Asad ya ɗaga mishi yana nufar ƙofa. 

“Asad…da ƙafafuwanka zan tafi tawa hidimar?”

Juyowa yayi ya daƙuna wa Anees fuska. 

“Waye ya ɗauko wannan motar? Sai dai kazo in rage maka hanya.”

“Ko kai ka ɗauko ai motata ce…”

Sanin gardamar su ba ƙarewa zatai ba yasa Labeeb katse su da faɗin, 

“Ya isa!”

Hannu ya sa ya zaro mukullin motarshi daga Aljihu. 

“Anees ka yi amfani da motata tunda komawa gida ka ɗauko wata ne zai zama…”

Kafin ya ƙarasa Asad ya warce mukullin da ke hannun Labeeb ɗin ya zaro na aljihunshi ya ajiye mai kan cinya ya fice da gudu. Dariya Anees yake yi. 

“Yaran nan bashida hankali ko kaɗan…”

Shima Labeeb ɗin dariya yake yi. 

“Ku dukkan ku ba hankalin ne da ku ba. Mu je ka mayar da ni gida inyi wani abun nima… Mu bar masu haɗa lefe. Ina jin cikin asibitin nan akwai wajen siyar da kaya.”

Labeeb ya ƙarasa yana miƙewa. 

“Za ku sha mamaki…”

Mamdud ya faɗi. Girgiza kai kawai Labeeb ya yi suka fice daga ɗakin shi da Anees. A ɗan tsorace Zainab ta kalli Mamdud.

“Yaya ya za mu yi… Wallahi dariya za su yi mana in muka kasa…”

“Calm down…kin manta ni da ke bama kasa yin komai? Oya kira Asad ce ya duba bedroom ɗina ATM card ɗina na kan gado ina jin ko cikin locker ɗin gefen gadon… Duka biyun zai ɗauko min.”

Wayarta ta zaro ta kira Asad ta faɗa mishi. Tukunna ta ɗago tana jiran Mamdud ya faɗa mata ko me za su yi. 

“Ina muka yi siyayyar kayan engagement ɗinki? Nan Za ki je ki haɗa komai.”

Murmushi Zainab ta yi tana tuna wajen. 

“Kuma suna kawo kaya masu kyau… To da wa za ka zauna?”

“Karki damu… Bari Asad ya dawo… Nima aiki nake da sho. Ki je ki yi wannan ke dai…”

Kai ta jinjina mishi. Asad bai jima ba ya dawo. ATM cards ɗin duka biyu ya ɗauko, ɗaya na Access Bank ɗayan na First Bank Mamdud ya ba wa Zainab ya ce tai amfani da su ta siya duk wani abu da take ganin ya kamata. 

Bai damu ba. Bai ga abinda zai tara wa kuɗi ba. Don yaranshi yake son yin arziƙi dama. Kuma kuɗin da ke ciki duka tare da Labeeb ya same su. Bai da asarar komai ko da ma da zufar shi ya samu don ya kashe wa Labeeb su. 

Asad da Zainab tare suka wuce. Wayar da ke hannunshi ya kunna yana jan numfashi. Komai tattare da abinda yake yi ba baƙo ba ne ba. Hakan ya mishi daɗi, don gaba ɗaya tun farkawarshi da baƙon yanayi yake cin karo. 

****

“Dama ina son mu yi maganar inda za ta zauna ne… Saboda Mami na maganar kayan ɗaki ɗazu.”

Dawud ya faɗi yana kallon Labeeb ɗin. Ɗan Jim Labeeb ya yi. 

“Kasan duk inda gidajena suke. Ita ma ta sani. Kowanne akwai kaya a ciki Don…ka tambayeta in za ta zauna a gidan da nake da Ateefa. Bana son raba musu waje. 

In ƙasa za ta zauna ba amfani muke da shi ba. In ma sama zata zauna akwai part ɗin da za ta iya zama…”

Jim Dawud ya yi. Haɗe Zulfa da Ateefa waje ɗaya bai dame shi ba. Kwanciyar hankalin Zulfa shi ne matsalarshi. Cikin sanyin murya ya ce, 

“Ban raina kayan da ke cikin gidanka ba… Amma ina son zuba mata sababbin kaya kamar yadda ake yi wa kowa… Don Allah kar ka ce za ka yi. 

Ka barmu mu yi mata yadda ake yi wa kowa…Na bar maka zaɓin inda za ka ajiye ta. Ka min text bayan kun kwashe wancan kayan.”

“Ba matsala…zan kiraka.”

Sallama suka yi da Dawud ɗin, kai tsaye gidan shi Labeeb ya wuce. Bai ga Ateefa a ƙasa ba don haka ya haura sama. Tana zaune ta zuba wa TV da ya tabbata hankalinta ba akai yake ba idanuwa. 

Ƙarasawa ya yi ya zauna kusa da ita. Sai lokacin ma ta ganshi. 

“Sannu da zuwa…”

Ta Faɗi cikin sanyin murya. 

“Yawwa Tee… Ina son jin in ba ki da matsala da zaman Zulfa a gidan nan… Kuma wanne ɓangare kike so? 

Za a kwashe kayan wajen ne… O. M. G. Ana siya wa mutum kaya in za a yi aure ko? Tee am so so sorry… Innalillahi…”

Labeeb ya ƙarasa yana jinshi wani iri. Murmushi Ateefa ta yi da ba ta san ya ƙwace mata ba. 

“Zuba maka ido nayi in ga ko za ka tuna…”

Fuskarshi ta sake shiga cikin wani yanayi. ‘Yar dariya ta yi 

“Wasa nake…”

Harararta ya yi. Cikin kanshi kuma yana tunanin irin abinda ya kamata ya siya mata. 

“Ko in sake miki kayanki kema?”

Da sauri ta girgiza mishi kai. Ba ta ga abinda kayan gidan suka yi ba. Kuma bata son wani baƙon abu banda Zulfa da za ta shigo musu gida. Tunanin hakan kawai na neman sa ta fashe da kuka. 

Da ƙyar ta iya haɗiye abinda ya tsaya mata a wuya. Duk da haka ƙirjinta zafi yake kamar zai faɗo. Cike da ƙarfin hali ta ce, 

“Kuma gidanka… Inda duk ka zaɓa ta zauna banda matsalar komai.”

“No… Kema gidanki ne. Duk da Zulfa ce a cikin shi za ta sameki. Ikon gidan a hannunki yake…na santa … Za ta girmama hakan.”

In so yake ta ji sauƙin kishin da take yi, duk kalmar da za ta fito bakinshi ƙara jefata cikin yanayi take yi.

“Ina son ƙasan….amma za mu yi sharing bedroom ɗaya kamar yadda muke yi a nan…zan kwashe kayana in mayar da su zuwa ƙasan…”

Kai kawai Labeeb ya ɗaga mata kafin ya matsa ya sumbaci kuncinta yana miƙewa. Aiki ne a gabanshi ba kaɗan ba. 

“Ina sonki, kinsan hakan ko?”

Kai ta ɗaga mishi tana miƙewa ita ma. Hannayenshi ya haɗe waje daya. 

“Koma ki zauna don Allah. Ni zan kwashe miki kayan… Babyna Tee… An hanaki aiki.”

Tasan gardama ba za ta yi amfanin komai ba. Don haka ta koma ta zauna tana kallonshi ya cire vest ɗin da ke saman kayanshi har da kwance agogo tukunna ya wuce bedroom ɗinta. 

***** 

RANAR ASABAR 

Kallon shi Yumna take yi yadda farar shaddar tai mishi kyau sosai. Kaya farare na mishi kyau ba kaɗan ba. Komai nashi daban ne. Kallo ɗaya za ka yi wa shaddar kasan tana da tsada. 

Babbar rigar ya ɗauka yana warwarewa tare da sakawa. Haka take plain ɗinta babu ɗigon aiki ko kaɗan a jiki. Wucewa Yumna ta yi ta ɗauko wata baƙar leda, takalmi ne da hula da agogo a ciki, ruwan kasa masu cizawa. 

Ɗan ware idanuwa Dawud ya yi yana kallon abinda ta fiddo daga ledar. 

“Tayyab na ba sautu ya siyo min. Cikin kuɗin da kake bani ne… Bansan ko za ka so su ba.”

Ta ƙarasa maganar tana miƙa mishi agogon. Karɓa ya yi ya haɗa da hannunta yana matso da ita, sannan yasa ɗayan hannun shi ya riƙe agogon yana kallon shi. Hublot ne, ya yi kyau sosai. 

Fuskar shi a daƙune ya ce, 

“Me ya sa ba a siyo fari ba? Ko baƙi?”

Cikin fuska take kallon shi. 

“Me yasa baka son kaya masu kala? Me yasa sai fari ko baƙi?”

Jim ya ɗan yi yana son fahimtar asalin dalilin shi. Kawai gani yake komai na rayuwarshi a da babu wata kala a cikinshi, komai baƙi da fari yake ganin shi, tun ranar da Abba ya watso musu kayan su waje. 

Runtsa idanuwanshi ya yi yana buɗe su kan agogon da ke hannunshi, a hankali wani abu yake warware mishi cikin zuciyarshi. Muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Kawai dai komai nake ji baƙi da fari… Ba na ganin komai mai kala a kusa da ni.”

Hannunta ta zame daga cikin nashi tana zagayashi kan kafaɗun shi.

“Kayan jikina ba su yi min kyau ba?”

Atamfar ya kalla, blue mai cizawa da yadda tai mata kyau ba kaɗan ba. 

“Sun miki kyau sosai…”

Juyawa ta yi da hannunta ɗaya a kan kaɗarshi ta miƙa ɗayan ta ɗauko hular tana ɗora mishi a saman kai tare da dai-daitawa sosai. 

“Tayyab ya ce min da wuya ka sa… Ba ka son kaya masu kala… Ni kuma nace za ka sa saboda ni… Za ka sa saboda ina so in ganka da kaya masu kala ko da na yau ne kawai…”

Jin ya yi shiru yana kallonta tare da sauke numfashi ya sa ta ɗorawa da, 

“Ka yi kyau sosai… Zo ka gani.”

Ta sake shi tana jan hannunshi wajen mudubi. Kanshi yake kallo da hular da ke sanye akan nashi. Sai ya ganshi wani iri. 

‘Ka yi kyau Dawud… Brown na maka kyau.’

Muryar Ummi ta dawo mishi. Wani abu ya haɗiye da ya yi mishi tsaye a wuya. Ganin yanayin da ke fuskarshi ya sa cikin sanyin murya Yumna ta ce, 

“Ka cire in ba ka so…”

Juyowa yayi ya kalleta ya girgiza kanshi. 

“Ba hular bace… Ummi… Ummi na son kalar nan idan na saka.”

“Ta maka kyau…”

Fuskarshi da yanayin da ta kasa fassarawa ya miƙa mata agogon da ke hannunshi tare da hannun duka. Karɓa ta yi ta ɗaura mishi. Ta koma ta ɗauko takalman ta tsugunna tana ajiyewa saitin ƙafafuwanshi. 

Sai yanzun take ƙare musu kallo. Ba kowa bane yake da kyan ƙafafuwa irin nashi. Ko ita yatsun ƙafarta ba masu kyau bane kamar na Dawud ɗin. Sai da ya sa tukunna ta miƙe. 

“A dawo lafiya… Banda kallon ‘yan mata.”

Murmushi ya yi har cikin idanuwan shi. 

“Wajen ɗaurin aure zan je Yumna… Ina zan ga mata kuma?”

Haɗe fuska ta yi 

“A kan hanya mana… Don ba ka ga kyawunka ba ne.”

“Da guntun hancina? Ke kadaii kike ganin kyauna… Kema don ba za ki kushe ba.”

Dariya ta yi. 

“Hmm… Ba ni kaɗai nake gani ba. Da ka yarda da na shirya saika sauke ni a gida ka wuce.”

Sauke numfashi Dawud ya yi. Ko kaɗan baya son fitar da za ta yi duk da gidansu ne zai sauketa. Ya fi sonta a cikin gidanshi ko da yaushe. 

“Da gaske ban yi niyyar ki fita a ‘yan kwanakin nan ba.”

Dariya take mishi, ya ƙara haɗe fuskarshi da ta yi mata kyau. 

“Na zama cartoon ko?”

Girgiza kai ta yi. 

“Yi haƙuri…”

Ta faɗi tana ci gaba da dariya. Hannu ya sa ya ja mata hanci. 

“Yi sauri to… Dama zan biya ta gidan in ɗauki Khateeb… Rikicin Khateeb ba zai tafi da Tayyab ba sai da ni.”

Da sauri Yumna ta ɗauko kayan ankon ranar da na dinner da ya kawo mata ta ɗauko jakarta ta saka su a ciki. Tukunna ta ɗauko mayafinta babba da takalma kalarsu. 

“Ina za ki je da mayafi?”

Kallon Dawud ta yi cike da rashin fahimta. 

“Hijabin nan zan zunduma kamar matan liman?”

“Mami ta sa dole a saka mayafan nan da ba ki gansu ba. Yanzun ma duka za ki haɗa a kyautar da su. Hijabi za ki ɗauko.”

Shagwaɓe fuska ta yi, gaba ɗaya hijabin da aka sako cikin lefenta dogaye ne har ƙasa suke ja. Buɗe baki ta yi za ta yi gardama. 

“Kika min gardama ba za ki fita gidan nan ba niƙab ba.”

Jan bakinta ta yi tai shiru ta ninke mayafin tana ajiyewa tare da nufar wardrobe ta buɗe ta ɗauko hijab milk. Ta mayar da ɗayan takalmin ta ɗauko kalar hijabin. 

Sakawa tayi a jikinta. Da murmushi Dawud ya kalleta. 

“Kin ga yadda kika yi kyau?”

Turo baki ta yi. Kowa ya yi kwalliyar biki ta sani sai ita Dawud ya saka ta zunduma hijab. Takawa ya yi yana haɗe space ɗin da ke tsakaninsu, yasa hannu ya ɗago da haɓarta. 

“Ba matar liman bace ke. Matar Dawud ce. Dawud na da kishi sosai… Matata ce ke Yumna. Ni kaɗai ya halatta in ga kwalliyar ki…”

Ko da maganganun shi ba gaskiya ba ne yanayin kallon da yake mata kaɗai ya isa yasa ta yarda da duk abinda yake so. Murmushi ta yi, ɗan yatsanshi ya sa yana goge mata jan bakinta. 

Sai da ya goge shi duka babu ko alama tukunna ya kalleta sosai. 

“Yawwa ko ke fa.”

Wani irin sonshi take ji a ko ina na jikinta, sumbatarshi ta yi. 

“Ina sonka sosai.”

Rungumeta ya yi a jikinshi. Yana shaƙar ƙamshin turaren ta da sai da ta yi kusa sosai da shi yake jinshi. Da dabara ta zame jikinta daga nashi ta sake zuwa ta ɗauko wani hijabin ta sa a jaka tukunna ta ɗauka suka fice. 

**** 

“Ni dai kar ki jagula min fuska… Da kin bar min a haka ma ya fi min…”

Zulfa take wa Nabila tsegumi tunda ta fara mata kwalliya.

“Ke ɗin banza… Ranar da ba a komai ma kika yi kwalliya balle ranar aurenki.”

Nabila tai maganar tana ƙarasa mata touch up ɗin da ya rage. Harararta Zulfa ta yi da ya sa Nabila dungure mata kai. 

“Bari ya zo ya biya ni kuɗin kwalliya tun da ko godiya baki min ba.”

Miƙewa Zulfa ta yi tana taɓe baki. Doguwar rigarta da ke kan gado ta ɗauka tana nufar banɗaki da ita. Duk da Nabila yar ‘uwarta ce mace babu kyautuwa ta sake kaya a gabanta. 

Babu wasu ƙawayen da take da su. Gara ma na secondary school ɗinsu da ta manta yaushe rabon da su ko gaisa. Banda Nabila yanzun ba ta da wadda za ta kalla ta kira ƙawarta. Duk da Nabilan ta ce mata ta gayyaci wasu cikin ‘yan ajinsu. 

Zuwansu ko rashinsa duk ɗaya ne a wajen Zulfa. Rigar ta gama sakawa. Silver ce da ta yi matuƙar karɓar jikinta, cikin mudubin banɗakin take kallon kanta tana murmushi. 

Ƙunshin da suka je aka yi musu ita da Nabila jiya take kallo. Dariya ta yi cike da nishaɗi. Awanni kaɗan suka rage mata ta zama mata a wajen Labeeb. Burin ta zai cika, wataƙila auren Labeeb ne sakamakon ƙaddarar da ta ɗauka. 

Ta ɗan jima tana kallon kanta cike da annashuwa kafin ta fito Nabila ta tayata ta ƙarasa shiryawa. Simple ɗaurin ɗankwalin ta yi ta ɗora veil shi ma silver da ya sha stones tun daga saman kanta ya sakko har kan cikinta daga baya kuma ya sauka har ƙasa. 

Nabila ta sa Pin tana makale mata shi saman kanta yanda ba zai faɗi ba ko ya za ta motsa.

“Ma sha Allah Zulfa… Kin yi kyau wallahi. Ko me hassada ba mai iya kushewa. Amaryar El-Labeeb…”

Dariya Zulfa ta yi, ƙasan kunyar da ta rufeta akwai jin daɗin kiranta da sunan can da Nabila ta yi. Hotuna Nabila ta ɗauke ta sun kai kala goma kafin suka ji an ƙwanƙwasa ƙofar. 

“Shigo…”

Nabila ta fadi. Turo ƙofar Tayyab ya yi yana sauke idanuwanshi kan Zulfa. 

“Ma sha Allah…”

Ya faɗi yana rasa ko da me zai ɗora. Ƙarasawa ya yi yana kallonta da yadda ta yi kyau duk da ba ya iya ganin fuskarta sosai. Baisan me zai ce ba, sosai yake kewar Ummi da Sajda. Sosai yake jin rashin su da cewar ba za su ga yau ɗin ba. 

Sai dai ya san suna inda ya fiye musu wannan ranar sau dubbunai. Suna cikin hutu in sha Allah. Suna cikin daular da ba za ta misaltu da ta duniya ba. Sanin hakan bai rage mishi kewar su da yake ji ba. 

Runtsa idanuwanshi ya yi yana maida hawayen da ke son zubo mishi. Nabila ya kalla kafin ya miƙa mata wayarshi. 

“Don Allah ɗauke mu…”

Karɓar wayar ta yi, Zulfa kuma ta miƙe tsaye. Hannunta ta saka tana ɗage mayafin da yake rufe da ita ta buɗe fuskarta, sannan Nabila ta soma ɗaukar su hotuna. Suna cikin yi ne Mami ta shigo riƙe da Khateeb a hannunta. 

“Ga yarona ya haskaku… Don nasan babu wanda ya fishi yin kyau.”

Mami ta faɗi tana jan hannun Khateeb da ke sanye da fararen kaya ƙal na shadda, aikin jiki iri ɗaya da na Tayyab. 

“Mami ki taho kema… Duk da na san ko na yi kyau ba za ki faɗa ba.”

Dariya Khateeb ya yi yana faɗin, 

“Mami ai dai na fi su Yaya yin kyau ko?”

“Ya ma za ka haɗa? Ai ba yau ba kawai… Kullum ma ka fi su yin kyau.”

Dariya yake sosai yana kallon Tayyab da ya harare shi. 

“Yaro na fi ka hanci dai.”

“Mami ta ce nawa ya fi kyau… Ko da bai kai naka tsayi ba…”

Dariya Tayyab ya yi. 

“Nanuwa…”

Shagwaɓe fuska Khateeb ya yi. 

“Mami kin ganshi ko.. Wai hancina ne nanuwa…”

“Assalamu Alaikum…. Waye ya ce hancin Khateeb ne Nanuwa…”

Dawud ya faɗi. Da gudu Khateeb ya ruga yana maƙale Dawud ɗin cike da farin ciki. Yumna ma da sallama ta ƙaraso tana nufar wajen Mami suna gaisawa. Kafin ta kalli Zulfa da ke mata murmushi. 

“Ina kwana…”

“Amarya kin sha kyau.”

A kunyace Zulfa ta sadda kanta ƙasa. Su duka suka mayar da hankalin su kan Dawud da Khateeb da ke tsaye. 

“Don…Ina ta missing ɗinka… Dama ni bazan je da Yaya Tayyab ba… Wai hancina ne nanuwa…”

Dariya Dawud yayi. 

“Rabu da shi… Yanzun ba a yayin dogon hanci…shi bai sani bane ba.”

“Ku zo mu yi hoto lokaci na tafiya.”

Tayyab ya faɗi. Ƙarasawa cikin ɗakin Dawud ya yi da Khateeb. Nabila ta soma ɗaukar su huɗun tukunna ta yi musu tare da Mami, sannan da Yumna ɗin. Sai Dawud ya karɓi wayar yai musu da Nabila.

“Kun ga hotunan nan ya isa haka… Mai ɗauka zai zo anjima kaɗan. Khateeb zo mu tafi.”

Da gudu Khateeb ya kama hanya yana ficewa.

“Khateeb! Sai ka faɗi ko?”

Bai ma saurari Dawud ɗin ba don har ya fice. Sauke numfashi yayi, yana bin bayanshi da faɗin, 

“Mami sai mun dawo…”

“Allah ya dawo da ku lafiya”

Ta Faɗi ya amsa yana ficewa daga ɗakin, kunyar mami ya hanashi ce wa Yumna sai ya dawo. A ƙofa ya ci karo da Abba sanye da irin shaddar jikinsu shi ma. 

“Dawud…”

Abba ya faɗi. Kallon shi Dawud yake wani abu na matsewa a ƙirjinshi. Don har yanzun gani yake ko yaushe Abba zai sake kubce musu. 

“Ina kwana…”

Ya faɗi a sanyaye. 

“Lafiya ƙalau… Ya hidima?”

Ɗan ɗaga kafaɗarshi Dawud ya yi yana rasa ko me zai ce. Wani iri yake jinshi. 

“Kasan ko menene za ka iya faɗa min ko?”

Sai da ya sauke numfashi kafin ya ce 

“Ina kewar ummi ne… Na kuma kasa yarda zan aurar da Zulfa yau. Duka yaushe Zulfar ta girma Abba?

Kamar na yi saurin yanke hukunci…”

Dawud ya faɗi yana jin damuwar shi kan auren na tasowa. Duk wani shakku da yake da shi yana dawowa. Murmushi Abba ya yi cike da yana yi da dama. Yana kallon yadda girma ya kama Dawud.

Shi ya kamata ace yana cike da kokwanton nan. Shi ya kamata ya ji son kariyar nan akan Zulfa don shi ne mahaifinta. Amma Dawud ne yake bata wannan kulawar. Shi yake mata ƙaunar da ya kamata yai mata. 

“Ka huta haka Dawud… Don Allah ka huta da dukkan damuwar nan… Ina nan ka bari in tayaka ko yaya ne…”

Abba ya faɗi cikin sanyin murya. Girgiza mishi kai Dawud ya yi. 

“Bansan yadda zan huta da kula da su ba… Bansan yadda zan yi wata rayuwa banda kula da su ba Abba… Su ne dukkan rayuwata.”

Cike da tausayawa Abba yake kallon shi. Yana jin rashin Aisha har cikin ƙasusuwan shi. Ita ce ba ta rasa kalamai masu nutsuwa duk idan kana cikin yanayi na damuwa. Har tashi mutuwar ba zai daina jin ta Aisha ba. 

Musamman a yanayin da ta riske shi. Kanshi sadde ƙasa ya ce, 

“Har abada bazan daina roƙar ku yafiya ba Dawud.”

“Ka daina Abba… Kawai har abada karka barmu. Ban yi da na sani ba ba kuma zan taɓa yi ba. Rashin ku ya ƙara mana kusanci da ƙaunar juna. How about mu raba kula da su?”

Jinjina mishi kai Abba ya yi. Wayarshi Dawud ya zaro daga aljihu. Yana kallon Abban a ɗan daburce. 

“Zan ɗauke ka…”

Gyarawa Abba ya yi. Dawud ya ɗaga wayar yana jin yadda hoton shi ne na farko na Abba a wayarshi. Don haka ya ɗauke shi sun kai kala goma. Kafin ya matsa kusa yai musu selfie. Yana ganin yadda sosai ya yi kama da Khateeb. 

Bai ce wa Abba su tafi tare ba. Don baisan ko yana da wani plan ɗin ba. Ya wuce ya buɗe motar suka shiga shi da Khateeb. Can ƙasan zuciyarshi yana wa Ummi da sajda addu’ar samun rahma.

***** 

Mutane ne ko ta ina. Masallacin cike yake da Al’umma. Yawansu har mamaki ya ba wa Labeeb. Gaisawa kawai yake da mutane. Ya ma kasa samun damar ya wuce ciki kafin ya ga mutane na matsawa suna badai hanya. 

Tsayawa ya yi yana kallon ikon Allah don ya ga ko me ake buɗe wa hanya haka. Asad da Anees ya gani da sai da ya kula da askin da ke kansu tukunna ya gane su. Kayan da suka saka da komai iri ɗaya ne. 

Wani irin dokawa zuciyarshi ta yi da ya yi ƙasa da idanuwan shi ya ga Mamdud cikin wheelchair a zaune. Babu bandeji a hannun shi. Amma akwai a gefen kanshi da ƙafarshi da take nannaɗe. 

Ware idanuwa Labeeb ya yi cike da tashin hankali. 

“Innalillahi… Wane irin hauka kuka yi? In su basu da hankali Mamdud kai ma haka? Ina Zee Zee ta barka ka fito… What if ka fama ciwonka? Innalillahi…”

Ganin yadda ya rikice ne ya sa Mamdud da ke zaune yin murmushi. Har yanzun ya kasa daina mamakin kalar Labeeb. 

“Likita ya ce it’s okay in dai bazan taka ƙafar ba ko in motsa ta sosai… Bazan yi missing ɗin ɗaurin aurenka ba El-Maska. Ko da hakan na nufin menene…”

Goshin shi Labeeb ya ɗan dafe da yake jin zufa saboda yadda hankalin shi ya tashi. Bazai yafe wa kanshi ba in wani abu ya samu Mamdud saboda ya zo ɗaurin auren shi. 

“Babu abinda zai faru In sha Allah…”

“Hankalina zai fi kwanciya in na san kana asibiti ana kula da kai.”

“Daga nan Asibiti za su mayar da ni…”

Kallon su Asad dake tsaye suna murmushi ya yi. 

“Oh-oh yaya… Wallahi sai da na yi da su suka ƙi ji na. Na ce za ka yi faɗa basu yarda ba…”

Anees ya faɗi ganin yadda Labeeb ke kallonshi kamar zai kwaɗa mishi mari. Sauke numfashi yay, da kanshi ya ƙarasa ya kama wheelchair ɗin da Mamdud ɗin yake akai yana tura shi suka shiga ciki. 

Daddy ya bayar da auren zulfa kan sadaki dubu ɗari cif. Mamdud ya ɗan kalli Asad da ya fiddo kuɗin ya bayar kafin Abba ya samu ya fiddo. Don har ranshi ya yi niyyar biya wa Labeeb sadakin ba don zai iya biyanshi rabin karamcin abinda yai musu ba. 

Sai din a kyautata maka ka kwantata abu ne mai kyau. Kallon Mamdud Labeeb ya yi cike da wani yanayi. Yana jin kusan shi yai mishi auren Zulfa. Tunda lefe da sadaki gaba ɗaya daga aljihunshi suka fito. 

Kallon da ke fassara ‘Don Allah kar ka ce komai’ Mamdud yake wa Labeeb don ya ga alama jira kawai yake su fita daga wajen ya yi mishi magana. Suna nan ciki aka ɗaura auren Labeeb da Zulfa. 

Sai da aka yi musu hotuna tukunna Asad da Anees suka ja Mamdud don su mayar da shi asibiti. Ko ta kansu Labeeb bai bi ba saboda yawan jama’ar da ke zagaye da shi. 

***** 

Ƙarfe takwas na daren suka sa lokacin dinar su dama. Ba a wani ɓata lokaci ba. Duk da Labeeb agogon shi kawai yake dubawa yana kallon ƙofa yana jiran ya ga ta inda Zulfa za ta ɓullo. 

Kwanan shi biyu bai sata a idanuwanshi ba. Ko text ba suyi ba balle waya. Sosai yake jin kewarta musamman ma yanzun da yake jin wani abu dabaisan ko mene ne ba ya canza a zuciyarshi tunda aka shafa Fatihar auren su. 

Tsalle zuciyarshi ta yi tana dokawa da yanayin da yake ji har cikin kunnuwanshi da idanuwanshi da ke kallon zulfa da Dawud ya riƙo hannunta cikin wata irin doguwar riga light pink. 

Sai da Labeeb ya sa hannu ya dafe ƙirjinshi don gani yake kamar zuciyarshi za ta iya fitowa a kowanne lokaci. Gani ya yi wajen ya ƙara nisa, kamar sun ƙi ƙarasowa da wuri. 

Da dukkan ƙarfin da yake ji a jikinshi ya yi amfani wajen danne zuciyarshi da ihun da take mishi na ya tashi ya karasa ya taho da Zulfa ɗin da kanshi. Har wani haske na ban mamaki ya ga ta ƙara yi mishi. 

Ƙamshin bakin turarukan dake jikinta ya cika mishi hanci da Dawud ya ƙaraso da ita ya zaunar a gefenshi. Ya kasa ɗauke idanuwanshi daga kanta duk da har lokacin ta ƙi yarda su haɗa idanuwa. 

Yana jin Asad da shi ne MC a wajen yana surutun da baya fahimta don nutsuwar shi na tare da zulfa. Hannu ya kai yana kama nata cikin nashi da yake ɗauke da ƙunshin jan da baƙin lalle da ya yi mishi kyau sosai. 

“Zulfaa…”

Ya ja sunanta da wani yanayi da ba ta taɓa jin ya kira ba. Ba ta san me take ji ba tun ɗazu da ta san an ɗaura aurenta da Labeeb. Dukkan mafarkinta ne ya zamo gaskiya. Ta kuma rasa yadda za ta yi da gaskiyar yanzun. 

Zuciyarta ta ƙi ta nutsu waje ɗaya saboda emotions da suka mata yawa kamar za su zubo. Ganin ta ƙi kallonshi duk da abinda yake so ne yasa shi murza yatsunta cikin hannunshi yana matsar da kanshi saitin kunnenta. 

“Na yi missing ɗin ki… Ko ɗan text ɗin ma ba ki min ba.”

Muryarta a dishe ta ce, 

“Muna ta hidima ne shi ya sa.”

Har lokacin ba ta kalle shi ba. Bai ce komai ba ya gyara zamanshi yana riƙe da hannunta. Baisan me yasa maganarta ta sosa mishi rai ba. Hidimar ta ta fi kiranshin da za ta yi. Ba ta da mintina biyu da za ta ware ko da text ta yi mishi. 

Hannunshi ya ji ta matse cikin nata da yanayin ban hakuri, numfashi kawai ya sauke yana maida hankalin shi kan abinda ake. Ba wani daɗewa suka yi ba. Ƙarfe goma suka gama komai. 

Kamar yadda Dawud ya kamo hannun zulfa haka ya sake kama hannunta ya sa ta mota suka tafi ba don zuciyar Labeeb ta so ba. Bai san me yasa za a ce sai gobe ba. Da baƙon yanayi a tare da shi ya shiga mota ya nufi gida shi ma. 

<< Rayuwarmu 45Rayuwarmu 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.