Yana fitowa ya kama hannun Zulfa suka koma sama. Hular da ke kanshi ya cire ya ajiye, kafin ya cire babbar rigar baƙar shaddarshi ya ajiyeta a gefen gadon, yana kwance agogon da ke hannunshi ne ya kalli zulfa
“Kin yi Isha’i?”
Kai ta girgiza mishi. Don ba ta yi ba suka fito.
“Zo ki yi alwala mu yi to… Nima ban yi ba.”
Veil ɗin kanta ta fara cirewa ta ajiye. Sai dai rigar dake jikinta ta yi nauyi sosai. Cikin sanyin murya ba tare da ta kalle shi ba ta ce,
“Sai na sake kaya. Bazan iya sallah da rigar nan ba.”
Kai ya ɗan ɗaga mata yana wucewa ya zira takalmanshi da faɗin,
“Bari in yi alwala in dawo to.”
Kafin ta amsa shi ya fice daga ɗakin. Ba ta ga alamar safe ko wardrobe ba don haka ta tura ɗayar ƙofar da ta gani bayan ta banɗakin da ke cikin bedroom ɗin. Ƙaramin ɗakin kaya ne, shiga ta yi ta buɗe wajen ajiye kayan, komai a shirye yake.
Riga da zani ta ɗauko, ɗinkin very simple har zanin ma ba mai style bane ba ta saka, sai take jinta wani sakayau da ta sake rigar nan, duddubawa ta yi ta ɗauko hijab ta fito, tana shiga banɗakin ta ji shigowar Labeeb ɗakin.
Alwala ta yi ta fito, tana jin yadda yake kallonta, tsayawa a gabanshi babu lulluɓi ba baƙon ta ba ne ba, amma yau wani iri hakan yake saka ta ji. Jan su sallah ya yi Isha’i tukunna suka yi nafila. Ya jima zaune yana addu’o’i kafin ya miƙe ya ɗauko ledar da ya shigo da ita.
Buɗe musu ya yi, ba ma wani da yawa suka ci kazar ba, don ma Zulfa na ɗan jin yunwa, tun abincin da Mami ta tsare ta ta ci da rana rabon cikinta da wani abu. Har suka gama ya ɗauke ya fita da kayan ya dawo babu abinda suka ce.
Yau sun zama kurame. A karo na farko sun rasa abinda za su ce wa junansu. Miƙewa Labeeb ya yi ya fita daga ɗakin , ganin ya fi mintina goma sha biyar bai dawo ba ya sa ta miƙewa ta cire hijabin ta ninke ta ajiye ta nan kan kafet ɗin.
Hawan gadon ta yi ta kwanta, ta kai hannu ta kashe fitilar ɗakin. Har lokacin Labeeb bai dawo ba. Tasan tausayin ta ya sa shi aurenta, ta san ba ta zo mishi da abinda kowace mace ke zuwa da shi gidan mijinta ba, ta san rayuwarta ta samu naƙasa. Ba ta sa a ranta za ta samu kulawa da ƙaunar da kowa ke samu a daren shi na farko a gidan miji ba.
Sai dai ba ta zaci ko sai da safe ba za ta samu a wajen Labeeb ba, bargo ta ja ta rufe jikinta, hawaye nabin fuskarta. Wani irin ɗaci na lulluɓe mata zuciya, runtse idanuwanta ta yi sai dai babu abinda take gani sai abinda take son mantawa.
Sai abinda tai zaton Labeeb zai taimaka mata ta manta. Dunƙule jikinta ta yi tana wani irin kuka mai cin rai, sam ba ta ji turo ƙofar da Labeeb ya yi ba, zuciyarta da tunaninta na wani wajen daban. Har ya hawo kan gadon, kuka kawai take.
Hannun da ta ji a jikinta ne ya sa ta firgita sosai saboda abinda take tunani, kuka ta saki tana ture shi da dukkan ƙarfinta, da sauri ya kunna fitilar ɗakin yana riƙota dam.
“Ni ne Zulfa… Ni ne…”
Yake faɗi yana jijjigata, da ƙyar ta buɗe idanuwanta ta kalli fuskarshi, ƙanƙame shi ta yi tana wani irin kuka mai cin rai, ya lumshe idanuwanshi yana jin ciwon yanayin da take ciki.
“Na ɗauka ba za ka dawo ba Yaya Labeeb…”
Cike da rashin fahimta ya ce,
“Saboda me zan ƙi dawowa? Wanka na yi na sake kaya.”
Sake ɓoye kanta ta yi a jikinshi tana tsananta kukanta maimakon amsa tambayar da yai mata. Ɗago ta ya yi daga jikinshi yana kallon fuskarta.
“Saboda me za ki yi wannan tunanin?”
Hawaye na zubar mata ta ce,
“Saboda komai… Saboda banda abinda zan baka…”
Sai lokacin ya fahimci abinda take nufi, ba kuma ƙaramin ɓata mishi rai hakan ya yi ba. Da yasan fitarshi za ta sa wannan shirmen zuwa kanta da ya yi wankan a nan.
“Wane hauka ne wannan? Bana son tunanin nan…”
Girgiza mishi kai take yi.
“Kar ka fara…kar ka fara faɗa min abinda bai fito daga zuciyarka ba.”
Buɗe baki ya yi zai sake magana ta shiga girgiza mishi kai. Sam ta ƙi bari ta saurare shi balle ya samu wannan shirmen tunanin ya fita daga kanta. Rasa abinda zai yi ne yasa shi riƙota yana sumbatarta.
Zuciyarshi na dokawa ta fannin da ya kasa fahimta tun da aka ɗaura musu aure. Yanzun kam jinshi yake kamar ya yi tafiya mai nisa, kamar ya daɗe yana yawo yana neman inda zai je ya rasa. Sai yanzun… A tare da ita ya iso inda yake nema. Tare da ita ya ƙaraso gida.
Ita kanta Zulfa ware idanuwa ta yi cikin mamaki take kallon shi, zuciyarta na barazar yin tsalle ta bar ƙirjinta, jan bakinta yake ji kan laɓɓanshi har lokacin. Wani irin kallo yake mata da ta kasa fahimta. Ko mene ne take gani cikin idanuwanshi ya kashe mata jiki.
Sake sumbatarta ya yi yana son tabbatar da abinda yake ji. Kafin ya ɗago cikin mamaki ya ce,
“Ina son ki!”
Ya saba faɗa mata, amma yau yanayi da ma’anar kalaman daban ne. Duk lokacin nan, duk shekarun nan, duk lokutan da yake ji kamar akwai ɓangaren da yake nema ya zama complete ya rasa sai yau ya gane. Muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce,
“Na sani…”
Girgiza mata kai ya yi. Ba wannan yake nufi ba, sai dai ya rasa kalaman da zai yi amfani da su ta gane exact abinda yake ji a yanzun. Komai taso mishi yake lokaci ɗaya, komai da ya jima yana ginuwa a zuciyarshi ne ya zaɓi ya fito yau. Sumbar ta farkar da yanayoyin da baisan suna kwance a jikinshi ba.
Baya jin an halitta kalaman da zai iya amfani da su don bayyana yanayin da yake ji. Zuciyarshi na dokawa, komai ya birkice mishi da yanayin da bai da fassara. Bai taɓa zaton akwai yiwuwar hakan ba, a ce mutum ɗaya ya ji yanayoyi da dama lokaci ɗaya haka ba sai yau.
Idanuwanta da ke kanshi cike da shakku, rashin fahimta da alamar tambaya basu yi komai ba sai tunzura yanayin da yake ji da son nuna mata ko me yake nufi, da son sa ta ji abinda yake ji. Sumbatarta ya sake yi yana kai hannu ya kashe fitilar ɗakin.
Farkon daren da zai canza musu komai, farkon dare cikin dararen da za su rayu su canza tare da junansu. Dare cikin dararen da ke kai su da duk wani ɗan Adam kusa da makwancin shi.
****
A hankali ta lallaɓa ta hau kan gadon, ta ja mayafi zata rufe jikinta.
“Kin fito?”
Dawud ya faɗi yana gyara kwanciyar shi. Runtsa idanuwa Yumna ta yi sannan ta kwanta tana gyara abin rufar.
“Duk yadda nake lallaɓawa sai da ka tashi. “
“Kina buɗe ƙofar toilet na tashi.”
Hannu takai tana wasa da yatsunta kan fuskarshi.
“Na gaji sosai. Jikina ciwo yake.”
“In haɗa maka ruwa mai ɗumi sosai ka yi wanka?”
Girgiza mata kai ya yi, yadda jikinshi ke ciwon nan ko motsin kirki baya son yi balle har ya tashi ya yi wani wanka.
“Ka yi bacci to.”
Ɗan murmushi ya yi mata. Duk yadda yake jin gajiyar nan in tana kusa da shi, in yana jin motsinta ba zai iya bacci ba. Janyota ya yi jikinshi sosai yana lumshe idanuwanshi.
“Zan yi…”
Ya faɗi cikin kunnenta a hankali. Shiru ta yi don ba ta son ta cika shi da surutu, har ya yi addu’a ya tofa musu. Ita ba ta jin bacci ko kaɗan, ba ta son barinshi shi kaɗai da kallo za ta yi abinta. Ko ya ta ɗago kanta sai ta sauke idanuwanta cikin nashi.
Zamewa ta yi daga jikinshi ta kai hannu ta kashe musu fitilar ɗakin don tana ganin ko hasken ne ya hana shi bacci, tukunna ta dawo ta kwanta a jikinshi. Ba ta san lokacin da bacci ya ɗauketa ba.
Farkawa ta yi ta ware idanuwanta cikin na Dawud da ya gyara mata kwanciya a jikinshi.
“Ba ka yi bacci ba?”
Ta tambaya tana murza idanuwanta da hannu.
“Shhh… Ki koma bacci.”
Ya faɗi don kanshi da ke ciwo kamary zai fado. Ya kuma san rashin bacci ne da gajiya da suka tarar mishi. Hannu Yumna ta sa tana taɓa jikinshi ta ji lafiyar shi ƙalau. Tashi ta yi zaune ta lalubo switch ta kunna fitilar ɗakin.
“Yumnaa…”
Tsare shi ta yi da idanuwanta.
“In wani abu ne yake damun ka ina son sani…”
Sauke numfashi ya yi, in zamansu zai ci gaba da kasancewa dole ne ya koyi faɗa mata matsalolin shi, duk da hakan ba ƙaramin abu bane a wajen shi, bai saba ba. Ya saba da ya ji matsaloli, nashi ya bari a cikinshi.
“Ina son jin damuwar ka…ba ka bari na. Ko bazan iya komai akai ba zan maka addu’a…”
Hannunta ya riƙo yana haɗe yatsun su waje ɗaya, ya kalleta cikin fuska.
“Baƙon abu ne a wajena. Faɗin damuwa ta…”
Zame yatsunta ta yi daga cikin nashi idanuwanta cike taf da hawaye. Ta koma ta kwanta tana juya mishi baya. Hawayenta na zubowa masu ɗumi ta gefen fuskarta. Ta ɗauka da suka yi aure hakan zai canza a tare da shi.
Amma ba ta ga alamu ba, ya mata komai a lokacin da take buƙatar kulawarshi, yanzun hakan tana buƙata, amma tana so ko yaya ne ya barta itama ta kula da shi. Ta ji damuwar shi.
“Yumna…”
Ya kirata. Ƙoƙarin shanye kukan da take yi ta yi kafin cikin rawar murya ta ce
“Na.. Na’am.”
Ba shiri ya kai hannunshi ya juyo da ita ta fuskance shi, ware idanuwa ya yi yana janta ƙirjinshi ganin hawayen da ya biyo fuskarta. Ciwon kanshi na ƙaruwa
“Ban damu ba da… Ban damu da ɓoye min matsalolinka da kake yi ba don na ɗauka hakan zai canza idan mun yi aure…”
“Bana iya bacci da wani a kusa da ni…shi ya sa nake yi da safe.”
Ya faɗi da sauri yana katse mata maganar da take yi. Zamewa ta yi don ta kalli fuskarshi sosai. Da wani nisantaccen yanayi ya ci gaba da magana.
“Tun barin mu gida na fara haka. Sai rasuwar Ummi… Ga Khateeb….Ga Sajda. Ina jin tsoro… Ina ganin kamar da na rufe idanuwana wani abun zai same ni babu wanda zai kula da su. Kamar in na yi bacci wani abu zai same su su ma.
Har suka girma… Har Sajda ta bar mu itama… Tayyab ba sosai yake iya bacci shi kaɗai ba. Abinda ya faru duk ya taɓa mu, har muka dawo wajen Abba… Duk idan ya shigo ɗakina in ya kasa bacci ni na gama yin nawa.
Ina da matsala Yumna… Ba rashin bacci a kusa da wani bane kawai… Zan yi ƙoƙari in wani abu na damuna in faɗa miki… Amma ban yi alƙawarin ko da yaushe ba…”
Tashi ta yi zaune ta goge fuskarta, zuciyarta ta mata nauyi da maganganun shi ba kaɗan ba. Ta rasa ko me za ta ce ko tai mishi, don haka ta kai fuskarta ta sumbace shi kafin ta riƙo hannunshi cikin nata.
“Babu abinda zai same ka ko ni In sha Allah… Yau ka kwanta….ni zan zauna har ka yi bacci.”
Murmushi yayi yana ɗaga mata girarshi duka biyun.
“Ka rufe idanuwanka. Ka yi tunanin abinda ke sa ka nutsuwa…kar ka ji komai akaina da nake kusa da kai banda son da kake min…”
Magana zai yi ta rufe mishi baki da yatsanta.
“Yau kawai….in bai yi ba za mu gwada wani abun daban.”
Janta ya yi ta kwanta. Wannan karon shi ya kashe musu fitilar.
“Ko da zan yi baccin tunanin kina zaune ke ba zai barni na samu nutsuwa ba.”
“To ka yi yadda nace…kar kai tunanin komai banda abinda yake sa ka nutsuwa…”
Gyara kwanciyarta ta yi a jikinshi, tana jin yadda ya riƙeta gam kamar zai mayar da ita cikinshi. Wani irin numfashi yake ja yana fitar da shi kamar mai son ɗanɗanawa ya ji ko iskar daidai take. Zuciyarshi yake dubawa, abinda ya fi komai saka shi nutsuwa Yumna ce.
Babu abinda yake samun nutsuwa da shi irin wannan sai in ya kafa goshin shi a ƙasa yana sujud, sai kuma in yana jin karatun Ƙur’ani. Nutsuwar ta daban ce, numfashi ya ja mai nauyi ya fitar da shi a hankali kafin ya soma karatun Ƙur’ani a cikin zuciyarshi.
Yana buɗe kanshi ya cire tunanin komai banda son fahimtar abinda yake karantawa a cikin zuciyarshi, yana sake riƙe Yumna dam a jikinshi. Baisan lokacin da ya ɗauka yana hakan ba, har bacci ya ɗauke shi.
Bai tashi ba sai da aka soma kiran sallar Subhi. Miƙewa ya yi ya sumbaci Yumna a goshi kafin ya sauka daga kan gadon fuskarshi ɗauke da murmushi, canji ya sake samunshi. Wannan karon ma ta hanya mai kyau.
Sai da ya yo Alwala ya saka jallabiya zai fita masallaci tukunna ya tashi Yumna. Ko da ya yo Sallah ya dawo tana zaune tana azkar ɗin safe, Ƙur’an ya ɗauko ya zauna a gefenta. Da ta idar ba ta tashi ba, gyara zamanta ta yi ta jingina kanta da kafaɗar Dawud ɗin.
Har gari ya soma wayewa tukunna ya tashi ya shiga wanka. Yana fitowa ta kalle shi cikin sanyin murya ta gaishe da shi.
“Ya kika tashi?”
“Alhamdulillah… Ya ciwon jikin?”
“Dama gajiya ce fa… Na gode.”
Yamutsa fuska ta yi cike da rashin fahimtar godiyar.
“Da jiya… Na yi bacci a kusa da ke.”
Dariya ta yi.
“Allah ya sa ya ɗore.”
Ya amsa da amin. Tukunna ta miƙe ita ma ta shiga wanka. Sa’adda ta fito ba ya ɗakin, shiryawa ta yi cikin riga da skirt na material tukunna ta fita falon. Ba ta ga Dawud ba, kitchen ta shiga yana ciki. Murmushi ta yi kawai ta ƙarasa ta ɗauko wata wuƙar ta ɗauki doyar da yake ferewa tana yayyankawa ita kuma.
Tare suka yi aikin duk da ba hira suke ba, ta saba da shirun shi. Ba sai ya yi magana za ta ji yadda yake sonta ba, a duk mintinan da za su wuce cikin nuna mata yadda yake sonta yake yi. Tare suka gama haɗa komai, suka zubo suka fito.
Suna gama ci ta kwashe komai ta kai kitchen ɗin ta dawo, tana zama ana soma doka gidan su kamar za a karya ƙofar. Da sauri Dawud ya ƙarasa yana faɗin,
“Ana zuwa… Waye?”
Don zuciyarshi dokawa take kamar za ta faɗo daga ƙirjinshi. Buɗe kofar ya yi jikinshi na ɓari, sauke numfashi ya yi ganin baban Yumna da matarshi Asiya. Duk da kallo ɗaya za ka yi musu su duka biyun kasan ba cikin hayyacin su suke ba.
“Ina Yumna?”
Baba ya tambaya yana tsare Dawud da idanuwa, da sai lokacin ya kula da Tayyab da ya ƙaraso. Ɗan ware idanuwa Tayyab ya yi yana ɗaga wa Dawud kafaɗa dayke fassara ‘Ni ma bansan me ke faruwa ba, yadda ka gansu haka na gansu.’
Ɗan jinjina mishi kai Dawud ya yi yana tsayar da hankalinshi kan Asiya da fuskarta take a kumbure. Sam bai yarda da ita ba, zuciyarshi ma ba ta sonta kusa da Yumna, don haka ya ƙara kare ƙofar yana ɗaure fuska tamau.
Rau-rau Asiya ta yi da idanuwa ƙwalla na zubar mata.
“Babu abinda ya kawoni sai alkhairi, don Allah ka barni in ganta…akwai kokwanton samun alkhairi a lahira ta in har ban ganta ba…”
Baba Dawud ya kalla.
“Don Allah tana ina…”
Ya sake tambaya da wani yanayi a muryarshi da Dawud ya kasa gane ma’anarshi. Sam shi kam bai yarda da Asiya ba, ya dai san babu wanda ya isa ya tako ƙafarshi ya taɓa mishi mata ya fita lafiya ƙalau.
Don haka ya matsa yana basu waje don su shiga ba tare da ya ce komai ba. Hannu Tayyab ya ɗaga yana wa Dawud alama da cewar za su yi waya. Kai ya ɗaga wa Tayyab ya tura gidan yana juyawa.
Yumna da take tsaye tana son sanin meke faruwa ta ga shigowar babansu da Asiya sai da zuciyarta tai wani irin dokawa saboda tashin hankali. Tunanin farko da ya fara zuwa mata shi ne Asiya ta kitsa wani abin da zai tunzuro Baba ya zo ya ɗaga musu hankali.
Ita kam ba za ta iya barin mijinta ba, tunda ya shigo rayuwarta komai ya soma daidaita. Tun da ta tako ƙafarta gidanshi tai bankwana da tashin hankali. Jiya-jiyan nan Dawud ya ɗan samu daidaito a wani fanni na rayuwar shi.
Tana tsoron abinda zai sake ɗaga mishi hankali. Baba kuwa Yumna yake kallo, tilon ‘yarshi ɗaya a duniya. Yana tuna farin cikin da ya shiga ranar da ya fara riƙeta a hannunshi. Yana tuna farin cikin da ya samu tare da mahaifiyarta kafin mutuwa ta raba su.
Kafin rashinta ya ba Asiya damar shigowa rayuwar su har ta yi nasarar saka mishi tsanar ‘yarshi. Juyawa ya yi ya kalli Asiya yana jin kamar ya haɗa mata kai da bango. Sannan ya ƙara juyawa ya kalli Yumna. Muryarshi na sarƙewa yake faɗin,
“Me zan ce miki bayan na kasa sauke haƙƙina a kanki? Da wanne baki zan soma roƙar yafiyar ki?”
Kallon Baba take tana jin iskar ɗakin na barazanar yi mata kaɗan. Tana jin kamar mafarki take da abinda zai yi wuya ya faru.
“Ki yafe min Yumna…”
Jikinta ko ina ɓari yake, ƙafafuwanta sun mata wani irin nauyi, hawaye na cika mata idanuwa. Da ƙyar ta cira ƙafarta ta taka tana ƙarasawa inda yake tsaye.
“Baba…”
Ta kirashi cike da shakku. Sai da ya haɗiye abinda yake tsaye a maƙoshin shi tukunna ya ce,
“Yumna… Ki yafe min.”
Faɗawa ta yi jikinshi tana ƙanƙameshi tare da rushewa da wani irin kuka da ba ta san daga inda ya fito ba, riƙeta ya yi yana jin yadda zuciyarshi ke soyuwa da rashin kulawar da bai bata ba na shekaru, yana jin ɗacin abinda ya rasa tare da ‘yarshi da ba zai taɓa dawowa ba.
Sosai Yumna take kuka tana gode wa Allah. Sun jima a haka kafin ta zame jikinta daga na Baba tana goge fuskarta.
“Baba ban taɓa riƙe ka a zuciya ba… Kullum addu’ata ka dawo gare ni… Fatana ka sa min albarka a aurena kamar kowacce ‘ya…”
Kai Baba yake ɗaga mata, kafin ya juya wajen Asiya.
“Ba sai na nemi Allah ya saka min abubuwan da kika yi min ba… Don da zuciya ɗaya na aureki na kawoki gidana cike da amana… Ba tare da na san burinki shi ne ki tarwatsa min farin ciki ba.
Na sake ki saki ɗaya!”
Cikin tashin hankali Asiya ta juyo tana kallon Baba kafin ta tsugunna ta riƙe ƙafafuwanshi tana sakin wani gunjin kuka. Gaba ɗaya rayuwarta a hargitse take. Allah ne ya so ta da rahma shi Ya sa ta yi mafarkin mutuwarta.
Allah ne Ya sa tana da rabon rahma shi Ya sa tai mafarkin mutuwarta da bala’in kwanciyar kabarin da babu rahmar Allah ko ɗaya. Ya sa ta tun cikin dare ta tashi ba tare da ɓata lokaci ba ta faɗa wa Baba komai da yake faruwa ta roƙi gafararshi.
Tun jiya take cikin wani irin matsanancin tsoro, don ko ƙara runtsawa basu yi ba, da ƙyar suka lalubo gidan su Dawud daga can aka rako su nan ɗin. Gani take ko yaushe mutuwa za ta iya riskarta. Cikin kuka take faɗin,
“Don Allah… Don Allah ka yafe min…yu… Yumna na cutar da ke… Ki yafe min don Allah… Kar mutuwa ta riskeni da haƙƙin ku akaina… Bansan ya zan kwanta a kabarina da haƙƙin ku ba….bansan ya zan kalli Ubangiji da tarun zunubaina ba.
Ban cancanci zaman aure da kai ba na sani… Ban kuma ga laifinka na zaɓar rabuwa da ni ba… Amma don Allah ka yafe min… Ku yafe min.”
Gaba ɗaya jikin Yumna ya yi sanyi. Maganganun Asiya sun sa ta ƙara tsorata da lamarin duniya. Hawayen da suka zubo mata ta goge.
“Baba ka yafe mata don Allah…wallahi ni na yafe mata. Ka mayar da ita ɗakinta… Allah na son masu yafiya…”
Girgiza kai Baba ya yi don ko ganin Asiya baya son yi.
“Me yasa za ki yarda da tubanta?”
“Banda tabbas akan tubanta…yafiya ta nake da tabbas akai Baba… Tsakanin ta da Ubangiji ne… Da niyyar da ke zuciyarta. Duka duniyar ba mai yawa bace… Burina ka dawo gareni dama… In har hakan ba zai canza ba… Ka mayar da ita don Allah…”
Ta ƙarasa wasu hawayen na zubo mata. Girgiza kanshi ya sake yi.
“Bana son ganinta… Ta je in huta tukunna… Ta fita.”
Ɗago ta Yumna ta yi ta kalli Dawud, wucewa ya yi bedroom ya shiga ya fito, dubu uku ya miƙa wa Yumna ta karɓa ta ba wa Asiya da ke wani irin kuka don ta yi kuɗin mota, ta kamata tana rakata har ƙofa.
“In sha Allah komai zai daidaita. Ki ba shi lokaci ya huce…”
Kai kawai Asiya ta iya ɗaga mata kafin ta fice zuciyarta cike da ɗumbin da na sani. Sannan ta dawo.
“Baba ka zauna…”
Girgiza mata kai ya yi. Sai lokacin Dawud ya saka musu baki.
“Baba ka zauna ko ruwa ka sha.”
Waje ya samu ya zauna, da sauri Yumna ta wuce kitchen ta ɗauko ruwa da kofi ta zo ta zuba ta ba shi ya sha. Ya fi mintina biyar ya dafe kanshi yana maida numfashi kafin ya ɗago ya kalli Dawud.
“Na gode da yadda duk abubuwan da suka faru ba su sa ka gaza ba wajen ganin ka aure ta ka fitar da ita daga wahalar da take ciki.
Ka yi haƙuri da duk abubuwan da suka faru, Allah ya sanya muku albarka a aurenku.”
Murmushi Dawud yayi, Komai ya yi farko zai yi ƙarshe. Komai kuma yana da lokaci. Cikin sanyin murya ya amsa da amin. Kafin Baba ya miƙe, ya sumbaci Yumna a goshi ya sake ba ta haƙuri tukunna suka raka shi har harabar gidan ya shiga motar shi ya fita sannan suka dawo.
“Na kasa yarda Baba ne ya zo gidan mu… Na kasa yarda Mami ce take roƙon gafara ta.”
Yumna ta faɗi tana kwantar da kanta a kafaɗar Dawud tare da ƙara dumtse hannunshi da ke cikin nata.
“Haka rayuwa take kullum… Cike da sabbin shafuka da abin mamaki kala-kala. Komai na da lokaci… Ina alfahari da ke da yadda kika yafe mata babu tunanin komai.”
Murmushi ta yi.
“A cikin soyayyar ka na koyi abubuwa da yawa…ciki har da yafiya da yarda da ƙaddara.”
Sumbatar gefen fuskarta ya yi yana yin shiru, ba shi da abinda zai ce da ya wuce hamdala. Abu ɗaya ne ya rage mishi yanzun. Kuma anjima zai samu Tayyab su yi magana ya ji ko me zaice.
****
Ya kasa bacci, ko runtsa idanuwanshi ya ƙi yi. Zulfa kawai da ke bacci akan ƙirjinshi yake kallo. Zuciyarshi na yawo a ko ina na jikinshi da wani yanayi mai wahalar fassarawa. Bai taɓa kawo wa ranshi ƙin son ko wanne namiji a kusa da Zulfa kishi ba ne.
Ko da wasa bai taɓa tunanin zazzaɓin da yakan ji in sun yi faɗa ba sa magana wata irin ƙauna bace sai a daren nan. Bai taɓa sanin yana dakon soyayarta ta wannan fannin ba sai yau. Bai taɓa tunanin zuciya za ta iya cika da soyayya mai yawan wannan ba sai da ya ji ta Zulfa.
Sumbatar goshinta ya yi yana jin kamar ya mayar da ita cikin fatar jikinshi. Abinda yake ji akanta ya mishi yawa, kuma ba ya son tashin ta don ba ta daɗe da yin bacci ba. Da ya rasata bai san yadda zai yi ba.
Da wani ya aure ta ba shi ba….kasa ƙarasa tunanin ya yi don ba shi da wata kalma da zai ɗora yanayin zafin da zuciyarshi ta yi da tunanin wani ya aure ta ba shi din ba. ‘Mamdud…’ zuciyarshi ta faɗa da sauri ya zame jikinshi daga na Zulfa ya miƙe ya nufi toilet.
Runtse idanuwanshi ya yi yana buɗe hotunan Zulfa da yanayinta kala daban-daban. Ƙarshen abinda zai bar zuciyarshi ta yi shi ne tunanin abinda ya wuce, tunanin abinda ba zai taɓa goguwa ko ya canzu ba. Ƙaddara ce mai ciwon gaske, zai mantar da Zulfa, ko da ba gabak dayae ba ne ba, zai disar mata da tabon ƙaddararta.
Mamdud ɗan uwanshi ne, abokin shi ne, ba zai bari kishi da shaiɗan su samu ɗarsa mishi abinda zai dame shi ba. Wanka ya yi tukunna ya ɗaura alwala ya fito. Wayarshi ya ɗauka ya duba agogo, biyu da rabi na dare.
Lambar Ateefa ya lalubo da nufin ya kirata, wata zuciyar ta ce mishi in kuma ta samu bacci fa? Ba ya so ya tashe ta, duk yadda zuciyarshi take son sanin ya lafiyarta take. Ya san kishinta, ya san halinta.
Kayan shi ya ɗauka ya saka tukunna ya soma jero salloli har wajen ƙarfe huɗu. Ya san in ya kwanta da wuyar gaske ya iya tashi sallar asuba. Don haka ya yi zamanshi a wajen ya buɗe wayarshi yana kallon hotunan da ke ciki.
Har ya zo kan na bikin Zainab, murmushin da ke fuskarshi ya ɓace da ya tsaida idanuwanshi kan hotonsu da Arif, bai ma san an ɗauka ba, don ya juya yana daƙuna wa Arif ɗin fuska saboda yadda ya ruƙunƙume shi kamar zai kayar da shi.
Kamar ya rufe idanuwanshi ya koma lokacin yake ji, zuƙo hoton ya yi daidai fuskar Arif ya kawo wayar bakin shi yana sumbatar hoton, sam ba ka sanin darajar hotuna sai sun zama shi ne kawai abinda kake da su tattare da wanda ka yi rayuwa da shi, ka kwashe shekaru kana ƙauna, zuciyarka ta saba.
Sai ka so ganin mutumin nan kamar ka ba da duk abinda ka mallaka ka samu ko da mintina biyar ne tare da shi, sai lokacin za ka san muhimmancin hotunan da su kaɗai suka rage maka. Ci gaba ya yi da kallon hotunan da wani yanayi mai nauyi a zuciyarshi.
Yana wa Arif ɗin addu’a, kafin ya sake tsayawa kan wani hoto da Arif ɗin ke sanye da uniform, bayanshi goye da jakar makarantar da ya saƙalo hannunshi jikin mariƙin yana dariya. Sai lokacin ya yi murmushi
“Na yi kewar ka sosai… Ba mu shirya ba ka barmu… Haka mu ma za mu biyo ka babu shiri ko Arif?”
Duk da bai tsammaci amsa ba, shirun ya mishi wani iri. Yana nan zaune zuciyarshi cike da tunani kala-kala, jikinshi ya yi sanyi da lamarin rayuwa har aka kira sallar Asuba. Ba zai iya fita masallaci ba. Don haka ya yi sallar shi a nan.
Zulfa kamar cikin kunnenta aka kira sallar. A hankali ta buɗe idanuwanta, zuciyarta manne da sanin inda take kwance ɗin, hannu ta ɗora inda Labeeb ya tashi tana jero hamdala cikin zuciyarta.
“Ina sonki!”
Zuciyarta ta tuno mata kalaman Labeeb da ta sha su jiya kala-kala, jikinta na amsawa da wani irin yanayi. Kamar a mafarki haka take jin komai, sai da ta miƙe daga kwanciyar da take tukunna ta soma gasgata abinda ya faru.
Da ƙarfin hali ta matsa tana dafa gadon ta miƙe, juyawa ta yi ta ga Labeeb na Sallah, da sauri ta shige banɗaki. Wanka ta samu ta yi tare da yin alwala tukunna ta fito ɗaure da towel. Lokacin Labeeb har ya idar da sallah.
Yana juyowa suna haɗa idanuwa, sauke nata ta yi wata irin kunya da ba ta taɓa ji ba a rayuwa ta lulluɓe ta, da ƙyar ta wuce ɗakin sake kaya, ta ɗauko riga da skirt na atamfa ta saka sannan ta fito. Ganin in ta tsaya shafa mai lokaci na tafiya ne ya sa ta ɗaukar hijabinta ta raɓa gefen Labeeb ta yi Sallah.
Idanuwanshi na kafe kanta har ta idar. Abinda yake ji a kanta na ƙaruwa da duk shaƙar numfashin da zai yi. Ya rasa inda zai sa zuciyarshi ko za ta samu hutu, emotions sun tarar mishi lokaci ɗaya. Ajiyar zuciya ya sauke da ya sa Zulfa juyowa ta kalle shi.
“Me nake yi tuntuni?”
Yai tambayi kanshi fiye da yadda ya tambayeta. Me yake tuntuni bai gane komai da yake ji akan Zulfa ya wuce son ‘yanuwanta ka ba? Sai yanzun komai ya taso mishi lokaci ɗaya yana son kwantar da shi saboda yawan da ya yi.
“Ina son ki…”
Ya faɗi yana kallon fuskarta. Yana son ganin ko nata son daban yake da nashi. Ta karanci hakan, gyara zamanta ta yi, tana yakice kunyarshi gefe ɗaya, menene bai sani tattare da ita ba yanzun? Sosai ta kalle shi cikin fuska.
“Ina son ka nima.”
Ta Faɗi muryarta na rawa da yanayin sonshi da take ji. Tana son shi fiye da yadda kalaman za su taɓa fassarawa. Dab da ita ya matsa tana jin hucin numfashin shi akan fuskarta. Kafin ya yi ƙasa sosai da muryarshi.
“No Zulfa … Ina son ki.”
Ya sake maimaitawa yana son ta fahimci kalar son da yake nufi. Murmushi ta yi saboda tana jin daɗin kalmar da ya furta, ba ta san ya mayen giya yake ba, amma tasan duk in kalmar ta fito daga bakinshi bugar da ita take yi.
Muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce,
“Ina son ka… Ina son ka Yaya Labeeb…tun kafin in yi hankali…tun da na yi hankali. Ina son ka tun kafin in gane ma’anar kalmar har na gane ta. Ina son ka tun a aurenka na farko… Ina sonka a aurenka na biyu… Ina sonka ko da na san ba zan same ka ba… Zan so ka har na daina numfashi…”
Kallon ta yake, kalamanta na mishi lulluɓi da wani irin ɗumi.
“Shhh…”
Ya faɗi, don ji yake in ta ci gaba zuciyarshi ba za ta iya ɗaukar komai ba, ta cika har yana jin zubar da take a jikinshi, haɗe goshin shi ya yi da nata yana lumshe idanuwanshi. Yana tuna auren shi na farko da yanayin ta. Yana tuna Ateefa da halin da ta shiga.
“I was so so stupid…ya aka yi ban gane ba?”
Hannuwanta ta sa tana tallabar fuskarshi ita ma ta runtse idanuwanta. Ba ta damu da abinda ya wuce ba, ba ta damu da kasa ganin da ya yi ba. Yanzun shi ne damuwar ta. Daren jiya shi ne farkon soyayyar su, gaba take dubawa.
Gaba za ta ci gaba da dubawa.
“Ya ɗaukeka lokaci mai tsawo Yaya… Bai dame ni ba. Ko da ba ka son yadda ka gane yanzun burin zuciyata ya cika…”
In ta ci gaba da magana bai san abinda zai iya faruwa ba, don haka ya buɗe idanuwanshi yana sumbatar ta. Cikin kanshi yake jin muryar da ke faɗa mishi hutu take buƙata. Sai dai sam zuciyarshi ba ta san wannan ba.