Skip to content
Part 50 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Karfe sha biyu dai-dai aka ɗaura auren Mami da Abba. Daga wajen ɗaurin auren, Dawud, Tayyab da Khateeb kansu tsaye gida suka dawo. Jikinsu sanye da manyan kaya na farar shadda ƙal da ita. 

Ɗakin Mami suka wuce inda Zulfa da Mamin suke zaune. Da gudun shi Khateeb ya ƙarasa inda Mami take, riƙo shi ta yi tana matsa mishi ya zauna gefenta, ɗayan gefen zulfa na zaune. 

“Mami an ɗaura… Mun gode sosai.”

Dawud ya faɗi yana kallon Mami da ƙaddara ta jeho musu ita a rayuwarsu. Lokaci ya sa ta shiga zuciyoyinsu tai zaune, ta zame musu Ummin su da suka rasa. Ba ta taɓa nuna gajiyawarta da kalar ƙaddarorin su ba. Asalima ita take ƙoƙarin ƙarfafa musu gwiwa wajen ganin sun yarda da komai mai wucewa ne.

Kallon Dawud take tana rasa abinda za ta ce mishi, don ita ya kamata tai musu godiya da dukkan ƙaunar da suka nuna mata, da yardar da suka miƙa mata na kula da mahaifinsu.

Tayyab ya fara ƙarasawa yana rasa inda zai zauna, hakan ya sa Mami ta ja ƙafafuwanta ta hau kan gadon sosai, Zulfa matsawa ta yi can gefenta tana jingina kanta da kafaɗar Mami ɗin. Khateeb ma haka ya yi. 

Tayyab ya zauna, Dawud ma ya ƙaraso ya zauna, a ƙasan zuciyarshi Mami na da matsayi mai girma, yau ta ƙara zama, ya san mutuwa ce kaɗai abinda zai raba su, bai da tsoron wani zai auri Mami ta yi musu nisa. 

Hannun Dawud Mami ta riƙe don ba ta da kalaman da za ta yi mishi godiya, haka Tayyab ma ya riƙe ɗayan hannun nata. Ba sa buƙatar kalamai don tabbatar wa da juna ƙaunar su. Zaune suka yi a wajen kowa da abinda yake sakawa cikin zuciyarshi. 

Ta fanni da dama rayuwa ta kayar da su, tare da junansu suke samu su miƙe, akwai tabon ciwukan faɗuwar da ƙaunar da suke wa juna yake sa su jin sauƙin ɗauka. Suna jin yadda rayuwa ta yi ta yawo da su kafin ta kawo su dai-dai wannan lokacin ta ajiye. 

**** 

Kallon su Asad da ke haɗa kayan su Mamdud yake yi, yana zaune kan gadon asibitin. Bai ko gwada taya su ba don yasan ba barin shi za su yi ba. Ya gaji da zaman asibitin dama, sai dai zai yi kewar kasancewa da su Asad kullum. 

Don ba kaɗan suke rage mishi damuwar halin da yake ciki ba. Baisan ta ina zai fara ba in ya sa ƙafarshi ya fita daga asibitin. Tun daga ranar da ya buɗe idanuwanshi kunnuwanshi suka ji yadda ƙaddara ta buɗe mishi wani shafi mai wahalar wucewa, yake faɗa wa kanshi zai iya jurewa. 

Yake faɗa wa kanshi, Allah ba zai ɗora mishi abinda ba zai iya ɗauka ba. Yake jin akwai alkhairi a cikin kowace ƙaddara in dai ka rungumeta da hannuwa biyu da zuciya mai cike da imani. 

Sai dai baisan haka nauyin tashi take ba sai yanzun da yasan zai rasa wanda za su raba nauyinta tare. Bai san haka zai ji ciwon yadda ƙaddara ta juya da shi ba sai duk idan sun fita ya ɗan zagaya cikin asibitin ya ci karo da yara. 

Sai yanzun da ya hango wani ya wuce ta cikin window shi da yaro rungume a kafaɗarshi. Zuciyarshi tai wani irin matsewa, hannuwanshi ya kalla, yana jin ɗumin Arif a zuciyar shi da wata irin kewarshi. 

Allah ba ya barin wani don wani. Da Arif na nan, zai ji sauƙin wannan ƙaddarar saboda shi kaɗai ne yake da kusancin da ɗa yake da shi da mahaifinshi a zuciyarshi. Gashi ba zai sake sanin yadda wannan ƙaunar take ba. 

Sosai ƙirjinshi yake zafi har sai da ya yamutsa fuskarshi yana wani irin sauke numfashi. Anees ne ya taɓa shi sannan ya ɗago

“Tunanin me kake yi? Na yi magana ya fi sau biyar ba ka ma ji ni ba?”

Da wani yanayi ya girgiza wa Anees kai. Kujera Anees ya ja ya zauna yana kallon shi sosai. 

“Don Allah ka rage damuwar nan… Kar wani ciwon ya kama ka.”

“Hmm…”

Kawai Mamdud ya iya furtawa, duk yadda suke tunanin sun fahimci abinda yake ji ko rabin shi ba za su taɓa ganewa ba. Ba ya jin akwai wani ciwo da zai kama shi da zai fi wanda yake ji raɗaɗi da ciwo. 

Ganin ya yi shiru ya sa Anees miƙewa suka ƙarasa haɗa komai. Ƙwanƙwasa ƙofar aka yi tare da turowa a hankali. Kafin Labeeb ɗin ya shigo da sallamar da Asad ya amsa mishi. 

Fuskarshi na ɗauke da sanannen murmushi daga shi har Anees. Jakar da ke hannunshi Mamdud ya fara kallo kafin ya tsayar da idanuwanshi kan yaron da yake riƙe da shi. Kamar su har ta yi wani irin yawa tsakanin shi da Labeeb ɗin. 

Jakar da ke hannunshi ya ajiye kan ɗaya daga cikin kujerun kafin ya ja ɗaya ya zauna a gaban Mamdud, cikin fuska ya kalli Mamdud da yanayin da ke ɗauke a fuskar Labeeb ɗin ya sa zuciyarshi dokawa. 

Muryar Labeeb ɗauke da wani yanayi ya ke kallon Mamdud da faɗin, 

“Bansan me kake ji ba… Duk yadda na so in sa kaina a matsayinka zuciya ta kasa jurewa don tunanin irin ƙaddararka kawai na wa numfashina barazana. 

Ba zan taɓa iya canza abinda ya sameka ba. Wallahi in har zan iya zan bada dukkan dukiyar da na mallaka don ka san mene ne soyayyar yara….ban san me zan ce maka ba…”

Sai da Mamdud ya yi ƙoƙarin haɗiye abinda ke tsaye a wuyanshi da ƙirjinshi da ke tafasa tukunna ya kalli Labeeb da yanayin fuskarshi da ke ɗauke da damuwa marar misaltuwa. 

“Nasan ya take El-Maska… Allah ya bani kyautar lokuta tare da Arif duk da ba masu yawa ba ne…Zan yi ƙarya in na ce maka bana jin ciwon abin nan. 

Na ɗauka ba zai min zafi haka ba… Wallahi da ciwo sosai…”

Kai Labeeb yake ɗaga mishi yana jin kamar ya karɓar mishi zuciyarshi na wani lokaci ya ɗan huta. Hannun shi ya kamo ya saka na Junior a ciki. Muryarshi na rawa ya ce, 

“Na san ba daga jikinka ya fito ba… Na san babu jininka a jikinshi…sai dai zuciyarshi yanzun take girma… Soyayyar mahaifi a wajenshi yanzun za ta fara tasiri. 

Ba zai gane banbancin jinin ba… Ƙaunar kawai zai fahimta…Allah ya sa zai iya rage maka raɗaɗin abinda ka rasa da wanda ba za ka samu ba…”

Hannun yaron da ke cikin nashi Mamdud yake bi da kallo, yana jin bugun da zuciyarshi take yi har cikin kunnuwan shi da idanuwanshi da suke cike taf da hawaye. Cike da tsoro ya ɗago yana kallon Labeeb, ƙwaƙwalwarshi ta kasa gama fahimtar maganganun da ya yi balle su samu wajen zama a zuciyarshi. 

“El-Labeeb Mamdud Maska…”

Labeeb ya faɗi yana kallon shi. Hawayen da suka taru a idanuwan Mamdud suka zubo da ɗumin gaske. Sakkowa ya yi daga kan gadon hannunshi riƙe da na Junior. Jikinshi ko ina ɓari yake. Hawayen shi sun kasa daina zuba. 

Tsoron ɗago kai yake ya sake kallon Junior, tsoron ko motsi yake ji kar wannan yanayin ya ɓace mishi. Tsoron kallon junior yake karya neme shi ya rasa, so yake ko na mintina biyar ne ya ji daɗin abin nan da ke faruwa kafin ya farka daga mafarkin nan. 

Ji ya yi an riƙo mishi kafaɗa. A tsorace ya ɗago. 

“Za ka fara karya dokar Doctor tun kafin mubar asibitin… Banda ɗora nauyi sosai akan ƙafarka…”

Asad ya faɗi yana ɗago shi, a rikice yake gaba ɗaya har ya mayar da shi kan gadon ya zauna. Junior ya sake kallo ya ganshi tsaye har lokacin hannunshi na cikin na Mamdud. Ɗayan kuma na riƙe da chocolate ɗin da bai buɗe ba. 

“Mafarki nake ko?”

Mamdud ya tambaya cikin kuka muryarshi na karyewa. Kai Labeeb ya girgiza mishi. Asad ya kalla da yake mishi murmushi shi ma nashi idanuwan cike da hawaye. Ba zai manta ranar ɗaurin auren Zulfa da Labeeb ba da Yamma sun fito da Mamdud ɗin ya zagaya. 

***** 

“Yaya Mamdud ka daina danna ƙafar nan sosai fa…”

Anees ya faɗi. Dariya kawai Mamdud ya yi. 

“Sai ka ce wata ƙafar da za ta narke in na taka…”

Ya faɗi, kama shi Asad zai yi kafin ya ga yaybi wani abu da kallo da wani irin yanayi a fuskarshi. Inda fuskarshi take shi ma Asad ɗin ya kalla ya ga wata ‘yar yarinya ce riƙe da hannun mamanta tana ta tsalle-tsalle.

“Na gaji… Mu koma”

Mamdud ya faɗi muryarshi ɗauke da wani yanayi. Ko kaɗan zuciyar Asad ba ta yi mishi daɗi ba. Da abin ya kwana a ranshi, kamar yadda duk wani motsi da Mamdud zai yi a daren kan kunnenshi yake yinshi ya san ba bacci yake ba. 

Hakan ya sa shi faɗa wa Labeeb yana son magana da shi. Da ya zo asibitin zai tafi binshi ya yi a baya. 

“Yaya bansan ko me za ka yi ba… Don Allah ka yi wani abu akan Yaya Mamdud… Kallon yara yake da wani irin yanayi dake karya min zuciya… Bazan iya ganin shi haka ba… Zuciyata ciwo take min…”

Asad ya ƙarasa maganar hawaye na zubar mishi da ya sa hannu ya goge su. Kallon shi Labeeb yake yi, ko kaɗan ba ya son damuwar su, daga shi har Mamdud ɗin. 

“Ya zan yi? Ya kake so in yi? Da damuwar shi nake kwana nake yini a raina. Wa ka taɓa ganin ya yi kokawa da ƙaddara Asad?”

Wasu hawayen cike da idanuwanshi ya ce, 

“Babu… Ni banda yaro… Da exam ɗinmu ta fito na gama service zan yi aure Yaya… In Yaya Mamdud ba zai iya haihuwa ba… Ni zan raba nawa yaran da shi in dai zai rage mishi damuwa…”

Sai yanzun abin ya faɗo wa Labeeb. Baisan me ya sa tunanin bai zo mishi tun tuni ba. Murmushi ya yi. 

“Zan ba shi Junior…Tee za ta haifo min wani babyn… Ga Zulfa kuma.”

Ware idanuwa Asad ya yi kafin wani farin ciki ya taso daga zuciyarshi yana bayyana kan fuskarshi. 

“Really? Bari in je in faɗa mishi…”

Girgiza mishi kai Labeeb ya yi. 

“No… Ba yanzun ba. Kar ka faɗa mishi tukunna…. Sai ma na yi magana da Mummy kuma sai na shawarci Zafira. Zan ba shi a lokacin da ya dace…”

Kai Asad ya jinjina mishi 

“I trust you.”

“Na gode….ka koma. Sai mun yi waya.”

Farin cikin shi na ranar bai ɓoyu a wajen Anees ba har sai da ya sanar da shi abinda ke faruwa. 

***

Kallon fuskar Mamdud yanzun, har Asad ya mutu ba zai manta yanayin ba ya sani. Abinda ke faruwa a gaban idanuwanshi yanzun abune da zai zauna a zuciyarshi har mutuwa. 

“Ba mafarki ba ne ba Yaya Mamdud… Yaro kake da…”

Anees ya faɗi zuciyarshi cike da wani irin nauyin ganin kukan da Mamdud yake yi. Kallon shi ya mayar kan Junior yana kallon yaran, zuciyarshi na buɗewa ta wanni fanni da ba zai faɗu ba. Ƙaunar yaron na shigarshi ta ko ina. Sai da ya ɗago ya kalli Labeeb. 

“El…”

“Ɗanka ne Mamdud…bai fito daga jikinka ba… A ko ina na rayuwar shi da sunanka zai yi amfani. Da shi zai yi alfahari…”

Wasu sabbin hawayen ne suka zubo wa Mamdud. Girgiza kai ya yi yana amfani da duk wani ƙarfin zuciya da ya rage mishi ya zare hannun Junior daga cikin nashi yana dumtse hannun tamkar akwai abinda yake a jiki da ba ya son rabuwa da shi. 

“A’a… Asalina zai taɓashi… Me ya sa za ka so gauraya ji…za ka gauraya shi da ni?”

Ya faɗi yana kasa ƙarasa kalmar jinin saboda alƙawarin da ya yi wa Zainab ya riƙe sauran kalaman ya hana su fitowa. Cike da takaici Asad yake kallon Mamdud. 

“Ka kalle ni Yaya Mamdud… Asalinka ya fara ne tare da mu… Ba zamu taɓa goge rayuwarka ta farko ba… Kamar yadda kai kanka ba zaka iya goge ta ba… Za ka iya zaɓan abinda za ka yi da rayuwarka ba tare da ka bari bayanka ya zaɓar maka hakan ba…saboda me ƙaunar mu ba za ta ishe ka ba? Me ya sa ba za ka daina faɗa mana mu ɗin ba komai bane a wajen ka?”

Asad ya ƙarasa maganar yana sa hannuwa ya murza idanunshi da ke zafi don hawayen da ke cikin su sun ƙi zubo mishi balle ya ji sauƙin abinda yake ji. Anees ya kalla ko zai taimaka ya faɗa wa Asad ba abinda yake nufi ba kenan. 

Matsawa Anees ɗin ya yi kusa da Asad yana nuna wa Mamdud yana goyon bayan duk wani abu da Anees ya ce. Wajen Labeeb ya juya da ya ce mishi, 

“Ka kalli Junior, Mamdud ka kalli fuskarshi ka ce ba ka son zama babanshi. Ka buɗe bakinka ka faɗa mishi ba za ka iya ɗaukar nauyin shi ba… Zan koma da shi wallahi.”

Junior Mamdud ya kalla, babu abinda zuciyarshi take yi banda tsara mishi rayuwa tare da yaron. Babu abinda duk jikinshi yake yi banda son ya rungume yaron a ƙirjinshi ya ƙaunace shi da dukkan zuciyarshi. Ya kula da shi da duk wani abu da ya mallaka. 

Fuskar shi ya tallabe cikin hannuwanshi yana son tsaida hawayen shi da sun ƙi daina fitowa. Kuka yake kamar ƙaramin yaro. Kafin ya ɗago da rinannun idanuwanshi, a dakushe yake kallon Labeeb yana faɗin, 

“Ka sani… Halayena ba su da kyau…”

“Za ka canza saboda ɗanka…”

“Bansan ta ina zan fara saita rayuwata ba in na sa ƙafata wajen asibitin nan…”

Ya faɗi yana son Labeeb ya fahimci tsoron da yake ji. 

“Tare da shi za ka gane hanyar da ta kamata ka bi…”

“Banda mata… Ta yaya zai samu kulawar da ya kamata?”

“Single Dad’s nawa ne suke managing a faɗin duniya? Ka kalle ni… Lafiyata ƙalau ban samu kulawar kowa a cikin nawa iyayen ba… Ka kalli su Asad… Me ya same su? 

Mamdud kai min shiru ka ɗauki ɗanka…”

Labeeb ya faɗi don zuciyarshi ta gama karyewa. Baya son hawayen shi su zubo ya rikita su Anees. Yana kallon yadda Mamdud ke kallon Junior yana kokawa da abinda yake ji, yana son yakice duk shakkun da ke ranshi. 

Kallon shi Junior ya yi, kafin ya juya ya ajiye chocolate ɗinshi akan cinyar Labeeb ya sake fuskantar Mamdud… Ya taka dai-dai inda yake, ƙafarshi ya dafa yana janyowa. Hannu Mamdud yasa ya ɗago shi ya ɗora shi kan ƙafarshi. 

Hannuwa junior ya kai yana goge wa Mamdud hawayen da ke zubo mishi. 

“Ya Allah…”

Mamdud ya faɗi yana rungume Junior a jikinshi. Yana jin kamar ya mayar da yaron cikin shi. Babu abinda yake ji sai wani irin tsoron Allah da ke shigarshi har tsikar jikinshi ke tashi. Ya kara tsorata sosai da lamarin duniya. 

Ya ƙara imani da cewa akwai sauƙi a cikin kowanne yanayi. Kuka yake kamar ɗan ƙaramin yaro. Yana rungume da Junior da ya zagaya ‘yan hannayenshi a bayan Mamdud ɗin. 

“Zan canza saboda kai Junior… Zan zama uban da za ka yi alfahari da shi. In sha Allah bazan taɓa ja maka abin da za ka yi da na sani da amfani da sunana ba…”

Miƙewa Labeeb ya yi, ya zaro mukulli daga aljihunshi ya miƙa ma Mamdud da faɗin, 

“Motarka na waje”

Ganin ya tsaya yana kallonshi ya sa shi ɗorawa da, 

“Don Allah karka ce komai…in har ɗan uwa na da ikon yi wa ɗan uwanshi kyauta ka karɓa kawai…”

Hannu Mamdud ya sa ya karɓi mukullin yana miƙewa tare da Junior a jikinshi. Da wani sabon yanayin, da wani sabon shafin da ƙaddara ta buɗe mishi tana kulle mishi ɗayan suka fita daga asibitin. Bayan sabuwar motarshi suka zuba mishi kayanshi. Shi da Asad da Junior sukai yi gaba. 

Labeeb motar Anees ɗin ya shiga don shi ya tuƙu ta Mamdud ya maida shi gida sannan ya bi su Mamdud ɗin. Yana shiga ya lumshe idanuwanshi, cike da nutsuwa yake tuna shigarshi gida ya fada wa Mummy zai ba wa Mamdud Junior. 

****

Ita da Daddy ya samu a zaune suna hira. Ya ƙarasa ya samu kujera ya zauna suna gaisawa. Mummy duk wani iri take mishi tun bayan rasuwar Arif. 

“Dama ina son faɗa muku wani abu ne Mummy.”

Hankalin su suka maida kanshi su dukkan su. 

“Zan ba Mamdud Junior…”

Cikin tashin hankali Mummy ta ce, 

“Ba ka rufe glass ɗin motarka ba halan? Ka shaƙi iska ta maka yawa ko Labeeb? Mamdud ɗin za ka ɗauki yaro ka ba wa? Tunda aka kawo shi a nan gidan yake dama ai. In ba za ka iya riƙe shi ba ne ka bar min shi tunda ban ce maka na gaji ba dama…”

Gyara zamanshi Labeeb ya yi kafin ya kalli Mummy ya ce, 

“Na fada maku abinda Doctor ya ce akan shi Mummy… Ba zai haihu ba. Menene don na ba shi Junior? In Asad ne ko Anees ba za ki ce komai ba…”

Juyawa Mummy ta yi tana kallon Dady. 

“Ka yi shiru ba ka ce komai ba.”

Sauke numfashi Dady ya yi yana kallon Mummy. 

“Yaran nan sun ga rayuwa ta fannin da muka sani da ma wanda ba mu sani ba. Bana jin gwagwarmayar da suka sha ni da ke mun sha ta. 

Basu san da kulawar mu ba tun lokacin da suke buƙatarta. Basu san hukuncin mu akan manyan abubuwa na rayuwar su ba sa’adda suke son hakan. Saboda me don rana ɗaya rashin Arif ya sa mun gane kuskuren mu za mu ce za mu yi musu abinda ba su saba ba? 

Albarka da addu’armu suke buƙata. Tun Labeeb bai da hankali yake yanke hukunci akan rayuwarshi da ta ƙannen shi. Tsakanin su da Mamdud Allah ne da ya haɗa su kawai Ya san ƙarshen zumuncin su. 

Na yarda da Labeeb na da hankalin yanke hukuncin da ya dace a rayuwarshi. Saboda ban haɗa jini da Mamdud ba bazan hana shi ba wa ɗan uwanshi yaron shi ba. 

In ma laifi ne su ya yi wa … A tsakanin su ne. In sun yafe wa juna meye nawa na ɗaga kai? Kema ki musu Addu’a Allah Ya sa hakan ya zama alkhairi a gare su.”

Duk da kalaman Dady sun taɓa Mummy bai hana ta faɗin, 

“Bai da mata fa… Ya zai kula da yaro shi kaɗai?”

Ɗan kula da junior da take kwana biyu ya sa ta gane abinda ta rasa a rayuwar yaranta. Cikin taushin murya Labeeb ya ce 

“Ba zai canza komai ba Mummy… Junior ba zai dawo miki da abinda kika rasa ba. Amfani da kulawarshi ba zai cike miki gurbin komai ba…lokuta ne da ba za su dawo ba… Duk yadda kike son su dawo… Sun riga da sun wuce…”

Kai take jinjina mishi ta sa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata. Lokacin da ta rasa na rayuwar su ba zai taɓa dawowa ba kam. 

“A hannun Mamdud Arif ya tashi Mummy….shi yake mishi komai. Da mata ko babu Mamdud zai zame mishi ko me yake buƙata.”

Cikin rawar murya Mummy ta ce, 

“Bansan yarintar ku ba… Girman da kuka yi na bani mamaki…”

Murmushi Labeeb ya yi. 

“Da sauri lokacin yake wucewa….haka zamu yi mamaki in mun jimu a kabari… Sai mu ga kamar bamu wani jima a duniyar ba…”

Su duka jikinsu yayi sanyi.

“Allah ya sa mu dace… Allah ya tabbatar muku da dukkan alkhairi…”

“Amin Mummy. Allah ya ƙara girma.”

Labeeb ya faɗi yana murmushi.

**** 

Yanzun ma murmushin ne a fuskar shi. Har Anees ya ja motar ya mayar da shi gida don ya taya su Dawud shirya harabar gidan da za su yi walima a ciki. 

**** 

Shi da Yumna ne, basu baro gidan su ba sai da suka yi sallar Isha’i don haka ya tsaya ya siya musu shawarma. Dukkan su ba wani yunwa suke ji ba. Fitowa ya yi da leda riƙe a hannunshi ya baro Yumna a mota, wayarshi yake ƙoƙarin mayarwa cikin aljihu ya ci karo da wani mutum. 

Cikin sauri yake faɗin, 

“Afuwan don Allah…”

Kallon shi mutumin yake yi. Cike da mamaki muryarshi ɗauke da rashin yarda ya ce, 

“Dawud?”

Sosai Dawud yake kallonshi yana mamakin inda ya sanshi, kafin wani abu ya matse a zuciyarshi, mamakin yanayin shigar da ya ganshi a ciki na saka mishi tsoron duniya ta fannoni daban. Kawun Ummi ne, wani yadi ne a jikinshi da ka gani kasan ya ji duniya, ya yi baƙi ya rame, tsufa ya fito mishi ƙarara. 

“Kawu?!”

Dawud ya faɗi muryarshi cike da rashin yarda cewar kawun ne wannan, mutumin da kayan jikinshi kawai in ka kalla kafin ka zo kan fatar shi da taji hutu kasan akwai wadata a tattare da shi. Fuskar kawu da wani yanayi ya ce, 

“Gara da Allah yasa na ganka Dawud…na je gidanku ya fi a ƙirga… Ko maƙwaftanku babu wanda yasan inda kuka koma…”

Kallon shi Dawud yake harya yaci gaba da faɗin, 

“Ina Aisha? Ina take in roƙi yafiyarta ko zan soma ganin daidai a rayuwata?”

Ya ƙarasa maganar muryarshi na karyewa. Wani irin ɗaci ne ya taso tun daga zuciyar Dawud yana tsaya mishi akan harshen shi yana hana mishi tausayin halin da ya ga kawun a ciki.

“Da gaske kawu? Ummi kake son gani?”

Kai kawu ya ɗaga mishi. 

“Wallahi ba kaɗan ba… Na zalunce ta… Na hau kan dukiyarta da ban taɓa zaton za ta ƙare ba na zauna. Dawud yau babu dukiyar. Rayuwa ta min wahala… Uwanin da take nuna min ƙauna ta bar ni saboda banda kuɗin da su kaɗai take so a tare da ni….ɗaya bayan ɗaya gobara ta dinga cinye duk wani abu da na mallaka… Tsohon gidana da babu gaurayen kuɗin Aisha ko daya ne kawai na tsira da shi…”

Hawayen da suka zubo mishi badu tausasa ɓacin ran da Dawud yake ji ba. Ummi na kwance a gadon asibiti yake tunawa a ranarta ta ƙarshe a duniya. 

“Na kasa yarda ummi kake son gani kawu…”

Dawud ya faɗi a kausashe. 

“Wallahi ita nake son gani… Na san na mata laifi… Ka kaini in roƙi gafararta ko zan samu daidai. Ko zan samu jin ƙai da tausayin yarana da na yi wa komai najin daɗin duniya…”

“Ka tuna ranar da na zo gidanka? Ranar da na zo na faɗa maka Ummi na asibiti? Me ka tambayeni a ranar? Kuɗin ne babu ko me? Haka ka ce min kawu…”

Dawud ke faɗi har wani huci yake ji na fita daga fuskarshi saboda ɓacin rai. Ganin kawu gaba ɗaya ya gama jagula mishi lissafi. Yana neman danne nishaɗi da farin cikin da yake ciki a yanzun. Musamman da yake tuna mishi abubuwan da suka yi wa Ummi. 

“Sanin Ummi na cewar dukiyarta duka na hannunka bai taɓa damunta ba. Saboda ba ita take buƙata ba. Abinda take so bai wuce zumuncin da ka zaɓi ka yanke ba a tsakanin ku… Bai wuce ta zo gidanka ku tarbeta da fara’a da mutunci ba. 

Zumunci… Shi ne kawai abinda Ummi take buƙata daga gareku… Ƙaunarku da tarin dukiya ba zai taɓa siya ba…”

Kawu na sharar ƙwalla, maganganun Dawud na sosa mishi zuciya. Musamman yanzun da ya gane muhimmancin zumuncin tunda ya rasa shi daga wajen iyalanshi. Ya san ɗacin abinda Aisha ta rasa a rayuwarta, da na sani marar amfani ne yake shigarshi. 

“Na sani yanzun Dawud…”

“Ka sani a ƙurarren lokaci… Sai dai in maka kwatancen maƙabartar da Ummi take ka je ka kai mata ziyara…”

Cikin tashin hankali kawu yake kallon Dawud yana girgiza mishi kai. Hawaye sabbi na zubar mishi. 

“Ta rasu? Innalillahi wa inna ilaihir… Dawud me ya sa ba ka zo ka faɗa min ba?”

Wata dariya Dawud ya yi. 

“In zo in faɗa maka ta rasu ka tambaye ni ko kuɗin zawwati ne babu? Mun samu… An kaita makwancinta ba mu rasa komai ba kawu…”

Ganin kukan da yake ya sa Dawud faɗin, 

“Kar ka damu da yafiyar Ummi… Ta jima da yafe maka tun kafin ka gane kana buƙatar hakan… Tsakaninka da Ubangiji ne yanzun…”

Yana ƙarasawa ya raɓa kawu da ya durƙushe a wajen ya ƙarasa wajen motarshi ya buɗe ya shiga yana jan murfin da ƙarfi kamar zai karya shi. Numfashi yake mayarwa kamar ya sha gudu. Yana jin yafda kanshi yake sarawa, jiri na ɗibarshi. 

Ya kuma san ɓacin rai ne, hawan jininshi ne ke neman tashi. Da sauri Yumna ta riƙo hannuwan shi. 

“Nur…”

Ta faɗi kamar yadda ta soma kiranshi da shi. Don Dawud haske ne a rayuwarta, haske ne a rayuwar duk wani wanda yake tare da shi. Hannunta ya kama yana matsewa dam kamar zai karya mata yatsu. Zafin da take ji bai sa ta ƙwace ba, sai ma ɗayan hannunta da ta kai kan kuncin shi tana son ya sauke idanuwanshi cikin nata. 

“Don Allah ka kwantar da hankalinka… Mene ne?”

Take faɗi kaman za ta kuka ganin yadfa Dawud ɗin ke maida numfashi. Sosai yake kallon fuskarta yana son duk wani abu da zai janyeshi daga tunanin ɓacin ran da kawu ya dawo mishi da shi. 

“Kawun ummi ne yumna… Wai yana da bakin da zai ce in raka shi wajen Ummi…”

Tana kallon yadda yake kokawa da maganar da yake yi kamar faɗarta kawai na ji mishi wani ciwo da babu mai gani, bata katse shi ba, fuskarshi kawai take tallaba da hannunta. 

“Yana son Ummi ta yafe mishi ne… Saboda dukiyar shi duka ta ƙare.. Shi ne ya zo neman ummi… Sai yanzun yake neman ta.”

Sai lokacin ta sauke hannunta daga fuskarshi tana riƙo ɗayan hannunshi tare da sauke idanuwanta a nashi. 

“Lokuta da dama ba ma gane kuskuren mu sai tsanani ya same mu… A cikin tsananin ma sai mai rabo… Sai wanda Allah ya so da rahma ne yake buɗe mishi zuciyarshi da gane laifukan shi…ban ce me yasa ranka zai baci ba… Sai dai zance ka duba zuciyarka… Me Ummi za ta so ka yi?”

Lumshe idanuwanshi Dawud ya yi. Yana ganin murmushin Ummi a ciki, yana jin ɓacin ranshi na sauka a hankali. Kusan yana jin muryarta da abinda za ta ce, 

‘Duka duniyar kwana nawa ce Dawud? Ba muna zama da juna ba ne don mun manta laifukan da muka yi wa juna. Muna zama da juna ne don mun yafe… In babu yafiya duka zamu rasa kanmu ne. 

Akwai laifukan da zamu aikata waɗanda da babu yafiya ba zamu iya kallon kawunan mu a mudubi ba. Akwai sauƙi mai girma a cikin yafiya…ka yafe duk sa’adda ka samu damar hakan.’

Buɗe idanuwanshi ya yi, yanayin Kawu na dawo mishi. 

“Ina tsoron duniya Yumna… Kin ga yanda rayuwa ta mayar da kawu? Ni bance sai na tara kuɗi masu yawa ba… Ina roƙon Allah da ya bani wadata daidai gwargwado… Talauci na ɗaya daga cikin manyan jarabawoyi…”

Murmushi tai mishi. 

“Sai ka ƙara addu’a…ka roƙi rufin asirin Allah. Ka ƙara taimako fiye da yadda kake yi… Allah ba zai ɗora maka abinda ba za ka iya ɗauka ba.”

Jinjina kanshi ya yi. 

“Ina ƙaunarki sosai…ina jin daɗin kasancewar ki abokiyar rayuwata”

“Ina ƙaunarka fiye da yadda kake min… Ina alfahari da kai… Je ka yi abinda ya kamata ka dawo.”

Sakin hannunta ya yi ya buɗe murfin motar ya fita. Kawu na inda yake a durƙushe. Ƙarasawa Dawud ya yi ya sa hannu ya ɗago Kawu da ke kuka yana riƙe shi a jikinshi.

“Don Allah ka yafe min… Ka yafe min Dawud…”

Kai kawai Dawud yake ɗaga mishi da faɗin, 

“Ya wuce har abada… Yanzun ina za ka je?”

Goge fuskarshi Kawu ya yi da hannayenshi biyu. 

“Gida zan koma…”

“Daga ina kake da daren nan?”

“Wani kamfani ne inda muke lodin kaya in an zo ɗauka …”

Runtsa idanuwanshi Dawud ya yi yana jin wani yanayi da ba zai misaltu ba. Hannun kawu ya kama yana janshi zuwa wajen motarshi ya buɗe murfin bayan motar. 

“Mu je gidana ka kwana… Ka huta. In sha Allah zan san yadda za a yi… Da shekarun ka bai kamata kana aikin ƙarfi irin wannan ba…”

Kallon Dawud kawai Kawu ya yi yana rasa abinda zai ce banda hawaye da suka zubo mishi. ‘Ya’ yanshi na cikin shi basu damu da halin rayuwar da yake ciki ba. Sai na Aisha da bai runguma a jikinshi ba, yau jininta ne yake tausaya mishi. 

Shiga motar ya yi Dawud ya rufe bayan motar. Ya zagaya ya shiga sannan ya ɗan juya yana cewa. 

“Wannan matata ce Kawu… Yumna ga Kakana…”

Juyawa Yumna ta yi ta gaishe da Kawu da ke share ƙwalla sannan ya amsa. Tausayin tsohon na cika mata zuciya. Da tsoron duniya da yadda ƙaddara za ta iya canza maka komai lokaci ɗaya suka ƙarasa gida, su duka jikinsu ya gama yin sanyi. 

**** 

Kwance yake kan gado yana tunanin rayuwa da yadda take canzawa. Zuciyarshi ta yi wani irin sanyi da ya tuna jajircewar da ke cikin idanuwan Mamdud da suka fito daga asibiti, yanayi ne a cikin su da yake nuna zuciyarshi za ta tsaya kafin ya sake yin wani kuskure.

Yanayi ne da yake nuna ko ya rayuwa za ta kaishi ƙasa zai ɗago cike da juriya da ƙarfin gwiwa saboda Junior na buƙatar hakan daga gare shi. Sauke numfashi Labeeb ya yi. Yana juyawa ya kalli Ateefa da ta fito daga wanka. 

Idanuwanshi ya tsayar akan cikinta da ya fara fitowa. Tashi ya yi zaune yana miƙa mata hannuwanshi duka biyun. 

“Mai zan shafa…”

Ta faɗi da alamun murmushi a muryarta. Kai ya girgiza mata yana sake ware mata tafukan hannuwanshi. Dole ta ƙarasa inda yake ta sa hannunta cikin nashi. Janyota ya yi ta tsaya a gabanshi ya ƙura mata idanuwa. 

“Babyna ya fara fitowa.”

Dariya ta yi yadda yai maganar kamar abinda ya daɗe yana jira ya gani ne. 

“Ki haihu mu tafi Hajji.”

Wani tsalle ta yi da ya sashi riƙota dam a jikinshi. 

“Tee! Kina da hankali kuwa? Ba ki san ba ke kaɗai ba ce ba…”

Kwantar da kanta ta yi a ƙirjinshi tana dariya. 

“Hajji fa ka ce?”

“Eh Hajji na ce… Mu duka zamu tafi In sha Allah…. Da kin haihu.”

Ƙara ƙanƙame shi ta yi, babban burinta na duniya ne ya kusan zama gaske tare da Labeeb. Ba za ta misalta daɗin da take ji a yanzun ba. Sai dai ta nuna mishi yadda ya sa ta farin ciki. 

****** 

Kwance take a jikinshi yana jin ƙaunarta a zuciyarshi. 

“Kirki a jininku yake.”

Cike da mamakin maganar da ta fada ya ce, 

“Me ya sa kika ce haka?”

“Zulfa…ina kula El-Labeeb yadda take zame hannunta daga naka duk idan ina wajen. Yadda take zama nesa da kai in muna mu uku…duk yadda zan kwanta a jikinka a gabanta ban taɓa ganin damuwa a fuskarta ba. 

Amma ita ko da wasa ba ta yin hakan don kar in ji babu daɗi … Wasu irin mutane ne ku?”

Ta ƙarasa tambaya zuciyarta cike da mamakin su. Ba za ta taɓa yin irin abinda Zulfa take yi ba. Ko unguwa Labeeb ya dawo suna zaune suka tashi su biyun za ta ɗan ja ƙafarta don Ateefa ta riga ƙarasawa wajen Labeeb ɗin ko da kuwa ranar girkinta ne. 

Takan tambayi Ateefar in tana marmarin wani abin ta dafa mata. Ko makaranta ta je takan yo mata tsarabar kayan da ta san masu ciki za su yi kwaɗayi. Mata da yawa na tsoron kishiya saboda halinta. Ita kam tata ba ta da wata matsala. 

Asalima matsalar daga ita ne. Don kishin Zulfa take kamar me, musamman da ta san ba za ta taɓa zama mai irin halayenta ba. Sai dai ta kamanta. In ta cire kishin da ke ɗaya daga cikin halittarta, a zaman su da Zulfa ta samu wani ɗan waje a zuciyarta. 

Kamar yadda akan ce zuciya na son me kyautata mata. Shiru Labeeb ya yi. 

“Ka ga kirkin da nake magana ko? Na san ba za ka ce komai ba.”

Dariya ya yi yana riƙeta sosai a jikinshi. 

“Ban san me zan ce ba ne shi ya sa.”

“Ba ka so ka yabi Zulfa don kar in ji babu daɗi dai…”

Shirun ya sake yi. Ya san halin kishinta, son da Zulfa take mishi ya sa take son Ateefa saboda yasan Mummy ce kawai macen da za ta fi Zulfa son shi a duniya. Ƙaunar da take mishi babu algus a ciki, ƙaunar da take mishi ba ta komai bace . 

Ƙaunar da ya kusa yin asara saboda zuciyarshi cike take da wautar rashin fahimtar ƙaunar. Sumbatar Ateefa ya yi yana faɗin, 

“Shhh… Bacci.”

Gyara kwanciyarta ta yi a jikinshi tana lumshe idanuwanta. Bayan addu’ar bacci da ta yi, godiya take wa Allah da dukkan ni’imomin da ya yi mata. A haka har bacci ya ɗauketa.

***** 

Da sallama ya tura ɗakin ya shiga, Zulfa da ke gaban madubi tana ta ƙoƙarin zage zip ɗin rigarta ta amsa mishi, ƙarasawa Labeeb ya yi ya kama zip ɗin ya zage mata yana zagaya hannuwanshi kan ƙugunta, ya ɗora kanshi a kafaɗarta yana kallon su ta cikin madubin. 

Nata hannun zulfa ta ɗora akan nashi da ke kan ƙugunta. 

“Ina kwana…”

Yana shaƙar ƙamshin turarenta da yake iri ɗaya da na jikin shi ya amsa. 

“Lafiya kalau… Ya kika tashi? Ya gajiya?”

“Alhamdulillah… Ya Tee ɗinka da babynmu?”

Murmushi Labeeb ya yi. 

“Tee ɗina ni kaɗai… Baby kuma namu mu duka ko?”

Dariya Zulfa ta yi tana ɗaga mishi kai, cizonta ya yi a gefen fuska ta ture shi, amma ko motsi bai yi ba. Sai ma girarshi da ya ɗaga mata duk biyun ta cikin mudubin. Kafin muryarshi ta juye serious. 

“Junior na wajen Mamdud… Ya karɓe shi.”

Yanayin fuskarta ne ya canza lokaci ɗaya da jin sunan Mamdud ɗin, wani abu na lulluɓe mata zuciya. Tun satin da Labeeb ya faɗa mata zai ba Mamdud Junior rabon da ta bar zuciyarta tai mata tunanin shi sai yanzun. 

Tana ji yana ƙara riƙon da ya yi mata a jikinshi. Ya kula da yadda fuskarta ta canza. Sai dai kamar yadda take a cikin rayuwarshi har mutuwa haka ma Mamdud yake a cikinta. Ƙaddarar su ita da Mamdud mai ciwo ce ta yafda ba zai taɓa fahimta ba. 

Hakan ba zai hana sunan Mamdud giftawa a tsakanin su lokaci-lokaci ba. Duk da ƙarshen abinda zai so shi ne tuna mata abinda zai yi komai don ta manta. Wani lokacin dole buƙatar maganar Mamdud za ta taso, a hankali zai koya mata sabawa da hakan.

Cikinta ya shafa yana son rage mata yanayin da take ciki tare da raɗa mata maganar da sirri ce a tsakanin su. Dariya ta yi tana runtsa idanuwanta. Shi ma dariyar ya yi kafin ya runtsa idanuwanshi ya buɗe su. 

“Ina son tambayarki wani abu… Amma bana son dariyar nan ta sake barin fuskarki”

Buɗe idanuwanta ta yi. 

“In ta bari za ka sake bayyana wata akai…”

Jinjina mata kai ya yi yana rocking ɗinsu a tsayen. 

“Abinda zan tambaya yana da nauyi sosai… Ba ni ya kamata in tambaya ba na sani ….amm shi da ya kamata ya tambaya ɗin zai yi wahala ya iya kallon fuskarki ya tambaya ɗin … Ki yafe wa Mamdud… Don Allah ki yafe mishi…”

Numfashi take ja a hankali tana fitar da shi. Ƙarshen abinda take so bai wuce ganin fuskar Mamdud ba. Ƙila wata rana, ranar da ba kurkusa ba, ba ta son ganin shi, inda za ta iya bin ko ina na zuciyarta ta tsige hotunan fuskarta zai fi komai kawo mata kwanciyar hankali. 

Matse hannuwan Labeeb da ke kan ƙugunta ta yi dam, tana son ɗumin shi ya hana ta ziyarar inda ba ta son komawa a rayuwarta, ranar da bata son tunawa. Sumbar da yake manna mata a duk inda bakinshi zai iya kaiwa ba tare da ya canza yanayin tsayuwar da suke ba ta taimaka mata sosai, duk da ba ta hana muryarta fitowa a raunane ba. 

“Na tsane shi… Bana son ganinshi… Wallahi ko kaɗan ba na son ganinshi…”

Ta ƙarasa muryarta na rawa, ya fahimci daga inda tsanar Mamdud ke fito wa Zulfa, ba zai kuma taɓa canza hakan ba duk yadda yake so. Mamdud ya rusa duk wata alaƙa da ke tsakanin shi da Zulfa . Babu wani zumunci da zai sake ƙulluwa kuma. 

Har abada ba zai taɓa komawa ba. Zuciyarshi ta matse da tunanin hakan, jin yadda jikinta ke ɓari ne ya sa Labeeb juyowa da ita yana rungumeta a ƙirjinshi da ta zagaya hannunta a bayanshi tana riƙewa gam kamar wani zai kwace mata shi. 

“Ba na son ganin shi…in da ba kai ya ƙwace min abinda zai zame min tabo har in mutu… In da babu kai ban san ya rayuwata za ta yi ba. Kai ka sa nake iya kallon kaina a mudubi lafiya ƙalau… Kai ka sa nake jin abinda na rasa ba komai ba ne ba. 

Na yafe mishi!”

Lumshe idanuwa Labeeb ya yi yana jinjina kanshi. Yana jin daɗin kalamanta na ƙarshe kafin ta ci gaba da faɗin, 

“Na yafe mishi saboda a cikin ƙaddarar da ta faru na samu riba mai yawa… A cikin ƙaddarar da ta faru na samu cikar burina. A cikin ƙaddarar da ta faru na sameka Yaya Labeeb…”

Ɗago da ita ya yi daga jikinshi yana ja mata hanci, ba ya son ganin hawayen da ke cike da idanuwanta. 

“Yaushe za ki daina cemun Yayan nan?”

“Sweetheart… Darling… Honey… Handsome.”

Ta faɗi tana murmushi. Daƙuna fuska Labeeb ya yi yana jin sunayen wani iri a bakinta. Dukkansu babu wanda yai mishi daɗi. Hakan ta fahimta yasa ta sake maimaita

“Sweetheart… Wanne ka zaɓa my darling?”

Girgiza mata kai ya yi yana taɓe mata bakinshi cikin sigar da ta ga ya ƙara mata kyau. 

“Ko ɗaya… Wancan ya fi daɗi.”

“Honey?”

Ja mata hanci ya sake yi. 

“Yaya Labeeb…”

Dariya ta yi don ba ta jin za ta taɓa canza sunanshin. Hakan ta saba da shi. Hakanne ya fi mata daɗi, hakan take jin kiranshi da shi saboda ya dace da shi, ya dace a zuciyarta, ya dace a bakinta. 

“Ki taho mu karya. Yau ba school ne?”

Labeeb ya faɗi yana nazarin fuskarta. Girgiza mishi kai ta yi. 

“Ba wani abu serious… Exams za mu fara ranar Monday ɗin nan mai zuwa.”

“Allah ya kai mu… Ki koyi tuƙi kin ƙi.”

Girgiza mishi kai ta yi. 

“Nikam ba yanzun ba.”

“Matsoraciya…”

Hannuwanta da ke bayanshi ta zaro tana mayar da su kan wuyanshi ta haɗe space ɗin da ke tsakaninsu. Idanuwanta ta sauke cikin nashi da wani yanayi. Hucin numfashinta akan fuskarshi

“Me ka ce?”

Ta tambaya tana yin ƙasa da murya dai-dai kunnenshi. Bai san ya aka yi ba , amma babu komai a cikin kanshi banda sonta da ya cike ko ina yana ƙin ba wani abu ƙofar tunanin komai. 

“Ina sonki.”

Dariya take sosai da ya sa ko mene ne tai mishi karyewa yana ba wasu tunanin damar shigowa. Ware idanuwanshi ya yi har lokacin ƙafafuwanshi babu kwari, da sauro ta zame jikinta ta nufi hanyar ƙofa da gudu tana dariya. 

Murmushi Labeeb yake yi. Ateefa ce strength ɗinshi. Zulfa kam weakness dinshi ce. Son ta da yadda yake jinta daban ne. Ya kai mintina biyu kafin ya iya jan ƙafafuwanshi ya bi bayanta.

<< Rayuwarmu 49Rayuwarmu 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×