Tun farkon satin har ƙarshen shi Aisha ta rasa gane kan Auwal. Tun tana iya ƙoƙarinta wajen ganin yaran basu gane akwai matsala tattare da Abbansu ba har ta haƙura.
Gara ma Sajda. Don in ka ga murmushi a fuskarshi cikin gidan yanzun to Sajda ke bayyana shi. Tun da aka haifeta wata irin shaƙuwa ke tsakanin ta da Abban nata.
Har yanzun da canji ya same shi da Aisha ta rasa ko daga ina matsalar take akwai shaƙuwar nan duk da bata kai ƙarfin ta da ba. Idanuwa ta ɗauka ta saka mishi. Duk dare tana tashi ta yi salloli ta gabatar da addu’o’i abinta. Yanzun ma zaune take kan gado tunda ranar Asabar ce ba aiki ke akwai ba.
Tana ta kallon Auwal ɗin yana kai kawo cikin ɗakin. Ita take taya shi shiryawa da. Yanzun kam baya so tana taɓa mishi komai.
Idanuwa ta saka mishi ba don baya mata ciwo ba. Sai don hakan zai fi musu sauƙi su dukkansu. Wani farin yadi ne ya saka ya ɗauki baƙar hula ya ɗora.
Turaruka ya feshe jikinshi da su. Sannan ya ɗauko brief case ɗin shi da yake zuwa office da ita da ya ɗauko wasu kayan kala biyu ya saka a ciki.
Kasa jurewa tayi ta ce mishi,
“Sai ina haka?”
Yadda ya yamutsa fuska kamar jin muryarta kawai wata takura ce a wajen shi yasa wani abu mai zafi sukar mata zuciya.
Kamar bazai amsa ta ba. Can ya ce,
“Za mu bar gari da Yaya . Sai ran Litinin za mu dawo.”
Lumshe idanuwanta ta yi. Tana kiran sunayen Allah a ranta. Tana ƙin barin zuciyarta karanta mata abinda ta gani a fuskar Auwal.
Ko me yake faruwa bai kai girman abinda bai taɓa shiga tsakaninsu ya samu wajen zama ba. Ba zata bari ba.
Buɗe idanuwanta ta yi tana ƙaƙaro murmushi ta ɗora a fuskarta da faɗin,
“Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya. Da ka karya kafin ka fita ai.”
Girgiza mata kai yayi. Ya tsugunna gefen gado ya ɗauko takalmanshi. Ya ɗauki jakarshi yana ficewa daga ɗakin ba tare da ya juyo ko ya sake ce mata komai ba.
Miƙewa ta yi ta bi bayanshi. Yana tsaye a bakin ƙofar falon yana saka takalma. Ganin ya sa kai ya fice bai ce mata komai ba yasa ta sake binshi har tsakar gidan.
“Baka yi ma yaran sallama ba fa.”
Ta faɗi. A daƙile ya ce,
“Kin faɗa musu na tafi.”
Sauke numfashi ta yi.
“Wata ya ƙare fa. Islamiyar yara.”
Juyowa yayi a fusace ya ce,
“Meye matsalarki wai Aisha? Na kula fa ‘yan kwana biyun nan ba kya son ganin farin cikina ne ko menene wai don Allah?”
Da mamaki take kallon shi. A raunane ta ce,
“Me ya kawo wannan maganar kuma? Ni ce bana son ganin farin cikin ka Abban Sajda?”
Runtsa idanuwa yayi ya buɗe su alamar takurar da yake ciki ba ƙarama bace ba. Danne abinda take ji tayi ta ƙarasa inda yake tsaye.
Matsawa yayi da baya ganin tana shirin haɗa jikinta da nashi. Kallon shi take. Tun shekaranjiya wannan abin ya fara. Rashin son ta matso kusa da shi.
“Allah ya tsare hanya. Allah ya dawo da ku lafiya. Ka kula da kanka.”
Ta faɗi da ƙyar sannan ta juya da sauri ta bar wajen. Bayanta ya bi da kallo har ta shige falonsu. Idan akwai sauran abinda yake ji akan Aisha bai wuce takura da ƙunci ba.
In yana gidan ji yake kamar ana hura mishi wuta. Shekaranjiya ma tana ɗora hannunta a jikinshi ya ji kamar wanda ta goga ma barkono. Sai ƙarshen gadon ya matsa.
Wucewa yayi abinshi. Yana saka ƙafa ya fita daga gidan ya ji kamar an cire mishi ƙaya. Har numfashin da yake shaƙa ya ji ya canza.
****
Gefen gado ta zauna. Jikinta ya ɗauki ɗumi da alamar zazzaɓi ke shirin kamata. Hawaye ne masu ɗumi suka zubo mata.
Ta sa hannu ta goge su. A karo na farko a auren su da Auwal ya jefeta da maganganu masu zafin gaske. Ta ɗauka shi zai yi shaidarta kan ta fi kowa son farin cikin shi.
Ba iya nan ya tsaya ba. Saida ya haɗa da nuna mata yadda baya son jikinta ya taɓa nashi. Bata manta yadda ya kama hannunta cikin hanzari ya ɗauke daga jikinshi ba shekaranjiya.
Kamar wadda zata shafa mishi wata cuta. Wasu hawayen suka sake zubo mata. Ta tuna ko kuɗin cefanen da za su yi a kwana biyun nan bai bari ba.
Balle kuma kuɗin wata na makarantar yara da ta yi mishi magana. Tunawa ta yi da kuɗi a hannunta har na wata biyu da ko taɓa su bata yi ba.
Ta saka hannayenta duka ta goge fuskarta sannan ta miƙe ta shiga banɗaki ta sa ruwa ta wanke fuskarta ta fito.
“Allah kai kasan me yake faruwa da mijina. Allah ka bani ikon cin jarabawar nan da take samun mu. Allah ka yaye mishi damuwar da ke tare da shi.
Na yafe mishi dukkan abinda ya min wanda ya sani da wanda bai sani ba. Allah ka yafe mishi.”
Ta faɗi a hankali tana ɗorawa da amin. Sannan ta fito falon. Tana zama Sajda na shigowa jikinta sanye da riga da skirt na atamfa.
Ƙarasowa ta yi ta zauna kusa da Ummi. Sai ƙamshi take.
“Sajda ina kika samo turare mai ƙamshi haka?”
Murmushi ta yi.
“Yaya ne ya bani rannan. Shi ne muke shafawa ni da ya Zulfa.”
Murmushi ummi tayi. Tun asuba da suka gaisa da yaran suka koma ɗakin su.
“Ummi yunwa nake ji. Cikina sai ƙara yake yi.”
Dariya ta bata sosai. Gaba ɗaya ƙuncin da take ji na lokacin ta ji ya ɗauke.
“Jeki taso su yayanki su zo mu karya.”
Tashi ta yi ta fita da gudu.
“Ki dai yi sallama kafin ki shiga.”
Ummi ta tuna mata. Da wuya ma in ta ji ta. Ko minti uku bata yi ba ta dawo ta zauna tana maida numfashi.
“Duk ba bacci suke ba ma Ummi. Gasu nan zuwa.”
Kai Ummi ta ɗaga mata tana miƙewa ta fita daga falon. Sajda ta bita. Wasu cikin kayan ta bata ta tayata ɗauka suka kai falon.
Su duka suke zaune. Tayyab ya soma tambaya.
“Ina Abba?”
Zuciyarta ta ji ta doka. Bai taɓa tafiya wani waje ya kwana bai faɗa wa yaranshi ba. A sanyaye ta amsa shi da,
“Sun yi tafiya yau shi da kawun ku. Sai jibi in Allah ya kaimu za su dawo.”
Da mamaki a fuskar Zulfa ta ce,
“Amma bai faɗa mana ba.”
Dawud ya karɓe da faɗin,
“Tafiya? Har kwana biyu Ummi baki tashe mu mun mishi sallama ba?”
Hankalinta ta mayar kan haɗa musu tea ɗin ta ce,
“Sauri yake shi yasa. Ku dai ku mishi addu’a kawai.”
Shiru suka yi. Babu wanda ya sake cewa komai. Tasan yadda duk suke son tea ɗinsu ta haɗa ta miƙa musu. Farfesun naman a babban plate ta zuba suka ci gaba ɗaya.
Ba don tana jin yunwa ko daɗin tea ɗin ba. Turawa kawai take saboda jikinta na buƙatar abinda zai yi aiki akai.
Sai dai ita da Sajda kaɗai ke ci. Dawud wasa yake da cokalin shi cikin kofin. Tayyab kuma ya ma matsa can gefe yana kurɓar ruwan tea ɗin kaɗai.
Zulfa ta kalla. Tun naman da ta sa hannu ta ɗauka ne take taunawa kamar tana cin cingam. Kafin ta kalli Ummi da faɗin,
“Bana jin yunwa. Barin yi shirin Islamiyya kafin ku gama.”
Bata jira Ummi ta amsata ba ta miƙe tana barin ɗakin. Tayyab ya ƙarasa kwankwaɗe tea ɗin shi kamar an mishi dole ya ajiye kofin yana miƙewa shi ma.
“Nima bari in shirya.”
Da ido ta bishi har ya fice. Da ƙyar ta iya haɗiye biredin da ke bakinta tana kora shi da tea ɗin. Ta ajiye kofin. Idanuwanta a ƙasa.
Har Sajda ta gama karyawa ta miƙe itama.
“Ummi in ɗauki sabuwar jakata in je da ita?”
Kai ta ɗaga wa Zulfa data fita da gudu tanajin dadi. Kafin ta tsayar da idanuwanta kan Dawud. Tunda yai sauka suka gama aji shida bai koma Islamiyya ba.
Yakanje ɗaukar karatu duk asabar da Lahadi ya dawo abinshi. Da tai mishi magana ya ce aji za su bashi. Baida haƙurin tsare yara shi yasa ya bar zuwa sai ta ƙyale shi.
“Sai tea ɗin nan ya huce ko Dawud.”
Sai lokacin ya kalleta yana jan wani numfashi tare da fitar da shi.
“Bana jin yunwa ne Ummi”
Jin ta yi shiru bata ce komai ba yasa shi miƙewa.
“Kaima baka ce komai ba.”
Wani guntun murmushi yayi.
“Allah ya dawo da shi lafiya.”
Ya faɗi yana ficewa daga ɗakin. Ta lumshe idanuwanta ƙuncin da take ji yana sake dawowa. Walwalar yaranta na da muhimmanci a wajenta.
Bata son ganin su cikin wannan yanayin. Suna kewar Abban su duk da yaune ya tafi. Yana nan suna ganinshi kullum a satin nan.
Amma baya cikin rayuwarsu kamar yadda ya saba. Jikinta babu ƙarfi ta miƙe ta shiga ɗaki. Kuɗin watan su ta ƙirgo da na Islamiyya.
Ƙara musu ta yi akan na kullum tunda sun ƙi karyawa sun ci abinci acan. Tasan su da gidan sai yammaci. Abincin rana ma Tayyab ne yake dawowa ya ɗaukar musu Kko Dawud ya kai musu wani lokacin. Har bakin ƙofa ta raka su tai musu addu’a ta sa su suka yi suma sannan ta dawo.
****
Gidan Hajiya Beeba ya fara biyawa ya ajiye kayanshi ya karya sannan ya fita ya wuce kasuwa.
Wanka ta sake yi ta ci kwalliya ta wuce gidan Huzai. Tana shiga ta zauna kan kujera tai wata shewa.
“Ke yau mutumin kayanshi ya kwaso kwana biyu zai yi a gidana.”
Wata dariya Huzai ta yi.
“Aikin Malam na kyau aminiyata.”
Ta ƙarasa maganar suna tafawa. Kafin Beeba ta nutsar da hankalinta da faɗin,
“Kinsan me nake so yanzun?”
Ta girgiza mata kai.
“In kin koma gidan Malam a yi min aikin da zan kama ‘yan uwanshi a hannu. Don na ga alama yana shakkar wani yayan shi da suke kasuwanci tare.”
Dariyar mugunta Huzai ta yi ta ce,
“Kin fara gane hanya kenan.”
Beeba ta riƙe baki.
“Ai dole wallahi. Yana gama cin maganin nan fa na samu kanshi gaba ɗaya. Jiya kamar wasa na ce sai ya zo yai min kwana biyu ai.
Dana ga yai shiru kinji yadda gabana ya dinga faɗuwa. Sai kuma ya ce to. Na yi mamaki sosai. Yau da safen nan sai gashi.”
Kaɗa kai Huzai ta yi. Kamar dama bata yi mamaki ba. Saboda ta san yadda aikin Malam yake.
“Ki ƙarasa amfani da turarukan nan a kwana biyun nan. Ki zuba masa na ruwan wankan nan.”
Harararta Beeba ta yi.
“ki ce kar in yi mana. Ai ko da wasa bazan bari ya kufce min ba. Kin ga yanzun ma kasuwa zani in yo cefanen da zan yi mana girki.
Na ce saina biyo ta gidan ki na gaya miki.”
Dariya Huzai ta sake yi.
“Shegiya ta wajena. Baki da kyau.”
“Zama da ke ne ai.”
Beeba ta faɗi tana miƙewa. Har ƙofa Huzai ta rakata. Kamar yadda ta faɗa kasuwar ta wuce ta yi cefane. Ta ji daɗin yadda Huzai ta takurata ta koyi girki kala-kala.
Dama ta ce mata wata rana suna iya buƙatar yin girki don yana cikin abinda za ka ƙara amfani da shi wajen kama namiji. Ta kuma ga gaskiyar abin yau.
*****
Sai da ta gama komai. Ta sake gyara gidan. Turarukan wajen Malam ta bi kowace kusurwa ko ina ta yarfa. Sannan ta shiga ta yi wanka. Sallah ba damunta ta yi ba. Sai ranar da abin ya kaɗo mata. Wasu lokutan ma sai ranar juma’a take cika sallah gaba ɗayanta.
Tana fitowa ta murje jikinta da turaren da shima malam ne ya bata shi. Atamfa ce a jikinta amma ɗinkin ya kamata ba kaɗan ba.
Ta dawo falo ta zauna ta kunna bidiyo tana kallon wani fim ɗin Amurka tana jiran dawowar Auwal.
*****
Bai shigo gidan ba sai da yammaci. Da fara’a ta tashi ta tarbe shi. Kallo ɗaya yai mata ya sadda kanshi ƙasa. Har ya ƙarasa falon ya samu waje ya zauna bai sake bari idanuwanshi sun wuce fuskarta ba.
Asalima, zuciyarshi ce ke dokawa da ƙarfin gaske. Kasancewa kusa da Beeba yana saka shi nutsuwa. Jin muryarta yakan yaye mishi ƙuncin da yake ji in yai nesa da ita. Amman ko da yaushe yake kusa da ita ɗin. Tattare da dukkan abubuwan nan akwai wani abu na daban da bai san ko meye ba. Kamar yanzun yana shigowa ya kalleta. Ji ya yi tana shigar mishi idanuwa da yanayi marar kyau. Kamar bai kamata ya ganta a yadda ya ganta ɗin ba.
“Sannu da zuwa. Ka taso ka watsa ruwa yadda ka kwaso gajiya haka ai sai da wanka.”
Aisha ce ta faɗo mishi a rai. Kai tsaye irin abinda take cewa ne in ya dawo. Sai dai murmushinta akwai nutsuwa tare da shi.
Akwai kunya a cikinshi. Ba irin na Beeba ba. Miƙewa ta yi tana gifta shi ƙamshin turarenta ya cika mishi hanci. Kamar an danne Aisha a zuciyarshi an mayar da ita can wani waje haka ya ji.
Neman tunanin ta yayi ya rasa. Miƙewa yayi ya bi Beeba har ɗakin baccin ta. Gefen gado ta zauna ta nuna mishi banɗaki. Babu musu ya wuce.
Ta tashi ta fito da murmushin nasara a fuskarta. Abincin shi ta haɗa mishi ta gama barbaɗe shi tas da magunguna. Daga ruwan sha har juice sai da ta zuba magani a ciki.
Haka ya zauna ya ci . Hira suke tana ta bashi labarai na ban dariya har Magariba ta yi ya fita sallah ya dawo. Suka zauna suna kallo. Ya sake fita Isha’i.
Abinci ya ɗan ƙara ci tunda ba yunwar kirki yake ji ba. Ya zauna suna kallo. Akwai abinda yake son tunawa amma ya kasa.
Sai ka ce wanda akai ma baƙin hijabi tsakaninshi da duk wani tunani da ba shi da alaƙa da Hajiya Beeba a ciki. Jin kanshi na shirin yin ciwo ya sa shi ya haƙura.
A falo ya kwanta. Babu yadda Hajiya Beeba bata yi ba ya tashi su shiga ciki ya kwanta. Ya ce mata kan kujerar ma ya mishi. Haka ta haƙura ta ƙyale shi. Shi kanshi ya rasa abinda ya hanashi binta su kwanta ɗin. Kawai yana jin abinda yai saura cikin hankalin shi ne yai rinjaye kan nufinta.
A haka bacci ya ɗauke shi. A karo na farko a satin da mafarkin shi ya canza daga na Hajiya Beeba. Wannan karon Aisha ya gani.
Tsaye take tana ta kuka. Daga can gefe Dawud ya ɓullo ya kama hannunta. Sannan Tayyab ya zo ya kama ɗayan hannunta. Zulfa na gabanta. Baisan ta inda Sajda ta ɓullo ba amma itama tana tsaye a gefen Zulfa.
Su dukkansu kuka suke suna kallonshi. Kafin wani irin rami ya soma buɗewa a tsakaninsu. Da gudu yake nufarsu yana son ya same su kafin ramin ya ƙara girma.
Kuka suke ta yi suna kallonshi amma ramin ƙara girma yake a tsakaninsu. Hannu ya miƙa yana nufin ya kamo su dukkansu. Amma babu wanda ya iya riƙowa banda Sajda.
Itama tana riƙe gam da hannunshi jikinta na cikin ramin tana ta ihun kiran sunanshi ya kasa ɗago da ita. Farkawa yayi yana wata irin zufa da kiran sunan Allah.
Tashi zaune yayi. Ba ƙaramin tsorata shi mafarkin yayi ba. Ƙamshin turaren da ke ɗakin ya shaƙa. Ya ji jikinshi ya wani irin mutuwa ko motsin kirki baya son yi.
Komawa yai ya kwanta. Har ranshi yake son tashi yayi sallah ya nemi tsari daga mafarkin nan da yayi. Amman ko motsi baya son yi a haka bacci ya sake ɗauke shi ko addu’a bai samu yayi ba.
****
Kwance take kan doguwar kujera gidan babu kowa. Duk suna Islamiyya. Dawud kuma ya ce mata za su je gaisuwa. Kakan wani ɗan ajinsu ya rasu.
Tun tafiyar Auwal take fama da faɗuwar gaba. Saima idan ita kaɗai take zaune abin ya fi damunta. Tana da alwala tun da ta yi sallar Asr.
Qur’ani ta shiga ɗaki ta ɗauko. Ta dawo ta kwanta ta buɗe tana karantawa. Sai ta ji wani nishaɗi da nutsuwa ta daban.
Tana ta karatu abinta take jin sallama. Kamar muryar Yaya Ibrahim. Sai da ta kai ayar da ta soma sannan ta rufe. Ta ɗauki hijabinta da ke gefe ta saka.
Tsakar gida ta fita. Aikam muryarshi ce. Wani irin dokawa zuciyarta ta yi. Jikinta babu inda baya kyarma ko wani abu ne ya samu Auwal.
Tana ta jero Innalillahi ta saka takalminta ta fita. Muryarta na rawa suka gaisa da Yaya Ibrahim ɗin.
“Auwal ɗin bai iso ba kenan.”
Cike da rashin fahimta ta ce,
“Ba tare kuka dawo ba?”
Murmushi yayi ya ce,
“Ai ya ma riga ni barin kasuwa. Ƙila ya biya wata hidimar ne. Na kwana biyu banga yara ba na ce bari in leƙo in duba su.”
Wani abu ta haɗiye tana danne shi a zuciyar ta sai Yaya Ibrahim ɗin ya tafi tukunna. Da ƙyar ta ce,
“Aikam duk suna Islamiyya.”
Ledojin hannunshi ya miƙa mata.
“Gashi to a basu. Ni zan wuce.”
Godiya tai masa da addu’a. Ta dawo gida. Tsakiyar falon ta ajiye ledojin. Ko hijabinta bata cire ba ta zauna ƙasa akan kafet.
Abinda ta hana zuciyarta furta mata ne. Tsoron da take yi ne ya tabbata. Auwal ƙarya yake babu inda suka je. Abinda bai taɓa yi mata ba.
Zafi ƙirjinta yake yi. Ga wani abu da yai mata tsaye a maƙoshi. Kife kanta ta yi a jikin kujerar wajen hawaye na zubo mata.
Ta wani ɓangaren hankalinta ya ɗan kwanta saboda Yaya ya ce ya je kasuwa. Koma ina ya kwana jiya yana lafiya.
Ta jima nan hawaye na zubar mata saboda yadda ranta ke ƙuna. Bata ga abun ɓoye mata inda zai je ba tunda bata isa ta hana shi ba.
Shi yasan hakan. Sai ya zaɓi yai mata ƙarya . Ya ba rashin yarda damar shigowa cikin zamantakewar da suka ɗauko shekaru wajen ganin sun ginata cikin yarda da junan su.
Sallamar Dawud ta ji. Da sauri ta sa hijabinta tana goge fuskarta. Zama ya yi kusa da ita. Kallon fuskarta yake da ta ƙi yarda su haɗa idanuwa.
Hannuwanta ya kamo. Cikin ƙunar rai ya ce,
“Ummi. Menene? Abba ne ko?”
Kai ta girgiza mishi. Wasu hawayen da ta kasa tarbewa suna zubo mata. Dawud ya lumshe idanuwan shi ya buɗe su.
A zuciyarshi yake addu’a yadda yake jin son Abba na juyewa da wani abu na daban. Duk wanda zai bayyana hawaye a idanuwan Ummi mai laifi ne a wajen shi.
A hankali ya ce,
“Ina kika ce Abba yaje?”
Kallon fuskarshi take. Tana tsanar yanayin da yake ɗauke da shi. Bata da wanda zata faɗa ma damuwarta. Bata da wani wanda ta yarda da shi banda mijinta da ‘ya’yanta.
Don haka ta ce mishi,
“Ya ce min za su yi tafiya da yaya Ibrahim ne. Kuma ba jimawar nan yayan ya zo ganinku……”
Ta ƙarasa muryarta na karyewa. Baya son abinda yake shirin gaya mata. Sai dai dole ne ya sanar da ita don tasan matakin da zata ɗauka.
Ya rasa ta inda zai fara. Muryarshi can ƙasa yana kallon hannayenta da yake riƙe da su ya ce,
“Bana son in faɗa miki wannan maganar Ummi. Bansan ta inda zan fara ba.”
Kallon fuskar shi take yi.
“Ka fara ta inda ya fi maka sauƙi.”
“Na ga Abba…….”
Ya faɗi da sauri yana ƙarawa da,
“Shi da wata. Inda muka je gaisuwa na gansu sun fito sun shiga wani gida ummi. Ba inda Abba yaje. Don Allah meke faruwa?”
Rufe idanuwanta ta yi. Tana jan numfashi da sauri da sauri. Tana faɗin Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.
Hannuwanta ya jijjiga.
“Ummi. Don Allah ki yi haƙuri. Ummi….”
Buɗe idanuwanta ta yi ta sauke su kan fuskar Dawud. Ajiyar zuciya yayi. Ranshi ya ɓaci sosai. Ba don ƙaryar da Abba yayi ba. Sai don yadda ƙaryar ta zafafi Ummi.
Yana ganinsu ya ji wani irin ɗaci a zuciyarshi. Me Abba yake da wata mace a waje. Har suna yawo tare a titi. Kishin Ummi ya soke shi.
Da ɓacin ran ya dawo gida. Ya kuma ƙara da ganin kukan da Ummi take yi. Ya kuma san Abba ne ya sata wannan kukan.
“Yanzun na san dalili Dawud. Inata neman dalili na rasa. Allah zai mana maganin komai. Kaima ka ƙara saka shi cikin addu’a ka ji.”
Kai ya ɗaga ya saki hannunta yana kai nashi hannun ya goge mata hawayen da ke zubo mata.
“Ina jin su har zuciyata Ummi. Bana son ganin ɓacin ranki. Ƙunci yake sakani marar misaltuwa.”
Ƙoƙarin danne zuciyarta ta yi. Tana roƙon Allah da ya bata juriya ko don ‘ya’yanta. Sannan ta miƙe. Da idanuwa Dawud ya bita har ta shige ciki.
Kanshi ya dafe cikin hannuwanshi yana rasa abinda ya kamata yayi.
****
Tsaye take tana kallon Auwal. Yayi baƙi ya rame sosai. Ba irin ramewar rashin lafiya ba, irinta wahala. Fuskarshi ɗauke da wani yanayi na ƙunci da damuwa.
Idanuwanshi kafe suke a kanta. Amma kamar baya ganinta. Inma yana ganinta bai nuna alamun hakan ba. Ƙarasawa ta yi inda yake tsaye.
“Abban sajda….”
Ta kira sunan shi. Idanuwan shi na kafe kanta amma baya ganinta balle ta yi tunanin ya ji kiran da ta yi mishi. Fuskarshi take nazari.
Har baƙin da ta ga yayi na wahala ne. Kamar wani abune aka kwaɓa aka shafa mishi tsilli tsilli a fuskarshi. Ja tayi da baya.
Ganin yadda baƙin yake ƙara yawa yana baibaye fuskarshi. Ko ina da ina na jikinshi baƙin yake yawo yana baibayewa. Kafin ya zama babu komai na daga siffarshi sai duhu.
“Abban sajda!”
Ta sake kira a razane. Amma babu komai inda yake tsaye sai duhu.
*
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…..!”
Take jerowa babu ƙaƙƙautawa. Wanna wane irin mafarki ne haka. Me ke faruwa da mijinta mai muni. Da sauri ta diro daga kan gadon. Banɗaki ta shiga ta wanke fuskarta. Ta ɗauro alwala ta fito. Jikinta ko ina kyarma yake saboda tsananin tsoro ga gabanta na faɗuwa sosai.
Kaya ta sake ta soma jero salloli. Sai da ta yi raka’o’i goma. Sannan ta zauna. Addu’o’in tsari ta shiga jerowa tana roƙon Allah da ya aika ma Auwal a duk inda yake a daren nan.
A duk halin da yake Allah ya kare mata shi daga halaka. Allah ya kawo musu jarabawar dake shirin samun su ta zo musu da sauƙi.
****
Bacci yake ya ji motsi. Da sauri ya miƙe. Don yau kwance yake kan gadon Hajiya Beeba. Yadda ta takura shi kan bata son yadda yake kwana a falonta kamar wani baƙo.
Ta ce ya kwanta zata tafi wani ɗakin ta kwana. Tukunna ya yarda. Yanzun kuma motsin da ya ji kamar an hawo gadon yasa shi miƙewa babu shiri.
A tsorace ya ce,
“Waye?”
Kasancewar duhun dake ɗakin, ji yai ta ƙara matsowa kusa da shi sosai. Ya shaƙi turaren nan da yake saka shi jin banda tunaninta da son kasancewarta kusa da shi babu abinda yake muradi.
“Beeba?”
Ya faɗi cike da shakku da alamar tambaya. Jinta yai a jikinshi ta riƙe shi. Baisan lokacin da ya ture ta ya miƙe ba.
Wani abu yake ji yana ratsa shi da wani irin ɗumi kamar ana hura mishi wuta a jikinshi. Saukowa yai daga kan gadon yana maida numfashi kamar wanda yai gudu.
Biyo shi tayi tana kiran sunanshi muryarta can ƙasan maƙoshi. Yau sai yake jin zuwan muryar kunnen shi kawai dafa shi take.
Matsawa ya sake yi. Muryarshi a sarƙe ya ce,
“Beeba me kike yi haka? Kina da hankali kuwa?”
Bai jira amsarta ba ya wuce yana lalubar ƙofa har ya ganota ya buɗe ya fita daga ɗakin zuwa falo. Tsaye ya barta a nan tana mamakin abinda ya faru.
Bayan malam ya tabbatar mata idan yai wanka da abinda ta zuba ɗazun ya gama yi mata musu. Jikinta a sanyaye zuciyarta cike da tsoro ta bishi.
Zaune ta same shi kan kujera ya dafe kanshi. Wasu hawaye suka cika mata idanuwa. Tunanin rasa shi ya fi komai daga mata hankali a rayuwarta.
Ƙarasawa ta yi ta tsugunna gabanshi. Muryarta na rawa hawaye na zubo mata ta dafa cinyarshi ta ce
“Kayi haƙuri Auwal. Bansan yadda zanyi bane ba. Baka san me nake ji a kanka ba shi yasa. Don Allah ka taimaka min.”
Ɗago kanshi yayi. Yana jin yadda wani abu ke ƙona shi inda hannunta yake ajiye a cinyarshi. Zafin ƙunar ya sa har zufa ke keto mishi.
Hannunshi yasa ya kama nata cak ya ajiye shi gefe. Kallonta yake ya rasa kome yake faruwa da shi. Koma me yake yi a wajen.
“Kin san me kike son muyi? Kinsan girman laifin da kike son jana mu aikata?”
Zama ta yi tana share hawaye. Abinda bata taɓa kawo ma ranta zai taɓa burgeta bane yake ɗarsuwa a zuciyarta.
Abinda inda wani yacee mata za ta yi sha’awar shi sai ta yi dariya saboda wautar tunanin. Muryarta babu alamun wasa ta ce,
“Ka aureni Auwal. Ina sonka wallahi. Zan iya komai saboda kai. Ka aureni in ba zaka iya zaman banza dani ba.”
Kai ya ɗaga mata kawai saboda yadda har lokacin yake jin zamanshi kusa da ita kawai wani abu na dafa shi.
Murmushi ta yi. Ranta ƙal take jinshi
“Muje ka kwanta to.”
Sai da gabanshi ya faɗi. Da sauri ya shiga girgiza mata kai.
“Zan kwana anan.”
Yanayin farin cikin da take ji bai sa ta mishi gardama ba. Ta wuce ta ƙyale shi. Kwanciya yai kan kujerar. Amma sam bacci ya ƙaurace ma idanuwan shi.
Haka har ya ji kiran sallah. Yai alwala ya tafi masallaci. Duk wanda suka haɗa ido sai ya ga kaman ya gane halin da yake ciki.
Ya kwana gidan matar da ba muharramar shi ba. Ya aikata saɓon Allah. Ya bari ta taɓa jikinshi. Sallah kawai akai da shi ko Addu’a bai bari ya samu ba.
****
Duk wata kissa da kisisina ta Hajiya Beeba yau bata yi aiki akanshi ba. Da ƙyar ta samu ya karya yai wanka.
Ya sake kaya ya ce mata tafiya zai yi. Bata son ɓata mishi rai. Musamman yadda ta kula aikin Malam na rauni a tare da shi.
Cewa ta yi zata sauke shi. Bai yi musu ba. Suka fita tare. Sai dai tun daga titi ya ce ta sauke shi ya ƙarasa gida. Zai koma su yi magana.
Sauke shi ta yi. Ta wuce gidan Huzai don su ƙara komawa wajen malam tai masa maganar auren Auwal ɗin.