Skip to content
Part 8 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Tsaye take tana jiran Auwal ya fito daga ɗakin Hajiya Beeba. Yau kwanan su biyar kenan. Idanuwa kawai ta ɗauka ta saka mishi. 

Sai dai ta ji shigowarshi. Da safe kuma ta ji fitarshi. Kamar ya manta da ita da yaranne gaba ɗaya. Sajda ce kawai ke yawan mita Abban su ya daina shigowa wajen su.

Su Tayyab kuwa a fuskarsu take ganin damuwarsu da yanayin yadda canjin komai na rayuwar yake taɓa su. Ba zata ce bata damuwa ba. Sai dai abin ya daina mata ciwo. Balle yanzun da ta san ba yin kanshi bane. Addu’a suke ita da yaranta ba dare ba rana. Canjin da take ji a jikinta ya tabbatar mata da tana ɗauke da juna biyu. Kamar duk cikin sauran. Ba ya damunta da laulayin nan. Ɗan zazzaɓi ne da takan ji wasu lokutan kuma shima da yayi wata biyu shikenan. 

Yanzun ma tana jiran ta ga fitowar Auwal ne ta tambaye shi cewar zata je asibiti. Tunda yasan da zuwanta wajen aiki. Amma haƙƙinsa ne ta tambaya kafin ta wuce wani waje daban ko don guje wa tsinuwar Mala’iku da fushin Allah. Ta kai mintina talatin, tun tana tsaye har ta kai da tsugunnawa. Sannan ta ga ya ɗaga labule yana wata dariya. 

Sauke idanuwanshi yai a kanta. Lokaci ɗaya fara’ar da ke fuskarshi ta ɗauke. Ya koma Auwal ɗin nan da ta kasa gane ko shi ne mijinta ko akasin hakan. 

Muryarta na rawa ta miƙe da faɗin, 

“Abban Sajda. Ina kwana.”

A daƙile ya ce, 

“Lafiya. Menene?”

Ta buɗe baki zata yi magana Hajiya Beeba ta leƙo ta bayan Auwal da faɗin, 

“Alhajina. Ya akayi ne?”

Juyawa yayi ya kalleta da fara’a. Wani abu Aisha ta ji ya tsaya mata a wuya. Kafin nan ya ce, 

“Ina zan sani Hajiyata. Na fito ne na ga wannan zaune anan.”

Wani kallon banza Hajiya Beeba tai mata. 

“Lafiya?”

Ta buƙata. Ko inda take Aisha bata kalla ba. Balle ta yi tunanin zata kulata. Asalima idanuwanta a kafe suke kan Auwal. Cikin sanyin murya ta ce, 

“Zan je asibiti ne dama. Na ce zan tambaye ka.”

Yamutsa fuska yayi. 

“Daga yanzun ba sai kin tambaye ni ba. Duk inda za ki je, ki je ba matsalata bane.”

Kallon shi take tana so ta gano mijinta a cikin shi. Auwal ɗinta da ta Aura amma ko alamun shi bata gani ba. Hajiya Beeba bata son kallon nan da take mishi.

Kishi take ji har ƙasan zuciyarta. 

“Ke kin ji, sai ki wuce ai ko?”

Ko kallonta bata yi ba. Ta wuce ta fita daga gidan. Halin ko in kula da Aisha ke nuna mata yana ci mata zuciya.

Haka shekaranjiya. Da ganga ta jawo Auwal tsakar gida. Din ta ji Aisha ta fito ta sumbace shi tana gaya masa kalamai masu kashe jiki.

Amma ga mamakinta, ko inda suke Aisha bata kalla ba. Balle ma ta nuna abinda Beeba ɗin ta yi ya dameta. Haka ta gama goge takalmanta. 

Ta zo ta gefensu. Ba tare da ta kalle su ba ta gaishe da Auwal bata ma jira ko ya amsa ba ko bai amsa ba ta fice abinta. Hannun Auwal ta kama ta ja shi ciki. 

Duk son da yake ya fita da wuri. Dole ya jira Hajiya Beeba ta gama shiryawa suka kulle gidan suka tafi tare.

***** 

Kamar yadda ta sani kam. Shigar ciki gareta sati kusan biyu da wani abu. Tana tasowa daga makaranta ta dawo gida. Tai mamakin ganin gidan a buɗe. 

Ta shiga da sallama. Ɗakinta ta wuce ta cire hijabi tai sallah. Sannan ta fito daga ɗaki zuwa kitchen. Tana da komai da take buƙata. 

Farar shinkafa ta ɗora ta ci gaba da gyara cefane. Tana tsaye sam bata ji takun tafiyar Hajiya Beeba ba sai wani abu da ta ji saman bayanta. 

“Hasbunallahu wani’imal wakeel.”

Shi ne abu na farko da Aisha ta faɗa kafin ta juyo ta sauke idanuwanta kan Hajiya Beeba da ke riƙe da wata kwalba. Don haka ta ci gaba da jerowa babu ƙaƙƙautawa.

Tana neman tsarin Allah daga koma wane irin abu ne Hajiya Beeba ta watsa mata. A fusace ta ce, 

“Yau zan ga ƙarshen abinda kike taƙama da shi a gidan nan.”

Ta juya ta fice. Dafa kantar kitchen ɗin ta yi. Tsoron da take ɓoyewa yana bayyana. A hankali take faɗin, 

“Allah bani da kowa sai Kai. Bani da abin dogaro sai Kai. Allah ka kareni daga sharrinta.”

Ta ci gaba da jero Hasbunallah. Nutsuwa ta ji ta samu. Ta koma kan aikin da take yi. Tana jin koma menene ta watsa mata yana mata raɗaɗi. 

Bata taɓa ba. Gudun kar ya taɓa abinda za su ci ma cikinsu. Kitchen ɗin ta zauna tana tsoron ta fita ta zo tai musu barbaɗe. Sai da ta gama tas ta kwashe ta zuba a warmer ta ɗauka ta kai musu ɗaki. 

Ɗakin baccinta ta wuce. Ta shiga toilet ta cire kayan jikinta, da su tai amfani ta goge bayanta. Sannan tai wanka ta fito ta sake wasu kayan. 

Ta koma ta yi Alwala duk da lokacin sallah bai yi ba. Ko don zama cikin tsarki da kariyar da ke tattare da hakan. Tana nan zaune yaran suka dawo daga makaranta. 

Abinci suka ci tunda babu Islamiyya suka zauna. Hira suka ci gaba da yi abinsu. Yaran na rage mata damuwa. Suna saka ta jin in tana tare da su cikin lafiya da kwanciyar hankali komai mai sauƙi ne. 

**** 

Da sallama ya shigo gidan. Dai-dai lokacin da Hajiya Beeba ta hankaɗo Zulfa waje tana faɗin, 

“In kika sake shigo min ɗaki saina karyaki. Mayya kawai.”

Da gudu ya ƙarasa ya ɗaga Zulfa da idanuwanta ke cike da hawaye yana riƙeta a jikinshi. 

Duddubata yake ko ta ji ciwo. Ya ce mata. 

“Me kika je yi mata a ɗaki?”

Takardar da ke hannunta ta ba Dawud. 

“Abba aka ce mu ba a makaranta. Shi ne na zo in kawo mishi. Wallahi har sallama na yi mata yaya.”

Ranshi a ɓace ya ɗago ya ce ma Hajiya Beeba da ke tsaye tana hure huren hanci,

“Da kin ji mata ciwo kuma fa. Idan kin mata gargaɗi kawai ya isa ba sai kin nemi taɓa lafiyarta ba.”

Dafe ƙirji tayi. 

“Na shiga uku ni Beeba. Dukana za ka yi? Auwal!”

Da sauri ya fito yana faɗin, 

“Lafiya, menene?”

Kukan munafunci Hajiya Beeba ta fara. Dawud na riƙe da Zulfa yana kallon ikon Allah. Yadda Abbansu ya bi ya rikice gaba ɗaya yana tambayarta ko lafiya. 

“Ka tambayi ɗanka gashi nan…..”

Ta ƙarasa tana sake sakin wani kukan rainin hankali. Rai a ɓace ya kalli Dawud. 

“Me kai mata?”

Muryar shi can ƙasa ya ce, 

“Zulfa ta hankaɗo waje. Na mata magana ne saboda yanayin ƙarfin da ta sa zai iya ji mata ciwo in……”

Bai ƙarasa ba Hajiya Beeba ta ce, 

“Ƙarya yake yi. Zagina yayi. Wallahi ni bazan iya zama ana wulaƙantani ba….”

A dake dawud ya ce, 

“Ƙarya take. Abba kai ka….”

Bai ƙarasa maganar ba, Auwal ya ɗauke shi da mari. Mamaki ya hana Dawud ko taɓa wajen. Idanuwanshi a ware kan Abban shi da tun tasowar shi ko faɗa bai taɓa yi mishi ba. 

Balle tunanin ɗaga mishi hannu. 

“Marar kunya. Yaushe ka lalace haka Dawud. Bata haƙuri wallahi ko ranka yai mugun ɓaci.”

Kanshi a ƙasa ya ce, 

“Kiyi haƙuri.”

Ya kama hannun Zulfa suka wuce zuwa ɗakin Ummi. Yana ɗaga labulen ya ganta a tsaye. Sauke ajiyar zuciya ta yi da alama ta ji duk abinda yake faruwa. 

Zulfa ta kama. 

“Karki sake zuwa musu ɗaki.”

Kai Zulfa ta ɗaga saboda hawayen da ke zubar mata. Ta ƙwace hannunta daga na Ummi ta ruga ɗakinsu. Kallon Ummi Sajda ta yi cike da tuhuma kafin ta miƙe ta bi bayan Zulfa. 

Dawud Ummi ta kalla. Bata son abinda take gani cikin idanuwan shi. 

“Abba ya mareni Ummi.”

Lumshe idanuwa ta yi ta buɗe su. Muryarta da sanyi ta ce, 

“Kayi haƙuri Dawud. Ku ci gaba da addu’a komai mai wucewa ne.”

Idanuwanshi ya ɗauke daga fuskarta ya ce, 

“Sai da safe.”

Yana juyawa ya fice daga ɗakin. Tayyab dake zaune ya ce, 

“Ummi ban miki alƙawarin in wani abu ya haɗo mu da matar can bazan kwaɗa mata mari ba.”

Da sauri ta ƙarasa gefen kujerar da yake zaune ta zauna. 

“Tayyab! Kar in sake jin irin maganar nan. Babu ruwanka da ita. Ka ji na faɗa maka in ba kana son raina ya ɓaci bane. 

Kome zata ce ka wuce karka biye mata. Ba kalar tarbiyar da na baku bace ba, in kuma zaka nuna min ban isa dakai bane to sai ka yi abinda kake so. Ni dai na faɗa maka yadda nake so.”

Tashi yayi. Sai da ya kai ƙofa sannan yai mata sai da safe. Zama ta yi kan kujera ta dafe kanta cikin hannayenta. Abubuwan da ke faruwa suna mata yawo. 

BAYAN WATA BAKWAI

Idan ka tambayi Aisha ya akai ta rayu cikin gidan mijinta da ya zame mata kamar zaman kurkuku. Daga ita har yaranta ba zata ce ga yadda suka kai wata bakwai a cikin gidan ba. 

Rabon da wani haƙƙi na aure ya haɗa ta da Auwal tun ranar da rabon da ke jikinta ya ratsa. Ƙwandalarshi bata haɗa su. Ita take hidimar komai. 

Wulaƙanci da cin fuska kuwa babu wanda bata gani ba a watannin nan. Hajiya Beeba da gangan zata tako har cikin falonta don ta biye mata. Bata kulata amma a hakan sai ta samu abinda zata faɗa. 

Haka Auwal zai zo ya zazzaga mata rashin mutuncin da inda a mafarki ta ga hakan ya faru zata ce wani ne da fuskar Auwal ɗinta ba shi ba. 

Yanzun ko da ya zageta ya kirata da mayya, marar aji, marar mutunci duk ba komai bane ba. Balle kuma azo ga yaranshi. Banda gaisuwa da itama dole ta sa Dawud yake mishi ita babu abin da ke shiga tsakanin su. 

Don a cewar Dawud ɗin baya amsawa. Ta ce haƙƙine akansu ko ba zai amsa ba su gaishe da shi. Banda Sajda babu mai nacin mishi magana. 

Ita kaɗai ce baya ma faɗa. Ita kaɗai take tunkararshi su yi magana ba tare da tsana ko hantara ba. Da alama ko me Hajiya Beeba ta yi ya kasa taɓa Sajda da Auwal ɗin. 

Hatta da ‘yan uwan Auwal da danginshi da matansu Hajiya Beeba bata bari ba. Sai su zo gidan ko gaisuwar arziƙi bata haɗa su. 

Duka duka cikinta ko wata takwas bai cika ba. Amma yayi wani irin girman gaske da yasa wajen aikinta suka bata hutu da alƙawarin zasu dinga biyanta albashin ta har ta haihu ta dawo.

Bata ji daɗin hutun ba. Saboda ya ƙara mata awannin zama cikin ƙunci da ke tattare da gidanta. Har cikin ɗaki Hajiya Beeba ta sha zuwa ta yi iƙirarin cikin da ke jikin Aisha sai ya zube. 

Amma da yake Allah ne Ya ke kare bawanshi ko ciwon kai. Sai dai damuwa mai yawan gaske. 

**** 

Zaune take a gaban malam. Yau ita kaɗai ta zo don Huzai ta yi tafiya zuwa Abuja ita da wani babban ɗan siyasa. Rai a ɓace hajiya Beeba ke cewa,

“Wallahi malam na rasa abinda matar nan take da shi haka. Duk wata kissa da ka sani na bi.

Ka ga dai magungunan da ka bani ba wanda banyi amfani da shi ba. Amma ko ciwon kai banga tana yi ba.”

Jinjina kai malam ya yi. 

“Gaskiya ta ɓangarenta ba za mu ci nasarar komai ba. Dama baki na yi ki gwada ba don na ga komai a kanta ba. Sai dai ki bada a siyo baƙin bunsuru da zakara shekararre. Ai musu farraƙu. Sai ki haɗa da dabara ƙila a dace.”

Jaka ta buɗe ta ɗauko kuɗi ta ajiye mishi. Ta ɗora da faɗin, 

“Sannan shegiyar yarinyar nan Sajda. Ko ɗakina ta shigo na koreta idan yana nan baya bari. 

Sonta yake kamar ranshi. Na shafa mata turaren nan da ka ce . Babu aikin da yayi.”

Ƙasa ya zana ya goge ya fi sau huɗu sannan ya kalleta sosai yana faɗin, 

“Itama abinda ke tare da babarta shinee tare da ita. Tana da kariya mai ƙarfi. 

Abu ɗaya ne nake da shi. Ba kuma na tunanin za ki iya. Tunda yarinya ce ga….”

Bai ƙarasa ba da hanzari ta ce, 

“Ko meye ka bani. Ai wallahi gara ta mutu da in ganta kusa da shi. Na tsane ta.”

Murmushi malam yayi ya miƙe ya shiga ciki. Ya fito da ƙullin magani a hannunshi. Bata yayi a hannunta ya ce, 

“Ki zuba mata a wani abu na ci ko sha ki bata. Za ki zo ki bani labari.”

Karɓa ta yi. Tai masa godiya sannan ta miƙe. Sai da ta biya restaurant ta siya musu abinci don ba girki take ba. Ba kuma ta bari Auwal ya ci abincin Aisha. 

Gida ta wuce abinta. Tana shiga ta kwanta a ɗakinta. Kan kunnenta akai sallar Magariba amma bata miƙe ba. Don batai niyyar yi ba ta san Auwal na gab da shigowa. 

***** 

A falo take zaune kan dardumar da ta yi sallar Magariba. Suna hira da Dawud. 

“Ummi saura paper huɗu fa mu gama NECO.”

Da murmushi a fuskarta ta ce, 

“Kai amma kun yi sauri. Allah ya bada iko. Kwanci tashi babu wuya.”

Sajda ta fito ta ce, 

“Ummi na tafi wajen Abba.”

Kai ta ɗaga mata. Ta wuce. Dawud ya ce, 

“Nikam bana son tana zuwa ɗakin matar can. Babu Allah a zuciyarta sam.”

Jinjina kai Ummi tayi.

“Babu abinda zata yi wanda Allah bai rubuta mana zai samu rayuwar mu ba.

Tunda bata yi nasarar shiga tsakanin sajda da Abbanku ba. In sha Allah ba abinda zai faru. “

Daƙuna fuska Dawud yayi. Shi dai baya son tana zuwa. Kauda kai irin na Ummi ba zai iya shi ba. Baya son yi mata musu ne yasa shi yai shiru. 

Tayyab ya shigo da sallama. 

“Ummi yunwa nake ji, cikina kamar an yi kwasa.”

Dariya Dawud yayi. 

“Aikai kullum ci dai. Gashi baya nunawa a jikinka.”

Zama ya yi a gefen Ummi kan kafet. 

“Don Allah Ummi ban fi Yaya ƙiba ba?”

Dariya Ummi ta yi. 

“Kun ga ku cireni a gardamar kun nan. Ga abinci can ka je ka zuba.”

Har ya miƙe Dawud ya ce, 

“Ka ga nikam zuba min akayi.”

Juyawa ya yi zai yi magana. 

“Ƙyale shi Tayyab. Zuba abincin ka ka ji.”

Dariya Dawud ɗin yayi. Ya so Ummi ta ƙyale shi. Tsokana yake ji yau kuma ta kula da hakan. 

Tana jin daɗin yadda suka barma Allah komai. Musamman Dawud da ke son ya ga ya sa kowa murmushi. Surutu ba damunshi yaiba. A watannin na dole ta sa shi ya koya. 

Haka zaita jan su da hira har sai ya ga kowa ya warware tukunna hankalin shi zai kwanta. Ummi takan kalle shi ne kawai, ga yarinta a fuskarshi da jikinshi amma girma ya kama zuciyar shi. 

Rayuwa ta canza mata Dawud ɗinta. Ta mishi wani sauyi na ci gaba. Sam bai more yarintar shi ba. Saboda bai samu wannan lokacin ba. 

*

Da sallama Sajda ta shiga ɗakin Beeba. Abban ta na zaune kan katifa fa faɗa jikinshi. Da murmushi ya riƙeta yana faɗin, 

“Sajda ‘yar gidan Abban ta.”

Dariya tayi. Ta gaishe da su. Hajiya Beeba ji take kamar ta caka mata wuƙa ta huta da ganin ta. Hatta kamanninta irin na abbanta ne. 

Duk ta fi sauran yaran gidan haske da hanci. Idanuwanta ne irin na mayyar uwarta. Juice ɗin da ta haɗa na musamman ne ta ɗauko daga gefe.

Ta ƙaƙaro wata fara’a ta ƙarya ta ɗora a fuskarta. 

“‘Yan matan Abban ta. Zo ga juice na ajiye miki.”

Girgiza mata kai Sajda ta yi. Don Ummi ta ja musu kunnen ko me zata basu kar su karɓa. 

“Hmm ka ga yaran nan sam basu yarda da ni ba. Uwar su ta gama kitsa musu mugun abu. 

Kome na basu basa karɓa. Kamar wadda zata yi musu wani mugun abu.”

Rai a ɓace Auwal ya ce, 

“Ni bansan lokacin da Aisha ta koyi mugun hali ba wallahi….”

Taɓe baki Hajiya Beeba tayi. Kofin ya karɓa daga hannunta ya ba Sajda. 

“Ungo kisha”

A tsorace ta karɓi juice ɗin. Saboda yadda suka kafa mata idanuwa yasa ta daburcewa. Ko Bismillah bata yi ba ta kafa kai ta shanye juice ɗin tas ta ajiye kofin. 

Tana jin yadda ɗanɗanon ya kama mata harshe. Fuskarta a yatsine ta miƙe daga jikin Auwal. 

“Abba bacci nake ji.”

Apple ɗin da ke gefenshi ya ɗauka ya bata. Har ƙofa ya rakata sannan ya dawo. Hajiya Beeba a ranta ta ce ai daga yau dai zata sa ido ta ga ƙarshen ƙauna. 

Sajda kam cikinta take jin yana wani irin yamutsa mata. Ga kanta da ya fara sarawa. Da ƙyar ta iya kaiwa ɗakin su. Tana shiga jiri na ɗibarta. 

Dawud ya soma kula da yanayinta. Kallonta yake yadda take tafiya har ta kusan ƙarasowa wajenshi kafin tai baya zata faɗi. 

Da hanzari ya miƙe ya riƙo hannunta. Da ƙyar take iya ɗaga idanuwanta. A jikinshi ta faɗi idanuwanta a lumshe. 

Ummi da su Tayyab suka taso da gudu. Da ƙyar Ummi ta zauna gefen Dawud saboda girman cikin da ke jikinta. 

Hannu ta kai tana taɓa jikin Sajda da ya ɗauki wani sanyi. 

“Me ya sameta?”

Tayyab ke tambaya a tsorace. Fuskarta Dawud yake taɓawa zuciyar shi na wani dokawa da jin yadda jikinta yai sanyi sosai. 

“Ba abinda ya sameta Tayyab. Sajda…. Sajda buɗe idanuwanki mana.”

Dawud yake faɗi muryarshi na rawa. Ummi ke ƙoƙarin karɓar Sajda daga jikinshi amma ya ƙi sakinta. 

“Ban ita ka ɗibo min ruwa a kofi Dawud.”

Kai ya shiga girgiza wa Ummi yana sake riƙe Sajda gam. Sai Tayyab ne ya tashi da gudu ya fita daga ɗakin. Zulfa kuwa ta yi tsaye a gefe tana kallonsu idanuwanta cike da tsoro. Ruwan Tayyab ya kawo ma Ummi. Ta ɗiba a hannunta ta na shafama Sajda jikinta na ɓari . Zuciyarta rawa take yi saboda tsoro. Amma ƙoƙarin ɓoye shi take yi. 

“Saida na ce karta je ummi. Na ce karta je wajenta. Wallahi in wani abu ya same ta….”

Kasa ƙarasawa yayi yadda yake jin ƙirjinshi na masa zafi da tunanin wani abu ya samu Sajda. Babu abinda basu yi ba amma ta ƙi buɗe idanuwanta. 

Sai jikinta da yake ƙara ɗaukar sanyi kamar wadda take cikin fridge. Da dabara Ummi ta miƙe ta shiga cikin ɗakinta. Sai lokacin hawayen da take tarbewa suka zubo mata. 

Hannu tasa ta goge su. Hijabinta ta ɗauko da kuɗi ta fito falon. 

“Tayyab ku zauna da zulfa. Karku fito sai mun dawo. Dawud ɗauko ta mu tafi asibiti.”

Kai Tayyab ya ɗaga wa Ummi. Dawud ya miƙe da Sajda a jikinshi. Ya saɓeta a kafaɗarshi.

Ƙafa ya ɗaga ba shiri ya sauke ƙafar saboda wata gigitacciyar ƙara da Sajda ta saki cikin kunnen shi. 

Su dukkansu babu wanda bai tsorata ba. Dirowa tai daga jikin dawud. Kafin su san me ke faruwa ta fice daga ɗakin da gudu. 

Tayyab da Dawud suka rufa mata baya. Da sauri Ummi ta bisu. Ɗakin Hajiya Beeba Sajda ta nufa. Su Dawud suka ɗaga labulen. 

Shaƙeta ta yi tana kai mata duka ko ta ina tana faɗin, 

“Saina kashe ki…”

Tare da wani irin gunji. Abba yai kan Sajda ya kama hannayenta da ke zagaye da wuyan Hajiya Beeba Da take kakari ta kuma kasa ƙwace kanta. 

Hannu ɗaya Sajda ta sa ta hankaɗe Abba. Tayyab ya ware idanuwa cike da sabon mamaki. Ci gaba ta yi da dukan Hajiya Beeba da ɗayan hannunta. Ɗayan kuma na shaƙe da wuyanta. 

Har Ummi ta ƙaraso. Cike da tashin hankali ta matsa kusa da Sajda. Ta kai hannu ta kama kafaɗunta. Ture Ummi ta yi.

Ba don Dawud da ya riƙeta ba da sai ta kai ƙasa. Abin mamaki yake basu. Duka Sajda ɗin nawa take da take da wannan ƙarfin haka. 

Dawud ne ya gwada bamɓareta daga jikin Hajiya Beeba amma a banza. Tun tana ihu har ta yi laushi. Sai da suka haɗu su dukkansu ukun sanna da ƙyar suka cire Sajda daga jikin Hajiya Beeba. Ihu take tana kai musu duka.

“Ku sakeni saina kasheta.”

A tsorace Abba ya saketa. Ya matsa wajen Hajiya Beeba da ta ja jiki tana wani tari a wahalce. Kallon Sajda yake yadda take gunjin ihu. 

Ba fuskarta yake gani ba. Cike da tsoro ya sauke idanuwanshi. A hankali ya ce, 

“Ku fitar min da ita daga nan. Bana son ganinta…. Ku fita!”

Jan Sajda suke yi da ƙyar. Hawaye na zubo ma Aisha suka fice da ita daga ɗakin suka nufi ɗakinsu da ita. 

Da ƙyar Hajiya Beeba ta miƙe. Bakinta duk ya fashe. Kuka take tana haɗa kayayyakinta.

“Ina za ki je?”

Harararshi tayi.

“Wallahi bazan zauna a gidan nan ba. Bazan kwana cikin gidan nan da mahaukaciyar ‘yarka ba ta kashe ni.”

Tana kuka tana haɗa kayanta. Dole ya ɗauki jaka daya shima ya shiga haɗa nashi kayan. Tare suka fita daga gidan zuwa motarta. 

Yana jin ihun Sajda har kusan ƙofar gida. Tsoronta na sake cika mishi zuciya da tunanin abinda ya gani a fuskar Sajda. Hajiya Beeba ta ja mota suka bar unguwar.

***** 

Tunda Ummi take a rayuwarta bata taɓa ganin tashin hankali irin wanda take gani ba yanzun. Danne Tayyab da Dawud suke da Sajda. 

Amma ihu take tana neman ƙwacewa. Zulfa na zaune can ƙarshen dakin ta haɗe jikinta tana ta kuka tana kallon su. 

Zaune Ummi take wajen kanta ta rasa yadda zata yi da Sajda. Tana kallon yadda hawaye ke zubar ms Tayyab. 

“Ummi me ya samu sajda? Meye wannan yake faruwa da mu?”

Ya tambaya. In ta buɗe baki tai magana kuka zai ƙwace mata. Zata ƙarasa rikitasu. Ganin da ta yi Dawud na tofa ma sajda addu’a ya dan dawo da ita hankalinta. 

Abinda ya kamata suyi ne tun ɗazu. Da yake babu nutsuwa tattare dasu bata tuna ba. Sun kai mintina talatin suna mata addu’a kafin ta daina ihun da take yi tayi luf a jikin Dawud. Kai ya ɗan daga ma Tayyab da alamar ya saketa. A hankali Tayyab ya saketa yana kallonta da tsoron karta sake ƙoƙarin ƙwace kanta. 

Addu’a suka ci gaba da tofa mata. A haka bacci ya ɗauke ta. Lumshe idanuwa Dawud yayi tare da sauke wata ajiyar zuciya. Nan suka zauna an rasa mai cewa komai. 

Tayyab ne ya miƙe ya kullo gidan ya dawo ya zauna. Yadda suka ga rana haka suka ga dare. Babu wanda ya runtsa a cikinsu. Haka Sajda ke farkawa ta ci gaba da ihu tana son tashi ta ruga. 

Sai sun jima suna mata addu’a sannan ake samu baccin da ko awa ɗaya bata yi tana yinshi in ya ɗauke ta. Har Zulfa da take kwance jikin ummi a tsorace tana kallon ‘yar uwarta ko gyangyaɗi bata yi ba. 

**** 

Kwanan su biyu a haka. Kallo ɗaya zaka yi musu kasan basu da kwanciyar hankali da nutsuwa. Ummi na son fita awo ranar amma tana zullumin bar ma su Dawud Sajda su kaɗai. 

Inda Allah ya taimaka weekend ne babu makaranta. Sai safiyar ranar. Ba yadda bata yi da su ba suka ce ba za su je ba. 

Tayyab cewa ya yi ma babu abinda zai fahimta a makaranta yana tunanin halin da Sajda take ciki, don haka ta haƙura ta ƙyale su. 

Jikin Sajda babu wani sauƙi sai wajen Allah. Haka zata yi ta ihu, wani lokacin sai ta yi awa biyu tana wani irin kuka. Addu’a kaɗai ke ɗan nutsar da ita. 

Ga Auwal ƙafarshi ko gidan bata sake takowa ba tun daren da abin ya faru. Ta gama shiryawa ta yi zaune tana kallon Sajda da ke bacci. 

“Tunda ba daɗewa kike yi ba. Ki je Ummi. In sha Allah babu abinda zai faru.”

Dawud ya faɗi muryarshi a tausashe. Kai ta ɗaga mishi tana miƙewa. 

“Ku kulle gidan. Sai na dawo kun buɗe.”

Tayyab ya miƙe. 

“A dawo lafiya. Allah ya tsare hanya.”

Dawud ya faɗi. Ta amsa da amin tana wucewa. Tayyab ya bita ya kullo gidan. A daidaita sahu ta shiga zuwa asibitin. 

Ta ko ci sa’a babu wani layi sosai. Ko awa biyu bata yi ba. Amma da zullumi ta yi su. Da tunanin halin da yaranta suke ciki. Sosai likitarta taita faɗa kan ta kwantar da hankalinta. 

Jininta ya mugun hawa wanda hakan ba ƙaramin haɗari bane a wajenta. Murmushin ƙarfin hali Aisha tai mata da cewar in sha Allah zata kwantar da hankalinta. 

Tana fitowa daga asibitin ta ga vice principal ɗin makarantarsu ya kawo matarshi itama awo. Gaisawa ta yi da su. 

Matar ta ce ya sauke Aisha gida tunda tasan zata jima bata gama ba. Da ta ƙi ma don sun matsa ne yasa ta shiga motar. Yana sauke ta gida ta fito tana ganin motar Hajiya Beeba tana tahowa. 

Saida zuciyarta ta doka. Hasbunallah ta ci gaba da karantowa don Hajiya Beeba abar tsoro ce har ta shiga gida. Zaune ta same su, Sajda na jikin Dawud. 

Su kuma suna zaune kusa da su. Da hannu yai mata alamar da ta yi shiru. Aikam a hankali ta ƙarasa cikin ɗakin. Tana ajiye jakarta Auwal na shigowa da faɗin, 

“Munafuka. Yau Allah ya tona miki asiri. Hajiya Beeba ta sha faɗa min kina ha’intata na ƙi yarda. Sai yau na gani da idona. Wallahi kinbani mamaki.”

Su dukkansu kallon hargowar da yake yi suke. Hajiya Beeba ta shigo ta tsaya a bayanshi. A wulaƙance yake kallon Aisha da kalamanshi kema wani ɗaci a zuciya. 

“Abban Sajda ka san me kake furta min kuwa?”

“Dole ki ce haka, tunda kwarton naki ya sauke ki na gani ba.”

Dawud da ke zaune ya zame Sajda daga jikinshi ya miƙe da faɗin, 

“Abba!!!”

Hajiya Beeba ta kalle shi.

“Marar kunya. Shigar mata za ka yi ne ka miƙe kana huci. Ko uban naka za ka daka?”

Harararshi Auwal yayi yana faɗin, 

“Ki barshi Hajiyata. Ba laifin shi bane ba ai…”

Hawayen da Aisha ke tarbewa ne suka zubo. Zuciyarta na ciwo na gaske da kalaman da ya jefeta da su. Don baya sauke haƙƙin shi a kanta baya nufin Allah baya tare da ita. 

“Auwal ka sanni. Kasan halayyata, karka bari Shaiɗan ya shiga tsakanin mu, karka bar zuciyarka ta saƙa maka abinda kasan bazan iya yi ba.”

Ta ƙarasa maganar cike da ɗacin zuciya. Farkawa Sajda ta yi tana sakin wani kuka. Dawud ya ɗauke ta ya riƙe ta a jikinshi yana mata addu’a cikin kunnen ta. 

Amma ko a jikin Auwal. Hannun Aisha ya damƙo yana janta. 

“Zo ki fitar min daga gida…..”

Kuka take tana girgiza mishi kai. Yadda jikinshi ya taɓa nata yasa wata wutar tsanarta sake ruruwa cikin zuciyarshi. 

Duk wata hudubay da Hajiya Beeba ta gama yi mishi a waje tana sake samun wajen zama a zuciyarshi. 

“Fitar min daga gida. Munafuka.”

Kuka take tana riƙe rigarshi. Hannu ya saka ya ɓamɓareta yana hankaɗata ta faɗi ƙasa ba tare da ya duba tsohon cikin da ke jikinta ba. 

Wata irin ƙara ta saki tare da dafe cikinta tana kiran sunayen Allah duk wanda suka zo bakinta. 

Zufa ke tsattsafo mata saboda azaba. Dawud da ke tsaye hannunshi riƙe da Sajda dakee wani irin kuka. Ya ajiyeta ya ruga yana kama Ummi. 

A ruɗe yake faɗin, 

“Ummi…. Ummi tashi don Allah. Ummi sannu.”

Auwal da ke tsaye babu alamar tausayi ko kaɗan a fuskar shi ya ce, 

“Bana son ganinki. Bana son ganin su suma. Wallahi ji nake kamar in yi ihu in naga ko da giccin ku a gidan nan. Ku fita ku bar min gida…..”

Kallonshi Dawud yake yana riƙe da hannun Ummi da har lokacin salati kawai take yi. Kafin ya mayar da hankalin shi kan matar da ta shigo rayuwarsu ta tarwatsa komai. 

Kamar jira take Dawud ɗin ya kalle ta ta ce, 

“Alhajina bana so kana ɗaga muryarka akan wannan banzar. Yau dai komai ya zo ƙarshe. 

In ka ce ta tafi ai dawowa zata yi . Wannan mayyar kuma.”

Juyawa yai, yadda yai mata fara’a za ka rantse da Allah ba shi bane ya gama rashin mutunci yanzun. 

“Wallahi kuwa Hajiyata. Bana son ganinta ko kaɗan.”

Wani murmushin nasara tayi. Tana kallonshi ya juya da tsana da ƙyamata a muryarshi ya ce,

“Na sake ki saki ɗaya. Ki tattara ki bar min gida. Ki nemi uban cikin da ke jikinki. Wannan yaran ma da bani da tabbas akan su ki kwashe su kuyi gaba.”

<< Rayuwarmu 7Rayuwarmu 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.