Skip to content
Part 9 of 51 in the Series Rayuwarmu by Lubna Sufyan

Bedroom ɗin Aisha ya wuce ya shiga ɗauko jakunkunan kayansu yana watsowa waje. Ɗaya daga cikin jakar Hajiya Beeba ta kai hannu zata taɓa Tayyab ya ce, 

“Kuskuren da za ki yi dana sani yana tare da taɓa jakar nan.”

Idanuwanshi da ta kalla ta gansu a bushe. Jira kawai yake duk wani ɓacin rai da yake ji ya sauke shi a kanta suka sa tataɓe baki ta matsa gefe ta riƙe ƙugu tana wasu girgije-girgije. 

Da ƙyar Aisha ta iya ɗago da kanta. Ta ga yadda yau Auwal ke watso musu kaya. Zuwa yai ya wuce. Ɗakin dawud ya fara shiga yana ɗibo kayanshi yana watsowa tsakar gida. 

Kafin ya shiga ɗakin Tayyab. Hannun Dawud Aisha ta kama ta miƙe hawaye masu zafin gaske na zubo mata. Yawo tunaninta yake. Ina Auwal yake so ta je da yara huɗu. 

Da tsohon cikin da babu kunya yake kokwanto akai. Yasan bata da kowa sai shi. Yasan cikin ‘yan uwanta babu mai riƙeta ita kaɗai balle da yara. 

Tsakar gidan ta fita. Duk cikin dake jikinta bai hanata durƙusawa ba ta riƙe ƙafafuwan shi. 

“Ka rufamin asiri Abban Sajda. Ina zani da yara? Ka duba Sajda bata da lafiya. Banda kowa kai ka sani.”

Taɓa shin da take ƙara rura wutar tsanarta take a zuciyar shi. Muryarshi a dake ya ce, 

“Bana son ganinki Aisha. Bana ƙaunar ganinku gaba daya. Inda za ku je ba matsalata bane. Ku bar min gidana shi ne abinda ya dame ni.”

Kuka Aisha take mai tsuma zuciya. Amma ko a rigar Auwal balle ya taɓa shi. Sallama suka ji. Da gudu Zulfa ta fito daga ɗakin.

Su dukkansu babu mai ƙarfin amsa ma Labeeb sallamar da yayi. Mamakin da yake yasa shi kasa ƙarasowa.

Zulfa ma da ya ji ta ruƙunƙume shi. Hannu yasa ya dafa kanta. Idanuwanshi a kafe kan Ummi da ke durƙushe riƙe da ƙafafuwan Auwal tana kuka, ga jakunkuna da kayyakin da ke watse tsakar gidan. Da ƙyar ya iya ɗauke idanuwanshi daga kansu ya juya gefe inda Dawud ya fito riƙe da Sajda a kafaɗarshi. 

Ɗago Zulfa yai daga jikinshi ya kama hannunta ya ƙarasa wajen Dawud. Muryarshi cike da rashin fahimta ya ce, 

“Dawud me ke faruwa ne haka? Lafiya?”

Baki zai buɗe ya amsa Labeeb. Auwal ya karɓe zance da faɗin, 

“Gidana nake so su bar min. Shi ne abinda yake faruwa. Ko ban isa bane?”

Da wani sabon mamakin Labeeb ya taka ya ƙarasa wajen da Auwal yake tsaye. 

“Abba? Subar maka gidanka fa kake faɗi. Abin har yakai haka? Suje ina?”

Da hanzari Hajiya Beeba ta ƙaraso inda suke. Cikin tsiwa ta ce, 

“Kai kuma a suwa? Tsare shi kake da tambaya a matsayinka na…..”

Bata ƙarasa ba ya ɗauke ta da wani irin mari da ya sa ta ganin haske a gilma mata ta cikin idanuwanta. Kunnenta ya daina jin iska. 

“Ba a ɗaga min murya. Ba a min ihu, ba a saka min baki idan ina magana mai muhimmanci….”

Ya ƙarasa maganar yana juyawa kan Auwal. A fusace ya sa ƙafa ya ture Zulfa da ke jikinshi. 

“Labeeb har cikin gidana za ka shigo ka marar min mata? Lallai rashin mutunci ka ya kai. Wallahi ba din Yaya ba yau sai na yi shari’a da kai.”

Wani kallo Labeeb ya watsa mishi. Ya tsugunna ya kamo Aisha da ke share ƙwalla da hannunta. 

“Ummi……”

Ya kira sunanta. Maganar da zai faɗa na maƙale mishi saboda ɓacin rai. Idanuwanshi har sun canza launi. Abba ya kalla. 

“Ba don su Dawud ba da nai shari’a da kai kan taɓa lafiyar mace. Macen da ke ɗauke da tsohon ciki.”

Mari Abba ya kawo ma Labeeb . Ummi ta ture Labeeb din gefe. Cikin kuka ta ce, 

“Labeeb don Allah ka tafi abinka. Bana son ka samu matsala da kawunka a sanadina.”

Kallon Ummi Labeeb yayi. 

“Tunda na taso, ban taɓa ganin bambanci ta ɓangarenki tsakanina da su Dawud ba. 

Tare dake na samu kusancin da na rasa da tawa mahaifiyar. Babu wanda zai ci zarafinki a gabana. Ko da kawun ne da kanshi.”

Cikin hargowa Auwal ya ce, 

“Ku fitar min daga gida! Ku fitaa!!”

Kama Ummi Labeeb yayi. Girgiza mishi kai take. Ta kasa magana saboda kukan da take. Ko ina na jikinta ɓari yake yi. 

Hanyar waje yayi da ita. Ya buɗe motar shi ya sakata ciki kafin ya dawo cikin gidan. Tayyab ya kalla yace mishi. 

“Tayani kwasar kayan nan ka kai min mota.”

Ba musu Tayyab ya shiga taya Labeeb ɗaukar kayan. Hajiya Beeba na kusa da Auwal ta riƙe hannunshi. Sai zare idanuwa take. Har lokacin bata jin iska ta gefen kunnen da Labeeb ya mareta. 

Gaba ɗaya duk wata giggiwa da take ji. Ya nutsar da ita. Da ido kawai take binsu. Har suka gama kwashe kayan dake tsakar gidan gaba ɗaya. 

Ɗaki Labeeb ya ga Tayyab ya shiga. Ya bi shi suka kwaso kayan Aisha dana su Zulfa da ke tsakar ɗakin suka fita. Dawud na tsaye inda yake da Sajda a kafaɗarshi. 

Labeeb ya ƙaraso inda yake. Ya ce mishi. 

“Dawud taho mu tafi.”

Kai ya girgiza mishi. Yana ƙare wa gidan kallo. Gidansu za su bari yau, yana kallon tsakar gidan da yake cike da memories ɗinsu.

Tsaye labeeb yayi. Yana jiran shock ɗin abinda ke faruwa ya gama sakin Dawud ɗin. Yana kallon shi ya taka har inda su Auwal suke tsaye. 

Kallon mutumin da yake tsaye a gabanshi yake. Idanuwa ya kafa mishi yana jin yadda zuciyarshi ke samun wasu akwatuna suna saka mishi duk wani memory me kyau da yake da shi na rayuwar su yana kullewa. 

Yana jin wata ƙofa ta tsanar mutumin da ke tsaye a gabanshi na buɗewa. Muryarshi a dakushe ya ce, 

“Me mukai maka? Me ya canza?”

Amsa yake nema a fuskar mutumin da ke gabanshi ya rasa. Yana kallon bakinshi ya buɗe da alama magana yake amma babu abinda ke zuwa kunnen Dawud. 

Bai samu amsar da yake son samu ba. Don haka ya taka ya wuce Abba ya ƙarasa cikin ɗakinshi. Komai a birkice yake kamar yanda rayuwar su take a birkice a yanzun. 

Yana tuna ranar da suka shirya ɗakin shi da Ummi. Yanayin farin cikin da suke ciki a lokacin. Baiyi mamakin yadda ya datse duk wani ɓangare da Auwal ya taimaka ba ciki. 

Don yana jin yadda komai da ke tsakanin shi da mahaifinshi ya gama warwarewa. Duddubawa yake cikin ɗakin ko akwai wani abu muhimmi da zai ɗauka ya rasa. 

Gaba daya yarintar shi da yake matukar ji da ita. Saboda ƙauna da farin cikin da ke cikinta ce zai bari. Ba tare da an bashi zaɓi ba. Ba tare da rayuwa ta duba halin da zai shiga ba. 

Fitowa ya yi daga ɗakin. Yana sake tallabe Sajda a jikinshi. Ɗakin Tayyab ya shiga. Shima ɗakin ba birkice yake fiye da nashi. 

Saboda ɗakin Tayyab ya fi nashi shirgi da yawa. Yana tuna kalar rayuwar su a ɗakin. Yana jin raɗaɗi a ƙirjinshi da abinda Abba ya ƙwace ma Tayyab. 

Da farin cikinshi da rayuwar daya saba da ya sa ƙafa ya ture shi daga cikinta. Sabuwar tsana ce take ƙaruwa a zuciyarshi. Fitowa yayi daga ɗakin shima zuciyarshi na nauyi fiye da na ɗazun. 

Falon Ummi ya shiga. Kallon komai na ɗakin yake yi. Yana tuna watarana da suke hira da Ummi. 

“Ummi in na yi kuɗi gida zan siya miki babba. Ke da abba ku koma ciki.”

Dariya ta yi.

“Allah ya kaimu lokacin Dawud. Ya kawo masu albarka. Ammanl nikam bazan iya barin gidan nan ba.”

Da mamaki ya ce, 

“Me yasa?”

Numfashi ta ja ta sauke. Da murmushi a fuskarta ta amsa shi da, 

“Akwai farin cikin da ke tattare da gidan nan da bazan iya bari ba. Zamantakewar mu da Abbanku. 

Mun ɗauki shekaru muna gina gidan nan da yarda da amana. Yarintar ku gaba ɗaya tana cikin gidan nan. Ina ƙaunar komai da ke tattare da shi . Bazan iya barin shi ba.”

Yau gashi tsaye cikin gidan da Ummin shi ke ƙauna kamar ranta amma Auwal yasa ƙafa ya hankaɗeta daga ciki. 

Ƙafafuwan shi ya ji sun kasa ɗaukar shi. Durƙushewa yayi a cikin ɗakin da Sajda a kafaɗarshi. Yana jin gunjin da ke fitowa daga zuciyarshi zuwa maƙoshin shi amma sauti ko ɗaya ya ƙi fita daga bakin shi. 

Hawaye masu zafi ke zubar mishi. Yana jin kamar zuciyarshi zata fito daga ƙirjin shi saboda ciwon da take yi. Da zata fito ɗin ma na ‘yan wasu mintuna da ya samu sauƙin azabar da yake ji. 

Yana jin Labeeb ya shigo ɗakin. Sajda yake ƙoƙarin karɓa daga hannunshi ya girgiza mishi kai. Muryarshi a sarke ya ce, 

“Dawud…..ka taho mu tafi.”

Ya kasa magana saboda abinda ya tsaya mishi a wuya. Hannu yasa ya goge hawayen da ke zubar mishi. Ya miƙa ma Labeeb hannu ya ɗago shi. 

Yana ji a jikinshi ba abu ƙarami bane zai sake fito da hawaye a idanuwanshi. Yana jin yadda wani irin girma ya saukar mishi. 

Yadda ya karɓi nauyin da rayuwa ta ɗora mishi. Muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Rayuwar mu ke nan yanzun ko?”

Kai Labeeb ya ɗaga mishi. Bai sake cewa komai ba. Ɗakin yake sake kallo. Sai ya ga duk wani abu da ke da wata kala cikin ɗakin na shigar mishi idanuwa. 

Saboda yadda rayuwarshi ta koma baƙi da fari kawai. Hannu ya ɗago yana kare fuskar shi. 

“Lafiyarka kuwa?”

Labeeb ya bukat. 

“I hate colors.”

Ya amsa shi yana jin maganar na zauna mishi kafin ya fita daga ɗakin. Bai sake duban inda su Auwal suke ba. 

Gabanshi yake dubawa jawai. Yasan wannan alƙawari ne ya ɗaukar ma zuciyarshi. Bazai taɓa waiwayar rayuwar shi ta baya ba. 

Ba kuma zai bari ƙannen shi da Ummin shi su waiwaye ta ba. Ranar litinin ɗin nan ta canza musu komai na rayuwar su. 

Gaban motar Labeeb ya buɗe mishi ya shiga ya zauna yana gyara wa sajda da ke bacci zama a jikinshi, sai da ya rufe murfin motar sannan ya juya baya. 

Ummi ce idanuwanta a bushe suke. Fuskarta ɗauke da yanayin da ya ƙara mishi zafin da ke ƙirjinshi. Zulfa na kwance a jikinta. 

Tayyab ya kwantar da kanshi a kafaɗarta. Su duka zaman makokin Abba suke yi ba tare da sun ga gawar shi ba. 

Dukkansu kukan rashi suke ba tare da komai nasu ya ɓace ba. Suna cike da buƙatar kulawa. Baisan lokacin da tashi buƙatar hakan ta ɓace ba. 

Nemanta yake ya rasa. Yaushe ya daina jin so ko buƙatar a kula da shi? Kallon su Ummi yayi sosai kafin ya maida kanshi. 

Jingina shi yai da kujerar motar ya lumshe idanuwanshi. Yana jin Labeeb ya tashi motar ya hau hanya. Cikin zuciyarshi ya ce, 

“Zan kula da ku ummi. Bansan ko tayaya zanyi hakan ba. Zan kula da ku da dukkan abinda nake dashi.

**** 

Wani ƙaramin flat house da ke nan Ali Alƙali road Labeeb yai parking. Ya buɗe motar ya fito. Bayan ya buɗe da kanshi ya shiga ɗaukar kayansu yana ajiyewa a bakin ƙofa. 

Saida ya kwashe su duka ya rufe bayan motar sannan ya ɗauko mukulli a aljihunshi ya buɗe gidan. Ya shiga da kayan cikin falon. 

Ya fito ya buɗe murfin bayan motar. 

“Ku fito Ummi….”

Ba musu suka fito. Ya rufe murfin. Zai zagaya ya buɗe ma dawud kenan ya ga ya fito. Shi yai gaba suka bi bayanshi. 

Suna saka kafa cikin falon gidan su ma suka saka nasu. Wadatacce ne da komai a ciki. Kan kafet ummi ta zauna. Zulfa ta zauna kusa da ita tana kwanciya ajikinta. 

Tayyab ma ya koma kamar ɗan shekara biyar. Gefen Ummi ya zauna yai shiru. Labeeb ya tsugunna gaban Ummi ya ce, 

“Bazan iya baki wanda kika rasa ba Ummi. Ɗaki uku ne gidan nan, Kowanne akwai banɗaki a ciki. Kitchen ɗin ba mai girma bane ba.

Shi kaɗai ɗanki yake da hali a yanzun. Akwai ayyukan da nayi ba a biyani kuɗina ba. Da kuma wanda na karɓa ban kai da yi ba. 

Inhar nan yayi kaɗan in……”

Da sauri Ummi ta katse shi da faɗin, 

“Bai yi kaɗan ba Labeeb. Ba zaka iya bani wanda na rasa ba, sai dai ka bani wanda ban zaci zan taɓa samu ba. Ban…..”

Kasa ƙarasawa ta yi saboda kukan da ya ƙwace mata. Kanta ciwo yake kamar zai faɗo ƙasa. Ta kasa yarda Auwal ya saketa. Ta kasa yarda abubuwan da ke gabanta suna faruwa dasu. 

Sai dai tasan babu yadda zata yi da ƙaddara. Allah Ya san dalilin da yasa abinda yake faruwa da su a yanzun yake faruwa. Ihun Sajda ya maida hankalinsu wajen da Dawud ke tsaye. 

Ta faɗo daga riƙon da yai mata din da alama bai zaci farkawarta a lokacin ba. Tako faɗi sosai don ta fasa baki jini na ta zuba. 

Yabita yana ƙoƙarin riƙeta tana ƙwacewa. Su Tayyab da Labeeb ne sukai kansu suna taimaka mishi. Amma sun kasa riƙeta balle su duba zurfin ciwon da ta ji. 

Ummi kam juya kanta tai ta kwantar jikin kujerar da bayanta ke jingine tana jin wani sabon kukan na zo mata. Bata da ƙarfin tashi saboda yada bayanta ya amsa sanadiyyar faɗuwar da ta yi ɗazu. 

Bata kuma san kalar ciwon da ke damun Sajda ba. Bata san me zata yi mata ba. Ko wa zata nufa da matsalarta ba. Allah ta riƙe. Shi ne abin dogaronta. 

Ihun Sajda in ya dira kunnenta wani yawo yake yana ci mata zuciya. Ta kai mintina talatin sannan ta ji ta yi shiru. Hanky Labeeb ya zaro a aljihunshi ya miƙa ma dawud. 

A hankali yake goge ma Sajda jinin da ke bakinta. Ta ko ji ciwo sosai a bakin. Kamar haƙorinta ta datsa a jikin lebenta na kasa. 

“Me ya same ta?”

“Nima ban sani ba.”

Dawud ya faɗa gaba ɗaya hankalinshi na kan Sajda. Dafe kai Labeeb yayi. Halin da suke ciki na taɓa shi ta fanni da yawa. 

“Tun yaushe take wannan abin?”

Tayyab ne ya amsa shi wannan karon, 

“Kwana biyu kenan. Bata cin komai, ruwa ma sai da ƙyar ake ɗura mata. Bamu san me ke damunta ba.”

Ya ƙarasa muryarshi na karyewa cike da rauni. 

“Kun kaita asibiti?”

Girgiza mishi kai suka yi su dukjansu. Miƙewa ya yi. 

“Dawud ɗauko ta mu tafi asibiti.”

Tashi Dawud ɗin yayi yana ɗaukar Sajda. Tayyab Labeeb ya kalla.

“Ka kula da su Ummi kafin mu dawo.”

Kai ya ɗaga mishi yana ɗorawa da,

“Yaya yana da exam ƙarfe biyu fa”

Kallon Dawud Labeeb yayi don ya tabbatar da abinda Tayyab ɗin ya ce. Maimakon ya amsa shi sai nufar hanyar ƙofa yayi ya fice. 

Da sauri Labeeb ya bi bayanshi. 

“Da gaske kana da exam?”

A gajiye Dawud ya kalle shi. 

“Bata da wani amfani. Ko na je ba abinda zan fahimta. Suna buƙatata.”

Girgiza mishi kai Labeeb yayi. 

“Ka koma ka sako uniform ɗinka. Daga asibitin in sauke ka makaranta.”

A daƙile ya ce, 

“Bazan yi ba fa. Muje kawai.”

Matsawa Labeeb yayi sosai. Ya kalli Dawud cikin idanuwa. 

“Kana jin sun zama ɗawainiyarka ba? Ban ce ka raba da ni ba. Da me kake son kula da su? In kana son basu abinda suka rasa kana buƙatar karatunka. 

Kana buƙatar tsayawa da ƙafafuwanka kafin su jingina da kai. Sai ka zaɓi me kake so ka zamar musu. Bangon da za su jingina da shi su huta. Ko wanda za su jingina ya ruguje da su.”

Yana kallon yadda Dawud ke tauna maganganunshi. Yake kokawa da zaɓin da ya kamata yayi. Miƙa mishi Sajda yayi. Ya karɓeta yana sauke ajiyar zuciya. 

Jiranshi yayi. Ya kai kusan mintina goma kafin ya fito sanye da uniform. Sajda ya karɓa daga hannun Labeeb. Ya zagaya ya buɗe motar ya shiga. 

Asibitin Dialogue ya nufa da su. Din nan yake da file. Kuma ya dai fi gane ma nan ɗin. Dawud ya ɗan kalla ta gefe kafin ya maida hankalinshi kan tuƙi yana faɗin, 

“I am sorry da dukkan abubuwan da suka faru.”

Ba tare da Dawud ya kalle shi ba. Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Ba laifinka bane ba. Mun gode da duk abin nan da ka yi mana. Bazan manta ba, ban……”

Katse shi Labeeb yayi da faɗin, 

“Bana son wannan shirmen Dawud. Ka sani kaima. Blood kowanne lokaci, abinda zakai min ne, abinda za kai min ne. Meye na min godiya saboda na fara yi maka?”

Dawud bai iya amsa shi da komai ba sai. 

“Hmm…..”

Kawai ya iya cewa, don baida kalaman da zai ɗora akan na Labeeb ɗin kuma. Bai sake cewa komai ba har suka kai asibitin. 

***** 

Suna shiga ciki sajda na farkawa. Wannan karin ma babu abinda ya canza saima ƙaruwa da yayi. Kamar ciwon jira yake su zo asibiti. 

Nurses huɗu suka taya su riƙeta. Saida doctor ya zo yai mata allurar bacci tukunna. Tambayoyi ya shiga jero ma su dawud.

Iya abinda ya sani yake faɗa mishi. 

“Gaskiya za mu yi running test da yawa. Za kuma mu yi mata scanning. Kamar ƙwaƙwalwar ta ce ta taɓu.”

A dake Dawud ya ce, 

“Ba abinda ya samu ƙwaƙwalwar ta!”

Hannunshi Labeeb ya riƙe. Yana son faɗa mishi yai controlling kanshi. 

“Duk abinda ya kamata ku yi mata ku yi doctor. Bari mu ɗan yi magana.”

Labeeb ya faɗi yana miƙewa. Bin bayanshi Dawud yayi. 

“Muje in sauke ka makaranta. In dawo.”

Kai Dawud ya girgiza mishi. 

“Karka fara Dawud. Ba haka muka yi da kai ba.”

Idanuwanshi a bushe ya kalli Labeeb ɗin. 

“Ba ina nufin bazan je bane. Zan hau mashin kawai. Zan samu ‘yar nutsuwa idan na san kana tare da Sajda a nan.”

Hannu Labeeb ya sa a aljihunshi ya zaro wallet ɗinshi. Ɗari biyar ya ɗauko ya ba Dawud ɗin saboda babu wadatattun kuɗi a

tare da shi. Bai kuma san ko nawa za ai charging ɗinsu ba. 

Karɓa Dawud yayi. 

“Ka kula da ita. In wani abu ya sameta……. Bazan iya ɗauka ba…..”

Da sauri Labeeb ya ɗaga mishi kai yana ɗorawa da,

“In sha Allah babu abinda zai sameta. Zan kula da ita har ka dawo.”

Ɗan jim yayi kafin ya juya. Labeeb ya bi shi da kallo yana jin kamar ya karɓa mishi wani abu cikin nauyin da ya ke a kafaɗunshi. 

Ɗago kai Labeeb ya yi ya ga mutane har huɗu suna kallonshi. Da sauri ya koma asibitin. Baya son mutane su gane shi. Matsala za a samu. 

**** 

Sallah kaɗai ta tashi Ummi daga inda take. Tana kallon Tayyab ya kwashe duk kayansu ya kai ciki. Tana idar da sallar waje ta samu ta zauna. 

Gaba ɗaya bata da lafiya take jinta. Bayanta ya fi matsa mata. Don da ƙyar ta iya sallah da shi. Tunanin halin da Sajda take ciki take yi. 

Bata da ƙarfin hana su Labeeb kaita asibiti ne ɗazu. Amma bata zaton ciwon Sajda na asibiti ne. Ƙwanƙwasa gidan ta ji anyi. Da sauri Zulfa ta tashi daga jikinta tana nufar ƙofar. 

Buɗewa ta yi. Ta ɗauka dawud ne ko Labeeb. Ga mamakinta Mamdud ta gani. 

“Zulfan El”

Ya faɗi kamar yadda yake tsokanarta. Ɗan murmushi ta yi. 

“Ina wuni Yaya Mamdud.”

Ya amsa ta da, 

“Lafiya ƙalau.”

Ledojin da ke hannunshi ya miƙa mata. Ko da Labeeb ya kira shi ya ce ya siyo abinci da lemuka ya kai gidan shi yai mamaki sosai. 

Ya ɗauka macece. Yasa shi tunanin wacece da matsayi har haka. Ganin Zulfa ya sake saka shi cikin wani sabon mamakin na me ke faruwa. 

Karɓa Zulfa ta yi. 

“Ka shigo mana.”

Kai ya girgiza mata. 

“Sauri nake. Ki gaishe da su Ummi.”

Bai jira amsarta ba ya juya. Wayarshi ya zaro ƙirar Motorola ya kira Labeeb ɗin ya faɗa mishi ya kawo musu abincin. 

“Yauwa. Kasan me, ka je kasuwa duk wani abu na kayan abinci da zaka iya tunawa ka siyo, ina nufin komai ka kawo musu.”

Sanin halin Labeeb ya sa shi amsa wa da,

“Alright.”

Ya kashe wayar. Motarshi ya buɗe ya shiga ya ja yana wucewa.

****

Ummi zulfa ta miƙa ma ledojin da ke hannunta. 

“Yaya Mamdud ne ya kawo.”

Karɓa Ummi ta yi ta ajiye tana buɗewa. Lemuka ne a ɗaya. Ta fiffito da su. Ɗayar kuma robobin abinci ne da tambarin ostrich rich bites a jiki. 

Ta miƙa ma zulfa guda ɗaya. Duk da tasan ba cinye shi zata yi ba. Tayyab da ke zaune kan kujera ta kalla. 

“Sakko ka ci abinci.”

Ba musu ya sakko. Roba ɗaya ya buɗe. Ya zari wani cokalin a jikin ɗayar robar ya saka a ciki guda biyu. Ture robar gabanta zulfa ta yi. 

“Yaya zan ci da ku.”

Gyara zamanshi yayi ya matsa mata. Ummi yake kallo. 

“Nikam na ƙoshi Tayyab.”

Girgiza kai yayi alamar bai yarda ba. 

“In ba za ki ci ba. Nima na ƙoshi wallahi.”

Tasan halin duka yaranta. Tayyab kan jima bai yi magana serious ba. Amma duk lokacin da yayi to canza ra’ayin shi abu ne mai wahala. 

Cokalin ta saka cikin abincin ba don tana so ba. Haka taita turawa. Su dukkansu roba ɗaya kawai suka iya ci. Garama su sun sha lemukan. Ita kam ruwa kawai ta sha. 

**** 

05:30pm 

Da sallama Dawud ya shigo gidan. Kallon su yake. 

“Sajda basu dawo ba?”

Ya buƙata. 

“Ka shigo ka huta mana.”

Cewar Ummi. Takardun da ke hannunshi ya ɗora kan kujera ya fice daga gidan da sauri. Motar Labeeb ya hango, ya sauke numfashi. 

Tsayawa yayi har Labeeb ɗin yai parking sannan ya ƙarasa inda suke. Bayan motar ya buɗe ya tallabo Sajda ya fito da ita. 

“Me ya sameta? Na ɗauka ko an kwantar da ku ne.”

Cewar Dawud. Girgiza masa kai Labeeb yayi. 

“Muje ciki dai.”

Cikin gidan suka shiga. Labeeb ya kwantar da Sajda kan kujera yana fita daga ɗakin. Ya dawo da sallama. Ƙasa ya zauna yana sauke numfashi a gajiye. 

“Sannu Labeeb…..”

Ummi ta faɗi tana rasa kalaman da ya kamata ta yiamfani da su. Murmushi yayi. 

“An duba ƙwaƙwalwar ta. Ba aga matsalar komai ba. Sun dai bada magunguna na sati ɗaya da allurai. Sun ce mu koma in an gama amfani da su.”

Ledar magungunan ya miƙa ma ummi. Sannan ya zaro kuɗi a aljihunshi da bata san ko nawa bane ba ya ɗora a saman ledar. 

“Ga wannan saboda cefane…..”

Wasu kuɗin ya sake zarowa a aljihunshi tare da waya ya juya ya miƙa ma Dawud. 

“Ka riƙe kuɗin makarantarku ne. In kuna buƙatar wani abu ka kira ni, na saka maka lambata a ciki. 

Zamu tafi Bauchi, nasan zamu iya wuce sati ɗaya.”

Karɓa yayi. Su dukkansu sun rasa bakin da za su yi ma Labeeb godiyar wannan hidimar da yake ta yi da su. Muryar Ummi a karye ta ce, 

“Labeeb bansan me zance maka ba.”

Murmushi ya sake yi. 

“Ki sa min albarka Ummi. Shi kowanne yaro yake buƙata.”

Ƙwallar da ta zubo mata tasa hannu ta share.

“Allah yai maka albarka. Allah ya ɗaukaka ka fiye da haka.”

Ya amsa da amin yana miƙewa don sauri yake yi. 

“Don Allah Ummi ki kula mana da kanki sosai. Banda yawan tunani.”

Kai kawai ta iya ɗaga mishi. Su Zulfa sukai mishi Allah ya tsare hanya. Dawud kuma har bakin mota ya raka shi. 

“Bansan me za mu yi ba idan babu kai.”

Ya faɗi yana kallon Labeeb ɗin. Har zuciyar shi yake nufin abinda ya faɗa. In da bai zo a lokacin da ya zo ba da baisan yadda za su yi ba. 

“Ka daina min magana kamar jinin mu ba ɗaya bane ba. Za mu yi faɗa ne kawai in har kuna buƙatata baku neme ni ba.”

Labeeb ya faɗi yana kallon Dawud ɗin don yasan da gaske yake mishi za su yi faɗa in suna buƙatar wani abu basu neme shi ba. 

“Zan kira in sha Allah. Mun gode.”

“Shhhhh. Ka kula da su, ka ƙarasa exams ɗinka. Karka manta kana bukatar karatunka in har kana son tsaya musu.”

Jinjina kai Dawud yai cike da yarda da maganar Labeeb ɗin. Kafin ya buɗe mota ya shiga da faɗin, 

“Saina dawo. Take care.”

“Allah ya tsare. Be safe.”

Kai kawai Labeeb ya ɗaga mishi ya ja motar. Tsaye Dawud yayi har sai da ya ga ɓacewar motar Labeeb tukunna ya koma cikin gida. 

*

Da alama kome sukai ma Sajda yayi aiki. Don har tara na dare bata sake farkawa ba. Sauran abincin da sukaci da rana shi suka ɗan ci da dare. 

Dawud ya ɗaukar ma Ummi Sajda da Zulfa ya kai mata su ɗaya daga cikin ɗakunan. Kallon Ummi yayi sosai tana zaune a gefen gadon ta yi shiru. 

Tsugunnawa yayi a ƙasa. Ya kamo hannayenta. Muryarshi da rauni a ciki ya ce, 

“Ummi bazan iya kula da ku babu ƙarfin gwiwar ki ba. Ina buƙatar strength ko ya yake daga wajenki. 

Nasan dukkanmu bamu taɓa hango faruwar abinda ya faru da mu a yau ba. Amma ke kike faɗa mana abubuwa suna faruwa da dalili. 

Nasihar ki ce cewar ƙaddara na zuwa mana ta fannoni da dama. Ba sai ta zo mana da abu me kyau za mu karɓeta da hannu biyu ba. 

Bance karki damu ba Ummi. Ina roƙonki ki rage damuwar karta taɓa lafiyarki. Allah yasan da mu, kin gani da idonki bai bari mun wulaƙanta ba.”

Tunda ya fara magana ya kashe mata jiki. Hawaye sun ƙi daina zubar mata. Ya kuma bata ƙwarin gwiwa. Ya ƙarfafa mata zuciya, ta ji daɗin yadda duk wata tarbiyya da ta ɗora shi akai yake riƙe da ita. 

Gashi yau da wannan tarbiyar yayi amfani yake mata nasihar da ta shigeta ba kaɗan ba. Muryata na rawa ta ce, 

“Allah yai maka albarka Dawud. Allah ya haɗa min kanku. In sha Allah zanyi ƙoƙari. 

Ka je ka kwanta ka huta. Ka ga gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta.”

Sajda ya ɗan kalla. 

“Ko dai duk mu kwana waje ɗaya ne. Karta farka da dare.”

Girgiza mishi kai Ummi ta yi. 

“Babu abinda zai faru in sha Allah. Ku samu bacci yau ko ya yake.”

Miƙewa Dawud yayi. 

“Kema ki yi bacci don Allah Ummi.”

Ɗan murmushi tai mishi tana saka hannu ta goge fuskarta. Zame jikinta ta yi ta kwanta. 

“Ka kashe mana wutar ɗakin in ka fita”

“To. Allah ya tashemu lafiya.”

Ta amsa da amin. Tana binshi da kallo cike da alfahari da godiya ga Allah da kyautar ɗa kamar Dawud. Ƙwan ɗakin ya kashe musu ya ja ƙofar a hankali yana ficewa. 

Tayyab ya samu tsaye bakin ƙofar ɗaya daga cikin bedroom ɗin. Sai da ya ji zuciyarshi ta doka. Da sauri ya ce, 

“Tayyab lafiya dai ko?”

Cikin sanyin murya yace. 

“Lafiya ƙalau.”

Numfashi Dawud ya sauke. Dafa kafaɗar Tayyab yayi tare da faɗin, 

“Wuce ka kwanta to.”

Cikin idanuwa Tayyab ya kalli Dawud ɗin da tsoro a nashi idanuwan. 

“Na san baka son sharing ɗaki da kowa. Na tsani tambayarka da zanyi. Yaune kawai na maka alƙawari. Bansan meke damuna ba….kawai ban sani ba ne…..”

Kai Dawud ya jinjina tun bai ƙarasa maganar ba. Yana katse shi da faɗin, 

“Na fahimta. Mu je mu kwanta.”

Wani numfashi Tayyab ya sauke. 

“Na gode.”

Kafaɗa yasa ya ɗan ture shi. 

“Don’t be silly. Ina nan duk in kuna buƙatata. Za mu yi sharing ɗaki daga yau har ranar da kake jin kana son zama kai kaɗai.”

‘Yar dariya Tayyab yayi yana tura ƙofar ɗakin ya shiga ciki da faɗin. 

“Really?”

Ɗakin Dawud ya shiga shima yana ɓalle maɓallan da ke jikin rigarshi. 

“Da gaske.”

Gabanshi Tayyab ya zo ya tsaya. Ya haɗe hannayenshi yana tafa su kusa da fuskar Dawud. Ƙara haɗe fuska yayi. 

“Meye haka?”

“Hello. Ko waye wannan ya ɗan kauce ina son Yayana Dawud ne.”

Hararshi Dawud yayi yana ci gaba da ɓalle maɓallan rigarshi. 

“Da gaske nake. I am freaking out anan. Mr. I don’t share room da kowa ne yake offering haɗa ɗaki da ni na tsawon lokaci.”

Rigar da Dawud ya cire ya dunƙule ya jefa ma tayyab a fuska. 

“Saika ƙarar da maganar ka. Sai ka bar mu muji kunnuwan mu.”

Ƙarasawa yai kan gadon ya kwanta. Tayyab ya zagaya ta ɗayan ɓangaren ya kwanta shima. Murmushi yake son gani a fuskar dawud ɗin ko ya yake shi yasa yake ta tsokanar shi. 

Kuma ya ga alama ba zai samu ba. Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Na kasa yarda Abba ya mana abinda yai mana yau.”

A daƙile Dawud ya ce, 

“Daga lokacin da muka fito da ƙafafun mu daga gidan can muka kulle alaƙa da shi. 

Hakan na nufin har maganarshi. Ba Za mu yi maganarshi ba. Za mu yi rayuwa kamar babu shi yadda nasan zai yi kamar babu mu.”

Gyara kwanciya Tayyab ya yi ya ce,

“Ina tsoron rayuwar nan. Yadda komai yake canzawa lokaci ɗaya yana tsorata ni.”

Juyowa Dawud yayi ya kalli ƙanin nashi. Banda fuskar shi har a muryarshi tsoron da yake faɗi ya fito. 

“Ka kalleni nan Tayyab. Bazan bar komai ya cutar da ku ba. Ina nan kana jina. Bazan iya zame maka abinda ka rasa ba. Zan zame maka fiye da mutumin da ka rasa yau. Saboda bazan taɓa wulakanta ka kamar yadda yayi ba. 

Ka bar min duk wannan tunanin. Abinda za ka yi shi ne, ka je makaranta, ka yi farin ciki, ka yi ƙoƙarin gyra rayuwarka kamar babu abinda ya faru. 

I will take care of you. Ku dukkanku, i promise.”

Wani numfashi Tayyab ya sauke mai nauyi. 

“Ka yi alƙawari babu abinda zai sake faruwa?”

Da sauri Dawud ya ɗaga mishi kai yana ɗorawa da, 

“In sha Allah.”

Kai Tayyab ya ɗaga mishi. Yana kallonshi yai addu’a ya shafe jikinshi kafin ya rufe idanuwanshi. 

“Allah ya tashe mu lafiya.”

Dawud ya faɗi. Ya amsa shi da amin. Kafin ya ji numfashin shi ya canza alamar bacci ya ɗauke shi. Tashi zaune Dawud yayi yana dafe kanshi cikin hannayenshi. 

Yasan ba zai iya bacci ba. Don baya iya bacci da wani a kusa da shi. Ya rasa dalilin hakan. Tunanin yadda zai kula da ƙannen shi da Ummi yake yi.

Miƙewa yai ya shiga toilet din dakin. Alwala ya ɗaura ya fito. Ya saka riga don singlet ce a jikinshi. Sallar Nafila yayi sannan ya zauna yana addu’ar Allah ya tsare mishi ƙannen shi da Ummi ya basu juriya. 

Tayyab ya ji yana ihu yana kiran. 

“Abba..!”

Da sauri ya tashi ya nufi kan gadon. Riƙo shi yai jikinshi yana girgiza shi. 

“Tayyab mafarki ne……mafarki kake yi.”

Yake faɗi yana rocking ɗin ƙanin nashi yana tofa mishi Addu’o’i har saida ya ga ya nutsu tukunna ya gyara mishi kwanciya ya sake mishi addu’a. 

Gefe ya kwanta ba don yana jin ko alamun bacci ba.”

*******

Ummi ma sallar ta yi. Ta jima tana addu’o’i da karatun ƙur’anj kafin ta koma ta kwanta. Ga mamakinta wata irin nutsuwa take ji ta daban. 

Bacci ya ɗauke ta babu tunanin komai a zuciyarta. Bata farka ba sai asuba. Zulfa ta tasa ta yi sallah. Sannan ta koma toilet ɗin tai wanka. 

Tasan sai ta yi aike yau. Don suna buƙatar kayan amfani na cikin gida. Daga kan tukwanen girki da plates, sabulun wanka dana wanki.

Ba su fito daga ɗakin ba sai wajen ƙarfe bakwai. Har lokacin Sajda bacci take don ɗaki suka baro ta. Dawud ya fito daga ɗaki suka gaisa da Ummi. 

“Ya sajda ta kwana?”

“Bacci take har yanzun.”

Kai ya ɗan ɗaga. 

“Ni da Zulfa zamu tafi. Mun yi magana da Tayyab ya ce zai zauna har saina ƙarasa exams zuwa ƙarshen satin nan. 

Saboda Sajda.”

Murmushi Ummi ta ɗan yi. Tana mamakin yadda yaran nata suka girma lokaci ɗaya. Rayuwa ta sa sun yi hankali har haka. 

“Sai kun nemi wani abu kun ci a makaranta. Labeeb ya sa an kawo mana komai jiya. Amma babu kayan aiki.”

Takalmi dawud yasa ya ce,  

“Ba matsala Ummi. Sai Tayyab ya fita ya siyo muku abinda za ku karya kuma. Zulfa ta so mu tafi, Ummi sai mun dawo.”

“Allah ya tsare. Ya dawo da ku lafiya. Ku dai yi addu’a.”

Suka amsata da In sha Allah. Suna ficewa. Jingina kanta ta yi da kujera, zazzaɓi take ji sama sama. Ga tashin da ta yi ɗazu ya tabbatar mata da rayuwar su ta yi wani sauyi da bata zaton zai koma dai dai. 

Komai ya canza. Ƙaddara ta ƙwace musu abinda suka saba da shi. Sai dai ta basu sauyi na daban. Ta fannin da bata taɓa hangowa ba. Godiya ta yi ma Allah. Don Shi yasan komai, Yake kuma da Iko da komai. Fatan ta ɗaya, Allah ya basu juriyar cinye jarabawar da ta same su.

<< Rayuwarmu 8Rayuwarmu 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.