A hankali ta fara bude idanunta da sukayi luhu-luhu saboda tsananin kumburin da fuskarta tayi sanadiyyar buguwar da tasha a kan fuskar tata, jingim taji fustar tayi mata ta yanda da kyar take iya bude idanunta, hakan ya taimaka matuka wajen rage mata ganin abinda take saita kallonta akanshi sai dai dishi-dishi.
Jikinta yayi mata nauyi matuka, musamman kafafunta wadanda suka kasance a kumbure, hakannema yasa dakyar take iya motsa su. Duk wannan matsanancin yanayin da Naja’atu ta tsinci kanta ciki ya samo asaline ta dalilin shigar kayoyi, tuntube hade da muguwar buguwa da tayi a yayin. . .
Masha Allah. Fatan alheri
Fatan nasara
Muna biye
Fatan nasara