Skip to content
Part 2 of 4 in the Series Rayuwata by Tripleaaa

A hankali ta fara bude idanunta da sukayi luhu-luhu saboda tsananin kumburin da fuskarta tayi sanadiyyar buguwar da tasha a kan fuskar tata, jingim taji fustar tayi mata ta yanda da kyar take iya bude idanunta, hakan ya taimaka matuka wajen rage mata ganin abinda take saita kallonta akanshi sai dai dishi-dishi.

Jikinta yayi mata nauyi matuka, musamman kafafunta wadanda suka kasance a kumbure, hakannema yasa dakyar take iya motsa su. Duk wannan matsanancin yanayin da Naja’atu ta tsinci kanta ciki ya samo asaline ta dalilin shigar kayoyi, tuntube hade da muguwar buguwa da tayi a yayin gudun tseratar da rayuwarta da tayi.

Koda yake bata iya gane kowaba a cikin samarin da suke tsai-tsaye akanta amma takan iya jiyo maganganun da sukeyi sama-sama, dalilin kenan da yasa ta fahimci cewa ta sami taimako ne daga wadan nan samarin kuma ba masu cutarwa bane a gareta. A hankali ta sauke sassanyar ajiyar zuciya tare da fara kokarin tashi zaune.

“Yi hakuri tukunna”

Wani daga cikin matasan ya ce mata.

Jin abinda matashin saurayin yace da itane yasa ta koma ta kwantar da jikinta kamar yanda yake a cen baya. Sannu a hankali zuciyarta taci gaba da bugawa cikin sauri banyan da tunanin yayanta da kakarta suka bijiro mata. Siraran hawaye masu dauke da wani irin yanayi na zafi suka gangaro ta gefen idanunta.

“Ai saidai hakuri sai kuma neman hakkin mu wajen ubangiji.”

Wanda yayi magana da farko ya sake yin magana bayan daya fahimci halin da Naja’atu take ciki tare da sauran yan matan da suka sami damar cetowa daga dimuwar da suka shiga a cikin daji.

 Kuka taci gaba dayi irin na wanda ke tattare da kunar zuciya hade da takaicin abinda ya faru da ita da sauran danginta

“Dan Allah ina yayana da kakata suke? Sun kashesu ko?”

Ta katse shirun dake dukan kunnuwan duk wanda ke wajen ta hanyar jero tarin tambayoyin  wa saurayin da ya kasance jami’in kato da gora.

Jim yayi tare da rasa amsar tambayar dazai amsa daga cikin jerin tambayoyin data jero mashi

“Kiyi hakury ana kan binciken hakan.”

Wani matashin dake dan nesa dasu zaune saman wani kutittiren icce yayi karaf ya amsa mata tambayar a takaice.

Shiru ne ya sake mamaye wajajen tun bayan amsar da abokin aikin matashin saurayin ya bata, babu wanda ya kara magana a wajen. Saidai haske-hasken fitulun dake hannun su da keta faman giftawa  nan da cen.

“Oga har yanzu akwai sauran mutane a cikin dajin nan fa”

Wani daga cikin yan kato da goran ya fadi yana kara haska fitilarshi izuwa wata kusurwa a cikin dajin.

“Ina sane da hakan,amma dai ai kasan yan bindigar nan basu bar cikin dajin ba kuma zasu iyayi mana dirar mikiya kowane lokaci ko?”

Wanda aka kira da ogan yayi maganar yana kallon sauran mutum biyar din da suke a tare dashi. Sannan yaci gaba da magana.

“abinda nakeso muyi shine wadan nan da muka samo mu rikesu har zuwa lokacin da asubahi zata kawo jiki, sai mu kasu gida biyu wasu sukaisu gidan mai unguwa wasu kuma su sake danna kai cikin dajin dan ceto wadanda sukayi saura”

“Kumafa hakane oga”

wani daga cikinsu ya tari numfashin ogan nasu yana kara yiwa zungureriyar bindigar dake hannunshi duri hade da zukar hayaki ta cikin lohen dake makale a bakinshi wanda yake cike taf da tazargade hade da katon garwashin wuta a tsakiya.

“Abinda nakeso daku shine a rage wannan haske-hasken sannan duk wanda yake anan yayi hakuri ya kama bakinshi yayi shuru zuwa na dan wani lokaci”

“To kundai jin”

Wani dan jelelen saurayi wanda yafi kama da an jika zakara da ruwan sanyi ya furta sa’an nan ya saka lohen dake rike a hannunshi wanda aka cika taf da lodin tazargade da katon garwashi a tsakiya cikin baki akan manyan labban shi ya sake maida lohen tare da zuka hade da fitar da hayakin ta baki da hanci bayan  kusan mintuna biyar  zukar farko da yayi daga baki sa. Sannan ya furta kalmar

“Allah dai ya kare bala’i, kowa ya zuki lohe kafin gari ya waye”.

Fadin hakan yasa kusan dukkaninsu biyar din sun kaure da dariya cikin nishadi.

 Kimanin manya da kananan matan biyar dake kwankwance a kasa cikin yanayi na gajiya da gala baita duk suka amsar da “to”. A galabaice wasu kuwa iya kasu kawai suka iya dagawa.

Naja’atu bata iya cewa komi ba sai dai hawayen takaicin abinda ya faru tare da sake-saken abubuwa iri daban-daban da zuciyarta taketa faman ruwaito mata akan dan uwa da kuma kakarta.

Shiru illahirin wajen yayi na kimanin mintuna talatin da bakwai amma kuma daga nan sai komi ya canza yayin da lamarin gaba daya ya sauya daga yanda suke ganinshi izuwa wata sifar ta daban.

A saman mashina suke mutum bibbiyu wasu kuma ukku, hannayen na goyen rike da manyan bindugu. tsananin hasken fitulun mashinan kanshi ya isa abin ban razani musamman ga wanda ya kasance dama a razanen yake. tamkar rana haka suke ganin ko ina a kusa da nesan su. Dalilin kenan dayasa  tun kafin su iso inda yan Kato da goran ke tsai-tsaye suka fara auno masu harbin bindiga.

Tuni yan kato da goran suka fara mayar da martani da bindugunsu masu tashi dai-dai ko kuma baushe kamar yanda suke kiranta, koda yake bata wuce a halbata sau daya ko biyu ta kare hakanne yasa ba’a jima da fara dauki ba dadin ba dole yan sa kai suka fara kokarin ja da baya tare da arcewa suna barin wadanda  suka ceto din a kwan-kwance kasan katuwar bishiyar da suke.

Tun sa’ar da naja’atu taji karar harbin bindigar farko ta shiga cikin yanayi na kaduwa da tashin hankali marar misaltuwa, ta gaza yin katabus da nufin tseratar da rayuwarta, tuni wasu zafafan hawaye suka gangaro akan kumatunta takaici da bakin cikin abinda ke shirin faruwa da rayuwar ta yaci gaba dayi mata kuna a cikin ranta. cikin abinda baikai dakika goma sha biyar ba ta ganta a tsakiyar mahaya baburan, kowannen su fuskarshi nade cikin rawani yayin da na goyen ke rike da manya-manyan bindugu masu sarrafa kansu, hakan yasa suka kasance masu matukar hadari

Dariyar mugunta suka dauka kusan su dukkanin su, bayan da suke kara haske duk matan da suke kwan-kance a wajen.

“An gudu ba’a tsira ba”

Daya daga cikin fulanin ya furta da wata irin murya mai kama data fulani.  A lokaci guda kuma ya diro daga saman mashin dinshi cikin gadara bayan kafe mashin din ya tunkaro inda naja’atu take a kwance.

“Iyakar gudun naka kenan”?

Yayi maganar tare da zungurarta da bakin bindigar dake rike a hannunsa.

Cikin kunar zuci naja’atu ta kalleshi da idanunta da basa budewa sosai

 “ka kasheni kamar yanda kuka kashe yan uwana”

Cikin azama yaja da baya tare da saita kanta yana shirin harbawa, karar harbin bindiga da sukaji a bazata a sararin samaniya ne yasa Naja’atu tasa hannayenta bibbiyu ta dafe kanta.

Katuwar muryar data biyo bayan harbin bindigar yasa sukayi shuru suna sauraren abinda zai fadi.

“Inada bukatarta da ranta”

Ya fadi tare da juyawa ya hau saman mashin dinshi

“Ru-ru-ruwwwa”

sukaji wata murya tana fadi cikin kakari

Kusan su dukansu suka dauka da dariya yayinda suke kara haskeshi da fitulun mashi nan su

Zungureriyar bindigarshi ta baushe tayi gefe guda yayinda lohen dake dauke da tazargade yake yashe a gefenshi. Cikin yanayi na ban tausayi ya biyo hasken da kallo ya sake furtakalmar

“ru-ru-ruuuu”

Bai idasa fadi ba kuma ya maida kanshi kasa

Kusan  dukkanin na kan baburan  saida sukayi dariya. faruwar hakan yayi dai-dai da umarnin da shigaban tafiyar ya daba akan matan da suke a kwankwance.

Tamkar sun kama bayi haka suka daddaure hannayen su sannan suka hada da bayan mashin guda daya suka daure.  A haka suka ja mashin din tare da sake danna kai cikin daji. tafiya sukeyi ba ji ba gani tun cikin dare har gari ya kusa wayewa, duk wacce ta tsaya to za’a sami wasu daga cikinsu su ringa zaneta da bulalar dake  rike a hannun su har sai sun mike sunci gaba da tafiya, a haka har suka samu suka izo wani waje mai yalwar dogayen itace,hakan yasa wajen ya zamto mai yalwar sassanyar iska mai tsananin ratsa jiki,  a lokacin al fijir ya keto, babu komi a wajajen sai manyan, tanti- tanti  hade da wasu dakuna da sukafi kama da rumbu.

Wasu zaratan matasa masu rike da kwatankwacin makaman da wadanda suka dawo din ke rike da.  suka iso suka tari wadanda suka dawo tare da tisa keyar matan da aka kamo izuwa daya daga cikin dakin mai kama da rumbu.

Saidai ita naja’atu wani daki aka kaita na daban da inda aka ajiye sauran matan da aka kamo su tare, ciki galabaita ta fada saman turbayar dake baje a cikin dakin bayanda aka bankadata ciki.duk da saman turbaya ta fada amma taji zafin faduwar kasantuwar hannayenta a daure suke har a lokacin, wani gwauron numfashi taja tana tunanin abinda zai biyo baya bayan kasancewarta a hannun yan bindigar.

Ksancewar naja’atu ita kadai a cikin dakin ne yasa ko kadan hankalinta ya kasa kwanciya, hakannema yasa kome suka kawo mata bata cinshi saidai suzo su tarar dashi yanda suka kawo shi. Ko dakan kuma ko alama basa damuwa da hakan illa wani mutum daya daga cikinsu da yakan dau lokaci ya tausasarta yana bata hakuri akan yanayin data tsinci kanta a ciki yana nuna mata ta daure ta ringa cin abida suke kawowa amma ko kadan bata kula ta tashi.

Dalilin kenan da yasa ta fara fita daga kamanninta saboda matsananiciyar yunwa dake damun ta, babu shiri ta fara sauya tunani tare da daukar shawarar da wani saurayi yake bata ganin kada ta rasa rayuwar ta  banza. Saidai me? Ko kadan bata cin abinda wani ya kawo mata idan dai ba wannan saurayin ba. Shi kanshi ya fahinci hakan dalilin kennan da yasa ya ke kokarin ganin ya kasance mai kawo mata abincin ko wane lokaci.

A haka har ya kasance sun fara sabawa da saurayin. Wata rana bayan ya kawo mata abincin ya juya zai fita har yakai bakin kofar katakon ya kama zai bude sai cewa yayi

“Don Allah ki ringa sakani a adduan da kikeyi, nima Allah ya kubutar dani daga cikin wannan kangi.”

A sanyaye ta dago tana kallonshi bayanshi da wani irin yanayi irin na rashin fahimta.

Bai kara cewa komi ba ya idasa bude kofar ya fita.

Tunani kala-kala suka ziyarci zuciyarta amma sai tayi watsi dasu ta hanyar mayar da kallonta izuwa dan karamin kokon dake ajiye a gabanta.

Furace da taji damu da madarar shanu

“Ko tantama banayi wannan nonon an sameshi ne a jikin shanun da aka sato”

Ta fada a cikin zuciyarta

Ta rasa yanda akayi sai ji tayi tana matukar son shan furar.

A sanyaye tasa dan karamin ludayin dake ciki ta kamfata tare da bisimillah hade da kaiwa cikin bakinta, dadin da taji furar tayi ne yasa ta kara mayar da ludayin ta kuma kamfato a karo na biyu tare da antaya damammayar furar  bakinta, kokarinta na kara shan furar a karo ukku ya hadu da mummunan cikas dalilin jin nauyin da jikinta hade da juyawar da taji gaba daya duniyar tanayi mata, da kyar take iya bude idanunta hakanne yasa ta saki kokon furar dake hannunta.

Da murmushi akan fuskarshi ya banko kofar katakon bambanta dakin bukkar da sararin subhana, kai tsaye ya tunkaro inda take kwance.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rayuwata 1Rayuwata 3 >>

4 thoughts on “Rayuwata 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×