Skip to content

Rayuwata | Babi Na Daya

3
(3)

Gudu take yi iyakar iyawar ta,ko ba’a tambaya ba daga ganin irin wannan gudun kasan ana kokarin tserema wahala ne ko kuma wani mummunan yayi da aka tsinci ake kuma kokarin tserema hakan. a duk inda kaga mutum yana gudu irin haka to tabbas hadarin da yayi tozli dashi yafi karfin tunanin mai tunani, Tabbas irin wannan gudun wuce sa’ar da budurwar keyi ko shakka babu za’a iya misaltashi gudun ceton rai, ko kadan kuma ko alama babu wani yanayi da zaka kalla a tattare da ita kaga alamun gajiyawa ko sarewa a cikin yanayin da take na sharar gudun duk kuwa da lokaci mai tsawon da ta share tana keta iyakar gonaki da kuma wasu daga cikin dannin gidajen fulanin da suma tuni suka nemawa kansu mafita ta hanyar tserewa tashin hankalin daya kunno masu a cikin tsohon daren. Tsananin zogi da zafin Tuntube ko karo da kananun kutittiren icce da kananan duwatsu ko kadan basusa ta gajiyawa ba bare kuma ta tsayawa ta duba inda ta bige din, a haka take jurewa dukkanin radadi tare da zafin dake shigarta duk  dan ganin ta tseratar da rayuwar ta daga harin yan bindigar da suka yiwa kyauyen nasu kawanya a tsakiyar daren.

Takan dimaucewa tare da kara azama aduk lokacin data ji dajin yayi amsa kuwwar amon tashin bindiga, wanda takeji kamar a cikin kwakwalwarta ake halba war, a duk sa’adda taji tashin bindigar tanaji ne kamar itama tata kwakwalwar akeson fiddawa daga cikin kanta kamar yanda taga an yiwa wasu mutane da kuma wasu daga cikin yan uwanta ace cikin kauyen nasu data baro,  tashin hankali tare da tsoro sukan kara mamaye illahirin zuciyarta wanda hakan kan kara mata dauriya tare da juriya hade da jajircema wahalar gudun da take faman yi,a iya nata tunanin da hangen ta hakanne kawai hanyar tsira idan tayi kokarin tserema yan bindigar da keta faman halbin kan uwa da wabi.

Wani sabon sautin harbe-harben bindigar taji acen nesa da ita ya amsa amon tare da karade ko’ina a cikin tsohon daren.

“Angudu ba’a tsira bah…” wani sahen zuciyarta ya ambato, tabbas wannan gudun tsirar da takeyi tanayinsa ne don ta isa dan karamin kauyen da suke makabtaka dashi ta sami mafaka anan.amma ga mamakin da takeyi sai taga suna suna cikin irin halin da suka tsinci kansu.  

Gigicewa ta karayi yayinda tashin hankalin da take ciki ya bayyana karara akan fuskarta, bata jira komiba ta fara kokarin canza akalar gudun nata izuwa wani sashen dataji babu alamun karar harbin bindigar, tayi nasarar canza akalar gudun natane bayan datayi karo da wani kutittiren icce wanda yayi sanadiyyar faduwarta hade da wuntsilawa harsaida ta furta kalmawa “wayyo Allah na” a bayyane sannan ta mike ta sake ranta a nakare tare da nausawa cikin duhun dajin batasan inda take tunkara ba.

Rashin sani kaza ta kwana kan dame,  Da Naja’atu tasan abinda zata tarar a inda ta nufa to data tayi abinda hausawa ke cema ‘gudun da babu tsira..’ bata jima tana keta iyaka da kunyayyakin gonaki ba ta sake cin karo da wani dandazon yan bindigar dayafi wanda ta baro a ce baya tayi.

Turus taja ta tsaya tana haki hade da maida numfashi lokacin da ta hangi duhun mutanen da sukayi gungu-gungu a wajaje daban-daban, yayin da wasu daga cikin su ke rike da bindiga a hannu suna ta faman kai komo hade da sauraren abinda zaije ya komo hade da sauraren abokan tafiyarsu da suka shiga cikin kauyukan.“menene abinyi? Tambayar kenan data bijiro ma ta cikin zuciyarta.

Wani iri haske mai tsanani yayi dirar mikiya akan fuskar ta tsam taji tsigar jikinta ta tashi, bugun da zucyarta keyi yayi matukar karuwa, tausayin kanta ya kamata data rigaya ta tabbatarwa kanta karshen rayuwarta ya rigaya yazo tunda har suka iya hasko inda take tsaye. “Ashe duk gudunnan da nakeyi azzaluman mutanen nan suna biye dani?” tayi maganar a zuciyarta.   Daya daga cikin yan bindigar dayaji motsin tsayuwar Naja’atu a wajen ya dallaro hasken fitilarsa dai-dai inda yaji motsin, cikin sa’a yayi dacen haske kan fuskarta, take jikinta ya dauki bari kamar mazari, kirjin ta yaci gaba da kabar sautin bugun da zuciyar ta takeyi wanda ya hade da maida numfashin gudun da tayi da kuma tsananin fargabar da take gani a zahiri.

“Ke! Zonan!”

Wani daga cikin su wanda ga dukkan alamu shine jagoran tafiya tasu ya ambata da wata irin barkekiyar murya mai kama da rugugin tashin injin markade. Yayi maganar da jin kai hade da nuna isa.

ji tayi wani sabon karfi ya shigi jikinta, bata tsaya wata-wata ba ta bashi amsa ta hanyar tsillarawa da gudu ta shige cikin duhun daren kamin kiftawar ido.  ta bace musu bat a cikin duhun daren.

“Ja’e, a kamota duk inda ta shiga, kuma kada wanda ya tabata a kawota da ranta.”

Siririn dan fulanin daya rufe kamanninshi ta hanyar amfani da katon rawani ya iso gaban mai maganar ciki biyayya tare da amsa mashi da cewa “an gama mai gida”Fadin hakan yayi dai-dai da nunin da yake yima wasu daga cikin mutanen da suka kima manyan rawunna kamar dai wannan na farkon da aka ba wa umarni, suma fuskokisu a rufe. biyu ya raba su ya dauki rabi suka bi bayan naja’atun da ta dade da bacewa ganinsu.

Tsananin hasken fitilar da aka haska ta dashi yayi matukar tasiri akan idanunta wanda hakan ya haddasa mata rashin  ganin komi saidai duhu dun d’um ta koina, duk wannan baisa ta saurarama sabon tseren gudun data keyi ba, dan hakanema take jefa kafarta duk inda ta samu ba tare da shakku ko gudun abinda kaje ya dawo ba. 

“Anya kuwa kina ganin zaki tserema wadancen zaratan mutanen dake shirin biyo bayan ki?

Tambayar da wani sashe na zuciyarta ya jefo mata kenan, sai dai tuni ta ba wa kanta amsa a zahiri ta hanyar kara kaimin gudun da takeyin, dukkuwa da halin da take ciki na rashin ganin komi sanadiyyar hasken da yayi matukar tasiri akan idanunta hakan nema yasa ta yawaita yin karo tare da tuntube da mafi akasarin abubuwan da take haduwa dasu a cikin gudun da takeyi. Wannan duk baisa ta hakura ba saima  kara azama da takeyi.“kadafa ki dinga wahalar da kanki a banza, Ki sani gudun da babu tsira…”

Wani sashe na zuciyarta yazo mata da shawarar yanke kauna akan gujewa mutanen masu matukar hadarin gaske da takeyi a karo na biyu,“Mummunar shawara kenan” ta raya hakan a bayyane cikin zuciyarta, sabon gargadin data samu a dayan sashen na zuciyarta ya taimaka mayuka wajen kara mata karfin gwuiwa.

“Yanda suka halbe na baya nakima sai yafi muni, kuma da jarabawa jirgi ya tashi, kada ki kuskura koda wasa ki tsayama wadannan azzaluman mutanen.”

Ji tayi abunda ke faruwa da ita ba komi bane idan ta hadashi da abinda ta gani a cen baya, tuni ta kara kaimi  da  dauriya ta kuma daura  aniyar  yin iyakar iyawarta don ganin ta tseratar da rayuwarta.

Zaratan marika bindigar suka  kama dariya ganin yanda budurwar ta debi hanya ta shige da gudu ba kakkautawa.

“Mun baki kore yan mata, da kanki zaki tsaya mu kamaki shikin ruwan sanyi.

Wani daga cikinsu mai siririyar murya irinta fulani ya ambata, yayinda sauran suka sheke da dariyar mugunta daga cikin su har wasu suna daga bindiga sama suka auna harbi akan iska.

Tashin hankalin Naja’atu ya karu lokaci dataji harbin bindigar da yayi amsa kuwwa acikin tsohon daren.

Take ta kara dimaucewa, wannan ne yasa a kara zabura ta kara nausawa cikin dajin tana mamungar jefa kafarta aduk inda ta samu saboda rashin ganin komi da takeyi gakuma tsanani duhun daren da ya mamaye koina.

Cikin rashin aune tayi wani mummunan karo da wata katuwar bishiya, dalilin da yasa ta callara tsuwwa tare da fadin “wayyo Allah na.”

Gefe guda ta fadi kamar wadda aka wurgar, da karfin hali ta sake mikewa da nufin taci gaba da gudun da takeyi, ji tayi juwwa ta debeta hakanne ma yayi sanadin fadawar ta cikin wata yar duhuwa mai dauke da ganyayyaki hade da kayoyi.

Da sassarfa yan bindigar suka karaso inda sukaji maganar ta,  saidai me? Babu ita babu alamarta ko sama ko kasa.

Ba karamin daure masu kai hakan yayi ba, take suka fara haske-haske da dube-duben inda ta buya kasantuwar wajen yanada tarin manya da kananan bishiyoyi  wanda suka hadu suka wadata wajen da duhuwa.

Bayan naja’atu ta fada cikin duhuwar ta kara jan jikinta tare da boye kanta a cikin duhuwar mai dauke da ganyayyaki da kayoyin da suketa faman tsirar jikinta, amma haka nan ta daure ma ranta tare da sa hannuwanta bibbiyu ta gumtse bakinta dasu.Sanyin wani abu taji yana bin hannayen nata, sannu ahankali data nakalci ko menene saita tabbarwa da kanta jinine da yake fita daga cikin hancina sanadiyyar karon da tayi da bishiya. wanda hakan ba karamin daga mata hankali yayi ba, ta kara dimaucewa tare da shiga mummunan hali lokacin da taga sun tunkaro inda take a boye cikin duhuwar. Ba karamar kadawa hantar cikinta tayi ba, wani irin kugi cikinta yayi sanadiyyar motsin yan hanjinta cikinta sukeyi, dukan da  zuciyarta keyi ya sauya izuwa wani irin bugawa da sauri-sauri kamar tana neman fasa kirjinta ta futo, zufa mai tsananin sanyi ta fara ketowa a saman goshi. Kara danna hannuwanta tayi a cikin bakinta don toshewa don gudun bayyanar wani sauti ta cikin bakin nata. Yayin da jinin dake futowa a hanninta yaci gaba dayo ambaliya izuwa saman hannuwanta.

Wani irin motsi taji mai tsananin laushi da kuma taushi a kasan inda take lafe hakan ya tabbatar mata da cewar tana kishingide ne akan wani abun da bazata iya tan-tance ko nene ba .Bata gama wannan tunanin ko komenene ba sai jin hucin maciji tayi dai-dai kunnen ta yana zare jikinshi daga inda ta danne shi. Runtse idanunta  tayi, sankarewa tayi tana jiran taji saran macijin data rigaya ta tabbatarwa da kanta shine take kwance akansa dukkuwa da ba ganinsa tayi ba. Shiru taji bayan wani lokaci yayinda yan bindigar dake binta keta kara matso inda take suna haske-hasken fitila.  

Fitar wani abu da gudu da sukaji a saman rairayin ganyen itacen da suka zuba a kasa ne ya dauki hankalinsu hakan yasa basu tsaya haska ko menene ba suka mara mashi baya da tsananin gudu. A tunanin su Naja’atun da suka biyo ce ta sake arcewa.  Basuga komi ba lokacin da suka fita sarari.

“Wannan akwai dan banzan mai rai.”

Wani daga cikin marika bindigar mai sifar fulani ya fadi yana kara haska wajen da suka biyo hade da mamakin irin batan dabon da budurar da suka biyo din tayi masu. Maciji ne bakikkirin irin bakin nan da yake sheki idan haske ya dira akanshi, ya nannade ya taru waje guda, alokaci guda kuma ya fasa kai yana jiran wanda karar kwana zata karaso dashi,  dan fulanin mai magana ya hasko.

Shekewa da dariya kusan dukansu suka yi.

“Tab! Lallai yaukam zakaga kalar tamu azabar”  wani daga cikinsu ya fadi tare da saitashi da bindiga yana shirin harbawa,

“Ai ba farat daya za’ayima shi ba” wani a cikinsu yayi saurin dakatar da mai shirin harba bindigar

“Wai kun manta da abinda oga yashe muyi ne” wani mai sifar fulani yayi maganar da alamun kagara a tare dashi.

“Kada ka damu Ja’e muna sane ai, so dai mukeyi mu gama da wanna dan duniyar tukun, kasan ya wahalar damu lokacin da mukeda shanu kafin azo a kwashe mana a sa mu dauki makami.

Kusan dukkaninsu saida suka fashe da dariya hade da sowa. Suna bashi kwarin gwuiwar kashe macijin. A haka sukaita wahalar dashi daga karshe suka kashe macijin.

Duk abubuwan dake faruwa naja’atu tana lafe a cikin duhuwar ta kasa motsa koda dan yatsanta, har yanzu jini yana ci gaba da fita daga hancinta, a haka idanunta suka lumshe,ta idasa sulalewa a cikin kayoyin da suka sami wadatacciya duhuwar ta sanadiyyar haduwar ganyayyaki.

 Bayan kase macijin kuma sai suka bazama tare da ciro fitulunsu suna faman haske-haske da sauraren jin inda sautin motsin naja’atu zai futo.

Abu kamar wasa sun shafe lokaci suna waige-waige tare da hange, amma kaf cikinsu babu wanda yayi tunanin haske fitilarshi izuwa ga kasan wannan duhuwar wadda Naja’atu ke kwance a sume.

Karshe dai hakuri sukayi da suka gaji da dube-bube  sukayi gaba tare da tunanin ba nan ta tsaya ba. Da wannan kwarin gwuiwar suka kara gaba. Haka suka koma suka hadu da sauran abokan tafiyar tasu.

Ahankali ta fara bude idanunta tare da  jan dogon numfashi da kyar ta iya motsa babban dan yatsan hannunta,ji tayi kafafunta sunyi mata nauyi jingim tamkar ba ajikinta suke ba, jikinta koina ciwo yakeyi mata saboda buguwa da kuma wahalar gudun da tasha ga kuma bubbugewa hade da tuntube data dungayi. Har yanzu jinin yana zuba daga hancinta.

Sassanyan iska mai dauke da tsananin sanyidake ratsa fatar jiki tsoka, kashi zuwa bargo taci gaba da hurota tako ina, tsananin sanyin da yake ratsa jikinta ya taimaka matuka wajen kara jin tsananin ciwon da jikin nata yakeyi mata, tuni tsigar jikinta ta karbi sakon da sanyin ke isarwa zuwa ga fatar jikinta, ba’a sami wani tsaiko ba wajen isar sakon sanyin zuwa kashi da bargon jikinta, babu shiri jikinta ya hau sabon bari na rawar sanyi. Wani irin hawaye mai hade da majina suka fara rige – rigen futo da kansu waje bayan da suka hadu da jinin dake futowa a hancinta.    abubuwa da suka faru akan idon tun faron daren suka fara dawo mata a cikin tunanin ta. Take kyarmar da takeyi ta karu. Duk da saurin bugun jinin da zuciyarta ta wanzu tanayi fiye dacen baya.“Kodai mafarkine ?” ta tambayi kanta a cikin zuciya.

“Ko kusa ko alama da gaske abin ke faruwa” wani sashe na zuciyar ta yayi gaggawar bata amsar data tambaya tare da tabbatar mata cewa tayi duba izuwa yanayin da take ciki.

Wasu zafafan hawayen ne sukayi rige-rigen sauka a gefen kumatuna.“Yanzu an halbe yayana da kakana kenan? Ina Kaka ta Salla ta shiga?

Su waye suka aikata mana wannan aikin hakan? Me mukayi masu suke kashe mu haka musamman yayana dan uwana daya tilo aduk fadin duniyar nan?”

Amsoshin da ko kadan bata da amsar su bare kuma mai amsa mata, iyakar abinda ta sa ni shine wasu mutane suna yawan zuwa cikin garinsu irin hakan cikin dare,

Amsar da ko kadan bata san mai amsa mata ita ba, iya abunda ta sani shine wani dare da irin wadannan mutanen sukayima gidansu kawanya suka kore masu dabbobi tare da fadama babansu cewa idan yanaso su maido mashi dabbobinsu saidai ya shiga cikinsu ko kuma ya bada babban danshi ya shiga ko kuma ya ringa basu kudi adadin abinda suka sara mashi. Hakan ya faru tun kusan watanni takwas da suka shude.

Wannan tunanin ne ya haddasa birkicewar idanun ta, take suka fara lumshewa. lokacin kumq Zufa ta fara yo tsartuwa a saman goshinta, tsananin sanyin dake busawar sai ya zamto baya tasiri gareta ko kadan. A haka ta wanzu har idanunta suka idasa rufewa.

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×