Skip to content

Rayuwata | Babi Na Uku

5
(2)

<< Previous

“Yaya injiniya Ka sani, duk dadin da nakeji a rayuwata, duk irin farin cikin da nake ciki idan har na tuno da wannan lokacin ina jin na tsani wadannan mutanen da rayuwata gaba daya.”

Na idasa maganar tare da share hawayen da suke kwararowa akan kumatuna  tamkar sabon idon ruwan da aka samu a lokacin gina rijiya.

“Kiyi hakuri kanwata, kowanenmu yanada irin tashi kaddarar rayuwar wadda bata goguwa dole saita auku” Ya ce dani tare da tsareni da idanu.

“Hmmm Yayana kenan, ni kadai nasan irin tashin hankalin dana gani alokacin da kuma bayan faruwar abinda ya faru.”

A sanyaye ya mike daga inda yake zaune ya tako tare da isowa gabana ya zauna a kusa da kujerar dake fuskantata sannan yace dani.

“Iya juriya da hakurin da kikayi ada cen baya, iya juriya da hakurin da zaki karayi anan gaba!

A sanyaye na dago na dubeshi da idanuna da suka karayin jajir.

Murmushi yaya injiniya yayi tare da gyada mani kai hade da tabe bakinshi cikin alamun karfafa zuciya da kwarin gwuiwa.

“Kiyi iya kokarin ki wajen fadawa duniya abinda ke faruwa da kuma abinda she shirin faruwa a kauyukan ku.”

A take ya miko mani biro da katon littafin dake rike a hannunshi yana rubuta labarin na da nake bashi.

Damm! Dammm! naji kirjina yayi wani irin bugawa danaji har kaina saida ya sara, take hannuna ya dauki karkarwa har saida yaya injiniya ya fahinci halin danake ciki.

“Haba Naja! Yanzu dan Allah menene a cikin rubuta labarin abinda kikasan ya faru dake?

Murmushin karfin hali nayi hade da share zufar da tuni ta cika soman tsatstsafo mani a saman goshina sannan nace dashi “babu komi”

“To karba nan ki rubuta da hannun ki.”

A sanyaye na karba hannuna na rawa.

Abubuwan duk da suka faru suka ci gaba da dawo mani a cikin tunanina kamar yanda sukeyi lokacin dana nake fadawa yaya injiniya yana rubutawa. Saidai wannan karon kara nake ganin hoton abubuwan a saman idanuwana

“Yayana bana…”

“Sako da akeson isarwa zaifi isa inda ake bukatar isarshi”

ya katse ni da fadin hakan a takaice

Jim nayi na wani lokaci sanna na dago da alamun damuwa akan fuskata na dubeshi

“Kada ki damu, kada kiji komi, babu wata matsala da kasan tuwar hakan”

ya bani kafin gwuiwa akan abinda ya fadi ta hanyar kallo hade da gyada mani kai.

“Shikenan yayana yanda kace haka za’ayi” na fadi cikin alamun sheshshekar kuka da wani irin yanayi na ban tausayi a lokaci guda kuma na dora biro a kan takarda naci gaba da rubutu.

Farkawata daga doguwar suma ko kuma mayen abinda nasha a cikin daddadar furar yayi dai-dai da cin karo da firar da mutanen biyu sukeyi rakube a bayan dan karamin dakin dayafi kama da rumbu wanda nake kwance a ciki.

Cikin abinda bai gaza dakika biyar ba tunani hade da nazarin abubuwan da suka faru dani musamman lokacin da idanuna suke kokarin rufewa suka fara dawo mani.

Wata muryar da nake da tabbacin nasa mai ita a bayan dakin da nake ya kara yamutsawa tare da hargitsa tunanina. Shin ina nasan mai wannan muryar? Tunanina ya kau daga nan ya koma kan ruwan mai sanyi dake bin kafafuna.

Hankalina yayi matukar tashi lokacin dana fahinci jini ne  jefi-jefi yake bin  jikina, yunkurin mikewa nayi amma ga mamakina sai na kasa hasalima sai naji duniyar tana juya mani dalilin kenan ya yasa hankalina ya kara mummunan tashi.

Me hakan yake nufi? Waye wannan wanda nasan muryarsa haka? Anya kuwa baya da sa hannu akan abin duk da yasamemu?

“kada ka damu yanzu ai wannan ta zama matarka saidai ayi fatan ka gama amarci lafiya”

Maganar mutumin dana tabbatarwa da kaina nasan muryar shi ta sake dukan dodon kunnena a karo na biyu.

Wanan maganar da naji ta kara ankarar dani wani abinda ya daga hankali har jini yake fita a jikina kuma nakejin ciwo da radadin da jikina keyi mani dalilin kenan da yasa na kwala wata uwar kururuwa hade da neman agaji.

Kamar za’a balle kofar haka naga wasu zaratan samari guda biyu sun banko kofar da karfin tsiya, kai tsaye kaina sukayo suka daddanne hade da cusa wani daddaudan tsumman dana tabbata bai taba ganin ruwan wanki ba a cikin bakina hakan tasa dole na dena ihun da nakeyi badan Allah ba.

Cikin takama da isa ya tsaya gabana bayanda samarin sukayi kama-kama suka mikar dani a tsaye yayinda bakina ke cike da tsumman da karni da zarnin da yakeyi ya fara tayar mani da zuciya.

Hannu yasa ya finciko tsumman daga cikin bakina. Hakan yayi dai-dai da isowar aman da yake ta hankoron fitowa daga cikin bakina.                                    

Cikin kiftarwa ido na wanke mashi jikinshi da furar dana jima da sha. ban gama komawa cikin hayyacina ba naji wani nagar taccen mari ya sauka a saman kumatuna, hakan yayi sanadiyya ganin wasu fararen taurari sunayi mani yawo a saman kaina.

“Ku saketa” ya fadi da alamun bacin rai

Sharaf na fadi a saman turbayar kamar wata gawa babu kwari ko na kwabo a jikina, takaicin abinda ya faru dani ya ziyarci zuciyata, hakan yasa wasu zafafan hawaye suka kwaranyo a saman kumatuna, sai a lokacin na san takamaimai yan da kunar zuciya yake, ji nayi duniyar gaba dayanta tayi mani kunci, bakina yayi salaf banajin zan sake jin dadin komi a rayuwata.

“Fyade akayi mani.”

Na ambata hakan a zuciyata, take naji na tsani rayuwata da duk wanda ya jefani a cikin wannan halin. Saina gwammace dama ace ina daya daga cikin wadanda suka harbe tun farkon faruwar al-amrin da banga wannan bakin lokacin ba,

Da kyar na iya dago kai na budi mutumin da tuni tsanarshi ta rigaya ta mamayi illahirin zuciyata nace dashi

“Kayiwa girman Allah ka kasheni”

Yanayin dana gani a tare dashi ne ya tabbatar mani da bata bakina kawai nayi,  bai iya ce mani komi ba saidai daga hannu da yayi tare da nuni gareni alamun gargadi.

Dalilin kenan da yasa na rushe da wani kalar kukan marar sauti saidai hawaye masu tsananin zafi.

Juyawa kawai yayi ya fice sauran matasan biyu suka mara masa baya.

Kusan yinin ko kwanan wannan ranar babu wani mahaluki dana sake sakawa a idanuna.

A haka naci gaba da rayuwa a cikin matsanan cin yanayin da na gwammace gara mutuwa dashi dan kuwa wannan kasurgumin mutumin ya mayar dani tamkar matarshi ta aure, bayan azabar duka da nake ci aduk lokacin da aka kawo abinci ko abin sha yaga banci ba ko bansha ba.

Mafi akasarin lokuta kuma ci ko shan abin shan dai-dai yake da shan kayan mayen da saidai ma farka naga wannan mutumin yayi duk abinda yakeson yi dani.

Wani abinda ya jima yana daure kaina kuma har yanzu na kasa ganewa shine muryar da nakeji wadda nake da tabbacin nasan mai wannan muryar kusan ko wane lokaci na farka a tsakiyar dare.

Hakanne yake yawan sakani tunanin ko wani ne daga cikin yan uwana yazo don ceto rayuwata daga cikin kangin da nake ciki amma tunanina yakan canza idan na saurara wasu lokutan naji kalar maganganunsu ko kusa ko alama basu kama hanyar da nake zato ko tsammani ba.

Tsanani yayi tsanani rayuwa ta wahalta gareni kusan ko wace rana adduar da nake shine Allah ya amshe rayuwata tunda bansan da wane ido zan kalli ahalina ba, bansan irin kallon da mutanen dake kauyenmu zasuyi mani ba, ta yaya zan iya jure wannna bakin cikin da duk sanda na tuna hawaye ke kwarara a idanuna?

Banko kofar da akayi yasa nayi gaggawar share hawayena da suke kwararowa daga cikin idanuna da suka dade da zurmawa ciki saboda tsabar rama.

“Ke!, futo.”

Wata garjejiyar murya ta ambata, bayanda mutumin mai kama da gunki yayi tsaye yana kallona bayan daya hangame kofar dakin.

Sassanyar iskar data shigo dakin dayafi kama da kurkuku ne yasa naji wani sanyi ya daki fatar jikina danayi kiyashin tayi kusan sati ukku bataga ruwan wanka ba. Wata irin niimtacciyar ajiyar zuciya nayi sannan na daga kai a sanyaye na kalleshi.

Duk da kasancewar duhun dare ya fara shiga amma ina iya gane cewa babu alamar sassauci a kan fuskarshi ko kadan.

“Wai bakiji ana magana bane”?

Ya sake yin magana a kagare.

Cikin yanayi najin ciwon jiki na daddafa na idasa mikewa dakyar. Tare da taimakon bangon dakin dana dafa.

“Muje mana” yace dani cikin tsawa

Tsoron danaji hade da kadawar da hantar cikina tayi ne yasa na saki abin da na dafa na zabura da nufin fita daga dakin amma ga mamaki sai jina nayi na fadi kasa sharaf kamar kayan wanki.

Hawayen tausayin kaina suka sulalo ahankali zuwa kan kumatuna

“Dan Allah…”

Saukar marin daya gigitani ne yasa na kasa fadin abinda nake kokarin rokonsa.

jan jikina naci gaba dayi har na samu nakai bakin kofar katakon.

“zaki mike kiyi tafiya kosai na”

Maganarsa ta yanke lokacin da mutumin dake cin zarafina ya karaso ya tsugunna gabana.

“Kyaleta habu kama gabanka”

Wata matashiyar bafilatana nagani ta taho wata katuwar roba a hannunta daya yayinda dayan kuma bokitine mai dauke da ruwan zafi yana turiri

Tausayin kaina ya kamani dakyar na iya bude baki a sanyaye nace mashi

“Kayiwa Allah da manzon sa ka kasheni na huta”

Dariyar ketar dana gani karara akan fuskarshi ce ta bayyanar mani da manufarsa taci gaba da cin zalina.

Wani irin daci naji ya ziyarci bakina yayinda bakinciki marar misaltuwa ya tokare mani a wuya, sai ji nayi na tsani rayuwar duniyar gaba daya bana sha’awar kara kasancewa cikin ta.

Kururuwar wata matace dake daure ana gana mata azabar da mijinta da aka kira a waya don karbar kudi dazaa fansheta ne ya kara tayar da hankalina.

“Kardai ince tawa azabar da ruwan zafi za’ayi mani ita.”

Na furta hakan a zuciyata alokaci guda kuma naga wannan matshiyar bafillatanar ta ajiye kayan dake hannunta ta juyo tana kallona tana wani irin mugun murmushi wanda nake da tabbacin na keta ne.

Duk da kasancewar akwai duhun dare amma hakan bai hanani ganin murushin nata ba.

Katsawar da cikina yayi wanda har saida sautin ya bayyana a zahiri ya tabbatar da tsoratar da nayi.

“kiyi mata abinda ya kamata”

Ya fadi tare da mikewa ya juya da nufin tafiya, Dariyarta ta fadada a bayyane sannan tayo kaina cikin azama.    

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share the story on social media.

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.