Skip to content
Part 13 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Kwana daya biyu, sati daya, biyu, uku, hudu har aka fara hararar watanni uku sannan Binta ta gane lallai da gaske Mujahid ya ke ya farka rayuwarta, zai shigo da qarfin gaske, wato bai fara sonta don ta qi shi ya daina ba.

Kusan kowa a gidan ya farga da halin da suke ciki in an cire mahaifansu da ko sun sha giyar wake suna qoqarin mallakar kai a gabansu.

Dadin da Binta ta ke ji ke nan, wato yadda Mujahid ke yin fuska ya ke nuna ba komai a tsakaninsu idan a gaban Hajiya ko Alhaji ne, ta haqiqance idan zai shekara dubu yana nuna sonta a tsakanin ita da shi da wasu a waje ya yi ta banzar, don za ta yi wannan shekarun ita ma tana tankwabar da son nasa.

Daidai lokacin ne kuma Mahaifanta suka fara matsa lambar lallai fa sun gaji da jiran ta fito da miji.

Kwatsam rannan Hajiya ta jefo mata wata tambaya.

Wai kuwa me ke tsakaninki da Mujahid?

Da cikin Binta ya debo wasu ganguna ya fara kadawa, ta yi shakkar in Hajiyar ba ta ji kotson da ta buga ba, amma dai ta yi qoqarin mallakar yanayinta ta amsa a nutse.

Me ki ka gani Hajiya?

Ina ga alamun yana sonki.

Kai tsaye Hajiyar ta amsa mata.

Binta ta san in ta zafafa abin yanzu Hajiya za ta ramfo ta, don haka ta tsuntsire da dariya da cewa Hajiyar.

Ya kamata ki koma makaranta Hajiya.

Duk Hajiya ta san wasa ne sai ta yi fuska ta amsa da gatse.

In bar auren in je in dauko dakon karatu na zo gida na ajiye kwalin ko, ayya ni ba sharholiya kawai na zo yi duniya ba bautar Ubangiji na zo?

Binta ta gane magana Hajiya ta gasa mata, amma tunda ba ta da hanyar kubuta sai ta girgije ta tafi a zuwan ba ta gane baqar maganar ba.

Aa Hajiya da aurenki za ki je, ki karanto jarida ko lauyanci ki zo kawai ki yi ta tasa mu a gaba duk motsinmu sai kin sa masa ido kin mana fassara.

Hajiya ta yi dariya cikin kada kai ta ce.

To fada min in daidai na fassara, sonki Mujahid ya ke?

Bakin Binta cike da dariya ta ce.

Wannan karon hasashenki ya dan kuskure kadan Hajiya

Cikin dariya Hajiya ta kada kai ta fice tana cewa.

Dole zan koma karatun ke nan, amma jarida zan koyo, wato neman labarai. Saboda na fahinci lauyanci ba ya iya wa Rigar Siliki irinki.

Ba ta bar Binta ta tanka ba ta fice ta bar mata falon.

Binta ta yi suguri shanye da baki tana bin wajen da ta bace da kallo, lokacin da ta ji tamkar ana dora mata buhunhunan sumunti a qwallon ka.

Wata qaddarar ta afko mata ke nan, iyaye sun fara shanshanar Mujahid na sonta, mutumin da ta haqiqance a idonsu ba shi da wani aibu da zai hana su wanke diyarsu dole su ba shi, bare wadda tuni suke da haushin ta qi kawo miji ta qi aure.

Ta ina za ta kubuce wa wannan qofar ragon? Dole ke nan sai ta billo wa Mujahid ta bayan gida ya janye wa soyayyarta da kansa?

*****

Ta zare jiki ita kadai ta kwashi ziyara gidansu Yaks, haka ma da za ta tafi ta yi dabarar yafitar Yaks don ya kai ta gida inda a hanya ta bijiro masa da qudirinta.

Yaks ina maganar da muka yi da kai kan Mujahid?

Yaks ya yi qwafa cikin kada kai ya ce,

Yanzu tunda kin tuno maganar ai zan iya taya ki mu yi, amma da har na fara tunanin yanke nawa danyen hukuncin.

Cikin tsura masa ido Binta ta ce.

Me ka shirya yi?

Ya ware hannuwa sannan ya bugi sitiyari idonsa na kallon titi, cikin yanayin fushi ya amsa mata.

A kan Nabila ban qi in dau ran mutum ba na rantse miki.

Da sauri ta kawar da kai zuwa kallon tagar mota tana tsaki.

Kai matsalarka danyen kai da cika baki wallahi

Ya juyo ya kalle ta da alamun fushi.

Rantsuwar da na yi kin turbudata a qasa ke nan? Kodayake ba ki san irin zafin da na ke ji a nawa qirjin ba, wanda shi ya ke ba ni tabbacin in ban kashe ba to tabbas ni za a kashe ni.

Ta ci gaba da dariyarta cikin yanayi na rashin ba wa maganarsa muhimmanci tana ce masa.

Ban da abinka ai ko a fim kisa shi ne hukunci na qarshe da ake dauka, wani lokacin sai ka ga Bos wani dan gwale-gwale kawai a ke samu a ba shi, abin da na ke so mu hada kai mu yi wa Mujahid ke nan.

Ya juyo kawai yana yi mata kallon rashin fahinta ba tare da ya tanka ba.

Ta dan ja fasali sannan ta tanka masa.

Mujahid mutum ne mai tsananin kishi, to abin da na ke so da kai shi ne, za mu yi wani game tamkar kana takara da shi a wajena, da ma can yana da sanin kai na Nabila ne, wadda ka ke so da aure. Ni muna iya zuwa da akasin haka, ina tabbatar maka ta wannan hanyar za mu iya ciyo lagonsa.

Duk da ci da zucin Yaks bai karbi lamarin a jiye ba sai da ya zurfafa tunani sannan ya cewa Binta.

Amma idan an yi hakan kamar ke kadai za ki amfana, ni qila Nabila ta qara tsana ta

Da ya ke tuni Binta ta shirya wa wannan qalubalen nasa nan da nan ta tare shi da cewa.

Nabila ba ta da zabin wani miji bayan kai, watanni biyu zuwa uku ya rage mata kammala sakandire yayin da kakarta ta ci alwashi ba za ta doshi wata makaranta ba sai da igiyar aurenta, ga ta da kalatar karatu, kuma duk manemanta da suke takara da kai ba su da raayin ta ci gaba da karatu, kar ma mu ja ta da nisa tun yanzu ma ta fara saukowa da jin kamar ya kamata ta saurare ka, ku daidaita.

Fuskar Yaks ta nutsu amma zuciyarsa ta kasa yarda ta nutsu, ya juyo ya cewa binta,

Har yanzu ban ji inda tayin da kika zo min da shi zai amfane ni ba?

Ta yi qarfin halin cigaba da murmushi tana amsa masa,

Na fi kowa sanin Nabila, saboda haka na san abinda zaa iya shawo kanta da shi,shugabansu shi ne yi mata kishiya ta sha sanar da ni ko bata son mutum tana kishinsa, ina da yaqinin idan ta ga ka fara shin shinar sona zata watsar da jan ajinta ta saurare ka, sai dai ita ya zamana a dinga boye wa idonta, amma wancam banzan Mujahid ko sumbata ta ne in ka ga idonsa kana iya yi

Yaks ya saki wani irin ihu irin nasu na gayu yana dukan sitiyari, ya dinga layi da motar sannan ya dire ta,

Dakata! Sumba wacce?

Ta zabga masa harara,

dan iska wadda zaka iya yiwa yar cikinka ko qanwarka ba matarka ko budurwarka ba, na tabbatar a kunci kawai ka ba ni guda daya sai Mujahid ya kusa mutuwa

Allah ya sa ma ya mutu kowa ya huta

Amsar da Yaks ya bata kenan bayan takaicinsa ya dawo sabo dal!

Ita kuma babu kunya babu tsoron Allah ta amsa,

Amin

****

Yammacin yau ya zo wa da Mujahid Qishin son ganin masoyiya Binta, ya so daurewa ya ji ba zai iya ba kawai sai yayi wanka ya cake ya fada cikin gida nemanta. Bai tambayi kowa ita ba sai Hajiya, wadda ta bi shi da kallon nazari ta bashi amsa,

Ta je gidansu Yaks, wani laifin ta yi ko?

Mujahid ya tsiri shafa kai wanda kai tsaye zai fassara matsayin da yake tsaye kansa wato matsayin suruki, yana girgiza kai ya amsa,

A haba Hajiya dan dai abin laifi ba ya wahala? Ni Binta ba ta laifi a wajena, wata muhimmiyar magana kawai zamu tattauna.

Hajiya ta kada kai tana shanye dadi da mamaki,

Yayi kyau, in ta ruba zamu ji.

Za ku ji alkhairi Hajiya

Ya fada yana dariya ya fice ya bar gidan. Ransa bai yi masa dadin jin cewa gidansu Yaks Binta ta tafi ba, Allah ya sani ko gaisuwa ba ya qaunar ta shiga tsakanin Binta da Yaks, da shi ne Shukuranu babu abinda zai hana shi datse wannan zumuntar.

Me zai faru? Yana shirin tashin motarsa ya ga Binta ta shigo tare da Yaks din a motarsa.

Yaks ne ya lura da Mujahid Binta ba ma ta ankara ba, sai yayi biris ya shammaceta, inda ya ya tsayar da motar sannan a guje ya bude qofarsa ya zagayo ya bude tata, duk cikin zafin nama yana caje harabar gidan don ganin cewa babu idon kowa sai na Mujahid.

Ya damqo hannun Binta ya janyo ta waje yana neman su buya a bayan mota.

Binta ta manta da game din da suka shirya ta tsiri neman cinye shi danye,

Kai giya ka sha ne?

Yaks bai damu da hargaginta ba don ya san Mujahid kunnensa baya jiyo abinda suke cewa, idonsa ne kawai a kansu.

Suna qarasawa bayan motar ya saki hannunta ya riqo kafadunta, tamkar zai rungume ta amma sai ya sunkuya kunnenta ya rada mata,

Wancan gasa-toron fa yana kallonmu.

Sai jikin Binta yayi sanyi, sai dai a can cikin qirjinta wasu matsiyatan ganguna sun yayimo kansu suna kadawa, ta san ita dai ba ita ke kada su ba.

Qiyayya ta sanya ta hawa turbar da mai mutunci irinta ba ya mafarkin ratsawa, ba tare da ta tanadi ko wanne irin soso don wanke kanta idan haqanta ya cimma ruwa ba.

Tana cikin rashin hayyaci ta ji yaks ya sumbace ta a goshi, ya zaga kai ya tsura mata wani mayataccen kallo yana riqe da kafadunta, yanayin da suka shiga yayi mata kama da fim na wadanda addini bai musu wankan tsarki ba.

Da Mujahid ya debo mota a cikin nasa rashin hayyacin yana neman kwashe su, sai gashi dukkansu sun yi tsalle sun fadi gefe guda suna hirji da mai da numfashi, shi kuma yayi tirjiya sannan ya kwashi motar a guje ya fice daga gidan tamkar mai shirin tashi sama.

Ba qaramar gigita Binta ta yi ba, har suman wucin gadi ta yi a wajen da kyar ta koma hayyacinta lokacin da ta hangi Yaks ya miqe yana faman tuntsira dariya.

Ta yunqura ta taso qafarta na karkarwa, murya a raunane ta ce,

Kai Yaks wannan mutumin wataran zai iya kashe mu.

Ya tare ta yana cigaba da dariya,

Ina zai gan mu ya kashe, baki ga ya tafi kashe kansa ba?

A gigice Binta ta dubi sawun motar Mujahid sannan ta juyo da kallonta ga Yaks, bai bari ta yi magana ba ya riga ta,

Yadda yake kwasar motar nan cikin mayen bacin rai ina mai tabbatar miki ko Tirela ya hango tana tunkaro shi tsammani zai yi shi yake bin ta a baya

Binta ta yi rau-rau tana girgiza kai,

Da alama yadda bana so a kashe ni, nima bana so na kashe, ba tsantsar maqiyi Yaya Mujahid yake amsawa a zuciyata ba yaks, da zai janye neman aurena duk dangina ba wanda nake so sama da shi, shi ne abokin shawarata.

Yaks yayi fuska ya basar da maganar,

To yanzu dai Allah ya rufa asiri, sai yaushe zan dawo?

Cikin rashin nutsuwar zuciya Binta ta dan yi tunani,

In komai lafiya zan maka waya ka dawo gobe.

In na zo gobe fita zamu yi.

Ya amsa mata.

Babu musu ta kada kai,

Zan sami gidansu wata qawar tawa mu je mu kwashi wani dan lokaci kawai ka dawo da ni ka ajiye.

Ya doshi motarsa yana cewa,

Gaskiya gidansu Nabila zamu je qarfe hudun gobe, ki zama cikin shiri.

Allah ya kai mu.

Ta amsa masa jikinta a sanyaye sannan ta doshi cikin gidansu, inda ta yi kacibis da mahaifinta yana fitowa.

Da ta kalli fuskarsa sai da ta ji gudawa na neman tsinke mata saboda yadda ta ga fuskarsa a daure tamau, babu yadda zaa yi ta kasa zargin ko ya ga halin da ta shiga da Yaks.

Tuni ta zube a wajen da zummar kwasar gaisuwa, amma zubewar kawai ta iya ta kasa cewa komai illa gumi da nan take yake sabunta mata wanka. Ina ma ta narke a wajen ta zama ba ita ba!

Ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya lokacin da cikin fishi mahaifinta ya ce,

Gaskiya in mutum ya rasa mafadi ya shiga uku, dole a dinga ganinsa da irinsa yana yawo kwararo-kwararo.

Ta ji zuciyarta na neman tsinkewa da dadi da wata fargabar,

Ka yi haquri Alhaji, komai zai wuce.

Ya wuce ya bar ta a wajen yana cewa,

Eh kafin ya wuce ai kin jawo min magana kin gama. Allah dai ya shirya.

Jikinta a salube ta miqe ta shige cikin gida cikin ranta tana cewa,

Ubangiji ka kawo min miji nagari na huta da wannan tsangwamar.

<< Rigar Siliki 12Rigar Siliki 14 >>

1 thought on “Rigar Siliki 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×