Skip to content
Part 17 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Kamar yadda Binta ta zarga dukkansu ba su sami damar baccin kirki ba, sun yi kankankan a jin bacin rai ko kuma samun farin cikin bata wa juna.

Mujahid ya ji farin cikin harbin da ya yi ya sami tsakiyar kan wadanda ya harba, wato Yaks da Binta a nasa makircin na nuna musu son Nabila, ga shaidanan ya gani Yaks ya kasa hadiyewa, har sai da ya tare shi gaba-da-gaba, shin ko ya ya Binta ta kalli lamarin? Duk yadda ta dauke shi yana da imanin bai yi mata dadi ba, kuma ya tabbatar ba za ta hadiye ba, ko ta hadiye ya ci alwashin zunguro ta ta fasa masa cikinta.

Yanzu qalubalen da ke gabansa shi ne, Alhaji Ibrahim wanda ya yi imanin idan ya sake shi zai iya nasara a kansa don da gaske ya ke so kamar shi, kuma yana da komai da zai iya nasarar, musamman a wannan lokacin da Binta ta zama tamkar wadda ta fada ruwa, wadda ko takobi aka miqa mata za ta kama.

Almakashi biyu sun sa ta a tsakiya, mahaifanta da suka matsa son ganin mijinta da kuma ita kanta da ta matsu ta sami wani mijin ba shi kansa Mujahid ba.

Saqe-saqen da ya raba dare yana yi ke nan, yana kuma tunanin ta inda zai sarrafa makircin da ya faro, ya ci alwashin tunda Binta ta nuna ita RIGAR SILIKI ce, to kuwa sai ya mayar da ita auduga, duk inda ta wargatse sai ya bi ta da injin niqa.

Binta ta tabbatar ba don zuwan Alhaji Ibrahim ba da ta samu ta yi amfani da shi ta ci fuskar Mujahid ba, da a yau din nan in an ce ta wayi gari da ciwon zuciya to babu musu, don ba qaramin rudu da tashin hankali ta shiga ba a sakamakon wannan kantamemiyar bidi’ar da Mujahid ya kinkimo ya kawo mata, wai kawai ya gama tozartata kuma ya je ya ce yana son Nabila, zuciyarta ta kusa tarwatsewa da wannan sha’ani, don dai kawai tarwatsewar ba a hannunta ta ke ba, amma yanzu ta ina zata shaqo wuyan Mujahid? Ba ta son ta yi kisa ko da na kashe zuciya ne kadai, amma Mujahid na son matsa mata ta yi haka.

Amsar wannan tambayar ta kwana nema, in dai ba karya billenta za ta yi ta tari Mujahid ta tambaye shi ba’asi ba, to ta ina za ta san mafitarsa tunda ta toshe lambarsa ko kiransa ba ta amsawa? Idan ma ta tashi tambayar tasa wanne ba’asi za ta gabatar, na kishinsa ko kuma na nuna isa? Ba lallai ya gane manufarta ita ce tattala dangantakar da ke tsakaninta da Nabila ba.

Ta kwana tana tunanin mafita tamkar Mujahid ya kwana yana kallonta, kuma ya samo matakin zuwa ya amsa mata tambayarta.

Qarfe bakwai da rabi na safiyar ranar ya shiga falon Hajiya cikin shirin fita aiki, bayan sun gaisa ya yi fuska ya ce wa Hajiyar.

“Hajiya, Binta fa?”

Hajiya ta yi tamkar ba ta da niyyar ta zargi komai a tsakaninsu cikin basarwa ta ce.

“Ka duba falonta? Allah sa ma ta tashi daga bacci, ka santa da lalaci”.

Ya yi gaba cikin hanzari yana cewa,

“Dole a taso ta yanzu, saqon da aka ba ni na ba ta bai kamata abar shi ya wuni ba”.

Cikin gatse da dariya Hajiya ta ce.

“Eh, gara a ba ta kam saboda kar ya rube.”

Mujahid bai fahimci komai ba, yana dariyarsa ma ya wuce yana yi wa Hajiyar sallama.

Ita kuma ta daga murya tana tambayarsa cewa, ya dauki fulas din shayinsa.

Ya amsa mata da cewa, ya dauka.

A falon Binta ya tarar babu kowa, saboda haka ya yi tsammanin duk suna bacci don yana da tabbacin ba ita kadai ta ke kwana a dakin ba, duk da cewa dakinta ne ita kadai ba tare da hadaka da sauran ‘yammatan da ke gidan ba, ita da kanta ta so hakan don dukkansu babu wadda ba ta girmewa  ba, duk da kuwa raba dakin ma bai hana su dabdala a nata ba.

Ya jima tsaye cikin fargaba da jiran wani ya shigo dakin ko ya fita, har sai da ya lura qarfe takwas na haramar cika, sannan ya yanke shawarar qarasawa qofar dakin ya fara qwanqwashinta, tare da sanya ran kowa ma zai iya fitowa daga dakin ba Binta kawai ba.

Bai jima ba aka murza qofar dakin, abin burgewa kuma Binta ce ta bude dakin, sanye da hijabi riqe da dogon carbi, ammaa cikin alamun farkawa daga bacci.

Tuni duk wani magagi ya sake ta, ta zaro ido cikin firgici, da sauri kuma ta dubi cikin dakin, da alama kamar ko wanne lokaci ba ta qaunar wani ya san abin da ya ke faruwa a tsakaninsu.

Cikin zafin nama ta ture shi ta wuce tare da janyo qofar dakin ta rufe, ta tafi can tsakiyar falon ta yi tsaye tana qare masa kallo cikin kala-kalar tashin hankali.

Ya yi fuska ya yi taku har gabanta yana cewa.

“Wai wannan firgicin na mene ne tamkar kin ga wanda ya fado daga duniyar Neftune?”

Ta dage da qyar ta hadiye wani mugun yawu wanda ya ba ta sararin gabatar da tsiwar da ta taso mata, cikin yatsine ta ce.

“Allah sarki, ai in daga can ka fado kai abin a tsaya a kalla ne, amma yanzu ai batan basira ne mutum ya tsaya kallonka babu dalilin ina ma din ya bude ido kar ya ganka.”

Ya dora mata ido sosai abin da ya san ta dade da tsana. Ba tare da ya nuna damuwa da kaifin harshenta ba ya zura hannu a aljihu ya fito da wani kyakkyawan fure ya miqa mata cikin taushin murya, yana cewa.

“Ni ba neman fada ya kawo ni ba sanyin raina. Mun kwana biyu ba mu gaisa ba ne, kuma ban yi wa soyayyata garambawul ba, karbi, ina sonki.”

Babu wanda ya fado mata rai daidai wannan lokacin sai Nabila da ganin da ta yi musu a jiya, wani jiri ya dinga neman nuna mata iyakarta tana dojewa, ba ta da niyyar tanka masa, don idan dai ba ashar ba a daidai wannan lokacin ba ta ga furucin da za ta iya yi masa ba.

Yana ta miqa mata fulawar tana binsa da kallo tamkar wata diban haukan bana, ba zato babu tsammani ta ji ya wafci hannunta ya yi wa tsintsiyar hannun riqon tsauri, yana mata kallon kashedi cikin tsattsaurar fuska.

Ta suma da mamaki da tsoro, sai kallon qofar dakin baccinta ta ke da qofar shigowa tana ta qoqarin ta yi magana ta kasa.

Bai damu da firgicin da ta shiga ba, ya bude tafin hannunta ya dora mata furen sannan ya dora yatsa a bakin alamar ta rufe masa baki, sai kawai ya fara qoqarin janyo ta zai rungume.

Wata irin jarumta ta zo mata, cikin fusata da zafin nama ta fizge hannunta ta yi baya tana nuna shi da yatsa, cikin kakkausar murya ta ce.

“Bana son iskanci Malam.”

Ya rage damarar da ya yi wa fuskarsa zuwa murmushi kadan.

“Ah! To ko sai an biya ne ake iya taba jikinki har a sumbace ki? Na san dai dalilin ba zai zama rashin son iskancinki ba, don ban taba ganin duniyar da dan iska ya ke gudun iskanci ba…”

Ta ji tamkar ya kwara mata ruwan dalma a zuciya, ranta ya dinga quna da furucinsa zuwa fassarar da ya yi mata, kodayake duk wanda ya sai rariya ai ya san za ta zubar da ruwa, yanzu abin yi bai wuce ta hana yadda wasu za su billo su ga nasa iskancin ko su ji furucin bakinsa ba.

Cikin hawaye da raunin murya ta ce.

“Ai ba matakin da ya kamata ka dauka ke nan ba, kawai cire sona za ka yi daga zuciyarka don ban cancanta ba, in ka ji haushin yadda na kasance kuma ba ka son wadda ka ke so ta kasance, to ka fita hanyata kawai.”

Ya dinga girgiza kai cikin dariya yana cewa,

“A’a, ban ji wani haushi ba ni, to me zai sa ma na ji haushi? Qaramar qwaqwalwa gare ki Binta, wanda ka ke so ba abu kadan ya ke yi maka ya ba ka haushi ba.”

Ya yi maganar ne don ya tura mata haushi, kuma ya ci nasara ta shaqa matuqar shaqa, har ta yi qoqarin magana ta kasa.

Ya tunkare ta kai tsaye, abin da ya sa ta zabura ta dinga ja da baya hannu a ka.

“Zan kurma maka ihu wallahi.”

Ya yi fuska ya amsa mata.

“Kar ki kurma don Allah, kawai tambayarki zan yi farashin sumbatarki, abin da na ke qwalama ke nan.”

“Allah ya isa idan ba ka ka fita ka ba ni guri ba.”

Ta fada cikin kubucewar kuka.

Ya dakata da bin ta, amma fuskarsa  ba ta nuna nadama ba, sai ma ya qara yin qasa da murya ya ce mata.

“Ya yi safiya ko? Na tuna sassanyar la’asar ko duhun dare ake kintata a faki ido ko? To za mu hadu da yamma.”

Ya juya ya kada kai zai fice yana sauraron tarin kukanta da ta ke shanyewa.

Sai da ya kai bakin qofa sai ya juyo ya dube ta, har wannan lokacin tana tsaye a wajen dafe da baki cikin qura masa ido, da alama har yanzu a suman mamakin abin da ya yi mata ta ke, abin da dama ya so ke nan, kuma ya samu. Ita a zatonta ita kadai ta iya makirci da cusguna wa mutane, ta zaci ita kadai za ta iya aron rigar iskanci ta yafa har ta biya mata buqata, ba ta san tunda ba kudi ake sa wa a siye ta ba kowa ma zai iya ara ya yafa.

Sai da ya dawo tsakiyar falon sannan ya dube ta da kyau, ya yi fuska ya ce,

“Zan ba ki muhimman shawarwari guda biyu kafin ki dira plan B dinki, Shawarar farko ita ce, duk abin da za ki aiwatar ki dinga tuna cewa, ni lauya ne, qwarewar aikina ba duniya kadai ta ke wa rana ba, ni ma tana yi min. ko ba na son abu in na qura masa ido ina iya gane ko wanne irin motsinsa, bare abin da na ke so wanda a cikin bacci ma ban fasa sanya masa ido ba, lallai sai kin yi taka tsantsan kafin ki iya binne azancina.

Shawarata ta biyu ita ce, duk yadda za a yi ki sanar wa Yaks da baqonki na jiya cewa, da Antaru fa suka shata layi, in an kasa da ni ba a qarewa qalau, saboda haka gudun da babu tsira tsayuwa ta fi shi.”

Ba ta iya tanka masa ba sai da ta ganshi a qofar fita sannan cikin fushin da tsana ta ce.

“Dukkansu ai sun fi ka kyan hali, duk abin da suka yi ai rayuwarsu kadai ya shafa daga duniya har lahira, amma kai fa? Mayaudarin mutum ma irinka, wanda qazantarsa ta kai hada Ya da qanwa yana so lokaci guda”.

Tana rufe baki ya amsa mata.

“Kin rage wa qazantar kaifI da ba ki ce uwa da ‘ya ba, ko kuma qila mantawa kika yi kayan nama ba ya kashe Kura”.

Ya kuma fice daga falon ba tare da ba ta sauraron raddi ba.

A guje ta shige bandaki ta kulle kanta inda ta yi zaman dirshan ta ci uban kukanta kamar wadda ta sami saqon mutuwa.

Ba ta taba tsammanin Mujahid mugun qwallon Shege ba ne sai yau, a sanin da ta yi masa da kallon da ta ke masa da, mutum ne da ta ke ganin babu wuya a yi masa wayo ko a juya shi son rai, ashe qwallon dan iska ne ya buya a malum-malum.

To ta ina zata bi  tayi nasara a kansa?

Dukkan lissafinta na yanzu ke nan kumaa tana da yaqinin amsar da za ta samo ita ce, wadda ya kira plan B ke nan ko amsar ta samu nasararta qila wa qala ce. To amma tunda an ce motsi ya fi labewa haka ta ci gaba da matsawa qwaqwalwarta zana qofofin shiga da fita.

<< Rigar Siliki 16Rigar Siliki 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.