Skip to content
Part 18 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Da yammacin ranar tana ji tana gani ta qala wa kanta cuta ta kulle can quryar daki saboda shakkarta ta fito fili Mujahid ya ganta ya nuna mata bariki gaban mutane.

Duk da ta yi wa Alhaji Ibrahim alqawarin ya zo za su tattauna, har yamma da kuzarinta na jin cewa za ta saurare shi, amma tana jiyo muryar Mujahid dab da zai zo sai komai ya kunce mata, qiri-qiri ta sanqare a gado ya zo dole aka sallame shi.

Bai jima da tafiya ba Yaks ma ya zo, da matsanancin kishin ganinta, shi ma tsoron karuwancin Mujahid ya hana ta ganinsa.

Kwana biyu ta yi tana wannan boyon, a na uku bayan sallar magriba ta jiyo maganarsa a falonta yana tambayar su Karima.

“Don Allah wa mai hotunan Nabila ya yi min alfarmarsa?”

A kwance ta ke sosai, amma ba ta ankara ba sai ganin kanta ta yi a bakin qofa tana musu labe.

Cikin mamaki Ummi ta ce,

“Hotunan Nabila kuma Yaya Mujahid?”

Ya yi fuska ya ce.

“Su mana, ba ki ji da kyau ba ne in maimaita?”

Nan da nan cikin sanyin jiki Ummi ta girgiza kai, duk da a tsorace ta ke ba ta fasa yarfa masa magana ba.

“Ai na zaci na Anti Binta ka ke nufi.”

Cikin bagararwa ya ce.

“Ita ma zan karbi nata, amma na fi matsuwa da na Nabilan, ita ta cika nisa sai mutum ya yi dogon tattaki ya ke ganinta.”

Yanzu kowa mamakinsa ya ta’azzara sai kallonsa suke tamkar suna shakkar idan shi ne.

Karima ce mai qarfin halin kawar da mamaki ta ce.

“Ina da su.”

Cikin nuna farin ciki ya ce.

“Yauwa diyar albarka, bari na bude flashshare ki turo min ta nan, za su kai nawa?”

Ta zolaye shi cikin barkwanci.

“Idan kana son guda dari za ka samu…”

Ya tare ta cikin nuna zaquwa.

“Yauwa, ko sun kai dubu turo min su duka.”

Binta dai na labe tana kasa kunne, tsayuwar ta gagare ta, tuni ta silale qasa ta yi zaman dirshan qirjinta na bugawa fat-fat! Can ta ji Hassana ta ce.

“A wayar Anti Binta ai ina tsammanin za a sami dubun.”

Ta kasa kunne da sauri don jin amsar da Mujahid zai bayar, sai ta ji ya ce.

“Qyale waccan ‘yar zafin kan, ita komai nata sai an siya.”

“Anti Bintan?”

Ummi da Karima suka hada baki wajen tambaya cike da mamaki.

Nan da nan shi kuma ya ce.

“Ita din fa, wai ma tana ina?”

“Tana cikin daki”. Hassana ta amsa.

Ya yi saurin rufe baki da hannunsa kamar gaske, sannan ya rage murya ya ce,

“Amma ku ka bari na ke zuba?”

Kallonsa kawai suka yi a mamakance.

Sai kawai ya basar ya ci gaba da duba hotunan da ake turo masa na Nabila, shi buqatarsa daya Binta ta jiyo shi yana nuna son Nabila, ya san bisa wannan turbar duk juriyarta sai ya zunguro ta, ko dai ta zo ta yi masa bala’i ko kuma in ta nuqu da kyau ta kwaso masa wa’azi. Don haka bayan dogon shiru a tsakaninsu ya sake zunguro zancen.

“Babu wanda zai iya sato min wayar Binta na dauki hotunan Nabila? Wadannan gaskiya sun yi min kadan.”

Yanzu su ma duk sun fara shakkar kar Binta ta jiyo su, ko ma tana ji su din, don haka ba a sami wanda ya tanka ba.

Ya jima yana jiran amsarsu, da ba su tanka ba sai ya basar amma wata tsokanar ya sake yi.

“Ita Binta nata hotunan turo min goma kacal sun ishe ni.”

Da rarrafe Binta ta samu ta koma kan gado ta tabbatar in dai ta ci gaba da tsayuwa a wajen tana sauraron Mujahid babu abin da zai hana a turo qofar a tarar da gawarta a wajen.

Ta sha cin alwashin Mujahid bai isa ya dami rayuwarta ba bare ya sanya mata hawan jinni, ashe ya isa?

Tana jiyo shi ya bar falon cikin dariya saboda wani zaurance da ya yi musu.

“Idan waccan ‘yar kasuwar ko kuma mai bayar da alakoro ta tashi ku isar da gaisuwa ta gare ta, a kuma tuna mata yammacina da darena.”

“To za a tuna mata.”

Ta jiyo Karima na amsawa.

Bayan ficewarsa kuma Karimar ta dora maganarta cikin mamaki.

“Wai me ya ke faruwa don Allah, Ba ku ga Yaya Mujahid ba? Komai fa nasa ya sauya tamkar ba shi ne na da ba.

Kwanyar Binta ta tsinke wa kanta wayar sauraronsa ta koma ji da abin da ya dame ta.

“Women service kai tsaye Mujahid ya ke son ya kira ta, duk maganganunsa abin da suke nuna wa ke na, ta ina za ta iya renon wannan alqiblar tasa ko ta kashe?

*****

Yau ma Mujahid na bacci Binta ta farkar da shi da waya, ya sha uwar birgima murna a gado kafin ya yi fuska ya daga wayar.

“To ya? Ni zan faki ido na zo ko ke za ki zo?”

Cikin rarraunar muryarta ma alamun ta gaji da kuka ta katsi numfashinsa,

“Da ma abin da na kira ka na yi maka kashedi kenan, ni ba karuwa ba ce, don haka ka daina siffanta ni da ita.”

Ya ja gwauron numfashi sannan ya bagarar.

“Uhum! Allah sarki.”

Ya fada cikin yanayin gwasalewa.

Binta ta qara rasa kuzari, alamunta a gajiye ta ce.

“Ban gane Allah sarki ba.”

Kai tsaye ya amsa mata.

“Eh mana, ai karuwar da ta bar gidan iyayenta ma ta je ta kama daki ba ta qaunar a kira ta karuwa…”

Ta qoqarta ta yi qwafa ta ce,

“To ka ci gaba kar ka fasa.”

“Ai fada ma batawa.”

Ya amsa mata cikin halin ko-in kula.

“Ko me na so ina da damar zaba a duniyata da lahirata,in kabarina daya da naka sai ka fada min.”

Ita ma ta amsa cikin rashin ko-inkula, a zuciyarta tana raya kawai za ta daina jin ciwon women service da Mujahid din ke liqa mata, tana da yaqinin siyasarsa ce kawai, amma abin na masa ciwo.

Bai fasa yi mata raddi da baqar magana kamar yadda ta yi masa ba.

“Ni ma ina da damar kiranki da sunan da na so Binta, kabari ma idan daya ne ai na san wutarki ba za ta lashe ni ba tunda ni aikin qwarai na yi a duniya.”

Dole ta yi dif cikin fushi da rashin abin cewa har tsawon sakanni ashirin, sannan ta nisa cikin rarraunar murya ta ce.

“Haka ne, amma ai bai kamata mutumin qwarai ya so wanda ba na qwarai ba, me ya sa ba za ka so Nabila ita kadai ba? Ita ta qwarai ce ta fi cancantar na qwarai irinka.”

Nan ma tana rufe baki ya amsa mata.

“Kafin in fara son Nabila ke na so, sannan ban san ke ba ta qwarai ba ce, to ni kuma ba na asarar so, don haka na yafito Nabila ta qwarai zan hada ku na so, don kar na yi asarar rashin macen qwarai.”

Binta ta ji wata matsananciyar tsanarsa ta mamaye ranta, a qufule ta ce.

“Ai kai ma ba ka cika na qwarai ba,  tunda dai ba ka zama namiji mai kishin iyali ba…”

Ya tare ta cikin tattausar murya bayan shi kansa yana jin ya gaji da rigimar, ita ma da ta ke yi don ba ta san yadda ya ke zurfin sonta ba ne da ta gane cewa, bai cancanci a farkar da shi cikin dare a daga masa hankali ba.

A matuqar tausashe ya ce mata.

“Iyalin wai ba Binta ba ce? Kin kasa  ganewa ne komai ki ka zama ba zan fasa sonki baa, in kin ga dama ki tafi ki kama daki… Na ci alwashin zan biki na ribato ki na auro, buqatata na ganki a gidana a matsayin matata, guraben da macen kirki za a cike ai in na gayyato Nabila ta cike min.”

Bai jira cewarta ba ya sauke wayar.

Shi ya fada shauqin qaunarta, ita kuma a nata bangaren ya barta da fashewa da kuka cikin shauqin tsanarsa.

*****

Yana da yaqinin za ta yi wani motsi tun daga kan Nabila har kan Yaks don haka washegarin ranar bayan sallar asuba ya kira Nabila a waya.

Cikin fargaba da mamaki ta daga wayar da sallama.

Bai ja doguwar gaisuwa a tsakaninsu ba ya tambaye ta.

“Na so in kira ki tun kwanaki in tambaye ki, rannan bayan tafiyata ya ya ku ka qare da Binta da Yaks?”

Muryarta a sanyaye ta ce.

“Yaks bai shigo ba, ina jin ya jira ta a waje ne ko kuma ya tafi.”

Ya yi shiru yana jiran ta dora da labarin Binta, amma sai ta ja bakinta ta tsuke sai da ya sake tambayarta.

“To Binta fa?”

Sai da ta dan ja fasali sannan ta yi magana cikin sanyin murya.

“Ka yi min wata alfarma ni ma.”

A nutse ya ce mata.

“Fade ta in dai ba ta fi qarfina ba na yi miki alqawarinta.”

Ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

“Don Allah ka daina tambayata komai dangane da Anti Binta, yadda ka ke jin ka dauke ni aminiyarka, Anti Binta ta dauke ni fiye da haka, lallai idan tana abu ina kwashewa ina fada maka cin amana ne, Allah kuma ba zai bar ni ba.”

Tsakaninsa da Allah ya ce.

“Na fahince ki Nabila, kuma wannan yana daya daga cikin dalilin da ya sa ki ka fara tasiri a zuciyata kwanan nan, ni ina son mutum mai nutsuwa kuma mai gaskiya.”

Nabila ta yi qoqarin ko nishi ne ta yi ta kasa, tasiri a zuciya kalma ce mai harshen damo, don haka mugun rauni za ta yi a irin tata zuciyar wadda ba ta haddace koma ba sai so, son ma na wanda bai san tana yi ba.

Kamar Mujahid ya san sharhin da ta rakito ta ke warwarewa, sai ga shi da qarin bayani.

”Na yi fatan da ma ke ce Ummi? Lallai da na more qanwa ta ciki daya, ko yanzu ma ina alfahari da ke a matsayin qanwar aro wadda ta yi min abin da kowa bai min ba.”

Mujahid ya yi mata wannan sharhin ne don ya tuna cewa Nabila fa tana sonsa, kwatankwacin yadda ya ke son Binta, ya tabbatar matantakarta ce kawai ta boye son, ya ma san albarkacin son ya ci Nabilan ta ba shi goyon baya, kenan yi mata kalamai irin wadancan babu fashin baqi, za su iya zunguro son daga maboyarsa. 

Babu laifi ta dan sami sukunin da sharhin nasa, har ta sauke ajiyar zucciya ta gode, sannan ta dora da cewa.

“Na ji dadi da ka fahimce ni, kuma a shirye na ke wajen yi maka ko wanne irin taimako ka nema daga gare ni, na san zan sami lada, domin sunnar manzon Allah (S.A.W) na ke hakilon a raya.”

“Ni kalmar godiya ta yi min kadan na gabatar miki da ita, ke ce kawai ki ka gane ina son Binta, ita ba ta san ina yi ba kuma ba ta son ta sani.”

Tsakaninsa da Allah ya yi wanan maganar, kuma muryarsa ta nuna, don haka Nabila ta danne nata raunin ta shiga rarrashinsa.

“Kar ka damu Yaya Mujahid komai zai wuce.”

Ya ji wata matsananciyar kasalar tausayin kai ta rufe shi, kodayake ba kansa kadai ya tausayawa ba, har Nabila ma ya tausaya mata a matsayinta na jarumar da ta boye so, kuma ta sadaukar da abin da ta ke so din domin wadanda ta ke so.

Ya ji a ransa babu abin da zai yi ya biya ta, don tana buqatar qololuwar sakamako ne wanda babu mai yi mata shi sai Ubangiji wanda ta yi so dominsa, kuma ta yi kawaici dominsa, sannan ta ke son taimako dominsa.

“Ubangiji ya biya miki buqatunki na alkhairi duniya da lahira Nabila”.

Ya fada bayan ya farfado dogon tunaninsa da qyar.

Cikin sauri da zumudi ta amsa,

“Amin Yaya Mujahid.”

Ya dora da cewa cikin rauni,

“Sannan na dauki alqawari idan Ubangiji ya amshi roqona Ya ba ni Binta a matsayin abokiyar rayuwa, diya mace ta farko da zan haifa sunanki za ta ci.”

“Ba haka na so ba”. Nabila ta raya a  ranta, idonta na tsattsafo da qwalla, “Abin da na so shi ne na zama matarka ba ‘yarka ta ci sunana ba.”

Ta sake rayawa a ranta, sannan ta yi qarfin hali a zahiri ta ce.

“Ni ce zan sami wannan karramawar Yaya Mujahid? Na rasa bakin da zan gode.”

Tana magana cikin murna da dariyar yaqe.

Sai Mujahid ya ji wani dadi ya dan cika ransa, ya ji kuma tausayinta ya qara shigarsa, wato ita Karimaar mace ce wadda karamci kadan ya ke wadatarwa?

“Ba don zai zama shirme ba in dai wannan zai faranta miki duk ‘ya’yana mata ina iya sanya musu suna Nabila.”

Yanzu ta sami damar sakin kukanta kadan a zuwan na farin ciki ne, cikin kukan ta ke fadin.

“Wannan ma ni ya ishe ni,kuma Allah ya cika muku burinku duniya da lahira.”

“Amin.”

Mujahid ya fada a sanyaye, don ya haqiqance wannan kukan na Nabila ba na farin ciki baa ne ta ke, na nuna tsantsar sonsa ne ta ke boyewa a rigar farin ciki.

Babu yadda ya iya, dole ya biye mata suka tafi a haka, suka dan jima suna hirar sannan suka gangaro abin da ya janyo kiran wayar. Mujahid ya ce

“Ki ka ce ba ku sake haduwa ko yawa da Binta ba tun daga ranar da muka zo gidanku?”

A taqaice ta amsa masa.

“Haka ne.”

Mujahid ya xan nisa.

“To ina tsammanin yau idan Binta ba ta zo gidanku ba tabbas za ta kira ki a waya.”

Nabila ta dan yi dum, sannan ta ce.

“Wani abu ya faru ne?”

Ya kada kai da sauri tamkar tana ganinsa.

“Oh tamu ce ta hado mu, ina kuma da yaqinin za ta nemi sako ki.”

“Uhum.”

Nabila ta dan yi nishi.

A nutse Mujahid ya ce.

“Abin da na ke so da ke shi ne, idan ta  zo ko ta kira ki, da ta nemi bayani a kaina ki ce mata jiya na zo gidanku.”

Nabila ta jima cikin shiru kafin ta tanka tana dariya.

“Ni dai fatana kar ka haqa min rami na zurma Yaya Mujahid.”

Ya amsa cikin dariya shi ma.

“Ki yarda da ni Nabila, ko zan cutar da kowa a duniya babu ke a ciki.”

Wasu kaifafan abubuwa suka dinga tseren soke mata zuciya da lissafi, dole ta ji babu wata mafita bayan ta yi sallama da shi salin alin, idan ba haka ba kuma ya haukata ta da irin wadannan kalaman nasa masu guba a cikin rarraunar qwaqwalwa irin tata.

“Na gode Yaya Mujahid, sai mun sake waya.”

Ya so ya fahimce ta, amma muryarsa ba ta nuna ba, cikin fargaba ya ce.

“To babu laifi, sai na kira.”

<< Rigar Siliki 17Rigar Siliki 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.