Skip to content
Part 19 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Duk qwarewar saqar Binta ta kasa saqa ragayar da za ta sagale kanta ba tare da damuwar rayuwa ko jumurdarta sun dame ta ba.

Yanzu ba Mujahid ne kaxai matsalarta ba, Alhaji Ibrahim da Yaks ma matsalolinta ne, na farko dai Alhaji Ibrahim ya sai silifas din da zai kashe a yawon yi mata naci ba tare da qosawa ba. 

Ba dare ba rana duk lokacin da ciwonsa ya mintsino shi sai ya baro sabgar gabansa ya taho don ya ganta, amma ta qi yarda qememe ya ganta, kamar yadda ta hana kanta daga wayoyin da ya ke damunta da su.

Wannan dan banzan nacin nasa ya fito da zallar qaunar da ya ke mata qarara, ba ita kadai ta fahinci haka ba, kowa ma agidan ya gane Alhaji Ibrahim.

To haka ma Yaks wanda zafin da Mujahid ya hada masa ya tashe shi tsaye wajen nemaan ta inda plan din Binta zai amfane shi.

“Binta ki fito da ni haske, ni fa gani na ke kamar kin min shigo-shigo babu zurfi, wannan shirin naki babu abin da ya amfane ni da shi sai qara nisanta ni da Nabila.”

Abin da Yaks ya ke ta faman mamaita mata ke nan, wayar safe daban ta dare daban, wani lokacin har da kukansa.

Kan Binta kamar ya yi bindiga don tunanin ta inda za ta kubuce wa wadannan qusoshin da suka saita ta.

Zuwa yamma dabara ta zo mata, zata zuga Nabila ta zabi Mujahid ya fito ya aure ta ta huta, in kuma ta qi yarda zata zuga Nabila ta auri Yaks ita kuma ta yi gaggawar tsayar da Alhaji Ibrahim ta aura ko da a maneji ne.

Kamar yadda Mujahid ya yi hasashe, da yamma sai ga shi Binta ta kira Nabila.

Qirjin Nabila na faman dakan uku-uku ta daga wayar tana karanto a’uziyya cikin ranta.

Gabadaya jikin Binta a sanyaye ya ke, ta ce wa Nabila.

“Ban san laifin da na yi miki ba Nabila, kwana biyu hatta a waya kin watsar da ni.”

Nabila da fara’arta ta ce.

“Lah, wallahi ba haka ba ne Anti, kin san mun tunkari WAEC kullum cikin darasi mu ke.”

“Kayya!”

Binta ta fada cikin alamun bayyana karaya.

Nabila ma jikinta a sanyaye ta ce.

“Kayya me Anti? Don Allah ki yarda da ni.”

Binta ta yi dariyar qarfin hali ta ce.

“Ban taba tunanin za ki cutar da ni da gayya ba, amma sai na ke jin yaqinin za a iya yaudararki a cuce ni.”

Kawai sai Nabila ta ji hawaye na taho mata jin Binta ta tabo mata abu mai kama da gaskiya, ko ma gaskiyar kai tsaye, sai dai kuskuren da Binta ta yi shi ne, ita ba yaudararta Mujahid ya yi ba, da qarfin tasirin so ya yi galaba a kanta. Tana so ko ba ta so ta san ranta zai mutu yana yn abin da Mujahid din ke so, ko da kuwa wanda za a cutar ya fi Binta daraja a duniyarta.

Tun daga nan jikin Binta ya qara mugun sanyi, don ta haqiqance banza  ba ta kai zomo kasuwa ba, shirun da Nabila ta yi ya tabbatar mata lallai abubuwa marasa kyau a labarinta da Mujahid sun ci gaba da faruwa.

Da qyar ta ja numfashi ta janyo abin cewa.

“Mujahid ya ci gaba da zuwa wajenki?”

Cikin tsananin rikita Nabila ta ce.

“Ban gane tambayar ba Anti.”

A raunane Binta ta ce.

“Na san kin gane Nabila, ina tsammanin amsar ce ki ke tunanin ba za ta yi min dadi ba.”

Nabila ta shaqi numfashi a gajiye tamkar wadda ta sha gudun famfalaqi, kai tsaye kuma ta sheqo qarya cikin rarraunar murya mai alamar son nuna nadama.

“Jiya ma ya zo Anti, amma bai jima ba ya tafi.”

Wata qaqqarfar kibiyar takaici ta soke Binta a qirji, ta dinga yamutse fuska tamkar mai jin kashi, sai numfarfashi ta ke tsawon lokaci ta kasa cewa komai.

Nabla ta qirqiro kukan dole tana cewa.

“Ki fahince ni Anti, ba laifina ba ne…”

Binta ta tare ta cikin murya mai alamar boye fushi.

“Laifinki daya, kina son Yaya Mujahid kin kasa ba shi hadin kai, ni ya fita daga rayuwata. Nabila wanne irin kwado ne da Mujahid zai hada mu ya so tare?”

Nabila ta ji kanta ya yi wani irin gingirin, sannan waswasi ya cika zuciyarta, a sanyaye ta ce.

“Ko Yaya Mujahid ba na tsammanin ya rakito so ya kawo min don na ba shi hadin kai ya manta da ke Anti, son da Yaya Mujahid ya ke miki ba irin wanda ake mantawa haka kawai ba ne Anti, don Allah ki sassauta zuciyarki ki fahimce shi.”

Ban da  zagi da hantara babu abin da Binta ta ke jin za ta yi ta fanshe wadannan maganganun na Nabila, sai dai Nabilan ta fi qarfin hakan a duniyarta, dole ta bige da fashewa a kan lebenta wanda ta dinga garzawa  cizo cikin huci kawai, har da qyar ta sauke ajiyar zuciyar jin sasaauci ta ce mata.

“Ba na son zafafa bayyana ra’ayina a kan hangenki ko kuma alaqarki da Yaya Mujahid Nabila, don za ki iya zaton kishi na ke, ba lallai ki gane ko mazan duniya za su qare ba zan iya maneji da Mujahid ba.”

Ta yi shiru tana sauke numfashi alamar jiran cewar Nabila, amma ina, ita Nabila tuni kanta ya qulle, abin da Antinta ta ke fada ji ta ke kawai ya ci karo da hankali, ita a wajenta Mujahid ne wanda za a dora a sikeli ya rinjayi duk mazan duniya a idon kowa, amma ga Binta ta zo da almarar cewa duk duniya shi ne bai mata ba.

Binta ta dinga kara-kaina da maganar da ke son fitowa bakinta, don fargabar yadda Nabila za ta karbe ta, amma tunda ba ta da wata mafita kawai sai ta ga babu abin yi wanda ya wuce ta furta din, amma dai ta sha ajiyar zuciya da gyaran murya kafin ta yi qarfin halin fito da maganar.

“Nabila ke zaki taimaka ki ceci rayuwarmu…”

Cikin fargaba da daga murya Nabila ta ce.

“Na yi me?”

Kai tsaye Binta ta amsa.

“Ki zabi daya cikin biyun nan ki aura, Yaks ko Mujahid…”

Nan da nan idon Nabila ya sake billowa da hawaye, cikin muryar son fashewa da kuka ta ce.

“Ba qyashi na ke son nunawa ba Anti, amma da gaske ne yadda ku ke son nuna wa gabadaya an halicci rayuwata ne na zama garkuwa ga baqin cikinku, kuma na zama mabudin farin cikinku.”

Ta katse saboda shesshekar kukaa, sannan ta dora.

“Na fada miki ba qyashi na ke ba, amma ni kamar nawa zabin da farin cikin ba a bakin komai ya ke ba.”

Binta ta yi mugun rikicewa  don ganin gajen haqurin da Nabila ta nuna, duk da kanta ya daure a lamarin jam’i da ta ke ambato, a maimakon ita kadai da ta yi mata ba daidai ba.

“Ni da wa muke tauye haqqinki Nabila?”

Ta ji tambayar ta fito daga bakinta ta fado ba tare da ta shirya ba.

Da sauri Nabila ta koma cikin hankalinta jin tana shirin tona asirin masoyinta wanda qauna ba za ta yafe mata ba idan ta tona, ita da kanta ma ba za ta yafe wa kanta ba.

Cikin shesshekar kuka ta ce.

“Ba haka na ke nufi ba Anti.”

A mamakance Binta ta ce.

“Ba haka ki ke nufi ba me?”

Nabila ta dan yi wura-wura da ta rasa abin da za ta ce, kawai sai ta ce.

“Ba komai.”

Kan Binta ya qara kullewa, ta yi tsam a rikice komai ya kwadance mata, so ta ke ta gaskata maganar Nabila kan zargin danne mata haqqi, amma tana jin kamar in ta karbi wannan laifin ba ta yi wa kanta adalci ba, so ta ke ta kubuta daga tarkon da ta ke neman fadawa kawai, ba so ta ke ta kubuta Nabila ta fada wanda ya fi shi muni ba, abin da zuciyarta ta sani ke nan, amma Nabila ba ta ba ta damar fayyacewa ba ta bi ta da zargi.

Kodayake tunda ta tsokano ma ai ya kamata ta dire ko don ta samu ta wanke kanta.

Cikin nuna sallamawa ta shiga yi wa Nabila bayanin qudirinta.

“In kin bai wa Yaya Mujahid qofar ya nemi aurenki, za ki amfanar da ni da janye hankalinsa daga rainin wayon da ya ke min, ni kuma sai na ququta na nemo wanda na ke so na aura kafin ya waiwayo kaina tunda ya ce mata biyu ya ke son aure, kai idan ma ba ki so ba, kina iya fasa aurensa lokacin da nawa neman auren ya kankama, ai dai dole zai ji kunyar mutane ya dawo da soyayyarsa kaina.

Sannan zabi na biyu, idan kin zabi Yaks, jihadi za ki yi. Yaks yana sonki kuma zai iya sauya komai dominki…”

Cikin dariyar tsabar takaici Nabila ta tare ta da cewa,

“…Sannan in auri Yaks, ke kuma za ki haqura ki auri Yaya Mujahid? In haka ne zan amince.”

Ta sake sauke zancenta cikin dariya.

Binta ta ji wani jiri na neman tiqata da qasa, harshenta ya sarqe don haka ta kasa magana, ta san ba komai ba ne sai tsabar qin da ta ke wa Mujahid.

Nabila ta fahimce ta, wannan ya sanya ba ta janye dariyarta ba ta ci gaba da cewa.

“Na dauki zabi na biyu don shi nake cike da sadaukarwa da jihadi, zan auri Yaks don kar mu hada miji daya kamar yadda ki ka yi hasashe, wato Yaya Mujahid. Kuma zan taimaki Yaks a matsayinsa na makahon sona da zai iya sauya komai domin ni, sannan ke ma za ki jihadin ceto mai qaunarki fiye da yadda Yaks ke sona, wanda bai hada soyayyarki da ta kowa ba…”

Ta dan ja fasali kafin ta xora.

“A  halin yanzu babu abin da na ke fata da dokin gani sai ranar da za ki gane irin son da Yaya Mujahid ke miki.”

Kawai ta kashe wayar ba tare da ta jira cewar Binta ba.

Duk dauriyar Binta na jin bai kamata ta yi wa Nabila rashin mutunci ba ko da a bayan idonta, a yau sai da ta sami kanta da cusa mata zagi bayan ta yi wurgi da wayarta. Ta dinga hada gumi ita kadai tana binsu daidai da daidai da zagi tun daga kan Mujahid din har kan Yaks da ita Nabilan. Amma daga qarshe ba ta da zabi dole ta sake kiran Nabila a waya cikin yanayin hadiye bacin rai da damuwa ta ce mata.

“Abin da na guda shi ya ke son faruwa, wato kin zargi ina kishin son da Yaya Mujahid ke miki, kaico!”

Maganarta ba ta bata ran Nabila ba bare ta sanya ta fargaba, dariya ma ta ke saboda ta fahinci lallai da gaske ne Mujahid da Binta sako ta suka yi a gaba tamkar qwallo, ko wannensu ita ya ke son ya doka ya zira a raga ya dau kofi. To me ya sa sai ita suka zaba su mayar qwallon? Dariya da son mayar da komai ba komai ba ba su ba ta damar kokawar amsa tambayar ba, kawai sai ta cewa Binta.

“Anti ai na zaci mun kashe wannan Bos din tunda kin ba ni zani na zaba…”

Binta ta tare ta a qufule.

“Wallahi zan cusa miki zagi Nabila”.

“Allah ya ba ki haquri Anti.”

Nabila ta fada cikin dariya.

Binta ta yi fuska ta ce.

“Ina son ganinki gobe da yamma, idan ba za ki sami zuwa ba ni zan zo har gida in same ki…”

“Kar ki damu zan zo ma.”

Nabila ta fada cikin dariya, sannan ta zarce da cewa.

“Ai babu yadda za a yi in share amsa kiran babbar Yaya bare na san za ta gayyato min Yaks.”

Binta ta zaro idon mamaki.

“Ya aka yi ki ka san hakan?”

Kai tsaye Nabila ta amsa.

“Ai ya kamata na sani ne saboda na ji cancantar na fara aiki da kwanya tamkar yadda ku ke yi ke da Yaya Mujahid.”

Sai abin ya sake daure wa Binta kai, ta jima cikin shiru kafin ta tanka.

“Me ya sa ki ka ce haka?”

Nabila ta sake dariya.

“Amsar wannan tambayar tana cikin maganar da na yi yanzu.”

Binta ta nisa a sanyaye ta ce.

“Na fahimci akwai magana a bakinki sosai,in kin zo lallai dole ki bude ciki mu yi ta.”

Nabila ta sake tuntsirewa da dariya.

“Ni zan zo ne don batun da ki ka kira ni a kansa, maganar da ki ka fahimta a cikina ki bar min abata a cikin, kawai duk mu hudun mu bude qwanjinmu mu zube basirarmu duk mai qarfi da sa’a sai ki ga ya yi nasara.”

Kan Binta ya sake shiga duhu.

“Duk mu hudu kamar ya ya? Mu da su wa?”

Nan ma cikin karsashi Nabila ta amsa.

“Ni, Anti Binta, Yaya Mujahid da kuma Yaks. Akwai alamar a cikinmu za a zabi gwarazan wannan shekarar.”

Kawai sai ta sake  kashe wayar ta bar kan Binta cike da hayaqi duk hasashe da basirarta ta kasa warware wannan zaurancen na Nabila, kuma wannan ya tabbatar mata lallai akwai wani qulli wanda idonta ko hannunta bai kai kansa ba bare ya fara shirin warwarewa, dole ta zama cikin taka tsantsan.

<< Rigar Siliki 18Rigar Siliki 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×