Skip to content
Part 16 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Tafiya kawai Binta ke yi ba tare da ta damu da neman mota ko mashin ta hau ba, ba don ba ta buqatarsu ba sai don gabadayan lissafinta bai lissafo da su ba.

Ba ta taba tsammanin kana mafarkin yaqi ka farka ka ganka da takobi a hannu ba, don haka ba ta taba tsammanin qaryar da ta shara wa Yaks ta cewa Mujahid yana son su da Nabila abin zai iya zama gaskiya ba, abin ya zo mata a ba-zata, in kuma ya tabbata ba ta san a wacce irin qaddarar za ta iya daukarsa ba.

Binta na tafe da matsalarta cikin rashin hayyaci, Alhaji Ibrahim na biye da ita cikin motarsa Honda, bayan babu zato babu tsammani tsuntsun son Binta ya fada tarkonta daga yi mata kallo daya.

Shi Agent ne a wani shahararren kamfanin tafiye-tafiye, yana da kimanin shekaru arba’in yana da mace daya da ‘ya’ya hudu.

Ya kawo ziyara unguwar su Nabila ne domin ganin wani gida da ya ke shirin siye. Mutum ne mai mutunci da sanin haqqin iyali, bai taba tunanin qarin aure ba sai yau daya kacal da ya fada tarkon matsanancin son wannan yarinyar mai kama da tana cikin maye.

Ya yi qoqarin hana zuciyarsa wannan son da ta rikito, amma ya gaza, illa ma ingiza shi da ta ke cewa, ko giya ta shawo lada zai samu idan ya ribace ta ya aura ya adana ta ya hana ta shaye-shayen, don haka ya ji babu wata kamata illa ya bi ta a boye ya ga inda za ta je, in yaso daga bisani sai ya yi tunanin ta inda za su warwaro ta.

A sannu ya dinga bin ta ba tare da saninta ba, idan ma ya wuce ta sai ya sami guri ya faka har sai ta zo ta wuce shi.

Cikin haka har ya ga ta dauki shatar tasi ta shiga, shi kuma ya rufa musu baya.

Tasi din ta tsaya a qofar gidansu, ta fito ta shiga gida, shi kuma ya tsaya nesa da su yana hange. 

Ya fahimci kudin motar ta shiga karbowa don bai ganta da jaka ko alamun kudi ba, ga kuma mai tasi din yana jiranta, har ma ya qagu ya fito ya fara waige-waige.

Da sauri Alh.  Ibrahim ya bude mota ya fito ya je ya same shi.

“Kudinka ka ke jira ko?”

Ya tambayi mai tasi yana zura hannu a aljihu.

Mai tasi ya sauke ajiyar zuciyar farin ciki, cikin saurin baki ya amsa.

“Eh wallahi ranka ya dade.”

“Nawa ne?”

“Naira dari huxu.”

Mai Tasi ya amsa.

Alhaji Ibrahim ya zaro dari biyar ya miqa masa, ya ba shi canjin dari.

Ya ja tasinsa ya wuce, shi kuma ya fara dakon jiran gawon shanu.

Binta za ta fito ta sallami mai tasi, ba zata fito ba, sai sama da mintina ashirin, duhu ya fara sako kai ke nan.

Nan ya qara gaskata cewa, macen da ya ke so a buge ta ke, lallai ta manta da mai motar da ya dire ta.

Ya fara tunanin jan jikinsa ya tafi in yaso wani lokacin ya dawo ya ganta, sai kuma ya shiga fargabar kar dai ba nan ne gidansu ba, kar ya yi kasassaba ya tafi kuma ya dawo a rasa gane wadda ya ke nufi. Nan fa ya fara du’a’in Allah ya koro masa mafita.

Ga shi dai gidan nasu babba ne, har ma da qaton get da harabar ajiye motoci, sai dai da alamar babu maigadi a qofar, don yana kallon ita ma kafn ta shiga ita ta zura hannu ta zare sakata ta ciki, ta bude ta shiga.

Yana nan yana du’a’insa sai ga shi Allah ya amsa roqonsa, maimakon ma ya aiko masa dan aike kamar yadda ya roqa, sai ga shi an jefo masa Bintan da kanta.

Ta fito a firgice hankalinta a tashe tana waige-waige, ba ya tantama direban tasi ta ke nema.

Cikin wani matsanancin farin ciki ya fito daga motarsa bayan ya matsa mata hon.

Cike da fargaba da mamaki ta zuba masa ido har ya qarasa kusa da ita.

Cikin matsananciyar fara’a, ya ce mata.

“Ni ki ke nema ko? To ga ni.”

Ta kalle shi da kyau, da sauri kuma ta juya ta kalli motarsa sannan cikin shakku ta qara kallonsa tana girgiza kai.

“Kai wannan motar na shigo da ma?”

Ya juya ya kalli motar tasa yana dariya.

“Au wai ba ki lura ba?”

Cikin shakku da saduda ta miqa masa takardar dubu daya tana cewa.

“Ban kula ba wallahi, dauki kudinka, kuma ka yi haqurin dadewar da na yi, sha’afa na yi wallahi.”

Ya sa hannu ya karbi kudin don ya riqe masa ita yana cewa.

“Ai na lura ma kamar ba a cikin hayyacinki ki ke ba.”

Ba ta tsinka masa ba, illa kallon agogon  hannunta tana sauke ganinta a qofar gidansu. 

Tana hasashen fitowar Mujahid ne don zuwa masallaci, ba ta son ganinsa a daidai wannan lokacin, akwai dai lokacin da ta tanadar masa, don ta san haduwar ba za ta yi musu kyau ba.

Alhaji Ibrahim da ya lura da zaquwarta na alamun son tafiya sai kawai ya fara gabatar da kansa.

“Sunana Ibrahim Usman, shekaruna arba’in, ina da mace daya da yara hudu, ni ma’aikaci ne na Nagarta Travelling Agency, a yanzu ina da qudirin zamowa mai igiya biyu, wato mai mace biyu bayan ban taba sha’awar hakan ba, sai yau daya da na dora ido a kanki farad daya kuma ki ka jefa min matsanancin sonki a zuciya.”

Tuntuni Binta ta rude, sai kallonsa ta ke baki bude tana jin wani irin kaico game da rufewar idon da ta same ta har ta tare private car ba ta sani ba, qila wani kallo ya yi mata daban shi ya sa zai rakito mata wani mugun rainin wayo da sunan so.

Da alamun fushi ta daga masa hannu ta ce.

“Ji nan Yallabai! Ba fa bisa sani ne na tare motarka na shiga ba, wani rudu ne ya gigita hankalina a dazu, amma ni mace ce mai mutunci da ban taba gwada hawa lift ba, don haka ina roqonka da ka dauki kudinka kawai ka ba ni canji na zan shiga gida.”

Tana sababi shi kuma yana shanye baki yana kallonta, daga fuskarta mai fushi  zuwa zazzaqar muryarta har ma’anar furucinta babu abin da bai faranta masa rai ba. Ya sha dandanar so a baya lokacin samartakarsa da kuma aurensa, amma bai taba dandanar mai zafin irin nata wanda ya ke shawagi a qirjinsa yanzu ba.

Sai da ta dire ya farko daga shagalar kallonta ya sami bakin tankawa.

“Alhamdu lillahi.”

Abin da ya ce ke nan.

Ta so ta zabga tsaki amma ta ankara daga furucin da ya yi har maganarsa ba su cancanci tsakin ba. Godiyar Allah ya furta, sannan a matsayinsa na mutum mai alamun dattako da kamala bai kamata ta yi wa kanta lambar fitsara a idonsa ba.

Ya sake jan fasali, sannan ya ce mata.

“Gaskiyar maganar ba motata ki ka hawo ba, na tsinto ki ne kina tafiya kina hada hanya kamar mai maye, tamkar ki dauki qaton dutse ki jefa rijiya ki ji qararsa tinjim! Haka na ji qarar fadawar sonki zuciyata, don haka na dinga binki a baya har lokacin da ki ka hau mota, na rufo muku baya, ni na sallami mai motar.”

Fiye da kashi hamsin Binta ta saki damarar da ta yi wa fuskarta, kuma ta yi godiyar  Ubangjin hadiye tsakinta da ta yi.

A wannan lokacin ne kuma ta yi nazarin baqon nata, farin mutum kamilalle mai matsakaicin tsawo da qiba, abu daya ne bai yi mata a shi ba shi ne, ma’abocin barin qasumba ne, duk da ta ji gyaran mai da aski, amma ita sam ba ta burge ta.

“Ka yi haquri gaskiya an yi min miji…”

Haka ta debo fada masa, amma da sauri ta katse lokacin da ta ji alamun bude get din gidansu, tana juyawa kuwa ta ga wanda ta yi zato ne, wato Mujahid.

Alamunsa sun nuna hankalinsa a matuqar tashe ya ke, sai dai ba kowa zai gane hakan ba sai wanda ya laqance shi, sanyin jikinsa da kasalar da ya ke nuna wa a rufe get din sun dakusar da kuzarin mazantakar da kowa ya san shi da ita.

Alhaji Ibrahim ma ya fada tasa duniyar tashin hankalin, kalaman Binta sun gigita shi qwarai, an yi mata miji baqar qaddara ce da bai san bayan da zai sa ya goya ta ba bare ya rungume ta.

“Ki qarasa mana, me ki ka ce?”

Ya tambaye ta muryarsa na karkarwa.

Cikin sakanni kadan wani makircin ya saqu a zuciyar Binta, duk duniya babu wanda ta ke son baqantawa irin Mujahid, don haka bai kamata ta dinga salwantar da duk wata damar baqanta masa da ta shigo hannunta ba.

Ga wannan man din ta silarsa yau ya kamata ta hana Mujahid baccin dare kamar yadda ta ke da tabbacin ita ma ba za ta runtsa ba.

Nan da nan ta saki fuska ta ce wa Alhaji Ibrahim.

“Wannan gumin fa?”

Ya sauke wata wawuyar ajiyar zuciya ya ce.

“Cewa fa ki ka yi an yi miki miji?”

Ta tuntsire da dariya ta ce.

“To share guminka na janye cewar.”

Suka yi dariya su duka, daidai lokacin da Mujahid ya zo ya gota su dariyarsu na kada masa ganguna a kwanya. In ya dauki alaqarta da Yaks ‘Game’ game da wannan gayen alaqarsu ba za ta tana zama game ba.

Kunnuwansa suka kwaso masa muryar Binta tana cewa.

“In shiga gida in kawo maka ruwan alwala in yaso bayan masallaci sai mu tattauna?”

Ya juyo  mutumin nata da amsawa.

“A’a raanki ya dade, lambar waya za ki ba ni, akwai ruwa a motata zan yi alwalar in na yi sallar wucewa zan yi, zan kira ki anjima mu dora inda muka tsaya.”

Yana jiyo Binta na karanto lambarta, can kuma ya ji qarar bude qofar gida alamun ta shiga.

Daidai wannan lokacin nasa makircin ya bijiro, kawai sai ya sami kansa da yin kwana ya dawo baya, inda ya sami Alhaji Ibrahim ya fito da ruwa a motarsa zai yi alwala.

Cikin sakin jiki ya same shi.

“Wai fa dawowa na yi in yi kashedin a haqura da zancen haka a je a yi sallah, in yaso sai a dawo a dora.”

Alhaji Ibrahim ya cika da farin cikin ya ga na gida, duk da Binta ba ta yi kama da Mujahid ba, domin shi farin bafullatani ne wanda ta ko ina kamarsa da fulanin ba ta nuya sam, sananin Binta baqa, kuma ba mai alamun santsin gashi irin nasa ba.

Duk da haka Alhaji Ibrahim ya ji imanin alaqarsu ta jini. 

Cikin sauri ya miqa wa Mujahid hannu suka gaisa kowa fuskarsa cike da fara’a, sannan ya zarce da cewa.

“Ai ni sabon zuwa ne, ba lallai a tarar da ni kamar kowa ba.”

Cikin nuna barkwanci Mujahid ya ce.

“Na fahinci haka, ai na dauka ma wani tsageran yaro ne mai cinko a ka, sam Binta ba ta yi daidai da shi ba amma ta ke sauraronsa, kodayake ta ce min tausayi yake bata don ya fada tarkon so da kyau, ina fatan kai sabon zuwa din nan za ka sanya kwanji ka ture gwamnatinsa, don na fahinci ta ko ina ka fi shi cancanta.”

Farin ciki ya sake mamaye zuciyar Alhaji Ibrahim, cikin karsashi ya amsa wa Mujahid.

 “Na fi shi jin so wallahi, amma ka dafa min kar na kasa, don in na gaza ana iya asarar rai, ba zan iya jure rashin ba…”

Wani mugun takaici ya kutufi maqogwaron Mujahid, amma dole siyasa ta sanya ya hadiye shi ya shanye ya dinga baza dariyar yaqe.

“Kar ka ji komai, ni ne babban wa, taho ka dafa kafadata.”

Duk suka sake tuntsirewa da dariya.

Alhaji Ibrahim ya kammala alwala suka rankaya masallaci tare suna ta faman barkwanci.

Bayan idar da sallah har wajen mota Mujahid ya rako shi, sannan suka rabu bayan sun yi musayar lambar waya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.6 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 15Rigar Siliki 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×