Skip to content
Part 15 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

LITTAFI NA BIYU

Binta ta yi qoqarin boye dukkan damuwarta a birnin zuciyarta, har ta gama kwasar gaisuwa a wajen Hajiya Inna kakar Nabila.

Dattijuwar mace wadda tsufa ya gama yi wa sallama, amma kirkinta sabo fil, ga kamala da yawan fara’a da alama duk halayen kirkinta Nabila ta kwaso.

Tana ganin Binta dayake ta san amincin da ke tsakaninsu da Nabila, ta hau kawo mata kukanta,

“Kin ga qanwarki ba kya yi mata fada ko Binta?’

Yaqe kawai Binta ta yi, don ba ta da abinda ya fi shi, fishin da ta kwaso da shi cikin gida gaba daya kirkin mutanen gidan ya tarwatsa shi, Nabilan ma haka ta dinga yi mata marhabin kamar zata dauke ta goye.

“Me qanwar tawa ta yi miki Inna?”

Cikin sanyin murya Inna ta ce,

“Ta qi yarda ta tsayar da miji, kowa ya zo sai ta kore shi, tana ganin lamarin kamar wasa, in Allah ya karbi raina Allah ne kadai ya san halin da zata shiga.”

Fuskar Binta cike da walwalar da ta taso tun daga zuciyarta ta amsa wa Inna,

“Ki sha kuruminki Inna, Qanwata zata baki mamaki, in ta kawo miji sai kin kalla kin sake kallo”

Cike da jin dadi Inna ta amsa,

“To Allah ya sa Binta, Allah ya sa kuma a fito mana da shi da wuri.”

“In sha Allah Inna.”

Binta ta sake amsawa.

Nabila dai na tsaye tana jin su babu abinda ke fuskarta sai murmushi, sai daga bisani ta ce cikin zolaya,

“Anti Binta kurumin da Inna kawai zata sha bai wuce na shirya mu mutu tare ba, tana mutuwa zan kwanta gefenta in dafe numfashi”

Duk suka yi dariya sannan suka tafi dakin Nabila wadda tuni ta binne dukkan abin da ya faru da siyasar cewa Binta ba ta gansu ba.

“Anti ziyarar ba-zata haka? Amma wallahi na yi farin ciki.”

Haka ta fada wa Binta lokacin da ta ke zuba mata lemo.

Binta ta karbi lemon kamar ta rusa kukan da ta ke hadiyewa saboda mugun rainin hankalin da Nabila ta zo mata da shi, maimakon ta sha lemon kamar yadda Nabila ta so, kawai sai ta dire tambulan din ta dubi Nabila wadda ta zauna akan kujera ta rungume filo.

Binta ta qura mata ido cikin qwallar da ta qara tsattsafo wa idon.

“Na yi kaicon ranar yau Nabila, na yi fatan da ma kafin ta zo Allah ya dauki raina…

Nabila ta girgiza da jin kalaman Binta, amma a fuska kawai, don ta yi hasashen jin wadanda suka fi su.

Jiki a sanyaye ta sake kallon Binta, kuma ta yi fuska ta ce mata.

“Me ya faru Anti?”

Binta ta daga mata hannu, cikin karkarwar murya ta ce.

“Ki bari haka Nabila, kar ki ci gaba da raina min hankali, don ban cancanci hakan ba a gurinki.”

Sai kawai Nabila ta yi kasaqe tana kallonta cikin rashin zabin abin fada, sai can ta kawar da kai ta ce.

“Ni ban gane nufinki ba Anti, don Allah me na yi miki na rainin hankali?”

Binta ta miqe cikin kuka ta zo har gaban Nabila ta durqushe ta dafa gwiwoyinta ta dubi cikin idonta ta ce.

“Namiji ya hada mu ko Nabila? Kin zabi ki ci gaba da wawantar da ni? Bari na taqaice wasa da hankalina da ki ke, na ganki tare da Mujahid, kuma ko me ye a tsakaninku bai boyu a idona ba.”

Nabila ta yi qasa da kai cikin alamun muzanta, damuwoyi biyu na kawo mata duka ta ko’ina, Mujahid da Binta, sai zuciyarta ta rabe gida biyu, kowanne bangare tana jin shi ne dan gida a duniyarta, saboda haka maganganunsu biyu suka dinga yawo a kanta.

“…Amma duk abin da ki ka zaba ki yi, wallahi ina da tabbacin a kanki ba za ki taba yin abin da zai cutar da ni ba”. In ji Mujahid ke nan.

“Namiji ya hada mu ko Nabila… bari na taqaice miki wasa da hankalina da ki ke, na ganki tare da Mujahid, kuma ko me ye a tsakaninku bai faku gare ni ba”.

Wadannan maganganun nasu ne suka dinga yawo a kwanyarta, suna nuna wa juna fin qarfi har a qarshe tasirin so ya sanya na Mujahid ya yi tasiri akan na Binta, ta zabi cika umarninsa da muradinsa ko da kuwa ita za ta kwana ciki.

Sai ta qara yin qasa da kai tana qiqqifta ido alamun jin nauyi da kunya.

Abin da kuma ya razana Binta ke nan, ta dakatar da dukkan rikicin da ta ke ciki, cikin zaro iddo da neman dauke numfashi ta dago kan Nabila suka dubi juna.

“Nabila da gaske Mujahid sonki ya ke?”

Nabila ta ci gaba da kallon Binta a sanyaye kuma a tsorace, cikin in-ina ta kwaso jawabi,

“Ki yi… haquri… Anti Binta… wallahi ba laifina ba ne…. kin ga dai shi ya kawo kansa…”

Binta ta saki habar Nabila ta miqe tsaye dafe da kai ta fara dan tattaki tana ambaton.

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.”

A rikice Nabila ta miqe ita ma ta sha gabanta.

“Ki yi haquri Anti, don Allah ki zauna ki saurare ni.”

Binta ta dinga kada kai kamar qadangaruwa ta sake tsayar da kallonta a kan Nabila cikin yanayi na shanye damuwa.

“To fada min da me ki ke amsa masa? Kin amince da shi?”

Da sauri Nabila ta amsa.

“Ban ce masa komai ba muka yi sallama Anti.”

“Au yau ya fara zuwa?”

Ita ma Binta ta tambaya cikin sauri da alamun zaquwa.

Nabila ta hadiye wani yawu muqut kamar gaske, tana kada kai ta ce.

“Eh wallahi.”

Nan take wani irin tunani ya shigi Binta ta hau zargin ko abin da ya faru jiya ne ya sanya Mujahid janyewa har ya dawo wa Nabila? Wannan zargin ya dan sanyaya ranta, sai dai ta ina za ta tabbatar da gaskiyancinsa?

Cikin wani dokin ta dubi Nabila ta ce.

“Da wacce sigar ya sanar da ke yana sonki?”

Nabila ta dan yi saroro.

“Kamar ya ya Anti?”

Binta ta ja hannun Nabila suka koma kan kujera suka zauna, sannan ta ce mata.

“Ya fada miki wata magana a kaina ne?”

Nabila ta dan yi dum! A hankali kuma sai ta girgiza kai, amma ta yi qoqari ta yi magana ta kasa.

“To me ya ce miki?”

Binta ta sake tambaya cikin zaquwa amma daga can qasan zuciyarta wata muguwar fargaba na halittar kanta, don alamun da Nabila ke nunawa shi ne, za ta iya goya wa Mujahid baya.

Ta jima tana jiran cewar Nabila sannan ta tanka ta cikin in-ina da rashin karsashi.

“Ba zan iya tunawa ba Anti… ki yi haquri.”

“Ba za ki iya tunawa ba?”

Binta ta maimaita cikin mamaki da takaici.

Nabila ta kada kai kai tana kallo qasa.

Binta ta shaqi wani daskararren numfashi, Ita ma ta kawar da kai cikin rarrauniyar murya ta ce.

“Ba za ki iya tunawa ba ko kuma ba za ki iya tona asirin munafiki irin Mujahid ba?”

Da sauri Nabila ta dago kai ta kalle ta a razane bakinta na rawa, amma kafin ta yi magana Binta ta tare ta cikin alamun fushi.

“Ni na tambaye ki ne domin in gane cewa ko Mujahid ya janye son da ya ke min ne, ya miqo miki, in hakan ta samu zan fi kowa murna amma zan fi kowa baqin ciki idan na tarar tare zai hada mu ya so, wannan maguzanci ne da jinsa kawai zai iya sanya amai.”

Da Nabila na da damar qalubale za ta iya tuhumar Antin nata da cewa,

“Sai ka ce mun fito ciki daya ni da ke?”

Sai dai a daidai wannan gabar kowanne irin qalubalenta zai iya zama yakushi a gurin Antin, don haka ta ja bakinta ta kulle, sannan ta shiga saurare.

Binta da ta riga ta fara daukar zafi ta ci gaba da magana.

“Abu na qarshe da zan iya tambayarki shi ne, wanne matsayi za ki iya zabar min idan daga baya muka gane cewa, Mujahid mu biyu ya hada ya ke so?”

Nabila ta sha dogon tunani, kafin ta iya amsa wannan tambayar.

“Ni ba ni da ko wanne irin zabi Anti, na san dai ni mai matuqar biyayya ce a gare ki.”

Ba haka Binta ta so amsar nan ba, amma ta ji matuqar raunin ci gaba da qorafi, ita kadai da fushinta suka taru suka dinga dambe har a qarshe ta yi nasara akansa.

Ta dubi Nabila cikin yanayin murmushin yaqe ta ce.

“Na gode da sauraron da ki ka yi min.”

Ba tare da ta jira cewar Nabila ba ta miqe cikin alamun tafiya.

Nabila ma ta miqe da sauri fuskarta a muzance tamkar mai shirin kecewa da kuka.

“Anti, kar ki bari namiji ya shiga tsakaninmu kamar yadda ki ka fada, ni dai roqona gare ki ki tuna qaunata da biyayyata gare ki ta baya…”

Binta ta rungumo Nabila lokacin da wani kangararren kuka ya subuce mata.

“Kar ki damu Nabila, za ki ji ni bayan na gama bincike, zo ki raka ni na tafi”.

*****

Yaks guda ya ke tamkar yana shirin tashi sama a state road bayan ya baro gidansu Nabila, ba ya hango ko qurar Mujahid, amma yana saka ran idan ya qara himma zai iya tarar da shi su yi uwa kuturwa kaka mayya ko da a tsakiyar titi ne.

Ya gama himmar gudunsa da qoqarin overtaking din motocin da ya ke riska a gabansa, amma bai yi katarin cin karo da Mujahid ba,har ya dangane ga gidan su Binta wanda da isarsa ya ci karo da motar Mujahid din a fake.

Cikin tsananin zafin kansa ya ke tamkar shi ne ashana, saboda haka a fusacensa bai zame ko’ina ba sai dakin Mujahid.

Ya same shi tsaye a falo yana kaiwa da komowa hannunsa riqe da kofin shayi yana kurba a sannu, yayin da fuskarsa ke nuna damuwa da cikawa kai nazari.

Babu sallama Yaks ya banka masa qofa, ya juyo da fuskar mamakin tuhumar wane ne mai wannan danyen kan? Yana ganin Yaks sai ya yi matuqar daure fuska tamkar ya ga mala’ikan daukar rai. Ya dauke kai lokaci guda yana ci gaba da safa da marwarsa cikin kurbar shayinsa fuskarsa a daure.

Wannnan yanayin da ya ganshi ciki ya yi mugun kwara wa zafinsa ruwan sanyi, don tunda ya ke bai san gizagon Mujahid ba sai fara’arsa da murmushinsa, saboda haka fuskarsa ta yau na nuna ko wace irin wuta ma za ta iya tashi daga qwallon kansa.Da ya ke ba qurmus zafinsa ya mutu ba, sai ya nemi kujera cikin gadara yana yi wa Mujahid kallon tara ahu ya zauna, ya dinga huci shi kadai kafin ya sauke da cewa.

“Gaskiya girma ya fadi, wai raqumi da shanye ruwan ‘yan tsaki.”

Ya yi maganar ne da nufin tunzuro wa da Mujahid fushinsa a haka, maimaikon haka sai ya ga ya juyo ya dube shi, shi ma cikn yanayi na rainin hankali ya dage gira ya ce masa,

“Ko?”

Yaks ya debo hayaniya yana so ya dire ta.

“To me ye in ba haka ba, in da kalmar da ta fi haka muni na rantse da Allah ka shirya yau zan fada maka ita.”
Mujahid ya dakatar da shi da hannu cikin bacin rai.

“Kafin ka fada ina son tuna maka wani abu guda.”

Yaks ya qara man zafin ransa, cikin hantara ya ce.

“Fadi mana, ai kunne ke ji.”

Mujahid ya qarasa kurbe shayinsa ya ajiye kofin kan tebur ya fuskanci Yaks sosai.

“Duk wani abu da ka ke jinshi zai zuga ka ka yi min tsageranci ni ma fa ina da shi, idan tashen balaga ka ke ji a ganiyarsa na ke, In zafin kai ka ke ji, ni bakin wuta ma haka ya gan ni. In gabunta ka ke ji don kana dan fari ni ma shi ne. In taqamarka jan fada a fayau ni fadan wani na ke shiga a biya ni… Kai Yaks duk iskancin da ka ke ji babu wanda ban iya ba, qila ba ka san na iya ba ne saboda amfaninsa bai zo na gwada ka gani ba, amma idan ka matsa qila a kanka na nuna samfur…”

Ya isa kujera ya zauna cikin murza yatsu yana ce masa,

“Uhum! Duk abin da ka zo da shi sauke shi ina sauraronka.”

Ran Yaks ya yi mugun baci, amma zahirin magana ya yi mugun tsorata, son Nabila ne kawai ya ba shi qarfin gwiwar buga teburi yana jan ido.

“Da ma kai dan iska ne…?”

Nan da nan Mujahid ya dakatar da shi da hannu cikin daure fuska.

“Haba dai, ai ni iskar ne gabadaya ke nan ni ubanka ne.”

Sai ga Yaks tsaye ya miqe yana fisge-fisge.

“Ni ka ke zagi?”

Nan ma Mujahid ya tare shi cikin halin ko’inkula.

“Laifi ne don na fara zaginka kafin ka zage ni? Share maka  hanya na yi don ka gane idan ka zo da kwandon ashariya ina da buhun  zubawa.

Yaks ya fara rasa ta cewa, ga baqin ciki ga tura haushi, kuma a dake ya san ba zai iya dukan Mujahid ba, sannan yadda ya ke nuna wannan danyen kan shi ma, maganinsa kawai in an ganshi a titi a bi ta kansa da mota, a kashe banza, qarqari ya biya diyya ko daurin wani lokaci mai qa’ida, idan ya ce bisa kuskure komai ya faru.

Tunda wannan gabar tana neman abin cewa, bai kasa nemo ta ba.

“Ni ban zo don mu yi maganganu kamar wasu mata ba, na zo ne don in tsine maka a matsayinka na maciyin amana, ka ce min za ka taimake ni shawo kan Nabila ashe neman kusanci ka ke da ita don ka nuna mata taka maitar, kuma saboda kai dan Akuya ne ka hada da Binta kana so…”

Mujahid ya yi murmushin tura haushi ya tare shi.

“Ka ce ba ka zo min qananan maganganu kamar mace ba, amma ban ganka da wuqaqen da za ka yanke ni kamar namiji ba, illa qananan maganganun da ka ke zuba min.”

Ya miqe tsaye cikin fushi yana nuna masa qofa.

“Kai ji nan, ba na son iskancin banza, zo ka fita ka je ka yi duk abin da za ka yi, na so Nabila, na so Binta idan ka isa ka zo ka dakatar da ni, ko kuma ka zama namiji in ganka da gariyon da za ka tsorata ni.”

Tuni Yaks ya miqe cikin fushi da matsananciyar fusata.

“Ai da ma tafiyar zan yi… zan yi maka duk abin da ka nema, na rantse da Allah ba za ka sami cikar burinka ba, idan ba ka yi wasa ba ni ne ajalinka… In ba haka ba ka sauya min suna.”

Mujahid ya tuntsire da dariyar tura takaici,

“Ai sunanka ya dace da kai Yaks, ko ba ka sami damar kashe ni ba ni na sami damar kashe ka da yakubunka za a binne ka.”

Yaks bai iya sake ce masa komai ba illa ficewa a fusace ya banko qofar tamkar zai balle ta.

Mujahid ya fada kujera a matuqar gajiye tamkar wanda ya yi tseren gudu, ba fatar jikinsa kadai ke zufa ba, zuciyarsa ma ya san tana yi. Abin ya zo masa a ba-zata, ashe qalubalen da ke tattare da son da ya ke wa Binta ya zarce duk yadda ya zace shi? Ta bayan gida Binta za ta billo masa ta hada shi  fada da mutane?

Ya yi ta yi wa kansa tambaya ya kasa amsawa domin amsar daya ke so ita ce wadda za ta samar masa Binta kawai ba wai wadda za ta sasanta shi da mutanen da Binta ke shirin hada shi fada da su ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 6

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 14Rigar Siliki 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×