Alhaji Ibrahim karimin mutum ne wanda ya iya mu’amala da mutane, kamar yadda ya iya tarairayar mace da nuna mata soyayya, macen ma irin Binta wadda idan sonta ya shirya fada wa zuciya ba ya yi mata ta wasa.
Cikin qanqanin lokaci ya sami fada a zuciyar Binta, ko ba ta ji sonsa dari bisa dari ba, ta ji dari bisa darin babu laifi idan ta aure shi. In ba ta sami komai da komai da ta ke so a mijin aure ba, to tabbas ba shi da komai na abin da ta ke qi, don haka kai tsaye ta sada shi da iyayenta a matsayin wanda za ta aura har suka tsayar da ranar da zai turo magabatansa.
Mujahid na da labarin komai, har ma da shi ake tattauna lamuran auren, a wajen Alhaji Ibrahim kuma shi ne babban wa, wanda ya ke ganin mutunci kuma ya ke zagewar qarfinsa don ganin ya sami auren masoyiyarsa Binta.
Binta dai na kallonsu har yanzu hankalinta bai kwanta da wannan sauyin ba don haka har yanzu ba ta saki jiki da shi ba.
Nabila ta yi nisa cikin jarrabawa don haka Mujahid ya rasa abokin tattauna damuwarsa ko da kuwa jaje kawai za a taya shi da shi.
Akwai shirin da ya yi don dawo da masoyiyarsa hanunsa, ba shi da tabbacin in nasara dari bisa dari duk da yarda da kan da ya yi wa kansa, qila shi ya sa ya ke cikin kishin ruwan ko mai qarfafa masa gwiwa ne da ce masa zai yi nasara, ya san kuma duk duniya ba shi da mai yi masa wannan sai Nabila.
Ana saura kwana biyu a kawo kudin Binta da sanyin safiya yana shirin fita aiki cikin kasala da saqe-saqen zuci kan yadda zai shirya gadar zarensa.
Wayarsa ta dinga kadawa yana share ta, saboda zaton ba za ta amfane shi ba, har dai daga qarshe ya dauko wayar don ya fahimci mai kiran saura kadan a rada masa sunan dan’anace.
Da sauri ya daga wayar lokacin da ya fahinci Nabila ce mai kiran.
Cikin doki ba tare da ko gaisuwa ba ya ce.
“Nabila ya garin?”
Muryarta ba ta boye cikin damuwa ta ke ba, ita ma a gaggauce ta ce masa.
“Lafiya qalau Yaya Mujahid.”
Cikin wani hanzarin ya sake cewa,
“Yau za ku yi Geography da English ko? Ina miki fatan sa’a da nasara.”
Ta matsa wa kanta fara’a tana cewa.
“Na gode.”
Ta dan nisa sannan ta dora.
“Jiya na yi waya da Anti Binta, ta kira ni takanas don ta yi min fatan nasara, sannan ta fada min cewa jibi za a kawo kudin aurenta, wai har ma da sadaki, haka ne?”
Ya qoqarta da qyar ya yi dariyar qarfin hali, sannan ya amsa mata.
“Haka ne, Alhaji Ibrahim za ta aura, ai kin sanshi ko?”
Cike da damuwa Nabila ta ce.
“Ni ban wani san shi ba, amma ya ya aka yi haka? Ka san cewa ba za ka iya kokawar ba ka sanya ni domin kai na sadaukar da lokacina da farin cikina na ke sauraron Yaks? Kawai sai na ji ka bar wa wani abin da ka ke so?”
Farin ciki kawai Mujahid ke shaqa Nabila na sababi, da ma abin da ya yi maraici kenan kwanan nan, wato qarfafa gwiwa da nuna masa zai yi nasara.
Sai da ya bar ta ta gama nuna fushinta sannan ya tare ta cikin tattausar murya,
“Haba Nabila, kwantar da hankalinki mana.”
Ta yi shiru kawai tana sauraronsa, gaskiya ranta ba qaramin baci ya yi ba, musamman saboda siyasar da suka qullo na danganta ta da sauraron Yaks tare da amsa wayarsa, kusan kullum sai ya zo gidansu, waya kuwa sai ya kira ta sau goma a rana ba don ma ta yi masa birki a kwanan nan ba bayan ta fahimci, in dai ta ci gaba da ganin fuskar Yaks tare da sauraron banzayen zantukansa, to babu abin da zai hana ta faduwa a jarrabawa, don jaruntarta ba ta kai yadda zuciyarta za ta iya dauke azabar so ta zo kuma ta dau na azabar qi sannan ta ci gaba da walwala ba.
Shirun ya ba wa Mujahid damar ci gaba da lallashinta.
“Ban da abin Nabila, jibi za a daura auren? ko jibi za a daura ai na san kin san mai rai ba ya rasa rabo.”
Ta qoqarta ta yi ‘yar dariya sannan ta fadi gaskiyar zuciyarta.
“Duk fafutukar da nake taya ka Yaya Mujahid ina taya ka ne kafin wani neman a kan Binta ya kankama, don dukkanmu ai ba za mu saba wa Manzon Allah (S.A.W) ba, na nema cikin nema.”
Ya dan ja numfashi sannan ya tanka.
“Fatana ke nan, saboda haka ki ba ni nan da jibi ki ga abin da zan yi kin ji? ki kwantar da hankalinki.”
Ba ta gama saduda sosai ba, amma a murya ta amsa masa da qarfin gwiwarta.
“To ina zuba ido, Allah ya kai mu jibin ya kuma tabbatar mana da alkhairi.”
Ya dan jima cikin shiru alamun tunani sannan ya nisa.
“Abin da na ke so da ke shi ne, don Allah duk runtsi kar ki bar Yaks ya turo neman aurenki.”
Nishi kawai ta yi.
“Hmn”
Cikin zuciyarta tana raya son kansa ya yi yawa ai, kai na ke so ba ka aure ni ba, kuma so ka ke ka zaba min wanda zan aura?”
Kamar ya san abin da ta ke rayawa kuwa ya tabbatar mata.
“Ni zan zabo miki miji salihi irinki, wanda zai kula da ke.”
Jin tana qoqarin rafshewa da kuka ta bayar da kai ya sanya ta fara yunqurin yi masa sallama.
Bai fahinci komai ba ya ce mata.
“Ki dan taba karatu kafin lokaci ya qure Nabila, na san na hargitsa miki kwanya.”
Da sauri ta riga shi sauke wayar babu ko sai anjima sai faman huci ta ke, amma ita kanta ta kasa gane abin da ya sanya ta hucin.
Tana ta laluben amsa, ga mamakinta sai ga shi ya sake kiranta a waya, da qyar ta daga, shi ma don tana zumudin ta ji abin da zai fada mata ne.
Ta dinga kasa kunne tana jiran cewarsa bayan ta daga wayar, ta ce,
“Hello”
Ba don tana jiyo sautin numfashinsa ba ma za ta zaci ko ba ya jinta, sai da ta sake cewa,
“Hello”
Sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tanka.
“Ba mu yi sallama ba ki ka kashe min waya Nabila”
Ya fada muryarsa a matuqar tausashe tamkar yana magana da Binta wadda ya ke matuqar so.
Da qyar Nabila ta mallaki kanta wajen tattaro wani marowacin yawu don ta sami abin juyawa a baki ya ba ta sauti, muryar tata a dakushe ta ce,
“Yi haquri Yaya Mujahid, na zaci mun gama ne.”
Ya sake jimawa cikin nazari kana ya amsa mata a tausashe.
“Duk wani abu mai kama da sabani ko wanne iri ne ko kuma adawa ba na maraba da shi a tsakaninmu Nabila, tsatsa a ranki kowanne iri ne zai iya taba raina fiye da komai a filin rayuwata yanzu, ina lura kamar akwai wani abu a tare da ke, don Allah ki tuna ni amininki ne ki sanar da ni.”
Wani qaqqarfan kuka ya yunquro wa Nabila, amma ta sanya qarfi ta tare shi ta hanyar hanzari ta ce.
“Zan makara Yaya Mujahid, za mu yi waya yau ko gobe, ko kuma ka jira na gama jarrabawa.”
Kai tsaye ya amsa mata.
“Na jira Nabila”
Ya yi hakan ne don shi ma gabansa faduwa ya ke kar ta ce sonsa ta ke, alhalin siyasa ta sanya shi siye ta da dadin baki.
Ita kuwa lokacin ta fada kan kujera, ba kanta ba, hatta dakin juya mata ya ke saboda rudewar da kwanyarta ta yi wajen lalubo abin da Mujahid ke nufi, sonta ya ke? Irin kalaman nasa daga masoyi kawai suke fitowa.
Ita dai ta banu, Mujahid ya sami zuciyarta da numfashinta yana ta wasa da su.
*****
Ranar juma’a misalin qarfe daya saura, Mujahid ya dawo gida don shirin tafiya masallaci, kwatsam ya ci karo da Binta da Yaks na fitowa da alama fita za su yi.
Da wani dunqulen kishi ya taso masa a maqogwaro kawai sai ya fashe ya zamar masa basirar da za ta zame masa tarkon cafke auren da masoyiyarsa ke shirin qullawa.
Ya wadata fuskarsa da fushi iyakar fushi, ya tunkare su gadan-gadan tamkar yana zuwa hadiye su zai yi dukkansu.
Duk sun sha jinin jikinsu da razana, musamman Yaks wanda yanzu ba ya tare da fushi, cikin shauqi ma ya ke domin yau Nabila ta amince masa, ya leqa ya ganta, kuma tuni Mujahid ya rage ba shi haushi saboda ba ya ma ganin alamun son Nabila a tare da shi.
“Ka nutsu Yaks, wannan gayen da rainin hankali zai zo mana, qila in ya zo ya kira ni karuwar da ya saba, ina son kar in guji sunan a yanzu.”
Binta dai ita ta ke cike da fushin sannan kuma tsoronta da razanarta ba su kai na Yaks ba ta fada.
Yaks bai iya tankawa ba don Mujahid ya sha gabansu duk ya tare hanyar, kaifafan idonsa akan Binta ya ci mur ya ce,
“Wai ke ina ki ke son kai ni ne?”
Ta yi masa kallon goma ahu ta watsar gami da tsaki.
“Ya wuce inda ya fi dacewa da kai, wato gwalalo.”
Mujahid ya juyo da mugun kallonsa kan Yaks, sannan ya juya ya dube ta ya ce.
“Na zaci tunda kina neman yin miji wannan za ki kai gwalalo?”
Yana nuna mata Yaks fuska a bace.
Ta yi murmushin tura haushi da basarwa, tana murguda baki ta ce.
“Ka manta ne kawai, ai kayan nama ba ya kashe kura”
Fuskar Mujahid ta qara cika da bacin rai, ya zare mata ido ya ce.
“Kar ki manta gobe fa har sadakinki ki ka nemi a kawo, na yi tsammanin duk jahilcinki kin san haqqin aure?”
Kalmar jahilcin ta qara tunzurata a qufule ta tari numfashinsa.
“Ni ba jahilar ba ce kenan, ai ko wanne namiji naman saniya ne a wajena, in ka cire kai da na mayar naman alade”
Ba qaramin dadi wannan amsar tata ta yi wa Mujahid ba, amma ya boye da murmushin nuna takaici, ya ce mata.
“Ni kuma ban cire ran ni kadai za ki mallaka a matsayin halak ba”Wannan karon Yaks ya yi qarfin halin shiga sa’in’sar.
“Ya za ka ce haka? Kai da bakinka fa ka ce gobe za a kawo sadakinta…”
Mujahid ya dakatar da shi da hannu cikin bata fuska.
“Ka ga Malam dakata min! ban zo kanka ba.”
Binta ta yi qoqarin ta tanka, amma haushi ya hana ta, sai qwafa ta yi ta hadiye.
Mujahid ya nisance su kadan yana murza hannu alamun barazana, ya nuna sashen da fararen kujeru ke zaune qarqashin bishiyar umbrella daga can saqo, matasan gidan na yawan hutawa a wajen, musamman lokacin yammaci.
“Jiya kun zauna a can kun kusa fasa min zuciya da haushi, don iskanci har da tafawa da qoqarin keta dokar Allah. Na rantse da Allah yau idan aka maimaita za a hadu da fushina.”
Bai saurare su ba ya wuce ya bar gurin.
An jima kafin a sami mai tankawa, Binta tsabar haushi ne ya hana ta magana, amma Yaks dariya ce ta cika masa ciki, don haka shi ya riga samo abin cewa.
“Wannan gayen anya bai sami tabuwar kwanya ba?”
Binta ta hadiye wani qaton haushi cikin gyada kai ta amsa.
“Mahaukaci hauka ake nuna masa sai ya zama mai hankali, don girman Allah ka ara min ranar yau ka janye zuwa wajen Nabila mu kashe wannan banzan da takaici mu huta.”
Yaks ya dan bata fuska.
“Na dade ban ga Nabila ba Binta, don Allah ki share shi.”
A fusace ta ce.
“Wallahi ba za a share shi ba, sai ka yi min wannan alfarmar dole, kar ka manta daga gobe kwantaraginka zai qare, ba abin da zai rage sai na taya ka yaqin neman Nabila.”
Maganarta ta qarshe wato samo masa Nabila ita ta qarfafa masa gwiwa ya biye wa Binta.
Ta juya cikin gida tana ce masa.
“Ka je kawai amma qarfe hudu na yamma lallai ka tabbatar ka dauko kwalabo ka zo.”
Yana dariya ya wuce yana cewa.
“Kamar da qasa”
Mujahid na saukowa masallaci bai zame ko’ina ba sai ofishin Alhaji Ibrahim ya nemi iso ya shiga.