Alhaji Ibrahim dawowarsa ke nan daga masallaci ya karbi Mujahid da murna da mamaki.
“Barista ai na zaci karbar adireshina da sunan wataran za a kawo min ziyara duk bogi ne.”
Bayan Mujahid ya sauke kofin ruwan da aka tare shi da shi ya amsa cikin dariya.
“Kai haba surukina, ai girman nawa ba a suna da fatar jiki ba ne kadai, ko ta ina muna kamantawa.”
Duk suka kacame da dariya.
Cikin tsananin farin ciki Alhaji Ibrahim ya ce.
“Ina murna da samun suruki nagari irinka.”
Cikin jin dadin nasara Mujahid ya amsa masa,
“Na fi ka. . .
I love reading your books because it inspire me so much I learned many things from your book God bless you all