Karo na sama da ashirin Alhaji ya shiga falon Hajiya ransa a bace, Hajiyar na tare da Binta ko wannensu fuskarsa babu sukuni.
Alhaji ya tsaya a bakin qofa riqe da labule yana yi wa dukkansu kallon tuhuma.
“Kun ji da kyau kuwa, yau suka ce kuma qarfe goma na safe?”
A ladabce Hajiya ta amsa,
“Na gaji da amsa wannan tambayar Alhaji, in dai ba so ka ke in maka qarya ba”.
Ya juya ga Binta wadda ke ta faman daddana waya hankalinta ya yi masifar tashi, ba ta san azal din da ke shirin afka mata ba. . .