LITTAFI NA UKU
An kai Binta da Nabila wani kyakkywan Pribate Hospital da ke kusa da Fadaman madan, babu bata lokaci aka basu daki daya me gadaje biyu, sannan aka koma dakon zuwan likita, wanda suka sami labarin ya fita daga asibitin.
Daukacin mutanen gidan hankalinsu yana tashe, hatta Hajiya wadda farkon faruwar abin ta so nuna babu komai, Binta ta yi sumanta ta gama aure ne an riga an daura, yanzu ta shiga rudu qwarai, don laluben me ya shigo da Nabila gigitar an yi wa Binta auren dole? Sannan in ta dubi Mujahid ma tana jin numfashinta na. . .