A daren ya kira Nabila, sai ya ji ta daga wayar tana kuka, karo na farko da ya ji zuciyarsa ta cunkushe tana son dauko sabon tunani akan wannan salihar yarinyar.
Duk da ya san abinda ke akwai amma sai ya binne kamar bai sani ba, cikin kulawa ya ce mata,
“Nabila me ya faru kike kuka?”
Muryarta ta qara rauni,
‘Don Allah Yaya Muajhid ka janye zumuncin da ke tsakanina da kai, ba wai ka datse shi ba, ka rage masa qarfi nake nufi”
Kai tsaye ya ce mata,
“Don dukkanmu Binta muke wa numfashi ko? Sai abinda take. . .