Skip to content
Part 34 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Sai da ta ji wani nauyi ya daki qirjinta, ta fara jin kamar ba ta kyauta ba, don zai yi zaton don ta tozarta Iyayensa ta ce ba zata ba, alhalin ita da shi ta ke yaqi ba da iyayensa ba, har yanzu tana jin qaunar iyayensa a matsayin nata kamar yadda take ji tuntuni.

Ta koma daki cikin sanyin gwiwa ta zube a falo ta rafka tagumi, ta yi kuka ta share har tsawon lokacin da mujahid ya shirya ya fito sama da awa daya da rabi.

Ta miqe tsaye da sauri lokacin da ta ji sautin takun sakkowarsa daga Bene ta fito suka hadu a tsakar gidan, kafin ta yi maganar da ta fito da ita shi ya riga ta,

“Wataqila sai gobe zan dawo, in kin ji shiru kar ki damu”.

Ta ji wani shegen tsoro ya kawo mata sura ta shiga kallon saman benensa tana sake bin gidan da kallo, ita kadai zata kwana a wannan wawaken gida? Kenan zata fara kadaicin dare don ta ceto kanta daga na rana tana fita aiki? In ba haka ba yaushe Mujahid yake zuwa boto ya kwana musamman gashi yau lahadi gobe litinin?

Bata iya boye damuwarta a fuska ba, amma maganarta ta boye, inda ta ce,

“To ka gaishe su, ka cewa Gwaggo ta manta da ni ne, sau biyu ina samun labarin zuwanta amma ba zata zo ta gan ni ko ta sanya a yi min waya ni na zo na gan ta ba”.

Mujahid yayi fuska,

“In na ce miki zan fada mata na yi miki qarya”.

Binta ta ji haushi, ta kebe baki,

“Ka tsayar min da gaskiya in zaka kwana ni tsoro nake ji zan je gida na bkwana”.

Ya kada kai ya wuce,

“In dai gidan zaki je ba wani wajen ba kawai ki yi tafiyarki”.

Ta zaro ido da alamun tambayar, ‘me kake nufi?’ sai dai bai ma san tana yi ba don har ya kai qofa, ya fice yar qaramar harabar da a nan yake ajiye motarsa, ta yi kamar ta bishi ta tuhume shi amma tana tuno yadda wani Niga ya baje a gabansa ya wanke ta da hoto sai ta ji ai duk wani abin tuhuma bayanta zai bi, dole ta yi baya tana hawaye. Lokacin daya kuma ta fara tunanin matakin da zata bi ta kawo qarshen wannan shegen auren da ba a fare shi ba sai dan a ga bayanta.

Ta hana kanta tafiya ko ina don kar ya zo yayi mata wani zargin, amma ta wuni tana addu’ar Allah ya sa ya fasa kwana, burika kala-kala ta ci su na zuwa ta roqe shi ita lallai in dai da gaske yana sonta to ya sake ta shi ne kadai farin cikinta, ya je can ya auri masoyiyarsa Nabila da wani ke shirin yi masa qwace.

Bayan sallar Isha ta ji tsayuwar mota a qofar gidanta, amma kuma aka dinga jero hon. Nan ta fara shakkun to waye haka? Ta san dai ba Mujahid ba ne, can kuma sai ga bugun qofa saboda haka da hanzarinta ta fito ta bude Qofar, sai ta ci karo da wani yaro, yana ganinta ya bada saqo,

“Wani ne ya ce na yo masa sallama da Binta?”

Ta shiga mamaki da shakkun ko wani dan’uwanta ne? amma sai ta ce,

“Je ka ce waye”.

Yaron ya amsa,

“Wai ya ce Muktar ne.”

Ta shiga duhu, ta dinga maimaita sunan tana son tuno inda suke da Muktar a danginsu amma ta kasa tunawa, yaron da ya ga ta sa kanta a duhu sai ya shiga suffanta mata shi, nan da nan sai ga kamannin mai daukanta hoto kuma mai aiko mata da katin gaisuwa ya bayyana, nan da nan hankalinta ya tashi, jikinta na rawa ta cewa yaron,

“Maza je ka ce masa gidan nan babu Binta”.

Jikin yaron a sanyaye ya ce,

“Wallahi na fada masa cewa Binta nan gidan matar aure ce, ya ce min ya sani, kodayake ai dan giya ne, yana ta daga kwalba yana korawa…”

Binta ta ambaci “Inna lilllahi wa inna ilaihi raji’un” sannan ta shiga tura yaron,

“To yi tafiyarka kar ka sake dawowa.”

Cikin barin jiki ta rufe qofa ta koma cikin gida, ta rufe falo nan ma sai da ta qule dakin bacci tamkar Muktar zai shigo ya damqe ta.

Ba ta san tsawon lokacin da ta bata tana kwance a gado tana kuka ba, babu wanda take dorawa alhakin wannan masifun da ke addabarta sai Mujahid, shi ya janyo mata, da ya bar ta je ta auri wanda ta ke so duk da ba ta yi ma abinda zata ja hankalin ‘yan giya irin Muktar ba.

Sama-sama ta jiyo ana buga mata qofar daki, sai ta qara razana, kafin ta shiga hankalinta ta raya cewa Mujahid ne ya dawo tunda shi ne mai mabudin gidan.

Ta taso ta zo ta bude qofar sai gashi tsaye hankali a tashe yana biyo ta da kallon tuhuma, baki na rawa tana son yi masa sannu da hanya ya tari numfashinta rai a bace,

“Kin san kina da baqo a waje?”

Hankalinta na neman barin jikinta tana qura masa ido, shi ma qura mata yake fuska babu annuri, sai ga hawaye ya fara biyo kuncinta, ta dinga gyada kai tana kallonsa kafin ta qwato abin cewa,

“Eh na sani, ai ya aiko.”

Duk da Mujahid ya san kwanan zancen sai da ya ji kayan cikinsa sun juya, ya maze ya kada kai cikin fishi yana shirin juyawa,

“Ai sai ki je ki ji da shi ko?”.

Ta fara kuka sannan ta sha gabansa,

‘Kai ne zaka je ka ji da shi, ai kai ka janyo min shi, saboda haka kai zaka je ka ji da shi.”

Zai yi magana ta sake tare shi tana ta cin uban kuka,

“Sai ka je ka fada masa cewa ina da aure, ka ce masa kai ne mijin da qaddara ta aura min ba don ina so ba, ina kwalliya in fita ne don in baka haushi in sanya ka tsane ni, ba ina yi dan ‘yan giya irinsa su biyo ni ba.”

Bai tanka ta ba ya lome baki ya kama hanyar qofar gida, tayi tsaye a nan tana cigaba da kuka, har lokacin tana jiyo tashin sautin da baqon nata dan giya ya kwarare unguwa, wannan abin kunyar da me yayi kama.

Ta jiyo tashin mota da raguwar sauti har a hankali ya bace, sai kuma ga Mujahid nan ya shigo gida fuska a bace, ya ma qara bata ran da ya gan ta tana tsaye, da kaya a hannunsa ya doshi store ya shigar ciki sannan ya kuma ficewa ya shigo da wasu, har ya gama zirga-zirgarsa tana tsaye tana kukanta shi kuma yana shanyewa, gaskiyar magana qarfin halinsa ya fara tuqewa, so yake ya rarrashe ta don kukanta yana taba masa rai, amma bala’inta na yi masa birki, ya san yana motsi zata fada masa cewa ba ta qaunarsa, shi da yake qaunarta kuma ba zai iya jure ganinta tana kuka ba.

Ana cikin haka ya sami gaba, don ta gaji da kukan ta yi masa magana da sassaucin murya,

“Wai kai zuciyar qarfe ce da kai da ba zaka saurare ni ba?”

Cikin rashin kulawa ya ce mata,

“Ni na gaji ne, kin san na yi tafiya sannan kaina a toshe yake, kawai ki yi duk abinda kika zaba, ai na fada miki ba na matsawa mutum ya bi Allah, wannan yin Allah ne”.

Ta ci laya,

“Wallahi sai ka saurare ni, in ka gaji ka shigo nan ka zauna”.

Ta nuna masa falonta, sannan ba ta ba shi zabi ba ta wuce, dama ya so hakan, kawai sai ya bi bayanta, amma dan nuna ko in kula sai ya zauna kan kujera tamkar wanda ya zauna kan wuta,

“Ina jin ki.”

Ta nuna shi da yatsa cikin zafin murya,

“Dama ba ka da tausayi yaya Mujahid, dama ba ka da Imani?”.

Kallonta kawai yake, masifa take amma ba shi sha’awa take, mutuniyar kirki da ita qiyayya na sanya ta bin turbar mutanen banza.

Ta cigaba da hayaniya,

‘Ka sake ni mana, ba zan iya zaman aure da kai ba don me zaka cigaba da cutar da ni?”

Ba ta kula ba tuni ya miqe ya kuma tunkare ta, yana zuwa ya jawo ya adana,

“Allah me na yi ka sanya ‘yan giya suka fara biyo min mata, Allah na tuba”

Binta na kici-kicin qwacewa amma ta ji hannun maza, tun bakinta na iya motsi har shi ma ya sami nasa kason don haka ta sallama face hawaye da matsanancin kukan zuci, wai ita ce yau a hannun Yaya Muajhid yake wa abinda ya so, ba ta sonsa, don haka ba ta son abinda yake mata yanzu, amma ba ta da qarfin ta hana.

Sai da Mujahid ya gaji don kansa ya sake ta, amma ya riqo kafadarta yana kallon qwayar idonta sannan nasa qwayar idon na nuna saqonni kala-kala wadanda suka dinga firgita Binta, ya fara yi mata magana cikin taushin harshe da muryar rada, hucinsa na sauka a fuskarta gauraye da kamshin Mintin da ke bakinsa, kodayake har cikin cikinta ma qanshin mintin take ji.

“Ke Imanin ne da ke da kike son raba ni da abinda nake so? ko tausayi ne da ke da za’a kawo min amarya wadda na ke so irinki amma tsawon sama da wata biyu ko farcenta ban taba tabawa ba? In kina maganar qi kanki aka fara auren qiyayya kuma a kwana da macen? Ni an fada miki iyawa ne ba zan yi ba…”

Ta fara qoqarin ture shi tana son komawa kukanta,

“Malam ni maganar saki na yi maka saboda ba na sonka, kar ka kawo min wasu maganganun banza nan wajen…”

Ya sake sanya mata qarfi ya rungume,

“Ai dan in nuna miki maganar sakin da kike batawa kanki lokaci kike, duk abinda na rasa a ke ni na so, in na so ba zaki yi aiki ba bare har ki fita tsirara maza ‘yan iska su dinga biyo ki, in na so ba zaki dafa abinci babu ni ba, in na so dole ki kwana shimfida daya da ni, in na so dole shekara mai zuwa ki haifi dana ko ’yata idan Allah ya bayar, meye zai yi saura a qiyayyar taki, zaki hada ni da ‘ya’yana ki bankawa wuta ne?”

Kawai sai ta sanya kuka gabadaya,

Ya cikata yayi gefe yana kallonta fuskarsa cike da annuri, yana ce mata,

“Ai kawai sai ki kwallawa Hajiya kira kamar yadda kika taba yi a baya”

Ta nuna masa qofar fita,

“Zo ka fita ka ba ni guri.”

Ya sa kai ya doshi dakin da ya fi kusa da shi,

“dakinki kuma ai na shigo kenan Binta, ba ni na biyo ki kamar kare ba, ke kika gayyato ni, ni kuma ba na qin wuce tayi.”

Ya dinga leqa dakunan ya fito daga wannan ya koma wancan, yana shegantaka,

“Allah Sarki dakunan nan gaskiya sun yi maraici, namu ne mu biyu amma ba su san kowa ba sai ke? Na san sun yi tir da baqin halinki da ya hana musu ganina”

Binta da qyar ta ja qafa ta je ta zauna a kujera tana ta faman Hirji, dafe qirjinta kawai ta yi don ta tabbatar da za’a fasa shi ba za’a rasa shi da hayaqin da bakin cikin Mujahid ya tasa ba, ta janyo wa kanta jangwam!

Hannu biyu ta sa ta tallafe haba tana kallonsa yana ta harbin iskarsa, tun tana masa duban takaici har ta koma yi masa na tausayi lokacin da cikin shawagin tunaninta Nabila ta fado mata, ga mai sonsa tsakani da Allah can amma ya zo yana asarar sonsa a inda ba zai sami raddi ba bare riba,

Da hawayenta shabe shabe ta dube shi ta ce,

“Ina yi maka Jaje Yaya Mujahid”.

Yanayinta bai nuna masa wasanta ko  izgilancinta ba, don haka ya tambaye ta,

“Jajen me?”

Tana cigaba da hawayen ta amsa,

“Da ka yi asarar mai sonka kamar Nabila, zaka bar ta da auren wani dan siyasa wanda bai aure ta dan komai ba sai don kyanta, kai ma zaka bige da aurena wadda ban yarda na aure ka don in dore ba, komai zaka yi ya kamata ka dinga tuna wannan”.

Ga mamakinsa sai maganar ba ta aure shi don ta zauna ba ta wani dada shi da qasa ba, amma maganar auren dan siyasa da Nabila ta yi ya tarwatsa damuwarsa, a jigace ya ce,

“Yaushe Nabilan ta yi aure ba ni da labari?”

Cikin gadara da jin alfahari ta amsa masa,

“Tunda da baka aure ta ba ai ko ma yaushe ne zata yi auren, wanda zata aura ba zai cancanta ba, don ba shi ta so aura ba kai ta so , kuma da kake maganar ba ni da imani kai imanin ne da kai? In kana maganar kana sona ba na sonka me yasa Nabila take sonka kake qinta?”

Ya tare ta a raunane,

Don Allah kar ki cika ni da surutu Binta, wai wa Nabila ta aura ko zata aura? In akwai abinda na tsana yanzu a filin duniyar nan yanzu bai wuce na Nabila ta auri wanda bai cancanta ba.”

Tana murmushin qarfin hali,

“Wadannan kalaman naka ba so ba ne ko?”

Shi ma ya girgiza kai,

“Kawai ba qiyayya ba ne irin naki.”

Ta sake wani murmushin,

‘To ka je ka yi tunani kar ka rasa so irin naka”

<< Rigar Siliki 33Rigar Siliki 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×