Skip to content
Part 35 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Ba kamar yadda Binta ta zata ba, Mujahid bai damu da sai sun kwana daki guda ba, ya dai yi ta jan ta da zolaya da hira har suka raba dare suna musun da ba su tsinci komai cikinsa ba sai barin zuciyoyinsu da zargi.

Da safe da ya dawo masallaci bai koma dakin ba Bene ya haye, har lokacin da ta gaji da jiran ya zo ya kai ta aiki ta bishi saman kamar yadda suka saba, ta fara ranqwasar qofar sai ta jiyo alamun yana waya ne, kuma karaf ta ji sunan Nabila, jikinta na karkarwa ta shiga kasa kunne, inda ta jiyo shi yana cewa,

“Haba Nabila, me zai sanya ki zabi wannan mutumin wanda ya kusa haifar ki? Ba don so zai aure ki ba sai don ki zama abinda tunqaho da nuna wa duniya ya auri mai kyau, ni kuma ina da tabbacin ke ba don kudinsa zaki aure shi ba…”

Binta ta tallafo qirjinta mai barazanar tarwatsewa, lokacin da Mujahid yayi shiru, ta fahimci yana sauraron Nabila ne. munafukan mutanen nan son juna suke amma zalinci ba zai bar su su bar ta su rayu tare ba? Sai dai kulle ta su yi ta azabtar da ita da azabarsu? Can ta jiyo Mujahid na cewa,

“Ki ba ni sati daya zuwa biyu, duk ma abinda zan yi zaki gani”

Yana magana ne cikin alamun kyautatawa da rarrashi.

Da sauri Binta ta nufi qasa kanta a hargitse. Ba ta tsawaita tunani ba ta yarda da shawarar da ta zo ranta, tana zuwa hankalinta ta shige ta janyo wayarta ta kira Yaks, ta yi qoqarin daidaita murya suka gaisa, dukkansu babu mai nutsuwa, don lokacin ma Yaks kuka yake, Nabila ta kubuce masa, jiyan nan dangi suka taru a kansa suna ba shi haquri, haqurin da bai ga qwaryar da zai kinkima ya dora a kansa ba.

Yana jin Binta ya fara yi mata surutai,

“Kin gani ko? Kin bata min suna da sharadin zaki samar min Nabila, amma Binta da saninki Nabila ta zabi wani ta bar ni…”

Binta ma ta fara kuka saboda tausayinsa da kuma tata matsalar,

“Ka kasa fahimta cewa yanzu ba ni nake da qarfi akan Nabila ba Mujahid ne, Na rantse maka da Allah da ya sa baki da tuni Nabila ta aure ka, da gaske shi yake son Nabila, bai san cewa ma ta zabi wannan mutumin ba da ba zai bar ta ba, yanzu gashi can ya wargaza zaben da ta yi masa, ka zuba ido ka gani nan da wani dan lokaci zaka ji cewa Mujahid zata aura…”

Kamar koyaushe Yaks ya kasa sarrafa tunaninsa, nan ya dinga cin alwashin sai ya wargaza Mujahid shi ma, Binta kuma dama dalilin kiransa kenan ta ce masa, in dai ya bata hadin kai qaryar Mujahid sai ta qare cikin satin nan, sai ya sake ta kuma sai auren Nabila ya gagare shi.

Nan da nan ya amince mata, suka fara shirinsu nan take, da Yaks ya ji niyyarta sai da ya zaro ido cikin firgici, ya ce,

“Amma kuwa Binta a wannan shirin ke ma zaki kwana ciki”.

Cikin rashin shakku ta tabbatar masa,

“Ba ni da wata damuwa game da yadda duk zan sami rayuwa, in dai ba na cikin ta Mujahid, in zan mutu gwauruwa ban damu ba, ni rayuwa qarqashin auren Mujahid ne matsalar duniyata.”

Cikin jin dadi Yaks ya ce,

“To ki zama cikin shiri, ba mamaki zaki kwanta yau zuwa gobe”.

Cikin azama ta ce,

“Yauwa ina jira.”

Da haka suka kashe wayar.

Ta yi saurin goge hawayenta ta dauko jaka lokacin da ta ji sakkowarsa daga sama ta fita.

Tun kafin ya sakko ya dinga jifanta da murmushi, yana zuwa kuma ya saqalo qugunta sannan ya sumbaci kuncinta,

“Don Allah mu dinga gaisawa mana, yawan gaisuwar ai ya fi yawan fadan”

Binta ta hadiye wani dunqulen takaici, amma ta kasa magana. Ya gama karadinsa da sumbace ta ba tare da shauqin komai yasa taji motsi a ranta ba, ta je  gaban windo ta sake gyara dankwalinta sannan ta juyo ta dube shi fuskata babu yabo babu fallasa ta ce,

“To mu tafi ko.”

Ya dan yi kasaqe yana kallonta,

“Yau ba ki yi kwalliya ba, kin kuma qwaquba mayafi a ka.”

Kai tsaye ta amsa,

“Ba buqata tunda kwalliya ba ta biyan kudin sabulu, kai nake son bawa haushi, kuma ba ka ji sai janyowa kaina yan giya da nake, gara kuma na sauya salo…”

A ransa ya ce,

“Saura na yi maganin fita aikin gaba daya.”

Yayin da a fili ya ce,

“Madallah, duk salon da zaki canja Ubangiji zai hore min shi.”

“Za mu gani.”

Ta fada cikin cije lebe, sannan ta riga shi hanyar fita, ya bi bayanta cikin nazari da canki-cankin me zata yi? Wannan Rigar silikin nasa ta fi ko wacce hargitsa lissafi.

*****

Hankalin Mujahid a tashe ya nufi asibitin da aka kira shi aka sanar da shi cewa matarsa babu lafiya an kwantar da ita, da kyar ya lalubo asibitin saboda surquqin da aka kai shi.

Yana shiga ya tarar da dangi har sun taru, Hajiya da yaran gida har ma da su qaninsa Sani da kuma Yaks kowa hankalinsa a tashe, haka suka tare shi da fuskar alhini, amma shi sai ware ido yake cikin alamun tsarguwa kowa ya fahimci yanayinsa.

Ana ta yi masa Jaje da yi yi wa matarsa fatan sauqi amma shi sam tamkar hankalinsa ba ya kansu, ya matsa kusa da Hajiya ya tambaye ta,

“Ban gane ba Hajiya, me ya faru da Binta wanda har kuka sani ni ban sani ba?”

Hajiya ta ji tambayar Bambarakwai wai Namiji da suna Hajara, amma sai ta bi shi da kallo bisa zaton rikita ce ta sanya shi manta inda yake, cikin qoqartawa kanta qarfin hali ta fara ba shi bayani,

“Tana wajen aiki kawai aka ga ta yanke jiki ta fadi ta suma, Allah ya taimaka lokacin Yaks ya je Bankin nasu kawai sai ya kwaso ta ya kawo ta nan asibitin saboda ya fi kusa da bankin…”

Kafin ta dire ma Mujahid ya bar gabanta ya koma na Yaks yana yi masa duban tuhuma,

‘Ka dauki matata ka kai ta asibiti ba tare da ka sanar da ni ba Yaks? Ba ka da lambar wayata ne zaka yi gaban kanka ko kuma don ban isa ba ne?”

Kusan kowa a wajen bai ji dadin abinda Mujahid yayi ba, qaninsa Sani sai da ya sha gabansa yana magana cikin bacin rai,

“Wai Yaya Mujahid me yake cin kanka ne? ka manta matsayin Yaks a wajenmu kake abu kamar wani maqiyinka ne shi, in da ba ya wajen ba ma wani qaton da ba ka sani ba ne zai dauke ta ya kai ta asibitin?”

Sani na magana a hankali ne dan kar na kusa da su su ji, amma shi Mujahi da ya tashi ba shi amsa sai ya daga murya,

“Ko daga duniyar wata mutum ya fado na lamunci ya dauko Binta ya kai ta asibiti, kuma ba zan zarge shi da komai ba, amma Yaks duk abinda zai min a kan Binta ina zargin cuta a ciki… kuma in na gano ba zan yafe ba…”

Kan kowa ya kulle  a wajen musamman Hajiya, domin hannu bibiyu ta sa ta dafe kanta alamun tana cikin tashin hankali.

Ganin Mujahid bai damu da kidimarsu ba, hasalima neman barin wajen yake ya sanya ta sanya hannu ta yafito shi, ya dawo fuskarsa babu annuri ya rusuna a gabanta. Cikin taushin murya ta ce,

“Haba Mujahid, wannan dabi’ar don me ka aro ta? Na san ba taka ba ce, ni ba wannan sanin na yi maka ba don Allah ka dena, in wani laifi yaks yayi maka ai kai mai hukunta shi ne, ba wai ka dinga daukar tsattsauran horon da zai iya taba zumuncinku ba, haba Mujahid.”

Mujahid ya jima cikin shiru da alamun son yayi magana amma ta qi fita, sai da qyar ya girgiza kai ya ce,

“Ki fitar da kanki daga maganar nan Hajiya, ni ban yarda da Yaks bisa kawo Binta nan ba kawai, amma in ta rube zaki iya ji.”

Ya tashi da sauri ya bar wajen, duk suka bi shi da kallo, sannan suka dami Yaks da kallo wanda duk yayi tsuru-tsuru ya nuna kalar tausayi, babu wanda ya hango alamun rashin gaskiya tare da shi sai Hajiya, wadda kawai ta ji qirjinta na harbawa idan ta kalli idon Yaks din.

Ta fi kusanci da Yaks akan Mujahid amma ta fi zaton gaskiya a Mujahid fiye da Yaks.

Kwana da yini likitoci na qoqarin shawo kan matsalar Binta abu ya faskara, da farko Mujahid yayi zaton shiri ne kawai wannan cuta da kwanciyar, amma ganin yadda Binta ke shan wahala, kwana daya da yini kadai ta wani zabge tamkar ta shekara a kwance, sai abin ya fara bashi tsoro ya fara shakkun in bai dauki haqqinsu ita da Yaks ba. Abin ya dinga damunsa har sai da ya tari Yaks din a gaban su Hajiya ya bashi haquri, inda shi kuma ya nuna babu komai ya yafe.

Wannnan ya yi wa Hajiya dadi, don ba qaramin zulumi ta shiga bisa wannan zaren da aka ja tsakanin Mujahid da Yaks ba, ko Mujahid bai auri Binta ba, ba zata so rashin jituwa ta shiga tsakaninsu ba tunda duk ta dauke su ne kamar ‘ya’yanta, bare kuma an qara qulla wata zumuntar sun qara zama daya.

Nabila har kwana biyu ba ta sami halartar asibitin ba bisa rashin lafiyar Innarta wadda ita ma ke kwance a asibiti, sai ya zamana Mujahid na jin kansa tamkar an jefa shi a kuratandu an rufe, ba shi da mai rarrashinsa kuma ba shi da mai ba shi bakin cewa Binta zata tashi, dole ma shi ne mai zuwa ya rarrashi Nabila, wadda take cikin damuwar Masoyanta biyu duk suna kwance babu lafiya.

Ranar juma’a ya baro wajen aikinsa qarfe tara da rabi zuwa asibitin, da zumudin zai karbi sakamakon gwaje-gwajen da aka yi wa Binta, ya dai ga menene yake damunta a huta, duk da yanzu dai ta fara warwarewa sai dai abinda ba a rasa ba, ko jiya da dare ma kafin ya je gida sai da ta dan taba masa rashin kunyar, shi kuma yana lallabata kamar qwai.

Da kuzarinsa ya shiga ofishin likitan, kuma dan iya shege irin na Mujahid sai ya ciro ID Card ya nuna masa, cikin raha ya ce,

‘Na ga kamar kana da sha’awar wasa da doka ne, kwananmu uku a asibitinka kana yi mana yawo da hankali, in ka kashe min mata ba yarda zan yi ba”

Dariyar yaqe kawai likita yayi ya turo masa takardu tana cewa,

“Taka dokar ka sani, amma ai ta lafiya dole ne a bi ta a sannu.”

Mujahid ya karbi takardu yana dariya, ya ce

“Kuma da gaskiyarka.”

Ya nutsu ya fara duban takardun daya bayan daya, nan da nan sai ga fuskarsa ta baci, a rikice ya miqe kamar an tsikare shi ya zagaya gaban likitan ya daga daya daga cikin takardun yana nuna masa, yana huci ya ce,

“Wannan takardar ta meye?”

Likita yayi fuska ya amsa,

“Ta sakamakon gwajin HIb da mu ka yi mata ce”

“Gwajin HIb?”

Mujahid ya jaddada cikin kallon likita da haushi da kuma mamaki.

Likita ya  kada kai yana tsura masa ido cikin tabbatarwa da nuna babu fa canji.

“Haka na ce”

Mujahid ya cakumi wuyansa kamar zai gwara kansa da bango, amma sai ya sake shi cikin huci ya shiga hargagi,

“Haka ka ce din addini ne, ko fadar Allah ce da ba’a gogewa?

Likita ya shiga gyara wuyar rigarsa da Mujahid ya cukwikuya, fuskarsa na son nuna haquri da shanye damuwa, ya dubi Mujahid da kyau ya ce,

“Abinda ka yi bai yi maka kyau a zamowarka lauya ba, yanzu in na tafi neman haqqi bisa wannan cakumar da ka yi min, me kake tsammanin zai biyo baya… a kan aikina kake cin zarafina?”

Mujahid ya tare cikin hargagi,

“Komai ma ya biyo bayan mana, ka tafi kotun duniya in ka so. Ban da kai dan iska ne, matar auren zaka kawo wa maganar gwajin HIb? In zargin hakan ne me yasa ba zaka ce ni mijinta zaka gwada ba? In dai ba shirin tozarta min iyali dama ka yi ba”

Likita ya dinga duban Mujahid cikin takaici, kawai sai ya watsa masa sakamakon gwajin HIb din da suka yi wa matarsa Binta.

“Gashi nan, ai yanzu ma bata baci ba, in ka gama duba wannan kana iya zuwa Lab kai ma mu gwada ka.”

<< Rigar Siliki 34Rigar Siliki 36 >>

1 thought on “Rigar Siliki 35”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×