Ba tare da ya dube ta ba, idonsa na kallon hanya ya ci gaba da cewa.
“In gwaninta ki ke son yi min kawai ki ci gaba da yi min addu’ar samun wadda na ke so ta karbi soyayyata ko da kuwa ba ta zamo kamar yadda na so ta ba”.
Binta ta dawo da dariyarta.
“In ba kyakkyawa ba ce gaskiya ta yi gaba, mu ba mu da kyau amma muna son mai kyau… Kuma addu’armu ta neman mai kyau bisa turba mu ke, cewa mu ke Allah Ka ba mu mai kyau mai alkhairi”.
Dole Mujahid ya murmusa, ta ba shi dariya ainun, ransa kuma ya yi sanyi da jin tana addu’ar Allah ba su mai kyau, ke nan tana yi wa kanta ma fatan samun miji mai kyau, shi kuwa ya san kansa, ko bai zo a sahun farko na kyawawa ba, a yi maneji da shi a sahu na biyu.
Cikin fara’a ya kada kai ya ce.
“Kyau ki ke nemar min ba wadda zuciyata ta ke so ba…”
Ta tari numfashinsa da fadin.
“Don Allah ka yi wa zuciyarka fada ta so mai kyau”.
Ta qarasa da yin dariya.
Shi kuma ya amsa cikin murmushi idonsa a titi.
“Ni idan na fara so ba na dainawa, in na ce zan yi abu da gaske na ke, ina gwada iyakar qoqarina, gaskiya a dabi’ata akwai mugun naci”.
“dan anaci ke nan”.
Ta fada cikin dariya ba tare da raunin muryarta da sanyin jikinsa sun dada ta da qasa ko sun ruda ta ba.
Wannan ne kuma ya kawo qarshen tattaunawar tasu, domin shi ya nutsu a tunani, ita kuma sai ta janyo waya ta shiga chatting har suka kai Voto.
Kash! An sami akasi da ya sanya Mujahid maimaita hirji sau babu adadi, tun daga zuci har zuwa fatar baki. Ya yi muguwar nadama da danasani mai tsanani bisa dauko Binta su taho Voto, kuma tsautsayi ya sa kai tsaye ya wuce da ita gidansu bai fara kai ta gidan kakanninsu ba.
Abin takaicin da ya tarar shi ne, mutane danqar a bangaren mahaifansa, sun taru suna karba kishiyar babarsa daga hannun mahaifinsa yana yi mata dukan shan gishiri, qartin maza ne suka hadu suna qwatarta tana kuka tamkar za ta mutu, tana neman dauki.
Gefe kawai Mujahid ya yi ya kifa kai a bango cikin tsananin nadama da ambaton Allah. Yana jin ina ma zai farka ya ga abin da ya ke faruwa ya zama mafarki? In hakan kuma ba za ta samu ba, ina ma ya girgiza ya zama ba shi ba?
Zuwansu ya taimaka wajen dakatar da mahaifin nasa aika=aikar da ya ke na neman kashe ‘yar mutane, musamman da Binta ta sanya hannu aka ta rushe da kuka iyakar qarfinta tana ambaton.
“Za a yi kisa, in an kashe mai za a ce wa Allah? Ku da ku ke tsaye kun kasa hanawa me za ku fada wa hukuma? Haka mata suke a wajenku… Dabbobinku sun fi su mutunci?… Kaico!”
Binta kuka ta ke wiwi tsakaninta da Allah, lamarin ya yi mugun taba ranta. Ta tausaya wa mata har da kanta duk da tana birni inda ba a cika mayar da mace jakar duka ba. Ta tsani maza har da na birnin da ta ke da yaqinin ba sa dukan, amma wawantar da matan na nan cikin ransu, kuma duk sanda suka sami sarari suna bayyana irin nasu duk da wasu har dukan ma ba su watsar ba.
Da qyar aka shawo kan Binta ta yi shiru, shi ma don ta ji Baban Mujahid ya dauko bayanin laifin da ta yi masa ya ke mata wannan neman fidda ran.
A hasashen Binta ta yi zaton za ta ji mugun laifi mai kama da ta zuba masa shinkafar bera ko ta zuba wa gyatumarsa a abinci, abin haushi sai ta ji cewa, wai jiya ne zai fita ta tuna masa babu fa ko qwayar dawar da za a girka a gidan, kasancewar damina ta yi nisa. Ya nuna mata shi fa ba abin da zai iya, ba shi da shi, kuma ba zai yi sata ya kawo musu ba, ya sa kai ya wuce abinsa.
Da dare da ya dawo sai ya tarar ta yi tuwo ta cika masa langa, ya share wuri ya tashi da shi. Da safe ma ta kawo masa dumame ya ci ya tafi gona, wai shi ne yanzu yana dawowa ta sauke masa ba’asin ai hatsin jiya rantowa ta yi a maqota, wai in ya sami sarari ya biya in bai samu ba ita ‘yarta na dab da haihuwa in ta sami hatsin biki za ta bata ta biya.
Wannan shi ne abin da ya faru, abin da kuma ya tunzura shi yin dukan shi ne, don me za ta tona masa asiri ta yo masa rance a maqota?
Yana ba da labarin yana tsine mata yana qarawa, yana kuma maimaita cewa, ita ba matar rufin asiri ba ce, bankadaddiya ce kawai.
Sai da Binta ta gwammace da ba ta saurari dalilin wannan zaluncin ba, domin wasu kala-kalar ciwon kai da suka dumfaro mata sai da suka gayyato mata jiri ya kai ta qasa, ranga-ranga aka kwashe ta zuwa dakin Gambo mahaifiyar Mujahid.
Hankalin Mujahid ya kai qololuwar tashi, ransa ya qara mugun duhu, sai ga shi da hawaye shabe-shabe amma babu sautin kuka. Ya bi ayarin ‘yan shiga da Bintu dakin Innarsa, ba tare da ya iya tabuka komai ba ban da hawayen da daukar mafici yana yi wa Binta fiffita ba tare da ya ce uffan ba.
Da kadan-kadan qafa da hayaniyar mutane ta fara lafawa a bangaren nasu, an ja mahaifinsa waje wanda zuwa wannan lokacin jikinsa ya yi sanyi, illa fadan borin kunya da ya ke yi, amma a tsakiyar zuciyarsa bai ji dadin yadda Binta ta ganshi a wannan halin ba, musamman saboda kalaman bakinta da kuma mummunan yanayin da ta shiga. Kai! Hatta Mujahid ma bai so ya ganshi ba, wanda zahiri bai haifi dan da ya ke taimakonsa irinsa ba.
Kande wadda aka lakada din ma ta yi shiru, samarin ‘ya’yanta ne suka sanyata a gaba suna rarrashi su kuma suna kukan.
Binta ta farfado sosai, zaune ta ke cikin mugun muzanta tana sharbar gumi, Mujahid kai a qas yana faman yi mata fiffita da mafici, shi zuwa yanzu idonsa babu hawaye, illa idanun sun soye da tsananin bacin rai.
Binta ta dinga raba musu ido, shi da mahaifiyarsa tamkar wadanda suka zo daga duniyar wata a gaban idonta.
Ba kadan ba Mujahid ya tsargu da kallon, ya ji kuma a ransa kallon nan ba mai alkhairi ba ne, sai wahalar gaske zai zo wa da duban qudurorin zuciyarsa da alkhairi a kan Binta. Don haka ya ci gaba da daukar zafi tun daga qarqashin zuciyarsa har zuwa kan fuskarsa.
Babu abin da Inna mahaifiyarsa ta tsarga a kallon face Binta na kallon tuhuma da neman ba’asin abin da ta tarar saboda haka cike da qwarin gwiwa ta fara qoqarin kare kanta da kuma wanke dan ta’addan mijinta a idon Binta.
“Wallahi Kande ke ma ta dauki haqqinki… Ko naman jikinta ake yanka ai iyakcin abin da za ta yi ke nan… Wani kwakwazon da ta yi na rantse da Allah na ganin idonki ne, da kuma wannan yaron, musamman ke da ta ga kin damu da yanayin da ki ka tarar da ita”.
Da sauri Binta ta dora wa Mujahid zafafan idanuwanta kallon da ta ke masa tamkar tana jaddada masa cewa, mahaifanka dukkansu masoya kawunansu ne.
Ba ta kallon idon Binta kai tsaye Mujahid ke gane karatun kallon da Binta ta ke masa ba, ta hanyar satar kallo ne, amma haka shi da zuciyarsa suka sha wuyar abin da suka karanto. Nan take kuma suka hau qoqarin kubuta da kuma wanke kai.
Ya dubi mahaifiyarsa cikin hawaye.
“Bai kamata ki ce haka ba Inna, ko da tsintsiyar kwakwa miji ya daki matarsa ya kamata ta yi kuka tun daga zuciyarta har kan fuska”.
Inna ba ta gane qalubalen da ta kinkimo wa soyayyar Mujahid ba, tsakaninta da Allah ta ke farke musu ra’ayinta, don cikin azarbabi ta tare shi.
“Amma dai ita ma matar ya kamata ta kiyaye abin da mijin zai dake ta ko? Ta fi kowa sanin Malam ba ya son cin bashi ko na kobo ne, balle ta je ta ciyo masa bashin hatsi, abin kunya ma akwai irin wannan?”
Sai Mujahid ya ji tamkar ta sake kwantara masa qaton dutse a gyambo, musamman da ya lura Binta ta sake shanye baki tana kallon Innarsa.
Ya yi wani irin nishi cikin kame kai, idanunsa suka kada suka yi jawur. Ya jima cikin tantance qofofin fita daga wannan qofar ragon da mahaifansa biyu suka yi masa. Da qyar cikin ragon azanci ya samo abin cewa.
“Wai ma ya ya aka yi aka rasa abin da za a ci a gidan nan? Ko sati fa ban yi da turo muku kudin da na san ya zarce na hatsin da za ku ci a wata biyu, wa na ke wa nema idan ba ku ba? Don Allah me na hana ku, me ya sa za ku saka min da tozarci?”
Idon Binta a kan Innar Mujahid tana jiran amsar wadannan tambayoyin cikin bugun qirji, tamkar tana qaddara cewa Mujahid qarya ya ke.
Babu wani alamun shakku Inna ta amsa.
“Ko rabin kudin ban ba wa Malam ba, yo abin nasu ne na ga da son kai, kana ganin danta Amadu yana yo aike, da qyar ta ke iya ba ni sinqin sabulu da barbaden gishri”.
“Innalillah wa’inna ilaihi raji’un “.
Kawai Mujahid ya ke ambato cikin kidima a dukkan illahirnsa, ya yi nadama da danasanin dauko Bnta su taho gidansu don ya bata soyayyarsa, wannan wacce irin rashin sa’a ya tako a farkon yaqin yada manufarsa?
“Ban ji dadin abin da na tarar ba, a tsayin rayuwa ta ina da tsammanin zai cutar da ni”.
Abin da ya dinga maimaitawa ke nan bayan ya haqura da innalillahi, har sai da inna da Binta suka fara zargin akwai wata a qas, sai dai duk su biyun hasashensu bai kai inda shi ya dosa ba.
Cikin kulawa Inna ta tare shi.
“To wai kai mene ne na damun kanka haka, sai ka ce yau ka fara ganin babanka ya daki mace? Ni kaina ai rufin asirin da Allah ya yi muku ne ya sanya na kubuta daga dukansa, sannan kuma ina kiyaye abin da zai dake nin, ita kuwa Kande ba ta san wannan ba…”
Mujahid ya fahinci idan ya ci gaba da sauraron Innarsa sai ta yi masa tsirara tik! A gaban Binta da sunan wayar musu da kai ta ke, bai bari ta rufe baki ba ya miqe tsam ya bar musu gidan ya miqe turba samval ya shiga dawa ya sami gindin bishiya ya rakube. Damuwa da bacin rai tare da hasashe kala-kala suka taru suka dinga dimarsa. Ya shafa ta inda zai karbi qaddararsu ya rasa.
Inna da Binta suka gama ‘yar shirunsu a sunan jimamin abin da ya faru har suka ware suka fada hira har daga bisani Binta ta ziyarci gidajen dangi.
Allah ya sani, qimar Inna da yawa ta tarwatse a idanun Binta, tana yi mata kallon tamkar wadda ba nono daya suka tsotsa da mahaifinta ba, don babbar lambar da ake yi wa mahaifinta na kyawun hali shi ne, son kyautata wa abokan mu’amalarsa tare da rashin ganin qyashi, Inna kuwa ko digo ba a samm mata wadannan kyawawan halin ba, ga shi kuma ta yi sa’ar mugun miji irinta.
Har la’asar ta kawo kai Mujahid bai dawo gida ba. Ba Inna ba, hatta Binta ta damu da rashin ganinsa, don ita ma gabadaya garin ya gundure ta, Allah-Allah ta ke ya zo su tafi gida.
Sai wajen biyar na yamma ya shigo gidan, bayan ya tsaya wajen mahaifinsa a waje ya cije damuwa ya yi masa nasihar guje wa fushin da zai dinga kai shi bugun mata. ya sallame shi da kudi masu kyau, sannan ya shiga gida fuska babu walwala.
Inna na ta rawar jikin yi masa hidimar kawo abinci, Binta kuwa tuni ta sagala jaka da mayafi ta yi zaune bakin qaramin gado tana jiran ya gama cin abincin ya tashi su tafi.
Komai ma ya gunduri Mujahid, don haka ko kusa da sha’awa abincin bai ba shi ba bare ya kai shi harshensa, gabadayansa ba ya cikin walwala ya zaro kudi a aljihunsa ya hau qirga. Ya miqa wa Inna nata sannan ya hau mulmula ragowar na hannunsa. Ya saba bai wa Inna na Kande ta ba ta, amma a yau ta tabbatar masa idan ya ba ta samfewa ta ke.
Da alama Binta ta karanci haka a tare da shi, kawai sai ta yi fuska ta miqa masa hannu.
“In na Inna kande ne, miqo na kai mata, kai ka yi ka ci abincin mu tafi”.
Ba musu ya miqa mata cikin kasalar jiki da ta zuciya, lissafinsa kuma na qara hargitsewar hasashen yadda Binta ta kalli al’amarin.
Ba ta bata lokaci ba ta fice, kuma ba ta jima ba ta dawo.
Tun kafin ta zauna zumbur Mujahid ya miqe.
“Ai mu wuce kawai”.
Ba Inna ba, ita kanta Binta ba ta so hakan ba.
Inna na binsa da kallo cikin kasa magana, ita kuma Binta ta daure ta bi ba’asi.
“Haba dai, me ka ci? Kalli bakinka fa a bushe qayau”.
Mujahid ya lashi busassun labbansa da qoqarin tare qwallar da ke qoqarin zubo masa saboda tausayin kai ba don an yi abin da ya isa sa namiji irinsa hawaye ba. Ya daure da qyar ya ce mata.
“Ba na jin cin komai wallahi”.
Cikin muzanta Inna ta tari numfashinsa.
“Yanzu don Allah kai wannan dan sai ka fi mai kora shafawa? Ko matar da aka daka ta fara warewa ta shiga harkokinta sai kai ne za ka kasa cin abinci saboda ita?”
Mujahid ya ji wasu tawagar hawaye na son dumfarowa kuncinsa, dole cikin rawar murya da tsura ido ya tanka wa Innarsa.
“Duk a gaban matan Dahiru da Auwalu malam ya daki surukarsu?”
Sai Inna ta rasa bakin tankawa kawai ta yi zuru tana kallonsa.
Cikin kada kai da son zubar da hawaye Mujahid ya sauke wa Binta wani kallo mai cike da tarin fassarori yana cewa.
“Duk wanda aka yi wa abin da aka yi mana, na rantse da Allah an gama qarshen murda masa hannun agogo baya, amma babu komai. Binta zo mu tafi”.
Binta ta yi mugun shan jinin jikinta, don kallon da Mujahid ya yi mata ba boyayyen kallo ba ne a duniyarta mai mazan da ke kawo mata tayin aure ko na soyayya.
Jikinta a sanyaye ta miqe cikin gyara mayafi tana yi wa Inna sallama, da ma tuni Mujahid ya fice.
Dole Inna ma jiki a sanyaye ta yo musu rakiya dauke da tsarabarsu.
Masha Allah thanks
Masha Allah ubangiji ya Kara basira