Skip to content
Part 51 of 59 in the Series Rigar Siliki by maimunabeli

Nabila na zaune a kujerar zaman amarya, yayin da qawaye da dangi ke filin rawa suna kwasar kida.

Wajen yayi matuqar kyau yadda dole duk wanda ya halarce shi ji nishadi da farin ciki ko da ya zo da zuciya mai duhu irin ta Binta.

Duk wanda yayi wa Nabila farin sani ya san cewa murmushin da ke kuncinta na zallar yaqe ne, ba haka murmushinta yake ba, ya fi haka kyau nesa ba kusa ba.

Filin zuciyarta tsananin kadaici ya quntata shi, filin bikinta ba dangin Innarta babu Binta da take jin kamar daga ahalin dangin Innarta take don kulawar da take ba ta a baya irin ta dangin Inna ce. Da wannan takaicin ta yi wa hawaye fuska ne kawai ta hana shi fitowa don kar ta bata Foundation din da ta ci kudi  kafin ta qara mayar da ita aljana saboda kyau.

Dangin Binta na ganin Binta da Mujahid suka ji dadi nesa ba kusa ba, don har zance ya fara yawo cewa Binta fa taqi bayar da hadin kai duk da Iyayenta ne suka yi hanyar auren.

Yammata da abokan wasansu suka zo suka rufa musu baya har wajen amarya Nabila, wadda daurewa kawai ta yi ta kasa tashi daga kujerarta ta je ta taro Binta.

Da suka qaraso ma kasa daurewa ta yi sai da sai da ta miqe ta rungume Binta.

Mujahid na ganin haka yayi saurin matsawa kunnenta,

“Ki na kuka kin karya alqawarin da dazun nan kika daukar min”.

Dole ta hadiye kukan ta tana ta ajiyar zuciya tana ambaton,

“Antina”

Mujahid ya tsaya gabansu rungume da hannu yana ta kallonsu cikin murmushi, ana ta daukarsu hotuna.

Binta ta dago Nabila tana ce mata,

“Na ce ki share ki manta komai ya wuce, kin ga kina neman raba mana abin fada a taro, zo ki koma wajen zamanki ki zauna.”

Tana qanqame da hannun Binta suka je kujerar Nabila ta zauna a mazauninta yayin da Binta ta ja baya tana bawa Mujahid guri don ya zauna a mazaunin da aka tanadawa Ango

Amma sai ya girgiza kai ya ce,

“Ki zauna kawai ki wakilce ni, ni da nake baqo, mu yi hotuna na kauce, ba na son zuwa irin wannan wajen.”

Sun sha hotuna sosai, har lokacin da makada suka kira amarya fili sai Mujahid ya miqe yana cewa Binta,

“Da gaske fa nake ke zaki wakilce ni, ku je don Allah.”

Kafin Binta ma ta tanka har ya bar wajen,

Wannan dalilin ya sanya Binta yin bajinta sosai inda ta dinga zubarwa da amarya Nabila kudi, dangin Binta ma abin ya burge su suka shigo fili suna yiwa Binta da Nabila barin liqin.

Yadda abubuwa suka kasance gaskiya sun burge duk wanda da ya ji labarin wa Nabila ta aura da kuma dangantakarta da Binta.

Ita kanta Nabila wannan ya sama mata salama a zuciya ainun, don ta fara fargabar yadda zata yi zaman rashin aminci tsakaninta da Antinta da take matuqar so tun fil azal, har ta fara roqon mutuwa da zuwan jibi da za’a kai su gida daya alhalin Binta na gaba da ita.

Ana kiran Sallar magariba, Binta ta yi wa Nabila sallama su ummy suka raka ta mota don tafiya, lokacin Mujahid ya je sallah, sai da suka jira shi ya dawo sannan suka tafi, su ummi kuma suka koma ciki.

Tunda suka zama su kadai Binta ta canja fuska, Mujahid na lura da haka sai ya ji wani rashin dadi ya ishe shi.

dazu da Binta ke cikin farin ciki sai ya dinga jin tamkar a aljanna yake, lokacin ya tuna lallai fa ba qaramin so yake wa Binta ba, hayaniyarta ce kawai ke boye son take sanya shi bacci, a dazun ne kuma ya qara godewa ubangiji da ya hada shi da Nabila. wanda yake da zaton ba don samuwar Nabila ba da qyar zai iya samun kan Binta cikin sauri haka.

Yana ta satar kallonta tana ta numfarfashinta, yana samo dabarar yadda zasu cigaba da zaman arziqi. Can kawai sai ya fara kwaso buhunhunan godiya cikin taushin murya yana sauke mata, tsawon lokci kafin ta tare muryarta a daure,

“Ya isa mana, ai kwantaragin wannan ya qare, na taya ku walwala kun yi farin ciki, shikenan ya wuce ni kar ka cigaba da damuna.”

Ya jima yana kallon titi, amma farin cikinsa bai gushe ba, yana dariya ya ce mata,

“Sorry na tuna, amma duk da haka ba zan gaji da yi miki godiya ba, musamman idan ina tuno lokutan da kike ta matsa min na auri yarinyar can, ko na qi ko na so kin bada taki gudunmowar.”

Binta ta ji haushi na cika ta, saboda haka ta harare shi ta kawar da kai.

Sai a washe garin ranar aka zo aka yi wa Nabila jere na gani na fada, Binta ba ta so wuni a gidan ba don dai kawai ba ta da wajen zuwa ne, gidansu har yanzu fushi take da su sosai, ko hanyar gidan ba ta son kallo, ta so a ce ranar aiki ne kawai ta fice ta bar gidan, amma dole haka ta haqura ta zauna, don ma yawancin masu jeren maza ne. mata biyu ne masu bayar da umarni, daya daga kamfanin punitures din, daya kuma daga dangin Baban Nabila wanda sai ta silarsu mahaifin Nabila ya samu yayi basaja ya sai kayan  a boye ya ce su je su kai a matsayin su suka yi, in an kawo wanda Momin ta laminci a yi sai a hada mata.

Da dare ma haka Mujahid ya kuma rakitar Binta dole ya kai ta dinner, sai qarfe daya na dare suka dauko hanyar gida ran Binta a bace, don bidi’ar da aka zubar Binta ba ta taba tsammanin Mujahid na da sauqin kan da zai bayar da damarta ba, musamman idan ta auna duk da kirarin sonta da yake ko qarfen yari bai taba jifanta da shi ba bare qwandalar yin wata hidima, kodayake mutumin da ya kwashe mata kaya ya siyar ta ina ma zai mora mata wani abu daga sama? wannan jumurdar tasa ta ba ta tabbacin qaryar sonta kawai yake ba wai son ba ne, amma Nabila kawai yake so, don ayyukansa sonta suke nunawa.

A lokacin ma har suka zo gida tana ta faman numfarfashin fushi da tunanawa kanta mafita. don haka ko jiransa ya shigo da mota ba ta yi ba ta shige gida a dari ta garqame qofa, shi kansa da ya zo ya tarar da haka dariya yayi ya ce,

“Yanzu wannan yarinyar almutsutsanta ba sa nisan kiwo”

*****

Wuyar aiki dai shi ne rashin fara shi, a washegari qarfe takwas na dare aka kawo Nabila gidan masoyinta, sannan gidan masoyiyar Antinta da ba ta da kamarta,

Wannan lokacin Binta ta kasa boye damuwarta har labari ya je wa Nabila cewa an ga Binta na share hawaye,

Wannan ya dagawa Nabila hankali sam ta rasa sukuni har zuwa lokacin da kowa ya dauke qafa qarfe goma sha biyu, ya zamana shigowar Ango kawai take jira wanda take saka ran shigowarsa shi kadai don ya ce ba zai kawo kowa ba, don haka ya bayar da umarnin abokai su mayar da ko wacce mace gida kar a jira shi.

Nabila ta yi amfani da damar kadaicin da ta samu ta ci kukanta ta qoshi, yadda har ba ta ankara da tsawaitar lokaci ba kuma ba ta ji wani motsi ba sai ganin Mujahid ta yi tsaye a kanta rungume da hannu yana ta faman kallonta, da alama ma ya jima a wajen.

Cikin barin jiki ta shiga rawar jikin goge hawaye, lokacin da ya gyara murya yake ce mata,

“Ke dama ba ki da alqawari?”

Ta yi saurin girgiza kai,

“Na kasa riqe kaina yaya Mujahid, an ce min Anti Binta tana kuka, ina ta fada maka, ko quda ba na son na cutar bare Anti Binta, in na tuna ni ce sanadin damuwarta sai na dinga jin dama…”

“Hush!”

Ya tare ta da daga sauti,

“To yanzu ki riqe kanki kar ki yi mana sabo.”

Ta bige da nacewa murzar hawaye nutsuwarta na dawowa, in dai akwai Mujahid a waje duk inda ta kai da damuwa ko wacce iri ce sai ta neme ta ta rasa musamman in ya sa kansa cikin damuwar.

Sun jima cikin haka, shi yana ta kallonta cikin saqe-saqen zuci, ita kuma tana ta qoqarin kintsa kanta don kar ta cigaba da bata masa rai, can jimawa kamar daga sama ta ji ya ce,

“Kodayake aikina ne na hana ki kuka, aikina ne na sanya ki farin ciki, tun ranar da kika shigo rayuwata na yi wannan alqawari, In sha Allah kuma Ubangiji zai hore min na sauke shi… ba ni minti goma sha biyar, ina da tabbacin in Allah ya so daga yau ba zaki sake kuka dalilin Binta ba.”

Bai jira ta yi magana ba ya juya ya fice daga falon, ta tashi da sauri ta biyo bayansa sai ta ga cikin azama ya sauka qasan bene, kuma kai tsaye ya shiga qwanqwansa qofar dakin Binta.

Nabila ta koma da sauri cikin toshe bakinta da ke son barewa da kuka.

Ya dan jima yana qwanqwasawa sannan Binta ta zo ta bude, bayan ta tambaya muryarta a dashe,

“Waye?”

Ya tuna mata da da muryarsa ta da lokacin da yake Yayanta sosai, lokacin maganar soyayya bata kunno ba, duk da dama shi ya dade da son ta a zuci.

 “Yayanki ne Mujahid.”

Wannan yanayin ya hana ta gardama, don ya tuna mata kansa lokacin da yake amininta, ko waya yayi mata zai ce mata, Yayanki ne Mujahid.

Da sauri ta bude qofar ta ja baya, cikin yanayin tambayar ba’asi.

Ya shiga ya wuce tsakiyar falon ya nemi kujera ya zauna, kallo daya yayi mata shi ma ya san ko yanzu cikin kuka ta ke duk da fuskarta na nuna babu komai.

Ta zo tsakiyar Falon ta tsaya tana kallonsa kawai.

Ya nisa yana nuna mata kujera yana cewa,

“Ki zauna magana na zo da ita muhimmiya, ina kuma zaton ita ce zata zama ta farko, kuma ta qarshe Insha Allah da sunan nasiha tsakanina da ke”.

Bakinta na rawa ta dubi agogo tana ce masa,

“Amma sai a irin wannan lokacin ne zaka zo da magana, ni ba ni da buqatar irin wannan lokacin daga gareka sam, ka tashi ka tafi ma yi maganar da safe”.

Ya dan yi murmushin yaqe,

“Ni ba na son barin kwantai, musamman na magana”.

Sai ta yi zuru tana kallonsa.

Ya dube ta da kyau ya ce,

“So da zumunci ya hada mu Inuwa daya mu uku, wato ni da ke da Nabila, Kafin na bijiro miki da sona na aure ina da tabbacin mu uku nan muna rayuwa da shawarar juna, kina rayuwa da shawarata, Nabila na rayuwa da taki, wadda ake yawan haifa daga gare ni, kin tuna wannan?”

Ta yi qoqari ta gyada kai amma ta kasa, don ta tuna din, sai dai tana qyashin ta nuna ta tuna, don haka ta cigaba da kalle shi kawai.

Bai damu ba ya cigaba da magana,

“Mu ukun nan duk muna da amana ko kin qi ko kin so, ba wai so da shaquwa kadai ke sarrafa mu ba, dama can mu masu aminci ne, kuma masu qoqarin kare haqqin juna”.

Ya sake nisawa yana wasa da remote din da ya dauka kan qaramin teburin kusa da shi, ita kuma har yanzu tana tsaye kamar an dasa ta.

“Kafin na furta miki so, daga ni har Nabila a gefen rayuwar juna muke, ke ce katangar da ke hada mu, don ke ce aminiyar mutum biyu wato ni da Nabila, duk mun gamsu ke mutuniyar kirki ce, kuma so da shaquwa da ke ya kai wani qololuwa a duniyarmu, amma daga lokacin da na fara qoqarin furta miki so, sai ke kuma kika dinga qoqarin kawo Nabila kusa da rayuwata, yadda har na san da zamanta a duniya har kuma na nazarce ta da kyau, zuwa lokacin da kika fara saka qarfi don ki kori soyayyata na gama nazarin Nabila, na san abinda take ciki da irin zurfin amanarta, don haka kawai sai na janyota don ta taya ni yaqin samunki, ranar da na je mata da wannan qoqon barar shi ne ranar da kuka je ke da Yaks kuka same mu, ni na tsarawa Nabila abinda zata ce, kuma ta ce din.

Tun daga wannan ranar har zuwa ranar da aka daura aurena da Nabila, kullum muka hadu a fili ko a waya, ba ni da maganar yi da ita sai zaiyana mata yadda nake sonki, na sha alwashin cewa duk filin duniya babu wanda ya san irin son da nake miki sama da Nabila.”

Yanzu kwanyarta a hargitse ta ke, so take ta dawo kan doka da oda ta fahimce shi sosai, don ta ga kamar akwai alamun nutsuwa da gaskiya a tare da shi, shi ma fahimtar hakan ya sanya ya tsagaita ya ce mata,

“Kina fahimta ta kuwa?”

Ta kada kai da sauri ta ce masa,

“Ci gaba”

Nan take ya dora cikin tara gira,

“Tun daga wancan lokacin har kawo yanzu duk amana ce ke tafiyar da mu, har ke din da kike ta faman kirarin ba kya sona, dole amanar ce take miki birki ko ba tawa ba ta Nabila na da tasiri a zuciyarki, to amma abu daya da zan tuna miki wanda shi ne bambancinmu da ke shi ne.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rigar Siliki 50Rigar Siliki 52 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×