Nabila na qule a bargo cikin tsanani kasalar zuciya da ta gangar jiki ta ji motsin an bude qofar dakinta an shigo, ta qara yin lamo saboda zargin cewa wata ce daga cikin qannen Momi ta zo tashin hankalinta.
Da ta yi satar leqowa ta bargon sai ta ga alamar me shigowar ai Namiji ne, ba san lokacin da ta watsar da bargon ta tashi zaune ba, amma cikin qanqanin lokaci sai ta gane cewa Mahaifinta ne.
Ta sauke wata wawuyar ajiyar zuciya cikin tsananin fargaba, ta san dai ba lafiya ce ta shigo da shi ba, amma tana da dan qwarin qwiwa ganin kamar shi ma a tsorace yake, ko kuma alamar yana boye kar wani ya san shigowarsa dakin.
ta tashi da sauri tana fadin,
“Dadi…”
Ya dora hannu a baki yana nuna mata qofar dakin da ya riga ya tura sannan ya fara magana murya qasa-qasa,
“Nabila a gurguje, har yanzu ba ki sami wani da kike so ba?”
Ta zura masa ido kawai tana qissima tashin hankali iri-iri da aka kunno mata, ta san dai wannan barin jikin na mahaifinta ba banza ba.”
Kamar dama shi ma bai fada dan ya ji ta bakinta ba ya cigaba da magana,
Mominki ce take ba ni shawarar kawai na samo wani na ba shi ke sadaka, bai kamata a raba bikinki da na Sadiya ba, to nima na ga dacewar hakan, amma ba na son ba ki wanda ba ki sani ba, don Allah in akwai wanda kike so ki nuna min, ba sai yayi wata hidima ba kawai sai na kira shi na bashi ke kamar yadda muka tsara da Momin ba wanda ya sani.”
In baqin ciki yayi yawa zuciya ma qeqashewa take, nabila kallon mahaifinta kawai ta ke, yanzu ba kanta take tausayi ba shi take tausayi.
Tsawon lokaci tana kallonsa ta kasa tankawa, shi ma sai ya fara kallonta a tausaye, don ya san kallon rashin hayyaci kawai take masa. Muryarsa a raunane ya ce,
“Ki yi haquri nabila, ki yi haquri kin ji.”
Ta matse hawaye kuma lokaci daya tana murmushi, ta ce,
“Babu komai dadi, amma don allah ka ba ni sati guda…”
Ya tare ta,
“Nabila sati guda ai yayi yawa nabila.”
Zata yi magana ya tare ta tare da dosar qofar daki,
“ina laifin kwana uku ma kawai Nabila? Ki duba nan da kwana ukun kin ji.”
Ba ta iya amsawa ba face bin sa da kallo. Sai da ya fita sannan ta ji qwalla ta fara cika mata ido.
Bayan tuntuninta bata tuno kowa ba sai Mujahid, wanda ya diba wa kansa sati guda domin samo mata mafita, satin tuni ya wuce, ba ta son takura masa duk da kuwa power qaunarsa a zuciyarta na jin in shi ya zabo mata mijin zata fi so ta kuma fi kwantar da hankali, dole don kar ta takura masa ta zabo waziryarsa binta.
Da hawayenta ta yi wa Binta waya ta sanar da ita, aka sami gabar daidai lokacin Binta ke saqa yadda zata raba Mujahid da ita, kawai sai ta baibaye ta da siyasar cewa ai kawai ta zo gida yau ta same ta.
*****
Tun kafin Likita ya gama sauraron muryar Binta da Yaks wanda Mujahid ya kunna masa ya hada gumi sharkaf, kuma duk ilahirinsa ya gama nuna rashin gaskiya.
Bayan hirar ta qare mujahid ya mayar da wayarsa aljihu ya ce masa,
“To me zaka ce?”
Likita yayi qoqarin yayi magana amma ya kasa.
Mujahid fuskarsa a murde ya miqe tsaye,
“Dama ni tun da na ga asibitinka, kuma na zo aka ce min kai ne likita, sai na ji ina da tabbacin zaka iya kashe mutum…”
“Wannan kisa ne Ranka ya dade? Ko sauro ba na kashewa a nan ka bincika ka ji, wannan ma in ka saurari uzurorina na san tun da kai mai fahimta ne zaka fahimce ni…”
Mujahid ya tare shi,
“Kar ka wahalar da numfashinka, wannan mummunan ta’addancin na neman ran aurena a tare da nawa ran, sai na bi haqqinsu a inda ya dace…”
Likita ma ya miqe hankali a tashe,
“Ka saurare ni don Allah”
Mujahid ya doshi qofar fita,
“Ba zan saurare ka ba wallahi, ko wanne dalili zaka kawo min na san son zuciyarka ne, ba zai bani qaye ba, amma zan iya yi maka adalcin ba ka zabi da hikima, na daga maka qafa nan da kwana biyu lallai ka kira surukaina ka fahimtar da su cewa ba haka abin yake ba, kana iya ce musu ai kukskuren sakamako aka ba ta na wata mara lafiya da aka yi musu gwaji kusan lokaci daya, shikenan zan kashe maganar, amma in ya wuce wannan lokacin tabbas zaka ga takardar sammaci.”
Bai jira cewarsa ba ya fice a fusace kuma cikin sauri.
Likita ya koma kan kujera jagwab ya zauna, a hankali tashin hankalinsa na hucewa, don wannan zabin ba zai taba aljihunsa ba ba zai taba mutuncinsa a idon mutane ba.
“Wai mata nawa ne suka zubar da ciki suka cigaba da rayuwa Saratu, sai ke ce kike jin qarshen numfashinki kenan? Haba ba na son qauyanci don Allah.”
Mujahid na qoqarin shiga motarsa don barin asibitin kunnesa ya kwaso masa wannan muryar da yayi wa farin sani, da sauri ya kai idonsa kansu, Yaks ne da wata doguwar budurwa mai tirtsetsen ciki, suna tsaye jikin motarsa yana faman rarrashinta, akwai alamun yarinta da rashin wayewa sosai a tattare da yarinyar.
Wani mugun haushi ya naushi Mujahid, ya juya ya sake nazarin asibitin yana jin kamar ya koma ya shaqo likitan nan, wato nan asibitin na zubar da cikuna ne da lalata mata, nan aka kawo masa mata yadda qila ma a zuba mata banju a ruwa ko allurar batar da hankali a bi ta kanta. Wannan ‘yan’uwantaka da Yaks ba ta amfane shi da komai ba, kuma ma Allah wadaranta.
Ya dan yi gyaran murya wanda ya dawo da hankalinsu Yaks gareshi, dama don ya jawo hankalinsu yayi, kawai sai ya dagawa Yaks hannu murya a bace yana cewa,
“Na ji dadi samunka a nan, in ka shiga zaka tarar da saqona wajen likita.”
Bai jira cewar Yaks da yayi mutuwar tsaye ba kawai ya ja motarsa ya bar wajen. Lokacin qarfe biyu daidai, yakamata ya je gida cin abincin rana, amma haushin Binta ya hana shi dosar gidan, ko qofar rufaffen dakinta ya kalla ya san zai dinga shiryawa kansa hoton an zuba mata Banju a ruwa yana jin tashin hankali, kawai sai ya koma ofishinsa cikin tunani barkatai na yadda zai raba Binta da Yaks da kuma yadda zai tabbatar da yaqinin ba a shigar masa mata ba, don tsakani da Allah bai yarda da Yaks ba, ya tabbatar uwarsa ce kawai ba zai iya nema ba.
*****
“Karo na biyu ina mai ba ki shawarar ki zabi Yaks ki aura Nabila, Yaks na sonki, zai iya mutuwa don ke ba wai kawai ya bar wasu halaye da ba kya so ba”.
Wannan ita ce hudubar da Binta ke ta faman jerawa Nabila mai kuka tana jinjina kai, sai can ta ce,
“Ni kawai ba na ma sonsa ne Anti, ba kawai halinsa na ke qi ba, wallahi in na gan shi har wani daci na ke ji a maqogwarona, ta yaya zaman aure zai yiwu a haka?”.
Binta ta qara zagewa da rarrashi,
“Na ji fiye da haka a me wannan gidan, amma ai ban kasa zama ba, ban taba yaji ba duk da nima har yanzu idan na kalle shi abinda nake ji kenan.”
Ciwo biyu ya hana Nabila magana, na yi mata tayin auren Yaks da kuma zage mata Masoyi, kawai sai ta fara ambaton Allah a zuci tana kai masa kukansu ita da Mujahid, a zuci take addu’ar, amma hawayenta na zuba a sarari.
Binta ta cigaba da yi mata famfo,
“Kin ga in ba ki yarda kin auri Yaks da kika sani ba, ita Momin ma tana iya ba ki wani tsinanne can da ba ki san nasa halin ba, gara Yaks kin san cewa shashanci yake da son mata, a ko ina zaki iya amsa sunan mace da bai isa samu a bariki ba, bugu da qari ga shegen son da yake miki, a sauqaqe zaki iya canja shi yadda kike so…”
Nabila ta dago hawaye,
“Kamar yadda kika canja Maigidan nan ko Anti Binta.”
Ba ta son komai na Mujahid ya rabi Nabila, ta ji haushin tambayar amma ta boye haushin ta amsa,
“Ki share wannan, shi komai nasa na musamman ne, ba shi da zafin so irin na Yaks, a bangaren mu’amala kuma wallahi ya fi Yaks hatsari”
Girgiza kai kawai Nabila take, ta kasa cewa komai.
Wunin ranar nan sai da Binta ta sanya Nabila ta zabi Yaks a matsayin miji, har ma aka yi masa waya ya baro budurwarsa a asibitin zubar da ciki ya zo nan gidan Binta suka yi hira da Nabila aka kuma tattauna yadda abubuwa zasu kasance.
Ba su bar gidan ba sai da ko wannensu ma yayi wa iyayensa waya ya sanar da su zabinsa, mahaifin Nabila bai so sosai ba don shi ma ya san Yaks, amma babu yadda ya iya.
Mahaifin Yaks kuwa ya cika da murna, har ya dinga cin alwashin goben nan zasu je su kai kudin aure.
Yaks ya fi kowa jin murna, don ya fi kowa jin ciwon so da fargabar rashin da ya sha shiga yana fita.
Bai qara tunawa da yarinyar da ya baro kwance asibiti ba, kamar yadda bai tuna yadda suka yi da Likita game da barazanar Mujahid ya fadawa Binta ba.