LITTAFI NA HUDU
Mujahid na fahimtar hakan ya san ta gama zuwa hannu, duk walankeluwarta da wannan kawai za a iya gane ita sabun shiga ce. Amma abinda ya sa shi a mamaki shi ne, ina qiyayyar da ta ke masa?
Ya wurgar da wannan tambayar da neman amsa gefe guda, ya dinga rakito salasalai kala-kala da mazantakarsa ta koya masa, daga dukkan gangar jikinsu zuwa harshensa da ya kasa shiru da bayyana qauna, suka hadu suka gigita Binta shi da salon nasa har da qyar ma take qwato numfashin da take shaqa, ta dinga jin dama ya karbe ta numfashin yayi mata.
Qiyayya ta manta tsab, sabani ta manta, son da yake wa Nabila ma ta manta, komai na aibu game da shi ta manta, da alama ita kanta neman manta kanta ta ke, babu komai a kwanyarta sai Mujahid da matsayinsa a yau.
Komai kamar mafarki a wajen Mujahid yayin da ita mafarkin ma bata tunawa, sai da ko wacce mai aukuwa ta auku sannan ta ji tamkar an kai ta wata zinariyar duniya an dawo da ita, sai kawai zuciyarta da gangar jikinta suka dawo suka mallaki kansu, nan da nan suka koma kan doka da oda.
Wani dan banzan kuka ya qwace mata, wai ko tana so ko tana qi dai Mujahid ya mayar da ita matarsa? Ya tashi daga wanta ko kuma wanda take ta cika bakin har ta bar gidansa a suna zata dinga amsa sunan matarsa, wannan alqwarin nata ya tashi, wannan mafarkin nata ya zama qarya?
Tana ta tirqar kuka Mujahid na jin ta, ci kanki bai ce mata ba, shi bai san da me zai ji ba, da farin ciki da ya cika zuciyarsa zai ji ko da rarrashinta, ko kuma da murnar ba ta shiga tarkon Yaks ba? Wadancan ne muhimmai ne, kukanta ba komai ba ne sai abinda zai qara masa matsayi, ya bata damar tunani mai kyau ya kuma bata damar nadama sannan ya share mata zuciya.
Ta yi kukanta ya ishe ta, ta sami sararai a zuciyarta, amma ta ji qullacin tana kuka bai rarrashe ta ba, sai lokacin da ta tsagaita kuka ne sannan ya sami damar cillo mata baqar Magana.
“Yanzu mun zama daya ko? Zamu rayu tare tsawon lokacin da ubangiji ya hukunto mana, in kuma ciwo ya kashe mu na san da qyar mutuwarmu zata sami tazara, zaki fara tafiya ni na bi bayanki ko kuma ni na fara tafiya ki bi bayana, fatana kenan mu hadu a aljanna Binta.”
Ta yi dif! Da bakinta tamkar an datse mata harshe, sai yanzu ta koma kan hayyacin wancan qullin ciwon nata, wannan tattauran man din nata mai taurin hali yayi fatali da komai, ya bar ta da batawa kanta lokaci.
Ya juyo da fuskarta sosai suka fuskanci juna yana zagaye fuskar da yatsansa yana faman yi mata murmushi, ta runtse idonta tana neman ina ma ta bude ta ga cewa mafarki take, wai ita ce a wannan yanayin da Mujahid?
Bai sake tanka mata ba, bai kuma damu da sai ta sake bude idonta ba a haka yake kalle fuskarta tana qara samun nasarar sace dubun dubatar qaunarsa.
Amma maimakon ya fada mata kalaman da zasu qara mata nutsuwa ko su fallasa mata asirin zuciyarsa sai ya kuma kunna ta,
“Wai me yasa ba zaki bude ido ki kalle ni sosai ba, kunyata kike ji, ni ne fa me ye a ni da zaki ji kunya, ko kuwa mamaki kike?”
Ta wantsalar da bargo a guje ta nufi Toilet tana kuka, ya bita da kallo yana dariya.
Ya sha jiran ta fito daga toilet don ya shiga, amma ta bawa minti talatin baya babu ko motsinta, dayake ya san kwanan zancen kawai sai ya tashi ya canja Bandaki yayi sabgarsa, sannan qarfe biyun dare ya zauna a falo yana juya al’amura cikin ransa, ta ina zai fara kuma a ina zai sauka? Wannan Bos din dai ya kashe shi, babu ciwon qanjamau babu wanda ya taba shiga gonarsa sannan Binta ta fara samuwa. Ragowar matsala yanzu ita ce yadda zai sama wa Nabila mafita ya raba ta da auren wancan Fasiqin yaron. Ya kasa tuno komai saboda haka ya cigaba da sabunta damuwarsa har dab da asubahin ranar. A nan ya qarasa kwana.
Binta ta fito bandaki ba ta ga Mujahid ba, nan take baqin cikinta ya qara qaruwa, irin wannan riqon ne ba ta so, shi yake qara mata tsana da fargabar auren Mujahid , gashi yana neman zame mata dole, dubi dai ya gama jin dadinsa ya watsa ta kwandon shara ya fice abinsa, ba ruwansa da biyowa ta kanta ko da dan rarrashi ta samu. Wannan ya qara mata kuka, ta ji ko ina a zuciyarta yana tsukewa yana hango zabar mutuwa sama da rayuwa, kafin mutuwar kuma lallai zata gujewa sake faruwar wani abu kamar haka tsakaninta da Mujahid a nan gaba.
Sai lokacin sallar asuba ya shiga da zummar tashinta ta yi sallah, har lokacin idonta biyu zuciyarta na tafasa.
Muryarsa babu yabo babu fallasa a gaggauce ya shiga kiranta,
“Binta tashi ki yi sallah, kin ma yi wanka kuwa?”
Ta qanqame jikinta hawaye na wanke mata filo, wannan sakaryar mu’amalar irinta qauye ba ta son ta, ta zargi samunta a Mujahid tun farko kuma yana daya daga cikin abinda ya qara mata qinsa, to ga shi tun yau da bai gama kama sonta a hannu ba, gangar jikinta kawai ya kama ya cigaba da gwada mata irinta.
Sauri yake saboda an tayar da sallah, don haka da ta yi masa banza sai ya sa kai ya wuce abinsa.
Ya dawo masallaci da wata sabuwar fuska a wajenta, ya dinga kula da ita yana kula da duk wani motsinta, daga dawowarsa zuwa su shirya domin fita aiki ba zata iya qirga sau nawa ya maimaita mata kalaman qauna ba, tamkar ma su ne numfashinsa.
Wannan ya dan ba ta nutsuwa ta rage cin magani ta kuma rage hawaye, sai dai har wannan lokacin bai ji furucinta ko qanqani ba.
Tana shirin fita daga motarsa bayan ya kai ta wajen aiki yayi saurin riqo hannunta, ta juyo ta dube shi da kallon tuhuma fuska babu walwala.
Ya ja fasali sosai sannan ya sauke numfashi ya dube ta da kyau.
“Wani assigment zan ba ki don Allah”.
Ta cigaba da yi masa kallon rashin fahimta.
Ya cigaba da magana a qasaice,
“Ba wani aiki ne babba da zai sha aikin gabanki ba, ki kwantar da hankalinki, tunani ne kawai zaki yi a zuci babu wanda zai san ki na yi”
a yi shiru har sai da ta gaji da jiran cewarsa ta tanka da dasasshiyar muryarta,
“Ina jin ka.”
Yayi fuska ya ce,
aske ba kya sona Binta?”
Ta yi wura-wura a firgice, ta kasa magana, da ta ce bata sonsa ba wani abu ne mai wuya ba, yanzu kuma ta san abinda yake son ji kenan sai ta ji ta kasa fada, ba don ta fara jin sonsa ba sai dan bisa abinda ya faru jiya sai ta ji tana kunyar fada.
Ta yi qasa da kai rai a bace ta kasa magana.
Bai yi tsammanin dama zata amsa ba, don haka ya sake cigaba da magana,
“Ina wani zargi”
Ya sake shiru tamkar yana ja mata rai, kuma hakan ta zarga saboda haka ta cigaba da jin tamkar akan qaya take.
Ya sha sharafin yangarsa sannan ya cigaba,
“Ina zargin akwai qwayar sona a cikin zuciyarki, kawai ba ki bata kulawar da ta kamata ba shiyasa ba ki san ki na yi ba”
Ya sake shiru, ita kuma ta sabunta jin haushi da jin kunya, ko ma menene ita ta ba da kanta da ya zo da buqata ta qi bijirewa.
Kamar ya san abinda ta ke rayawa, sai yayi magana tamkar yana amsa mata ko kuma yana mata raddi,
“Ba ke ce da zuciyarki ba, ba ke ce da gangar jikinki ba bare in na zo da buqata ki bijire, amma ko yaya so da qi suna nuna kansu in an kasance tare.”
Ta tsuke ido tana rakito qarfin hali saboda jin kamar yana son ci mata fuska,
“In dai abinda nake ji a Qirjina na bana son zama da akai a matsayin miji ba qi ba ne, to gaskiya nima ban san kaina ba.”
Tana direwa ya amsa cikin murmushi da tausasa harshe,
“Haka kika saba ganin auren qi, haka kika saba ganin amaryar bata taba daka yaji ba, haka kika saba gabin auren qi amarya da ango a daren farko salin alin tamkar wani auren soyayya, duk tambayarki nake haka kika saba gani?”
Kawai sai ta balle murfin motar ta fitar da rabin jikinta waje tana jiran ya sakar mata hannu ta fice ta bar masa motarsa.
Ya kai hannunta lebensa ya sumbata cikin gwaninta sannan ya saki hannun yana cewa,
“Ki je wunin yau aikin da na ba ki shi ne, ki laluba zuciyarki ki ji, in akwai guntun sona ko jariri ne don Allah in mun hadu ki fada min, ni na san yadda zan reni abina ya girma…”
Ta fice daga motar da sauri.
Shi ma da sauri ya fito daga motar yana kallota ta saman motar, cikin nishadi ya ce,
“Ina sonki, zan cigaba da sonki ko yaushe.”
Har hardewa take tana sauri saboda yadda take jin ta muzanta da jin kunya. Ko waiwaye ba ta sake yi ba ta shige da sauri, sannan shi kuma ya koma mota yana jin nishadi duk da Nabila ba ta bar filin qirjinsa babu damuwarta ba.
*****
A ranar qarfe goma na safiya tuni magabatan Yaks sun dawo daga kai wa Nabila kudin aure har ma sun ji cewa nan da kwana hudu za’a daura auren tare da yar’uwarta Sadiya, sai dai su suna iya daga bikinsu tunda ba su shirya ba.
Momi da Binta ne kawai ke farin ciki Nabila ta auri yaks, Momi don ta bincika ta gane Yaks qwararren dan duniya ne, Binta kuma tana murnar Nabila zata yi wa Mujahid nisa, don haka su kadai suke farin ciki sai shi Yaks din da yake jin kamar ya zo duniya ne don yayi ta nasara akan mata.