Tagumi Alhaji ya zuba hannu biyu yana kallon likitan Binta da ya kira shi ya tare shi da daddadan labarin cewa kuskuren gwaji aka yi Binta ba ta da komai, ya gama wannan murnar kuma kawai sai gashi likitan ya kutso da wata maganar daban ita ma ta tashin hankali.
Tiryan tiryan likita ya ja shi dakin da ya kwantar da Saratu, yarinya mai tsohon cikin da Yaks ya kawo a cire mata ciki, ana cikin maganar zubarwar ne kuma aka yi masa waya ya fita a sukwane, kuma daga ranar ba’a sake jin sa ba yau kwana biyu kenan. Ya qi daukan waya ko kuma in ya dauka ya ji su ne sai ya kashe wayar.
Suna shiga Alhaji ya fara yi masa bayani, tare da shaida masa ai bayan tafiyar Yaks sun dakatar da shirin zubarwar suna jiransa ya dawo kafin ayi aikin, cikin wadannan sa’o’in ne kuma Saratun ta haihu, ta haifi ‘ya mace.
Alhaji yayi saqare yana kallon Saratu wadda komai nata ke bayyana damuwa da tsanani tashin hankali, a gefe kuma ga jaririyarta kwance kan gado cikin qoshin lafiya tana kwashar-kwashar.
Da kyar Alhaji ya kalato yawun da ya ba shi damar furuci,
“Ikon Allah, dan kuka mai ja wa iyaye da na kusa jifa, in ban da haka ina ni ina a titsiye ni ana tuhumata da laifin da ba ni na yi ba wani ne?”
Likita ya dage yana yi masa bayani don ya fahimci kamar ba cikin hayyacinsa ya ke ba,
“Ba wannan ne dalilin kawo maka maganar ba, saboda ya qi ba da hadin kai ne, sannan yarinyar na cikin wani hali da in an yi sake komai zai iya faruwa da ita ko ba yarinyar, in an sanadin rai me za’a gayawa Allah…”
Alhaji ya tare shi a fusace,
“Lokacin da ya kawo ta ka cire mata cikin, ‘yartsana ce a cikin zaka cire mata ba mai rai ba”
Likita ya sake zagewa da rarrashi,
“In mai laifi ya janye laifi fahimtarsa da yabonsa yakamata a yi Alhaji, ka taimaka ka shiga maganar nan zaka sami lada.”
Alhaji ya dinga kallon Saratu cikin kaico da godewa ubangiji ba diyarsa ko kuma wata makusanciyarsa ba ce ta yi wannan aikin, ya tausayawa iyayenta, ya tausaya mata ita ma kanta, don ya ji a ransa ciwo fiye da lokacin da aka ce ‘yarsa Binta na tare da qanjamau, yadda ya iya binne matsalarsa daga shi sai wanda ya so ya ji, amma in shege ‘yarsa ta je ta kawo ko yana so ko yana qi sai duniya ta kalle shi da aibu.
Bayan doguwar muhawara Alhaji ya yarda ya shiga maganar, inda a nan take yayi wa Mahaifin Yaks waya ya gayyato shi, Kafin ya zo shi kuma ya bar asibitin.
Da Hajiya ta sami labarin sai da ta yi kuka, ba don kowa ba sai don Nabila da take ganin ko wanne irin juyi za’a yi ba ta cancanci auren mutum irin Yaks ba, kuma qila daga shigarta gidan a kai mata shegiyar ‘ya ta riqe.
Sai d ai labarin cewa Binta ba ta da Qanjamau ne bai gamshe ta ba, ta ji a ranta kawai wani makirci Mujahid ya je ya shirya da me asibitin duk suka ninke su Baibai.
Sai dai ba ta nuna wa Alhaji cewa ba ta yarda ba, haka ta taya shi suka yi ta kakacin murnar wannan, su na kuma jimamin abinda ya faru na su Yaks.
Bayan fitarsa ta dami kanta da tunani, neman hanyar yaqini kawai ta ke, wanda zai sanya hankalinta kwanciya da garantin Binta fa lafiyarta qalau.
Tana cikin shawagin tunaninta sai ta tuno da yadda aka sha qwarbai da Mujahid game da darun da yayi wa Yaks akan kai Binta wannan asibiti, dole cikin biyu a sami daya, ko dai Mujahid ne ke da gaskiya Yaks ne ya qulla masa qaharu tunda ba sa jituwa aka jonawa Binta ciwo, ko kuma da gaske ne Binta na da ciwo Mujhadi ke tsoron bincike ya nuna shi, shi ne yake nade tabarmar kunyarsa da hauka.
Cikin siyasa da rarrashi ta kira Ummi qanwar Mujahid tana bincikenta.
Ummi ba ta da ko wacce irin amsa game da ciwon Binta amma da aka hada ta da Allah kan ta fadi abinda ta sani wanda ya janyo rashin jituwa tsakanin Mujahid da Yaks sai kawai ta runtse ido ta sanar da Hajiya iyakar gaskiya da Mujahid ya sanar da ita dangane da shirin da Binta ta yi da Yaks kawai don ta ci fuskar Mujahid.
Babu shiri Hajiya ta yi dabarar sallamar Ummi ganin Allura ta tono mata garma, tana kuka shabe-shabe da hawaye tana hana kanta ambaton mummunar kalma a kan Binta don kar ta fi haka lalacewa.
Duk dangi gani ake Yaks ne kangararre ashe yana da ‘yar uwa Binta ba a sani ba? Ta fara tsoron Allah ya sa ma ba a wajen Yaks din ta kwashi Qanjamau din ba don ita ko wuqa za a aza mata a wuya ba zata taba yarda da cewa game ne Binta da Yaks suka yi dan su hana Mujahid son ta ba, qila sun yi watsewarsu.
Ta dinga godewa Allah da ta dinga shanye kan fushinta, ba ta yi abinda Mujahid zai gane shi ta laqa wa laifi ba.
*****
Kwana biyu da suka biyo baya komai ya qara kwadancewa, ran kowa babu dadi tun daga kan Binta da Mahaifiyarta ta kira ta a boye ta yi mata wankin babban mayafi, ta saba mata irin yadda ba ta taba ganin ta yi wa kowa a duniya ba.
Binta ba ta san mahaifiyarta na da fushi ba sai ranar, sai da ta gwammace dama tun farko kwantawa ta yi Mujahid ya dinga bi ta kanta qarewar qasqanci akan ta yi abinda zata gamu da fushin mahaifiyarta irin haka, ta tabbatar ba don Mahaifiyarta na da Ilmi ba a irin wannan fushi zata tsine mata.
Binta kuka kawai take babu qaqqautawa ta kasa cewa komai, duk da ma Hajiya ba ta ba ta damar cewar ba.
Har sai lokacin da ta ce mata,
“Zan shawo kan Alhaji ya kai ku gwaji daga ke har Mujahid da kansa, ko za’a dace a tarar Mujahid bai gogi ciwonki ba, sai ya sake ki kawai ki zo ki auri Yaks dan uwanki mai ciwon…”
Cikin kuka da girgiza kai Binta ta ce,
“Hajiya maganar fa ba ta yi zafin haka ba, wallahi babu abinda ya taba faruwa tsakanina da Yaks, haba Hajiya kar ki cigaba da yi min mummunan zato irin haka mana, sai ka ce a garin arna, Yaks din Hajiya?”
Cikin zafin rai Hajiya ta ce,
“To meye marabar dambe da fada da abinda kika yi da wanda zai sa ki kwashi qanjamau din? In ba rami me ya kawo rami da za’a ce kina da qanjamau a dawo kuma a fasa? Ban da ma tsabar samun waje, wacece ke da yaro zai dinga yi miki irin wannan son kina zabar dan iska kina barinsa shi kuma bai fasa sonki ba, kuma bai fasa kokawar rufa miki asiri? Wallahi da mun san haka ne tun farko matsa masa muka yi ya auri Nabilan ya bar ki, kin san dai ta fi ki komai da komai.”
Da dai Binta ta ga babu sarki sai Allah kawai sai ta zauna cikin kuka ta bawa Hajiya labarin komai tun daga farko har qarshe, ba ta boye mata komai ba hatta dangantakar da ke tsakanin Nabila da Mujahid, da iyakar tata fahimtar. Qarshe ta rantse mata da cewa,
“Ba ni da wani dalili Hajiya, ni kawai ba na son Mujahid ne, abu na biyu kuma na ji tsoron Nabila ta zarge ni da cin amanarta alhalin ni na cusa mata sonsa ta dalilin labarin qaryar yana sonta, ina son ta gamsu ba da son raina Mujahid ya so ni ba”.
Hajiya dai gabadaya kanta ya kwance har ba ta iya lissafin komai, sai qofa ma ta nuna wa Binta ta ce mata,
“Tashi ki tafi gida, ban san ta yadda zan yi nazarin wannan hatsabibancin naki ba”.
Yanayin Hajiya bai nuna tana son jayayya ba, don haka Binta ta miqe tana ta faman kuka tana bata haquri tare da neman gafararta, Hajiya dai ba ta sake tanka mata ba, don ji take kamar ta dora hannu a ka ta rafsa ihu, ita ba ta san kangarar ‘yarta Binta da kowa ke wa kallon Saliha ya kai haka ba.
Wutsiya a zage Binta ta sa kai ta tafi gidanta hankali a tashe, ba ta yi tsammanin in liqinta ya tashi ballewa zai hada mata jini da majina haka ba.
Zuwa wannan lokacin an kai jaririyar Saratu gidansu Yaks an dire, Saratu karatu ya kawo ta bauci, har ta yi cikinta ta haife iyayenta da ke Jigawa ba su sani ba, lokacin da ta je musu hutu cikin bai girma ba, hasalima ita kanta ba ta san da shi ba, niyyarta ta haifi jaririn ta jefar aka sami akasin da mahaifanta suka san halin da take ciki, suka kuma ba ta sharadin in dai ta kashe ‘yar nan sai dai ta nemi wasu iyayen ba su ba, lallai ta nemo uban cikin ta ba shi dansa. Don haka yanzu ma Saratu na gidansu Yaks bayan sallamarta daga asibiti.
An yi ta kakkare kar Nabila ta san halin da ake ciki, amma aikin gama ya gama, ta sani ta hanyar amininta a tasa fuskar, kuma mosoyinta a tata fuskar.
Takanas ya je har gida bayan ya kasa shawo kan fushinsa ya sanar da ita, amma wai ya roqe ta kar ta tashi hankali, wai ya fada mata ne don kar ta ji zance katsahan daga wajen wani, ko kuma a lokacin da bai kamata ba, ya kuma ce wai kar ta bari a ji a gida.
Gaskiyar magana kuma tarko ya dana, don ya tabbar babu budurwar kirkin da zata ji wannan danyen zancen sannan a ce wai ta share kar ta damu, kuma ta qi damuwar.
Kuka Nabila ta dinga yi tana kallon Mujahid kawai, ba ta ji ko wacce irin asara ba na daga abinda ya faru face asarar masoyin kirki da ta yi, shi take so shi ya cancanta kuma shi ta rasa.
Duk kukanta ko kadan ba akan Yaks ba ne a kansa ne har lokacin da yayi mata sallama ya tafi, sannan ta dawo kan doka da oda ta koma kan tunani da yadda zata iya rayuwar bauta da wannan mutumin mara kyan hali kuma wanda ba ta so.
Da kadan da kadan damuwa ta yi wa Nabila yawa, a ranar sai a gadon asibiti ta kwana cikin mawuyacin hali.
Qarfe goma daidai na safiya mahaifin Nabila ya sami Alhajin Binta hankali a tashe da maganar halin da Nabila ta shiga, a cikin sambatunta ta bayar da labarin abinda ya faru da Yaks. Mahaifin Nabila ya qarqare maganarsa da cewa,
“Amma dai Alhaji ka san yaron nan ba shi da hali ba ka kwabe ni ba lokacin da na zo maka da maganarsa a waya? Ai Alhaji matsuwata da aurar da Nabila wallahi ba ta kai haka ba, tunda gashi ina neman rasa ta ma gabadaya”
Alhaji wanda dama tun daren jiya da matarsa ta bashi labarin Binta da Yaks yake cikin wani mawuyacin hali na damuwa da saqa hanyoyin shiga da fita. Yanzu sai ya rasa da wacce fuskar zai karbi mahaifin Nabila, abu daya dai ya tantance hankalinsa ya qara tashi da jin cewa bisa wannan labarin Nabila babu lafiya har ma tana kwance.
Ya dinga jinjinawa yana nemar mata sauqi kafin lokaci daya ya fito da hukuncin da ya kwana yana saqawa,
“Alhaji ina neman wata alfarma saboda Allah”
Kallonsa kawai mahaifin Nabila yayi cikin damuwa da rashin fahimta, shi ya zo da damuwa, in da alfarma shi yakamata ya nema ba wai a nemi tasa ba… don haka ya kasa haquri sai da ya tanka,
“Zan fada maka gaskiya ba zan iya aurawa danka Nabila ba”
Kai tsaye Alhaji ya tare shi cikin tausasawa,
“Dana wanne ne ba zaka iya aurawa ba? dana Yaks ko kuma dukkan “ya’yana?”
Kafin yayi magana Alhaji ya sake tare shi,
“Idan Yaks ne kawai ba zaka bawa ba, ka ba ni dama na canja wani.”
Mahaifin Nabila yayi zuru yana kallonta cikin rashi fahimta, Alhaji bai yi qasa a gwiwa ba ya cigaba,
“Ka canja mata da mutumin kirki Mujahid, na rantse maka da Allah zai riqe maka ita amana In sha Allah”
Tuni mahaifin Nabila ya zaro ido, don ya san waye Mujahid, a matsayinsa na da kuma surukin Alhaji, muryarsa na rawa ya ce,
“Mujahid mijin Binta wai?”
Cikin qarfin gwiwa Alhaji ya ce,
“Shi fa, na san dai ko kai zaka iya shaidar cewa mutumin kirki ne, a matsayin da ya dauki Nabila na qanwarsa shi wanta, na san zaka iya kula da salon kulawarsa, bare kuma idan ta zama matarsa.”
Abban Nabila ya nisa ya sauke numfashi cikin alhini,
“Ba wai tantamar halinsa nake ba, kawai dai ta ina ka taba ganin an yi haka ? Binta fa yake aure, haka ne?”
Dariyar Qarfin hali kawai Alhaji ya ke,
“Fate kawai ake tonawa abokina ban da ciki, ba abubuwan da yakamata mu mai da hankali kansu yanzu ba kenan, a’a duban shirinmu na alkhairi, da kuma ceto yaranmu daga shiga hannun da bai kamata ba… kar ka damu da duba wata dangantaka in dai ba ta shiga haqqin ubangiji ba, ka taimake ni ka karbi tayina, a daura auren nan da Mujahid gobe”
Da mamaki Mahaifin Nabila yake ta kallon Alhaji.