Ya maze ya tunkari dakin amarya Binta, sai dai bai bar fuskarsa da alamar wasa ko damar karbar raini ba.
Ya sameta kamar da rana tana kance a gado, sabanin dazu yanzu ba kuka take ba, kuma lullube take da bargo, da alamu tana fama da zazzabi.
Yana ganin haka yayi saurin ficewa daga dakin ba tare da ya ce mata komai ba, ya je ya laluba Kitchen babu abinci, ya jona Kettle ya fice ya siyo Kaji ya dawo, lokacin ruwansa ya tafasa ya juye a flask, haka ma naman ya juye a plate ya kwasa duk ya kai. . .