Skip to content
Part 48 of 59 in the Series Rigar Siliki by Maimuna Idris Sani Beli

Da alamar Binta ta qullaci qara tsamama dangantaka tsakaninta da Mujahid, yadda a daren wannan ranar ma barambaram suka yi da ya shigo mata daki, ta ce in ba zai fita ba sai dai ita ta fita.

Bai nuna fishi ba kamar yadda ya saba, ya dan gaggasa mata baqar magana ya haye benensa ya kwanta.

Washegarin ranar ko bi ta kansa ba ta yi ba ta shirya tayi ficewarta aiki, sai da ya sakko qasa ya ga qofarta a kulle, ya ji damuwa sosai, yadda bai daure ba har sai da ya buga mata waya ya tambaye ta,

“Kina ina ne?”.

Cikin gadara ta amsa,

“Ina wajen aiki mana wani abu ne?”

Ya cije damuwarsa yana tattara basirar da zai ba ta haushi,

“Gaskiya kin yi kyan kai da tun yanzu kika fara koyar kai kanki wajen aiki, In Nabila ta zo akwai daukar haqqi ace kina buga mata qofa da sanyin safiya kina dauke mata miji”.

Da qyar ta qarasa sauraronsa saboda quncin da ta ji ya ishi qirjinta, nan da nan ta kashe wayar ta yasar.

Shi kuma ya shiga dariyar jin dadin ya ba ta haushi kamar yadda ya so.

Ita haka take, ta san ta shiga ko wacce iri ce amma ba ta san ta fita ba, ta iya shiryawa mutum kayan haushi amma ba ta san ta inda zata danne fishi idan shi ya shiryo mata ba.

Yana ta hasashen wasu haushin da zai tura mata ya bar gidan.

Da yamma bayan ta tashi qarfe shidda ta dinga azamar tafiya don ma kar ya zo ya dauke ta, har ta tafin ba ta ga qeyarsa ba, a hanya ta dinga qyashin ma kar ta koma gidansa, sai dai ba ta da wajen zuwa yanzu, gidansu haushinsu take ji su ma suna jin nata, don tana da yaqinin da hadin kansu ya auri Nabila, don haka ne ma babu wanda ta yi wa waya, duk wanda kuma yayi gangancin yi mata in dai mazaunin gidan ne tana sane take kife masa kira.

Gida na biyu da take zuwa in ta so turawa Mujahid haushi gidansu Yaks ne, shi ma yanzu ya fi qarfinta, tunda Yaks yake zargin da hadin kanta aka yi masa fashin soyayya.

Babu gaira babu dalili ta rakici shiga super market siyayya don dai duk ta bata lokaci kafin ta isa gida.

Sai bayan magariba ta isa, amma abinda ya daki qirjin ta shi ne, an yi fata fata da gidan ana fentin saman benen, wanda ta haqiqance wajen Nabila ake gyarawa,

Ta ji zuciyarta na wani irin suya, musamman da ta ga Mujahid ya dago mata hannu daga sama yana mata maraba, sannan ya mayar da hankalinsa kan masu fentinsa.

Cikin quncin zuciya ta ja qafa ta bude dakinta, kai tsaye kuma ta wuce Toilet don dauro alwala, ta haqiqance idan ba ta kusantar Allah lokacin da Mujahid ke quga mata wannan rashin mutuncin babu dalilin da zai hana wata ran a wayi gari da gawarta bayan zuciyarta ta buga an huta.

Amma dayake maye ne kamar yadda ta raya a ranta, tana idar da sallar magariba ya shigo ya same ta, ba don komai ba sai don ya qarawa zuciyata duhu.

Da fara’asa ya ce mata,

“Baiwar Allah don Allah ki yafe min, gabadaya wannan aikin ne ya dauke min hankali ya sa na manta da ke, sai kika yi kyan kai ma kika taho abinki”.

Bai bata damar ta ce komai ba ya wuce  dinning table ya dako fulas din shayi ya zo ya wuce ta ya fice.

Babu shiri ta janyo carbi ta fara ja tana ambaton Allah, daga bisani kuma kawai sai ta fashe da kuka.

Ba ta sake sanya shi a idonta ba sai washegari bayan magariba da ya shiga mata da wani kayan turin haushin,

Girma girma ya tusar baqo kamar abin arziki ya sami guri ya zauna sannan ya dauki ruwan da ke kan tebur ya tsiyaya ya sha hankali kwance ya ce mata,

“Don Allah alfarma na zo nema”.

Kallonsa kawai ta yi tashin hankalinta na raguwa saboda ta zaci wata baqar maganar ya zo mata da ita, ashe alfarma ya zo nema, ita ya zo ya ji tata baqar maganar, don kama shi sosai ta qi tare shi,

“Ina jin ka”.

Ya sake gyara zama,

“Ke kuwa zaki iya hado kayan lefe? Na ga kwalliya ba ta dame ki ba da qyar zaki iya sanin abinda ya dace”

Haushinta ya dawo sabo, ta tsare shi da ido ta ce,

“Wannan maganar ce alfarmar kenan?”.

Yayi fuska,

“A’a, wai da ke zan bawa ki siyo don dai na zama me adalci, saboda naki ita Nabilan na bawa ta siyo miki, to kuma gaskiya ina fargabar ki yo min shirme…”.

Bai gama rufe baki ba ta miqe a fusace ta shige cikin daki, ya bi da kallon yana hasashen abinda zata yi, can jimawa sai ga ta ta fara turo akwatunan lefenta, sai da ta kawo su daya bayan daya sannan ta zauna cikin cin magani ta ce,

“Tun tuni na fahimci komai cikin kayan zabinta ne, shaidar dama ita ka siyowa, to ko tsinken allura ban taba tabawa ba a ciki, babu damuwa kana iya sake akwatuna ka juye mata kayan ciki, ni kuma na koma daura ganye ma sabda tsabar rashin iya kwalliya, babu abinda ya shafe ka”.

Ya san haushi ta ke son tura masa, sai ya basar ya shiga janyo akwatunan yana budewa yana ce mata,

“A haba ke kuwa kar ki damu mana, abin ai ba na fada ba ne haka, ko dan barasoso zaki koma sawa ai ni a haka nake sonki”.

Suka yi shiru sai hucinta da qarar kayayyakin da yake budewa, bai dire da dauke komai ba sai Undies dinta ya shiga daga mata, fuskarsa a sake yana ce mata,

“Ai ba ki san inda gizo ke saqar ba, kin so kyauta amma da qyar zata sami shiga, wadannan qananun abubuwan ai ba zasu yi mata ba”.

Dole Binta ta yi shiru, don qarshen matakin da zata dauka bisa wannan cin fuskar da yayi mata shi ne ta rusa masa ashar, to kuma tana tsoron ya rada mata suna ‘yardaba, don ta san zai runa har Nabila ta zo ta ji yana fada, sai kawai ta yi shiru tana kallonsa. Ya gama sharrace-sharracensa sannan ya miqe yana cewa,

“Na gode da kyauta Allah qara danqon qauna, in ana samun mata irinki masu yi wa mazajensu tallafi lokacin da suka yi aure ai da duniya ta zauna lafiya, ki adana min su zan canjo jakankuna na kwashi atamfofi da lesuna, wadanna qananan abubuwan kuma sun mata kadan, wasu kayan a ciki kuma yanzu tsofaffin yayi ne dole ana buqatar sababbin zubi.”

Ya sake yin fuska ya fice ya bar mata daki ba tare da ya karanta tashin hankalin fuskarta ba.

Yau takaicinta ya fi qarfin kuka face mutuwar zaune, ko yatsanta ta nemi ta daga shi ta kasa, sai bin wajen da ya bace da kallo take.

Babu wani sauyi a kwanakin da suka biyo baya, duk inda tura haushi da tsokana take, duk yadda ta so ta nesanta kanta da Mujahid sai ya rarumo ya iske ta har gadon baccinta ya sauke mata, wannan dalilin ya sa ta fara hasashen dama can Nabila yake so ba ita ba, kawai makirci ne na Namiji, shi kadai ya san dalilin da ya sa ya auro ta ya garqame a kurkukunsa.

Wannan hasashen ma na ba ita yake so ba Nabila yake so, ta rasa dalili ba qaramin qona mata rai yake ba, a da yadda take jin qiyayyarsa da ta zaci cewa abu mafi sanya farin ciki da zai burge ta shi ne a ce Mujahid ba ya sonta, yadda sakinta ba zai yi masa wahala ba, amma abin mamaki sai takunsa na yanzu ke wahalar da zuciyarta, shiga dari fita dari in dai zai gan ta sai yayi mata maganar Nabila, sai ya nuna yadda Nabila ke da muhimmanci a wajensa.

Wannan dalilin ya sanya ta qara jin haushin Nabila, kwata-kwata ma ta toshe lambarta a wayarta.

Ranar da ya rage kwana uku Nabila ta tare, ta dawo aiki da dare ta lura da cewa Mujahid ya bude akwatunan da ta bar su nan zube a falo tun daga ranar da ta debo masa su ta ce ya kwashe su ya canja jaka ya kai wa Nabila.

Cikin fargaba da zumudi ta shiga bincike su, sai ta tarar da cewa ya kwashe duk atamfofi da lesuna da shaddodin ciki, da su Material, abubuwan da ya rage duk qananan kaya ne da kayan shafa.

In ranta yayi dubu ya baci.

“Ashe wannan qulumin mutumin da gaske yake?”

Abinda ta dinga maimaitawa kenan a fili hankali a tashe, da ba ta taba damuwa da kayan ba, ji take har ta mutu ma ba zata sa su ba don kar yayi farin ciki, amma tunda ta yi masa gatsen ya kai wa Nabila ya ce mata zai karbi atamfofi sai ta ji a ranta shi kansa idan ya karbi kayan zai ji kamar ya karbi aurensa, don haka ta dinga raya cewa kawai fada yake ba dauka zai yi ba, ashe da gaske yake zai yashe lefen da yayi mata ya kai wa wata daban. Hakan da yayi babu abinda ya tuna mata sai babansa, su babu ruwansu da kyautatawa mata ko gudun zaluntarsu, kawai buqatarsu ta tara matan ce.

Yau dai kam ba zata yarda ba, zai shigo su yi ta ta qare.

Amma me? Ranar sai sha dayan dare ma ya shigo gida, sannan ta gama cika da batsewarta, daga shi har Nabilan sun sha tsinuwa.

Tunda aka yi fentin sama ya daina kwana a saman, da tsiya da arzuqi wajenta dai yake zuwa ya kwana.

Ya shigo falon salin alin yana sanye da qananan kaya masu duhun ruwa, fuskarsa ta yi fari tasa da dantsen hannunsa ma haka, fuskarsa da annuri don haka yayi matuqar kyau, in ba idonta ke gizo ba ma har qiba ta ga yayi.

Ya daga mata hannu tamkar irin ya zo wuce maqotansa zaune yana gaishe su,

“Hi! Madam barka da gida”.

Babu jiran amsa ya doshi dakin da yake kwana, duk don ya ba ta haushi, shi yana iya gane rikici idan ta rarumo.

Hakan da yayi mata ne ya qara mata haushi, ta kasa magana har ya shige.

<< Rigar Siliki 47Rigar Siliki 49 >>

1 thought on “Rigar Siliki 48”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×