Shi kuma da yaga bai sami abinda yake so ba kawai sai ya canja kaya ya sake fitowa ya dawo falon ya zauna a kujerar da ke fuskantarta ya dauki filon kujera ya rungume.
“Nabila ta ce a gaishe ki.”
Ta san in ta sauke fishinta a wannan gabar zai yi ta mata gorin don kishi ta yi, saboda haka ta tura baki ta ce,
“Ina amsawa, dama ta daina wahalar da kanta aikoka ka gaishe ni, ai ni da ita kullum cikin gaisuwa mu ke…”
Ya tare ta yana dariya,
“Allah ko? Amma ko ni yanzun nan na dauki wayar na gwada kiran sai na ga kin toshe mu, ni na kasa ganewa laifina ne ya shafi Nabila saboda kin tsaneni kika tsane ta ko kuma don ta aurar miki miji ne? zabi na qarshen nan kunya yake ba ni ni kaina ba ke ba Binta, yaya za’a yi wanda kake mugun qi, wanda ma kake jin da ana gaiyatar mala’ikan mutuwa kai zaka gaiyato shi ka nuna masa shi ya zare masa rai, kuma don kawai zai auri wata ‘yar kucilar yarinya ka hana kanka kwanciyar hankali?”
Ta daure gira,
“Allah ya sauwaqe, ni hankalina a kwance yake, sai dai in naka da nata ne a tashe ku da ba kwa iya sabgar gabanku sai kun sako ni ina can tawa sabgar…”
Ya tare ta yana dariya,
“Eh gaskiya mu mun cika kyan hali, mun san darajar zumunci mun san darajar maqotaka, mu kuma ba mu yarda da mu rayu kamar mayu ba, shi ne kawai bambancinmu da ke.”
Ta jima cikin juya haushi da qoqarin boye shi, tunda yake mata zaton komai don kishinsa take har ma yana ganin abin kunya ne.
Ganin kamar ba ta shirin sake tanka shi ya rakito wata tsokanar,
“Gobe za a kai min lefe, zaki sami halarta?”.
Ta tsuke ido,
“Ni ce ma motar da zan dau mutane in dau kaya”.
Ya hadiye dariya,
“Ai abin ba na fada ba ne”
“Na kwanciyar hankali ne”
Ta sake fada a fusace.
Yayi saurin sa hannu ya kame lebensa da zummar yayi shiru.
Ita ta cigaba da magana a fusace,
“Da alama ka fara karbe kayan aurenka, yaushe ne zan fara tsammanin za a ce na dawo da sadaki duk da kuwa an dora min idda?”
Ya maze,
“Kai haba daga gwaji, me zan dorar da zaki yi tutiyar idda? Kin san nawa aka biya min sadakinki kuwa kuwa?”.
Ta qufula,
“Ko nawa aka biya maka na zaci zasu qirgu?”.
Ya sake yin fuska,
“Qirguwa kai”.
“To ai ba zasu gagara ba.”
Ya canja fuska kamar abin kirki.
“Ko nawa za a ba ni ba zasu iya maye min gurbinki ba, kayanki kuma da na diba na zaci da yardarki na diba? Dama ba tsakaninki da Allah kika ban ba? In dai haka ne to ki daina yi min gatse, wataqila ni ban san gatse ba ne.”
Yana rufe baki sai ya tashi zai bar mata wajen, babu zato ta sha gabansa ranta a bace,
“Wallahi tallahi Mujahid ba na sonka”
Cikin shassheqar kuka.
Da farko tsayawa yayi kawai yana kallonta, yanayin kukanta na nuna sassauci take so da rarrashi, zuciyarta abinda take so kenan amma bakinta yana furta wata qaryar daban, ya san har yanzu da sauranta, don haka ko kusa ko alama bai ji zai iya taimakarta da dadin rai a yanzu ba, saboda haka tana cikin maimaita ba ta sonsa ya sa hannu ya damqe lebenta ya murde shi sosai yadda dole zata ji a jikinta, yana magana cikin yanayin zafin rai,
“Daga diban kayan lefen da ba kya so wai tayin soyayya na kawo miki ne da zaki ishe ni da raddin ba kya so na? an ji ba kya sona, kuma ba kya son kayana yanzu hayyatar da kike min ta meye?”.
Ta yi nesa sosai da shi tana qara kuka,
“Abin ya fara zuwa da duka da muzgunawa? Wallahi babu abinda zai hana ni tafiya gidanmu da safe, ni ban gaji duka a gidanmu ba…”.
Ya tare ta cikin yanayin rauni, don ya san abinda take son goranta masa,
“Ni na gada, a kanki kuma har yankar mace da wuqa zan iya, duk da ke ma qarya kike ba gyatumarki kika gada ba, ko sati ba a yi ba da mahaifinki ke yabon gyatumarki yake jera ta cikin matan da yake sa wa ran rahmar ubangiji da aljanna, ke aikin me kika yi da kika kwafo su? In zaki zage ni ki yi min gori ki fito fili ki yi, dukan mace rashin kyan hali ne, qin bin iyaye da qin bin miji har ya fi shi, sai ki zabi wanda ya fi munin hali tsakanin ke da mahaifina da kike son ki ci fuska…”.
Yana dosar daki yana qarasa maganarsa har lokacin da ya shige da ragowar kayarsa.
Tun lokacin da ya fara magana ta ga fushi a fuskarsa da zafafan maganganunsa ta ja bakinta ta bame dif! Tamkar an kashe radiyo, ba ta taba nadamar ko wanne irin furuci tsakaninta da shi ba sai a yau, ta ji tamkar ta zama ba ita ba saboda nauyi da yarda ba ta aikata daidai ba, gashi nan ita ma ta janyo wa kanta cin fuska, har yana neman ma quga ta wuta da bakinsa.
Jiki a sanyaye ta janye jiki ta fice ma daga wannan falon ta koma dayan ta qule dakin bacci ta haye gado ta shiga sana’ar kuka, wannan karon ba kukan qiyayya ko kishin an auro mata Nabila ba ne, kukan jin takaicin yadda tun da Mujahid ya shiga rayuwarta komai nata yake tarwatsewa, tana rasa kyan hali tana rasa mutane, kowa yana ganin ta fiye rashin kirki ciki har da mahaifanta da suka zabi bare suka bar ta? Mujahid bai karbi rayuwarta ba babu wanda ya gane hakan, kuma in ta cigaba da nunawa ta cigaba da haduwa da uqubobi iri-iri? Kukanta ya qi karewa ranar kwanan zaune ta yi.
Qari a kan wannan da safe sai ga Mujahid ya bullo mata da fuskar gaba tamkar farkon aurensu, haba sai hankalinta ya qara tashi da ta tabbatar shikenan ta gama barewa da ita, Nabila zata shigo gidan a sa’a ta san cewa ba a bakin komai ta ke a wajensa ba, ta sha ji a bakin masu kishiyoyi wannan ba qaramin naqasu ba ne yadda ko fada mace ta yi da miji ba ta so kishiyarta ta sani, to bare irin wannan gabar ta Mujahid.
Qiri-qiri yau ba ita ta zabi ficewa ta bar shi ba, shi ne ya ja motarsa ya fice ya bar mata gidan.
Qarfe uku ta nemi alfarma ta bar wajen aikinta ta bar shi ta koma gida tana kuka tana zuba kaya a jaka ta ficce kai tsaye ta nufi gidansu.
Allah ya sa gidan babu mutane a gidan duk an dade zuwa kai lefen Nabila, daga Hajiya sai Mahaifiyar Mujahid a gidan.
Binta ta yi sallama falon Hajiya a raunane, suna hada ido da Hajiya ta jefa mata wani banzan kallo ya sa ko sauraron gwaggo da ke amsa sallamar ba ta yi ba ta isa ga gwaggon ta fada jikinta ta shiga rusar kuka.
Gwaggo ta gigice da tambayar ba’asi, yayin da Hajiya ta kebe baki ta tsaya tana kallonsu kawai.
Tsawon lokaci da kyar gwaggo ta shawo kan Binta ta yi shiru.
Gwaggo ta dubi Hajiya ta ce,
“Yaya zaki zuba mana ido Hajiya?”…
Cikin azama Hajiya ta tare ta da cewa,
“To ya ba zan zuba muku ido ba? Ke ce kike ban tausayi da kika tsaya kike bata lokacinki wajen matar da wutar kishi ta koro”.
Gwaggo ta ce,
“A’a ba haka ba ne, da ganinta tana da matsala Hajiya, dube ta fa? Ba haka na san ta ba dubi yadda ta qare kamar me hadiyar allura”.
“Hmn”
Hajiya ta sauke nishi kawai ta cigaba da kallonsu.
Gwaggo ta mayar da hankali wajen lallaba Binta wadda rashin qwarin gwiwar yadda Hajiya ke basar da ita ya sa ta saki baki ta dinga sakin qarya da gaskiya wai duk dan ta nuna bunqasar laifin da Mujahid yayi mata.
Gwaggo ta shiga sosai, musamman magana kwashe mata lefe, sai ta shiga fada kamar ta ari baki.
Hajiya dai ta yi kasaqe duk da haka tana kallonsu. A yau Binta ta qara ba ta kunya da tabbatar mata duk abinda aka fada game da ita zata iya, ba don an san albasa na bijirewa halin ruwa ba da ta bude baki ta ce ta ji kunyar a ce ita ta yi tarbiyyar Binta, shekaru ashirin da kusan biyar amma Binta ba ta san dacewa da abinda yakamata ba.
“Kina jin mu fa Hajiya”
In ji gwaggo da ta gama fadanta.
Hajiya ta yi murmushin da Binta ce kadai ta gane daga qarqashin takaici ya taso ta ce,
“Me zan ce ne a labarin gizo da qoqi irin wannan? Kar ki manta Mujahid da Ummi da Karima da Nabila suka je siyo kayan nan, kin ga sun hado da kayanta ciki? Ai mutum in zai yi qarya ma yakamata ya tuna ta nesa da ta kusa da gida”
Ranta ya gama baci, kuma ba ta son nuna fishinta a kan Binta gaban Gwaggo wadda sam ba ta taba sani ainihin abinda ke faruwa ba. Sai ta tashi tana gama magana ta bar Binta da gwaggo.
Binta ta qara fashewa da kuka da ta fahimci ta qara wani laifin, Mujahid ya haqa mata ramin mugunta ta afka, yanayin Hajiya ya gama bayyana mizanin fishinta.
Gwaggo sai rarrashi take kamar yawunta zai bushe, qarshe ita da kanta ta yi waya ta ce in ya taso aiki ya zo tana nemansa kafin ya koma gida.
Hakan yayi wa Binta dadi, don dai ta san in ya zo qarshen maganar a ce ya dauke ta su tafi, ta fi son hakan akan wutar da ta kawo kanta, yadda Hajiya ta fusata ta san Alhaji zai fi haka don yana fushi da fushinta, kuma saboda kwanakin da yayi bai yi mata waya ba, ya sa ta tabbatar yana cikin tsananin fushi dama.
Mujahid bai kawo zuwan Binta ransa ba ko kadan, sai dirar fadan Innarsa ya ji kamar zubar ruwan sama a kwanyarsa, ta wanke shi tatas ta ce ya dawowa da Binta kayanta.
Shi dai bai musu ba bai kuma karbi laifin ba, amma a gaskiyance ya ji barewar wannan dabi’a ta Binta, shekarunta da zurfin ilminta ba su cancanci yaji da tonawa kai asiri ba ko da kuwa ba ta son mijin tunda aurenta bai qare ba.
Ya dai bige da bawa Gwaggo haquri kawai, ita kuma ta sanya Binta ta tashi ta bishi, dama abinda take so kenan, don tunda Hajiya ta qule dakinta ba ta sake sake fitowa ba, da ta yi dabarar bin ta ma sai ta tarar ta sa wa dakin muqulli.
Suna fita daga harabar gidan suka wuce ‘yan kawo lefe sun dawo, suna ta faman daga musu hannu amma Mujahid ya share kamar bai gani ba ya fice.
Sai da suka yi nisa sannan ba tare da ya dubi Binta ba ya ce,
“Na qi tsayawa ne don wataqila zasu yi tunanin su yi miki Allah ya sanya alkhairi, ke kuma ki ga kamar sun ci fuskarki, ta yiwu kuma a je maganar lefe ki kwashe musu labarin cewa naki na kwasa na kai mata, ko wanne aka yi ba za’a kyauta ba”.
Yayi magana ne cikin fuska mara walwala.
Ko daga ina wannan maganar ta fito an yi ne don a bata ran wanda aka yi wa, ko Mujahid na gasa mata baqar magana don ta ji ciwo, to tana da tabbacin wannan ita ce asalin baqar maganar da ya taba fada mata wadda ta taso daga haqiqanin birnin zuciyarsa.
Ba ta kula shi ba don dukkansu zuciyoyinsu sun fada nazari, Mujahid ya lula tunanin yadda zai kafe Binta a gida bare har ya ta sami kafar da zata fita ta dinga yi masa baranbarama irin wannan, ya qudurce a ransa wannan ne sanadin barinta aiki idan ba ta yi wasa ba.
Ita kuma tunanin yadda zata kama kanta take, tunda yanzu ba ta da ko wanne irin gata, kamar yadda ta tuna dazu, in ta cigaba da fuffuka nan gaba cewa za’a yi ita mahaukaciya ce babu wanda zai damu da duba birnin zuciyarta.
Kamar daga sama Mujahid ya ji ta jefo masa tambaya,
“Ina ka kai min kaya? An ce ba su ka kai lefenka ba”.
Tana rufe baki ya amsa fuska babu walwala,
“Siyar da su na yi na sai sababbi”.
“To madalla.”
Ta fada yayin da ta kishingida a kujerar mota cikin ajiyar zuciya da shirin sakewa kanta zuciyar.
Ch hi